Showing 198001 words to 201000 words out of 479911 words
baƙar fata, hausawa masu riƙo da addini da al'ada. Ni ban shekara sha takwas ɗin ba, idan ma na yi ai sai da yadda ta da amincewa ta. Kawai saboda bamu da kuɗi ka yi mini fyaɗe ka je har gidanmu gaban uwata ka ɗaukko ni, ka rabani da ita, kuma ka koma ka karɓo kayana ka ce mata ta daina nemana kai ba aurena ka yi ba, kai ba wani abu ka yi da zaka taimaki rayuwata ba, ka ɗauki hakkinmu ba ka yi mana adalci ba"
Ya ce "Ke kin isheni, sai ka ce ke kaɗai ce 'ya? Ni fa ban taɓa ɗaukar wata mace na ajiye ina lallaɓata ba sai ke, kuma ma ku da ake haihuwar ku barkatai babu tsari, har wani damuwa za a shiga dan an ɗauki ɗaya? Kashe ki fa na yi niyyar yi na ƙyale ki".
"Mu ba ai haife mu barkatai ba, mu uku ne, yayanmu ya rasu, ƙanina ba shi da cikakkiyar lafiya, ni kuma ka ɗauke mata ni, ban da dalilin maraici babu abun da zai saka ka ganni a birni aikatau, har ka keta mini haddi, bayan ka turo mana wata azzaluma, da fari ta ce zata taimaka mini, ta koma gaya mana yahudanci, ka ɗauke ni a gaban uwata, ka zo ka mayar da ni karuwa ka yi wa kanka adalci dan Allah kuma nima ka yi mini?"
"Naja'atu Bunkure ba ƙarya ta gaya miki ba, tun a lokacin da ba ku nuna taurin kai ba, da ba a zo nan ba, ku ku ka janyo koma menene ai"
Ramma ta haɗa hannayenta biyu, ta rufe fuskarta tana kuka ta ce "Ka cuce ni, ka lalata mini rayuwa, dama kasheni ka yi na huta, ka wulaƙanta rayuwata a matsayina na 'ya mace musulma da addinina ya suturta. Da ƙanwarka ce ni ko 'yar ka, ba zaka zuba mini ido ka ce na je na yi tarayya da wani ba aure ba, kayi amfani da kuɗi, ka wulaƙanta ni dan ni 'yar talaka ce ba ka kyautawa rayuwata ba" ga ta yarinya ƙarama, sai iya tsara magana.
Abun da bai taɓa ji ba sai a wannan karon, kukan ramma a cikin zuciyarsa, maganganun ta suka tsaya a zuciyarsa, amma a zahiri ya nuna ko a jikinsa, ya tashi ya bar ta a falon ya tafi ɗaki.
***
Ɗan mama yana ta kaiwa yana komowa, tsakanin ɗakin Viper da tsakar gida, yana jiran Walid ya fita, amma ya ƙi fita ya zauna ba shi da niyyar fita.
Viper kuma sai bin ɗan mama yake yi da ido.
Walid ya ce "Kai ɗan mama, kamar ba ka da gaskiya"
Ɗan mama ya ce "Haba Oga walid me ka gani?"
"Ba sai na gani ba, alamun hakan na gani, wallahi na ga abun da bai yi mini ba, sai ranka yayi mugun ɓaci"
Ɗan mama ya ce "Kar ka damu Oga walid, babu wani abu da zaka gani wanda zai ɓata maka rai"
Walid ya jinjina kai, ya cigaba da shan sigari.
Al'amin ya yinƙura ya tashi, Walid ma ya tashi ya ce "Ina zaka?"
Al'amin ƙura masa idanunsa da suka yi wani irin mugun jaa.
"Ba wai tuhumarka nake yi ba, ko wani abu ba, kawai dai ba na son ka yi wani abu da zai wargaza mana shiri ne"
"Iska zan je sha, ko yau ma yinƙurin kashenin zaka yi?"
Walid ya girgiza kai ya ce "Last time ɗin ma, ni ba niyyar kasheka na yi ba, ƙoƙarin hanaka abun da ka yi niyya na yi, a dawo lafiya" Al'amin ya nufi ƙofar fita, ɗan mama ya ce "Oga Viper, bari na zo mu je na taka maka" Walid ya riƙe rigarsa, ya tsare shi da ido.
Ya sosa kai ya ce "Dama raka shi zan yi"
Al'amin bai waiwayo ba, kawai ya fita, Walid ya fara saka hannu a aljihun ɗan mama yana caje shi, Ɗan mama ya riƙe hannunsa ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri zan yi maka bayani".
"Sakar mini hannu, ko na kwaɗa maka mari"
Ɗan mama ya sakar masa hannu ya ce "Amma dai da ka tsaya na yi naka bayani"
Walid ya ciro baƙar leda a aljihunsa, ya buɗe, ampoules ɗin allura ne da sirinji, sai baƙin capsule.
Walid ya kalleshi, ɗan mama ya ce "Wallahi cewa yayi sai na nemo masa su, idan ba haka ba, ba ya iya bacci, kansa zai fashe ni kuma sai ya bani tausayi, daga ƙarshe kuma ya ce wallahi idan ban samo masa ba sai ya kashe ni"
"Sai ya kashe ka, kai ka taɓa ganin ya kashe wanin?" Ɗan mama ya girgiza kai.
"Wallahi idan ka kuma sayo wannan hard drugs ɗin ka kawo masa, sai na saka maka ƙarfe ka ji na rantse" ɗan mama ya ce "To, amma dan Allah shi ma ka gaya masa, ka san idan na ce masa a'a ba zai yi mini da daɗi ba".
Walid ya ce "Idan ya ce ka kawo masan, ka ce masa to, ka gaya mini" ya jinjina masa kai.
Viper yana zaune a kan dutsen, ya zubawa wuri ɗaya ido, kansa kamar ya tarwatse haka yake ji, ga ƙirjinsa kamar an ɗora masa dutse, da ƙyar yake iya numfashi, ga jikinsa sam babu ƙwari, banda kashe masa jiki babu abun da ƙwayoyin nan suke yi, soyake yayi bacci mai sunan bacci, ko ya manta komai da yake cikin ƙwaƙwalwarsa amma abu ya gagara.
"Madaki! Indabo!" Ya faɗa a hankali yana sunkuyar da kai, ya ɗaga kai kamar a mafarki ya hangota, ta sauka daga adaidaita sahu, sai waige-waige take yi, yana saman dutsen sosai, dan haka yana hangota. Ta tsaya tana kallon hanya, in da yake take facing, amma ita ba ta ganinsa.
Dogon hijjabi ne a jikinta yau, a hankali take tafiya tana cigaba da waige-waige, mamaki ne ya kama shi, me kuma ya dawo da ita wurin nan yau? Zuciya ce ta tinziro shi, ya ji kamar ya sauka ya je ya naɗa mata shegen duka. Mata halin su ɗaya, cin amana 'yar madarar sa ce kawai ta fita daban sai umminsa, ta sace masa waya ta gudu, ta saka an kama liti, saboda tsagwaron rashin kunya ta sake dawowa, ko uban me ta dawo yi oho?.
Hakan ya ƙara tabattar masa he's not safe, za ta iya kawo jami'an tsaro su kama shi, sai dai kash, shi ba ya fargabar a kama shi, a kama shi ko a ƙyale shi, shi ba wannan ne a gaban shi ba yanzu.
A yau ma ba ta iya gane hanya ba, bulayi take ta yi, tana nema, amma ta kasa ganewa.
Babu tsammani suka yi kiciɓis da ɗan mama, ya kalleta ta kalle shi, ya ce "Ke! Me ki ke yi a nan wurin?"
Ta ce "Yauwwa, kai ne wanda na gani a gidan Viper ranar ko?"
"Ke, ki ka kuma kama sunansa, sai na ƙara wa ƙofar bakinki faɗi wallahi, kar ki sake ambatar sunansa ko ki kama sunansa".
Nabila ta ce "Tom, ba zan sake ba, dan Allah taimakona nake son ka yi, ganinsa nake son yi dan Allah"
Ɗan mama ya ce "Ka ga wata mayyar kuma, baki ji kashedin da yayi miki ba kenan? Kin ɗauka da wasa yake yi da ya ce "Ya sake ganinki zai kashe ki, kin san waye Viper kuwa?"
"Ba zai kashe ni ba, muhimmiyar magana nake son mu yi da shi, na san na yi muku laifi, ku yi haƙuri dan Allah, ka taimaka mini ka haɗani da shi dan Allah"
Ɗan mama yayi mata wani irin mugun kallo ya ce "Ya aka yi ki ka san ba zai kashe ki ba?"
"Viper ba ya kashe mutane, mussaman mata da ƙanan yara, dan Allah ka haɗa ni da shi na kasa gane gidan".
"Ke bar nan wurin, na haɗaku ki saka a kama shi ko, to ta Allah ba taki ba, wuce ki bar wurin nan"
Ta sake marairaicewa za ta yi magana.
Ya zaro wuƙa ya ce "Idan shi ba ya kisa ni ina yi, ware ko na zaro hanjinki yanzun nan" wuƙar sai ƙyalli take yi, ya fara tunkarota, yana wulwula wuƙar, ba shiri ta juya, gwiwa a sanyaye ta bar wurin.
Har ta miƙe ta ɓacewa ganin Al'amin yana hangota, ya miƙe ya kwanta a kan dutsen, ya lumshe idanunsa rana tana dukansa, yana jin yadda zafin ranar ke ratsa shi, yana ƙara masa ciwon kai, amma ba shi da niyyar tashi.
***
"P.A"
"Na'am honorable"
"Ka tabattar binciken da ka yi a kan yarinyar nan daidai ne, babu kuskure a cikin sa?".
P.A ya jinjina kai ya ce "Babu fa, ka san ba na yadda a samu kuskure a irin wannan lamarin, mussaman a irin wannan ƙadamin, ba a samu kuskure ba, yadda na gaya maka hakan ne"
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, ina ita ƙawar ta ta, ana cigaba da bibiyarta?"
"Eh, a wurinta muka samu wasu abubuwan ma"
Indabo ya ce "Haryanzu ina mamakin yadda aka yi ta ce ayi mata bincike a kaina ne, shiyasa nake ta tantama anya ka yi binciken a kanta dai-dai?"
P.A ya ce "Haba honorable, ya ma za ayi wannan ƙaramar alhakin ta yi wani bincike a kanka, wataƙila hakan yana da alaƙa da harkar siyasa ne kawai, ko kuma sakata aka yi".
"Ba ita ce a gabana ba, Viper mai zamani, shi ne babbar barazanata, shi ne damuwata, ku cigaba da aikinku kawai, duk abun da ake ciki, ka din ga sanar da ni "
P.A ya ce "In sha Allah, ai yaronsa ɗaya yana hannu, sai dai na bincika an ce Haryanzu bai yi magana ya faɗi in da yake ba"
Indabo ya ce "Ƙyale 'yan sandan nan, sonake na riga su samunsa, idan na riga su kawai kashe shi za ayi salin alin, duk madaki ne yayi mini shirme wallahi, amma yanzun ma komai zai daidaita"
"Kar ka damu honorable, ai kai maganin kowane shege ne a ƙasar nan, ba ma ɗan daba ba, zamu yi maganinsa, amma da alama kamar kana da maguatan ɓoye, da suke tallafa masa"
"Na sani, amma yanzu duk ba wannan ba, a cigaba da abun da yakamata"
P.A ya ce "To shikenan, na barka lafiya "
Bayan fitarsa Indabo ya shiga cikin gidansa, ya tarar da Abdul a falo, tare da mahaifiyarsa.
Ya kalli indabo ya ce "Welcome"
"Thank you" ya zauna ya kalli Abdul ya ce "Dama nemanka nake yi".
Abdul ya ce "To gani"
"Ya maganarmu ta rannan?"
"Daddy maganganun namu ai da yawa, wacce daga ciki?".
"A'a, ka san wanda suka fi muhimmanci ai, mun daddale da jam'iyya, kai za a tsayar mataimakin gwamna, tun yanzu yakamata ka fara harkar campaign, da buga pastoci. Amma ka san dole ka daina duk wani shashanci da kake aikatawa. Sannan maganar da nake yi, maganar aure, shekara talatin da biyar, uban me ka ke jira? Muddin lokaci ya cigaba da gabatowa, abokan adawa suka san baka da aure, sai ku samu matsala a harkar takarar nan, amma da na yi maganar auren sai ka din ga gocewa"
Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Wai constitution ne ya ce dole sai mutum yayi aure zai yi shugabanci meye amfanin auren mutum a cikin siyasa to?"
Indabo ya ce "Ban sani ba, idan ba zaka yi ba, ni ina da wadda zan haɗaka aure da ita, ga 'ya'yan abokai da yan uwa nan sai dai ka ji an yi".
Hajiya Bilki da tun ɗazu ba ta yi magana ba sai yanzu ta ce "Haba distinguish, ka bi shi a hankali mana, zai yi, ba sai an yi masa dole ba".
"Ba zan bishi a hankalin ba, na gaji da wannan shirmen nasa, rayuwarku nake ƙoƙarin ingantawa, wataƙila idan ya zama mataimakin gwamna, shi ya fi ni samun dama, ya kuɓutar da ɗan uwansa".
Hajiya Bilki ta ce "Distinguish, kai da ka fishi daɗewa a harkar, ba ka samu yin hakan ba sai shi, ni na karaya da lamarin jafar"
"No, kar ki yi mamaki ya fi ni samun authority, da damar fitar da shi, da dai a nan Nigeria ne, da tuni an daɗe da wuce wurin"
Ta ce "Haka ne, Abdul dole ka yi haƙuri ayi maganar auren nan, tun yanzu za a fara share fagen samun damar yin nasarar ka, dan idan ku ka gama tenure ku, kai zaka yi gwaman nan gaba"
Cikin sangarta ya ce "Mummy ba ƙi na yi ba, auren ne ba na so"
"Aikuwa haka zaka yi haƙuri" suka cigaba da tattaunawa a kan yadda tsare-tsaren za su kasance.
***
DSP Nasir na tsaka da aiki, aka sanar da shi yayi baƙuwa, ya ce ace ta shiga, tana shiga ya ga Nabila.
Yayi murmushi ya ce "Ke ce baƙuwar dama?".
"Eh mana, ko na koma ba ka san ganina?"
"A'a ni na isa na na ce haka. Zauna bari na kawo miki lemo, daga wurin aiki ko daga ina?"
Nabila ta kashingiɗa ta ce "Na je wani trial ne"
Ya ɗaukko mata ruwa a fridge ya ce "Sannu"
Ta ce "Yauwwa" ta karɓi ruwan ta sha, ya ce "Amma kin bawa kanki wahala da yawa, wace court ɗin ki ka je, har ki ka iya biyowa nan?"
Ta ajiye robar ruwan ta ce "Wani wuri na je, na ga wani client, DSP"
"Na'am barrister Nabila maitama "
Tayi murmushi ta ce "Wai ina mutumin nan?"
Ya ce "Wanne?"
"Wanda ku ka kama, haryanzu bai faɗi in da Vipern yake ba?"
"Ina fa zai faɗa, yana ta wahalar da mu".
"Dan Allah ka nuna mini shi"
"Ki yi masa me?"
"Babu komai, ganinsa kawai zan yi"
Nasir ya ce "To bari na gama aikina, sai mu je ki ganshi"
Nabila ta zauna ta jira Nasir ya gama abun da yake yi, ta ɗauki jarkar ruwanta suka fito, yana ta nuna wa abokan aikinsa ita, yana gaya musu ita yana gaya musu ƙanwarsa ce, lawyer ce. Suka gaggaisa da abokan aikinsa, sannan suka ƙarasa in da liti yake.
Laɓensa duk ya bushe, saboda yunwa da ƙishirwa, yana ganin Nabila ya ganeta ya ƙura mata ido, ta kawar da kanta ta ce "DSP tun da ya ce bai san in da yake ba, haka zaku cigaba da ajiye shi?"
"Eh har sai ya yi magana tukuna"
Ta girgiza kai ta ce "Amma a doka, ai kotu za a kaishi ko a sake shi, ina ga fa tun da ya ce bai sani ba, bai sani ɗin ba"
Nasir ya ce "Ya sani ba zai yi magana ba ne" ta miƙa wa liti ruwan hannunta, ta ce "Ga ruwa" banza yayi mata, Nasir ya juya ya fita yana amsa waya daga wurin ogansa.
Tayi ƙasa da murya ta ce "Na san na yi muku laifi, amma dan Allah ka yi haƙuri, zan san yadda zan yi ka bar wurin nan".
Ta ciro wani ruwan a jakarta ta bashi, ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, na fahimci kuskuren da na yi, ban kyauta ba amma zan gyara komai"
Nasir ya dawo ya ce "Mu tafi?"
"Eh, amma gaskiya, yakamata a san abun yi, kar a taka doka da yawa"
Ya ce "To masu doka, mu je gida"
"Da gaske fa nake, ko mu shigar da hukumarku ƙara".
Ya mayar da abun wasa, suka tafi gida.
***
Ƙarfe huɗu na yamma, Nabila ta shirya ta fita, ta tafi gidan matar da aka ce an yi laifin fyaɗen nan a gidanta.
Ganin Nabila cikin shiga mai kyau, ya sanya masu gadin ba su tsaya tuhumar wacece ba, suka bata damar shiga gidan.
Sai da haushi ya fara kamata, saboda jiran da aka bar ta tana yi, daga baya matar gidan ta fito, suka gaisa da Nabila.
Nabila ta ce "Na san baki sanni ba, sunana barrister Nabila Yusuf maitama, lawyer ce ni mai zaman kaina. Akwai mai gadin gidan nan malam isyaku, da ake accusing da laifin fyaɗe, ni ce lawyer sa. Na zo ne dan Allah in ji details ɗin abun da ya faru".
Matar ta tsuke fuska ta ce "Ke, ni ki ka zo ki yi wa wannan tambayar? Wurin 'yan sandan na je na fara karɓar report, an ce na dawo station ɗin da aka fara case ɗin, amma na ga dacewar fara zuwa gidan nan, tun da an ce yarinyar 'yar aikinki ce, kuma ainihin wanda ya yi laifin kina da alaƙa da shi, ku ka yi framing ɗin sa aka ce shi ne. Yanzu duk ba wannan ba a matsayinki na uwa kuma 'ya mace nake so mu fara magana. Ina yarinyar take? Ina ne gidan iyayenta? Ban damu da sanin koma waye yayi laifin ba, fatana kawai a wanke mai gadi, tun da kun san wanda yayi laifin "
Matar ta miƙe ta ce "Ki koma wurin jami'an tsaro, su zaki yi wa wannan tambayar, kuma ba ki da wata hujja, da take tabattar da ba shi yayi ba, idan kin gama kina iya tafiya"
Nabila ta miƙe tsaye ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai antyna da bani lokacinki" ta juya ta fice.
Station ta sake nufa, wanda a nan aka fara case ɗin, aka nemo statement ɗin da aka rubuta, da sunan Asibitin da aka kai ramma, na cikin gari, tana tsaka da dubawa, wanda yake evening duty, shugaba a wurin, ya fito afujajan, ya ƙwace file ɗin wai ba a ba su damar su bata file ɗin tayi bincike ba.
Cikin mamaki da takaici Nabila ta ce "Waye zai bayar da damar, bayan wadda ƙasa ta bayar, lawyer ce fa ni, dan me za a hana ni damar dubawa, doka ta bani damar neman hujjojin da zan gabatarwa kotu, na wanda zan kare, yaya za ayi a hana ni"
Fafur suka hanata, suka ce ta tafi, ta kira Nasir a waya, amma wayarsa ta ƙi shiga, ranta yayi mummunan ɓaci.
A gajiye ta koma gida, ana ta kiraye-kirayen sallar magariba, ta yi wanka tayi salla, ta ɗaukko wayarta ta kira sumayya.
"Ke ya ki ke aikin?"
"Sumy raina a ɓace yake, kin san menene?" Sumayya ta yi sauri ta katse wayarta, ta saka a Flight mode, ta ɗauki wayar ummanta, ta kira Nabila ta ce "Sorry wayar ce caji ya ƙare"
Nan ta labartawa Sumayya abun da yake faruwa.
Sumayya ta ce "In dai ƙasar nan ce, ai kaɗan ki ka gani d.....
Cikin sauri Nabila ta katseta ta ce "Sumayya few months back, ina wannan case ɗin da yaya murtala ya saka, har aka kusa korarsa? The case are similar".
Sumayya ta ce "How?"
"In so many ways, dan Allah ki sake binciko mini labarin, ko ma ki haɗani da yaya murtalan, ke zan ma zo na same shi, the same yadda matar ta ce an yi wa yarinyar fyaɗe, ɗan yayan matar gidan, shi ma dattijon nan haka ya ce