Showing 312001 words to 315000 words out of 479911 words
wanda take kulawa, ko abincinsu ba ta ci.
Ta shirya tsaf cikin uniform ɗin ta, ta shirya ta fice.
Nabila ce a tsaye a gaban kotu ta nemi kotu ta bata damar gabatar da shaidun da take da su, wanda ba ta gabatar ba a kotun baya.
Kotu ta bawa Nabila dama, Nabila ta taso wata mata, matar ta zo ta tsaya a gaban kotu Nabila ta ce "Hajiya ko zamu iya sanin sunanki?"
"Sunana hajara wali"
"Wacece ke a wurin rahama?"
"Ni mahaifiyarta ce, 'ya ta ce"
"Ko zaki iya yi wa kotu bayanin meyafaru"
Mahaifiyar ramma, tayi bayani tiryan-tiryan.
"Kin san wannan?" Tayi maganar tana nuna mata dattijon.
"Eh, tare da shi muka yi ta ɗawainiyar zuwa kai rahama Asibiti"
"Shi ne ya dawo ya ɗauke ta?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba shi bane ba, wancan matashi ne"
Nabila ta ce "Yanzu ina rahama take?"
Cikin kuka ta ce "Ban sani ba, tun da ya ɗauke ta ban sake ganinta ba".
"Kafin ya zo ya ɗauketa meyafaru?"
Ta goge hawayenta ta ce "Wata mata ce ta zo ta ce mu karɓi kuɗi, a rufe maganar, na ce ban yadda ba, hakkin 'ya ta nake nema, shi ne bayan ta tafi ya zo ya ɗauke ta, bayan kwana biyu ya dawo ya ce mini na bashi kayanta, ta zama mallakinsa"
"Ko zaki iya gaya mana sunan matar?"
lauyan gwamnati, ya nemi kotu ta dakatar da Nabila, tambayoyinta na ƙoƙarin ƙetare iyaka.
Ya taso zuwa gaban majaifiyar ramma ya ce "Hajiya wanda ya zo ya tafi da itan, bayan ya tafi da ita, meyasa baki sanar da jami'an tsaro ba?"
"Na sanar da su, amma suka ce na je gida za su neme ni"
"Da basu nemeki ba kin koma?"
"Na koma har na gaji, amma babu wani cigaba"
"Sai aka neme ki aka rasa, ko sama ko ƙasa"
"Bibiyar abi mini hakkin 'ya ta da nake yi, ya sanya aka fara yi mini barazana, shiyasa na bar gidan" ya yi wa kotu godiya ya koma ya zauna.
Nabila ta sake komawa gaban kotu ta kalli dattijon nan ta ce "Baba a kotun baya, ka amsa kai ne ka yi wa rahama fyaɗe, shin da gaske kai ne ka yi mata fyaɗe?"
Ya girgiza kai ya ce "Cewa aka yi idan na ce bani bane ba, abun da ya samu rahama zai samu 'ya'yana".
"Meyafaru ranar da abun ya faru?"
"A ranar aka ɗaukko ramma daga ƙauye, akwai ƙanin matar gidan ya zo a buge, ya tambayeni matar gidan sun dawo, na ce masa a'a, amma ya shiga, bayan wani lokaci ya fito ya ɗauki motarsa ya tafi. Sai bayan zulai ta dawo daga sayayya, ta fito tana ihu, ta ce na zo na gani, muka tarar da ramma a kwance a ɗakin girki, cikin jini"
Nabila ta ce ta gama tambayoyin da zata yi, mai shari'a ya ɗaga shari'ar zuwa sati biyu domin yanke hukunci.
Suka fito tare da barrister Habib da mahaifiyar ramma, da yaran dattijon, ta ce "In sha Allah, mune ke da nasara, hukuncin da kotu zata yanke zata yi mana adalci"
Barrister Habib ya ce "In sha Allah, komai ya kusa zuwa ƙarshe"
Nabila ta ce "Zai dai zo, burina kawai a wanke baba, daga nan mu ɗora da cigaban shari'a" iyalan dattijon suka din ga yi mata godiya.
FEW DAYS BACK
Cikin tsananin mamaki, kankarofi yake kallon Nabila. Ya ce "Barrister, ke ce da kanki a office ɗina? Ya aka yi ki ka san wurin nan?"
Tayi murmushi ta ce "Ba abun mamaki bane ba, matambayi ai baya ɓata, yau gani a ofishin masu ƙasa"
Ya ce "Allah ya sa ba laifi nayi ba aka zo kama ni?"
Ita ma murmushin ta yi masa ta ce "Yan sanda ai su ne suke kama mutum" ya bata izinin zama.
Ta samu wuri ta zauna ta ce "Na yi sa'a, kana kano baka tafi Abuja ba kenan?"
"Eh, ina hutu ne, amma haryanzu mamaki nake yi, yadda aka yi ki ka tako da kanki, ki ka zo har in da nake"
Ta numfasa ta ce "Ka san komai dalili ne yake kawo shi"
"Haka ne, bari na saka a kawo miki abu mai sanyi"
Ta ce "A'a, Alhamdilillah tambayoyi ne nake da su a gareka Yallaɓai"
"To gimbiyata ina jinki"
"Case ɗin da nake yi, na yarinya da aka yi raping, ashe a gidanka aka yi. Na sake komawa na lura da sunan street ɗin sunanka ne, kuma na tambaya aka nuna mini gidan aka ce naka ne. Abun ya ɗaure mini kai, sai dai na jajje amma ban samu abun da nake so ba, matar gidan ta koreni, kusan sau biyu ma, yaya aka yi haka yallaɓai?"
Yayi murmushi ya ce "Waye ya ce miki gidana ne?"
"Sir gidanka ne mana, Mu'azzam wada kankarofi street, kuma aka nuna mini gidan aka ce gidanka ne, sir ban yi tsammanin haka daga gareka ba, ɓoye mai laifi a ɗorawa wanda bai ji ba bai gani ba mai gadinka?"
"Nabila, ina iyakar ƙoƙarina, am even supporting you, baban yaron nan abokin adawata ne, matata kuma akwai yara a tsakanin mu, bai kamata na tona mata asiri haka anyhow ba"
"Amma yarinyar mutane da aka zalunta fa? Maigadinka da aka rufe ba da laifinsa ba fa? Wannan ba hujja ba ce ba, what if ɗanka aka yi wa haka? Haba yallaɓai"
"Nabila, lamarin ƙasar nan ya wuce duk in da ki ke zato? Dole sai mutum yana lissafi, amma in tambaye ki mana? Waye ya ajiye miki tarihin Bunkure a Office ɗin ki? Waye ya tura miki message ɗin babar ramma? Duk kina tunanin wannan, ko kuwa kawai sabgarki ki ke yi?" Waro ido ta yi tana kallonsa.
"Mayar da idanun madam"
Cikin mamaki ta ce "But how?"
"Through barrister Habib my dear. Ba zan tona wa yaron asiri kai tsaye ba, saboda ubansa ne tushen lalata shi, ba kuma nayi haka ne dan na ɓoye laifinsa ba, ina jan ƙafa a lamarin ne, saboda ki gano komai a sannu, yadda babu mai zargina, duk da akwai jiƙaƙƙiya tsakanina da ubansa.
Mahaifiyar ramma na tare da ni, ni na saka aka ɗauketa, tun kan a illata ta saboda case ɗin nan. Zan haɗa ki da ita, zata yi miki bayanin komai, amma ki daina zargina a kan ɓoye mai laifi, am supporting you, program ɗin ma da ki ke yi am supponsoring the program sweetheart, ki daina zargina please, tabbas a gidana aka aikata laifin, kuma ina iya ƙoƙarina a kai madam. Ki je ki cigaba da aikinki, zan cigaba da ƙoƙarina in taimaka miki"
Saroro tayi tana kallon kankarofi kamar sokuwa.
"Akwai alamar gajiya a tare da ke, ki je zan saka Habib ya kai ki in da take"
"Amma duk tsawon wannan lokacin, kuka rufe ni ka ke yi mini yawo da hankali?"
"Akwai dalili ne, amma ki yi haƙuri dan Allah, a dalilin haka aka saka miki wuta a office, aka kusa taka ki da mota, duk dan ina tsayawa ina tsawatar wa ne, akwai hatsari a abun da ki ke yi nesa ba kusa ba, shiyasa nake taimaka miki ta ƙarƙashin ƙasa, amma kiyi haƙuri" ba ta ce masa uffan ba, ta ɗauki jakarta za ta fita.
"Ina baƙonki kuwa? Idan kun sake haɗuwa ki ce ina gaishe shi" ta tsaya ta waiwayo ta ce "Wane baƙon kuma?"
"Viper" ya amsa mata kai tsaye.
"Ka san Viper?"
Kankarofi ya ce "Na san shi, akwai labari mai sarƙaƙiya ne, amma kar ki matsa, ki bi a hankali, zai kawo ƙarshen labarin, kamar yadda ya faɗa, a sauka lafiya abar ƙaunata" ba ta iya magana ba, ta murɗa ƙofar ta fice.
Tun a hanya ta kira barrister Habib, take yi masa masifa, a kan abun da ya yi mata, ya din ga yi mata yawo da hankali da nuna bai san komai ba.
Sai da suka haɗu, yayi ta bata haƙuri, yana ƙara yi mata bayani, kankarofi yayi mata kwarjinin da bata tsigale masa ba, amma ta yi wa Habib ta tas.
****
Nabila tana tafe tana kallon hotunan hannunta, ta kira Viper ya ɗaga ta ce "V ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, ya ake ciki?"
"Ina hanya zuwa zan yi"
"To, Allah ya kawo ki lafiya"
****
Ramma ta tsurawa Abdul ido, ya ce kunun gyaɗa yake so, yana sha yana waya, ya ajiye kofin kunun ya ce "Daddy ni dai dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito maka da rahama ba"
Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce "Wallahi zan saka jami'an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a faɗi cikakke waye kai ba, ga maganar kuɗi na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?"
"Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma....
Wata ashar ɗin indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar, Abdul ya ajiye wayar ya dafe kai.
"Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai ɓoye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah" tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata dining ɗin.
***
"Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai kaƙi gaya mini wacece?"
"Yaya shari'ar ta kasance?"
"Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah"
"Mhmm, a ina aka ganta?"
"Ta gudu ne wani wuri ta ɓuya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota"
Viper ya jinjina kai ya ce "ya nawa, ni ya ake ciki?"
"Shiyasa na zo ai"
"Ok"
"Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina buƙatar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu su bayar da shaida"
"Wane bugaggen?"
"Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi haƙuri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi exposing ɗin su a kotu"
"Rashin ji kamar yaya?"
Ta kalleshi ta ce "Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ƙulla wiwi black market duk da ka yi"
Haɗe rai yayi ya ce "Amma ba prison zan koma ba ko?"
"Idan ta kama ai dole ka koma"
Ya ce "What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?"
Ta zumɓura baki ta ce "Ni na ɗaureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda zamu yi da su, sai anjima"
*****
Nabila ta tafi ɗakin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta ɗauke da addu'a, ta shiga ɗakin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a ɓace.
Ta je ta durƙusa ta ce "Abba gani"
"Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
"Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila?
Sai kin tozarta ahalin nan gaba ɗaya ko Nabila?"
Ta girgiza kai ta ce "Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan taɓa aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah kar abun da zan nema ya ɓata maka rai"
Ta miƙa wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce "Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan.
Abba ya saka hannu, ya karɓi hotunan yana dubawa.
Ya gama ƙarewa hotunan kallo, ya ce "A ina ki ka samu hotunan nan?"
Ayshercool
08081012143
75
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "A office ɗina na gansu"
A take Abba ya fara yayyaga hotunan, cikin kuka ta ce "A'a Abba, dan girman Allah ka gaya mini idan ka san ta jikin hoton, Abba ba ka ga yadda kamaninmu suka ɓaci ba, dan Allah Abba ko sau ɗaya ka nuna mini wani a dangin mahaifina dan Allah Abba" ƙarasa yayyaga hotunan yayi, ya watsa mata cikin matsanancin ɓacin rai ya ce "Ki koma in da aka baki hotunan, su gaya miki koma wacece, ubanki kuma ga hanya nan, ki bar mini gida ki tafi yawon nemansa, yayi miki abun da ban yi miki ba, tashi ki bar gabana kan na tattaka ki, da uban naki ya damu da ke, da zuwa yanzu shi ya nemi in da ki ke".
Anty ta ce "Haba major, dan Allah ka yi haƙuri kar ka yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kan ta, kayi haƙuri dan Allah " gaba ɗaya jikin Nasir yayi sanyi, ganin yadda take ta uban kuka.
Cikin tsawa Abba ya ce "Ki tashi daga gabana, ki tafi ki bar mini gida, ki je ki nemi ubanki, amma ki bar mini gida kar na sake ganinki a gidana"
Wata irin ajiyar zuciya ta din ga yi, ta yinƙura ta tashi da kyar, ta bar ɗakin, ta koma ɗakinta ta kifa a kan gadonta, ta fara sabon kuka, shi kuwa Abba wace irin zuciya ce da shi haka? Ko menene a tsakanin sa da mahaifinta, yakamata ace ya wuce, ta san ya gama yi mata komai a rayuwa, yayi playing role ɗin uwa, yayi na uba a rayuwarta, amma duk da haka gurbin ido ba ido bane ba.
Baba magajiya ce tayi sallama, ta ƙarasa kan gadon, ta dafa kafaɗarta ta ce "Haba Arfa, ke a rayuwarki ba zaki iya haƙuri da tawakalli ba, tun da ya nuna miki baya son zancen nan ba sai ki haƙura ba, shekara nawa ana abu ɗaya kin ƙi ki gane ki haƙura".
Nabila ta tashi zaune, idanunta sun yi jawur ta ce "Baba magajiya"
"Na'am arfa"
"Kema laifina ki ke gani?"
Baba magajiya ta yi shiru tana kallonta.
"Ki bani amsa mana, laifi nayi dan na nemi sanin in da mahaifina yake na ganshi ko sau ɗaya? Baba magajiya mahaifi fa, a duniya na san Abba ko baki yayi mini, sai ya kamani, bana nufin yi masa butulci ko tozarta shi, amma ina son sanin babana, baba magajiya dan Allah ina da wata yar uwa ne? Ke kin san komai, hoto aka bani da wata a jiki irina ɗaya da ita sak, ko yar uwata ce, dan Allah ki gaya mini. Ni idan kin san in da zan ga babana ki gaya mini, ko sau ɗaya na je na ganshi na dawo dan Allah"
Baba magajiya ta girgiza kai ta ce "Ni ban san komai ba, lokacin da na zo gidan nan, an gama dambarwar da za ayi, na zo, ni bani da wani labari a kan mahaifinki"
Nabila tayi murmushi mai ciwo, hawaye na bin fuskarta ta ce "Haryanzu kallon yarinyar da ki ka raina ki ke yi mini ko, shiyasa ki ke tunanin bani da wayo ko? Shekaru ashirin da biyar a doron duniya, ai na girmi ki yi mini wayo baba magajiya, amma shikenan, ai Abban ya ce na je ne nemi babana, zan neme shi kuwa in sha Allah "
Baba magajiya ta waro ido ta ce "Baki san gatse ba Arfa?"
Nabila ta jinjina mata kai alamar eh, ta mayar da kai ta kwanta.
Baba magajiya ta ce "Arfa na san har da damuwar matsi da takura da ake yi miki a gidan nan, ya sanya ki ke damuwa da son ganin mahaifinki, ni dai roƙona da ke, ki yi haƙuri idan da rabo zaki haɗu da mahaifinki ko danginsa, amma dan Allah dan Annabi, kar ki bari ku samu saɓani da maitama"
Nabila ta yi mata shiru, dan gani take yi babu wanda zai fuskanci halin da take ciki.
Tamkar zuciyarta Abba ya yaga, haka take jin zuciyarta, idan ta tuna yadda ya yayyaga hotunan nan, sai dai har a lokacin tana ganin hotunan yarinyar mai kama da ita a cikin idanunta.
****
Duk da Nabila bata jin daɗin komai na duniyar, jin ta kawai take yi gata nan dai, haka ta cigaba da up and down a kan muhimman abubuwan da ta saka a gaba.
Ta sake shigar da koke gaban hukumar'yan sanda, ta nemi su kama madaki da wasu daga cikin yaransa, bisa zargin kisan matar Viper, shekaru shida da suka gabata.
Yau tana da program a gidan radio, kuma yanayinta ya nuna wa Sumayya tana cikin matsananciyar damuwa, sai dai ta shigo a ƙurarren lokaci, zasu fara gabatar da shirin, dan haka ba ta samu damar yi mata tambayar meyake damunta ba.
Nabila tayi iya ƙoƙarin ta, wurin ajiye damuwa a gefe, suka fara gabatar da program.
Sumayya ta kalli takardar hannunta sannan ta ce "Jita-jita ta cika gari, cewa kin shigar da koke gaban kotu, a kan lallai kotu ta hana hukumar'yan sanda kamar shahararren ɗan ta'addan, da addabi wani yanki na garin nan, kuma akw zargi da kisan matarsa, duk da yadda hukumar ta 'yan sanda, take nemansa ruwa a jallo?"
Nabila ta kalli sumayya da rinannun idanunta, tayi mamakin yadda sumayya tayi mata wannan tambayar, a tsakiyar program ɗin su haka, saboda ba magana ce da ta fita ba, balle ta ce an yi Jita-jita a kai. Sumayya ma ta tsare ta da ido, alamar tana jiran amsa.
Tayi wani irin murmushi ta ce "Ba ɗan ta'adda bane ba, mutum ne kamar kowa, kuma ɗan ƙasa da ya dace ya samu duk wani 'yanci da kowane ɗan ƙasa ya dace ya samu. 'yan ta'adda na yawonsu a gari, an san in da suke, an san in da za a same su, hakkinsa muke nema a kotu, ba shi ya kashe matarsa ba. Na san mutane za su yi mamakin yaya aka yi mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi, amma a bibiye ni a cikin shari'ar da zamu gudanar".
"Amma ba kya ganin hakan kamar taka doka ne, zaki yi amfani da damarki ta lauya ki taka doka, ki kare mai laifi?"
"Sam, dokar da aka wulaƙanta, da ita nake son yin amfani wurin gyara kuskuren da aka yi. Tayaya mutum zai shafe shekaru babu Shari'a, daga baya alƙali da saka hannunsa da umarninsa da komai, a sake shi bisa doron doka da ƙa'ida, kuma daga baya a zo ana nemansa. Shin wanke shi aka yi daga laifin? Ko kuma akwai wani ɗaurin ɓoye da yakamata a warware? " Tayi maganar tana ƙure sumayya