Showing 372001 words to 375000 words out of 479911 words

Chapter 125 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6060

ya yi a hakan ba, ya yi musu shiru, su ka yi ta kukan, ya ce a fara kai sumayya gida, sannan su koma barrack washegari sai su je wurin su ramma.

***

Major ya sha mamakin yadda Nabila ta nuna fushi take yi da shi, taƙi saurarsa.

Mama kuwa sai ziga shi take yi, ta ce "Dama ga ubanta yaushe za ta saurare ka, ai kai ka gama yi mata amfani kuma, shiyasa tuntuni da yaranka ka kama, da ya fiye maka" shi dai bai furta komai ba, amma abin ya din ga cin zuciyarsa.

Rahila ma aka sallameta daga asibiti, bayan an yi mata ɗorin karayar hannunta, sai da Abbu ya dage ya ce sai Abba ya bar masa gidansa, aka kaɗa aka raya ya ce ba zai ci gaba da riƙe shi ba, idan kuma ta dage sai ya zauna, to sai dai ta bi shi su bar gidan.

Shahida ma ta dage a kan raba aurenta, da fari Abbu bai sani ba, amma bayan ya takurata, da ta gaya masa bai tausayawa halin da rahila take ciki ba, yayi mata tas, ya ce sai an raba auren, ba za a saka masa 'ya a halaka ba.

***
Sumayya ta labartawa ummanta abin da yake faruwa, sumayya na ce mata jalingo, ummanta ta ce ta san mahaifin Nabila, amma ba wani sani ba, ta dai san abokin aikinsa ne.

Madam halima ta gaya wa Nabila Viper ya zo, yana jiranta su fita.

Kallo ɗaya ya yi mata, ya san ba ta samu isasshen bacci ba, fuskar nan babu walwala.

"Ina kwana" tayi maganar a hankali.

Ya tsura mata ido, ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa.

"Akwai sauran damuwa ne? Kin haɗu da mahaifinki ba shi ne fatanki ba?" Yayi maganar yana kallon ta.

Ta girgiza masa kai.

Ya ce "To me ya yi saura kuma?"

"Kewar yar uwata, da tunanin yadda zan daidaita Baba da Abba, kowanne ya na da muhimmanci a gare ni, amma Abba ba zai saurare ni ba, saboda Nasir ba zai daina ziga shi ba, saboda haushin tsaya maka da na yi, zai ta ziga shi a kan lallai ya yadda kai ka kashe jauhar, ba ni da gaskiya ina tsaya maka"

"Ƙalubale ne ma hakan, amma yakamata tun ba yanzu ba ki san kuka ba magani bane ba, na san duk ni ne silar komai, shigowa ta rayuwarki, ki yi haƙuri"

"Ba kai ka shigo rayuwata ba, ni na shiga taka, ko in ce ƙaddara ce, amma in sha Allah zan yi iya yi na, sai an hukunta wanda su ka kashe 'yar uwata, ku ma na tabattar da an kwance sarƙar da aka sanya wa mijinta alƙawari ne na yi wa kaina" ta yi maganar tana share hawayenta.

Ya jinjina kai ya ce "Allah ya ba da sa'a"

"Amin" har ya yi gaba zai fita, ta ce "Viper" ya tsaya ya waiwayo.

Ta ƙarasa gabansa ta ce "Ina son ka ji abin da na ji a lokacin da na rungumi mahaifina, ina son ka yi amfani da nasihar da ka yi mini, a kan kanka. Mahaifinka yana da muhimmanci a rayuwarka"
"Wannan ni ya shafa, ba ke ba, dan haka babu ruwanki a ciki"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "Ina roƙonka ne a matsayina na ƙanwarka, ba lauyar ka ba, ina fatan ka kasance cikin rahamar Allah kamar yadda nima ka ankarar da ni nawa kuskuren" Ajiyar zuciya ya yi, ya fice ta bi bayansa.

Haka kurum su na tafe a mota, yake tunanin da gaske yanzu Nabila a matsayin yaya ta ɗauke shi kawai?.

Harabar wurin 'yan sandan cike da motoci.

A can su ka tarar da sumayya, mahaifiyar ramma ma ta je wurin ita da ramma, Alhaji mu'azzam ya saka an kai su.

Nabila tana matuƙar jinjinawa gudunmuwar da Alhaji mu'zzam ya ba su, ya cancanci yabo da godiya, amma goga Viper hakan ko a jikinsa, balle ya nuna masa yabawar sa da jin daɗin sa.

Suka gaggaisa, ramma da ƙyar ta iya gaida Viper, saboda matsanancin tsoronsa da take ji.

Su liti tuni sun je wurin, dan sun kai wa ɗan mama abinci.

Sumayya ta zauna su ka sake tattauna wa da ramma, kasancewar su na jiran ƙarasowar su Abdul da lauyoyin sa a ɗauki statement ɗin su duka.

Sumayya ta naɗi wani sashi mai muhimmanci, na tattaunawar su da ramman, wanda zai yi wa Sumayya amfani haka Nabila, mussman ta ɓangaren Naja'atu Bunkure.

Viper kuwa cikin isa yake yawonsa a headquarter yan sandan, ya je ganin ɗan mama da kansa.

Sumayya ta dubi Nabila ta ce "Nabila, haryanzu ina mamakin yadda aka yi ki ka haɗu da Viper, ikon Allah ashe duk wannan haƙilon a kan sister ɗinki ki ke yin sa, amma Nabila idan ba shi ne ya kashe Jauhar ba, wanene?"

Nabila ta gyaɗa kai ta ce "Mu haɗu a kotu kawai sumayya, abubuwan su na da girma da faɗi sosai"

"Meye wani sai mun haɗu a kotu, ki ƙarasa mini, kin bar ni a cikin duhu da zullumi Abla, kamar yadda na ji ana kiran ki, Nabila gayen nan kuwa ba son ki yake yi ba?"

Nabila ta numfasa ta ce "Sumayya, ba ki yi ƙarya ba, ni ina son Viper, na kamu da sonsa ba tare da na shirya hakan ba, dan da farko dan na taimaki rayuwarsa ya dawo hayyacinsa ya sanya na ce ina son sa, sai dai ban yi aune ba, na faɗa son shi da gaske. Saboda Viper mutum ne na musamman ya kai a so shi, kin san meya ƙara jefani cikin ƙaunar sa da gaske?"

Sumayya ta ce "Sai kin faɗa"

"Zamantakewar sa da ya yi da jauhar" Nan Nabila ta fara ba wa sumayya labarin abin da ba ta sani ba, matakan da ta bi wurin haɗuwa da shi, zuwa labarin sa da Walid ya bata.

Ramma ta yi shiru ta na sauraron su, kawai ta din ga jin, idan jauhar tayi haƙuri da Viper mutum mai ban tsoro ta zauna da shi, ta yi wannan gwagwarmayar lallai idan aka yi haƙuri Abdul ma zai iya shiryuwa.

Wani ɗan sanda ne ya leƙo, ya ce su shiga, sun ƙaraso. Gaban ramma ya faɗi, maman ramma na can ta na shan hantsi, Nabila ta yi mata magana ta ce ta taso.

Gaban ramma ya tsananta faɗuwa, aka yi musu jagora zuwa ofishin da za a ɗauki statement ɗin.

A ciki su ka tarar da Viper a zaune, har da manyan mutane abokan Indabo da su ka zo, ga mahaifiyar Abdul yasar a wurin ita ma.

Ai su na shiga office ɗin, Abdul ya miƙe, kallonsa ramma ta yi, ya rame sosai da sosai, ba wai rama ta damuwa ba, rama ta ciwo.

"Rahama" ya kira sunanta a raunane.

Mugun kallon da Viper ya yi mata ne,ya sanya ba shiri ta nemi wuri ta zauna.

Tashi ya yi ya nufi in da take, wani ɗan sanda ya daka masa tsawa, amma bai saurare shi, ba ya nufi ramma. Ƙafa Viper ya saka masa, abin ka da mara lafiya, ya tafi luu zai faɗi, Viper ya riƙe rigarsa ya hana shi kai wa ƙasa.

Aka saka ɗan sanda ya janyo shi, ya zaunar da shi, tuni ramma ta fara kuka.

Kawai ya zuba mata ido ko ƙiftawa ba ya yi.

"Abdul da ma wannan ce yarinyar da ka ke ta wannan haukan a kanta, duk matan garin nan? Wallahi ka bani kunya" mahaifiyarsa tayi maganar a ƙule.

Aka tambayi ramma sunanta ta faɗa, aka nuna mata Abdul aka ce "Kin san wannan?"

Ta jinjina kai alamar eh.

"Waye shi?"

"Mijina ne" ta faɗa kai tsaye.

Gaba ɗaya su ka Kalle ta, cikin takaici mamanta ta ce "A gidan uban wa ya zama mijin naki?"

Nabila ta tashi ta je gaban ramma, cikin raɗa ta ce "Dan Allah ki nutsu rahama, ki yi bayanin komai, saboda a ƙwatar miki hakkinki"

Aka sake tambayar ramma "Meye alaƙarki da shi, me ya yi miki?"

Tayi shiru ta na kuka taƙi magana.

Abokin Indabo ya ce "Ni fa ina ga wannan abun duk da masalaha aka yi, aka sasanta abun nan, dan gudun ɓacin sunan yarinyar nan, tun da akwai aure kuma abin nan ya wu....

"Shut up, ba rikicin jam'iyya ba ne ba ko na siyasa, a ƙwatarwa yarinya hakkinta mu ke buƙata" Viper ya yi maganar cikin tsawa.

"Aminu Viper, mai bunu a ƙugu ba ya kai gudunmuwar gobara, ka bari ka fara kashe wutar gabanka, kafin ka zage ka na ɗaga jijiyoyin wuya, haryanzu ɗa na ya na da gatan da za a iya shafe ko ma me ya aikata, mu ka zaɓi ayi masalaha".

"Gobarar da nake ƙoƙarin kai gudunmuwar kasheta, ai ku ne gobarar, dan kun fi ni shiga matsala da hatsari, a ɗauki statement a gabatar da ƙararmu a gaban kotu "

"Ya isa haka, nan fa gaban hukuma ne, ba teburin caca ba. Ke ki yi magana mu na jiranki" Ɗan sandan yayi maganar yana kallon ramma.

Da ta ɗaga kai ta kalli Abdul, sai ta ji ta karaya.

"Talk" Viper ya daka mata tsawa, ta zabura ta rirriƙe Nabila ta na kuka.

A hankali Abdul ya ce "Ku daina yi mata tsawa, yes i rape her, na amsa laifina"

"Ba ka da hankali, lauyoyin ka ba su gargaɗeka a kan kar kayi magana ba?"

Nabila cikin rarrashi, ta ce "Rahama ki yi magana, dan Allah kar ki bari tausayi ya yi tasiri a zuciyarki, ki yi magana"

Cikin kuka ramma ta ce "Ai ya nemi yafiyata, kuma da gani ba shi da lafiya, dan Allah a sassauta masa, ko a bari wataran idan ya warke sai na yi magana".

Ayshercool
08081012143




Abu na farko da zamu buk’ata daga wajenka shine mahaifar matarka, Ma’ana ba zaku haihu da matarka ba.” Imaam ya ‘dago yana kallonsa Ya ji kansa ya wani sarà masa, amma sam ya kasa masa musu… Alwan yana murmushi ya ce “Ka kirata ku yi shawara…” Ya fice ya bar masa wajen. Da sauri Imaam Ya kira Safna. Tana d’agawa ta ce “Yaya? Imaam Allah yasa dai baka musu taurin kai ba?” Ya saki huci ka’dan ya furta “Ba zan iya abinda suke so ba….” “Zaka iya Imaam, ka yi koma me suke so? Yanzu fa ba abinda baa yi saboda ku’di, ana ya Kai Kai, mutum yana kwanciyar da y’ar cikinsa, da Uwar data haifeshi ma saboda ku’di, ana luwa’di da ma’digo saboda ku’di, ana bada Uwa ko y’a Yaya ko k’anwa, K’ani ko wa? Duk saboda ku’di, don haka ka yi ko me suke so Moddi Saboda ku’di… bana son musu…” ta fa’da tana zame kanta a duk sunayen da ta ambata, bata k’i ya yi komai ba in dai zai samar musu da ku’di, bata damu ta ji shara’din da suka bashi ba. Imaam Ya saki ajiyar zuciya, sai ya ji ya samu k’warin gwiwar bayar da mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta ta ce ya yi komai saboda ku’di. A zuciyarsa Ya dinga jin baya so, amma harshensa ya kasa amince masa ya furta baya so d’in. Ya kalli Alwan da Ya shigo d’akin idanunsa a kansa shima ya ce “Yaya Aboki? Ka yarda ko a’a? Abu guda dana sani baka isa ka San sirrinmu sannan ka bijire mana ba…..




Cab’di kin fara bibiya ko har yanzu… Hadarin gabas dai da zafinsa yazo akwai cakwakiya anan gaba… Za’a yi kuka za’a yi dariya za’a sha soyayya a cikin littafin nan. Hanzarta ki fara Ina Imaam Muhammad Moddibo Ya kai kansa?

89
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

  *_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata💃😍

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻

Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi

Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi

Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra

Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327  Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327  sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊


Sake kallon wayarsa ya yi, ya ga location ɗin wayarta ya na harba hanyar gidan mahaifinta.

Kasa nutsuwa ya yi da hakan, kawai ya tashi ya sanya kaya ya fita.

Saifu ya riga su Nabila ƙarasawa, Allah ya sa Baba bai kai ga fita ba.

Saifu na sanar masa, Nabila ta na hanya, bakinsa ya ƙi rufuwa, ya fasa fita, ya ce a haɗa mata kayan abinci.

Ya ce "Saifullahi ita da wa za ta zo nan ɗin?"

Saifu ya ce "Itakaɗai ce, kai take son gani"

Cike da fara'a ya ce "To Allah ya kawo mini ita lafiya cikin aminci"

Ana haka Nabila ta yi sallama, hafsa ta fito da gudu daga ɗaki, ta rungumeta ta na "Oyoyo ga jauhar"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Nabila dai, ba jauhar ba" ta yi shiru ta na kallon Nabila.

"Kin ƙi yadda haryanzu ko?" Ba ta sake cewa komai ba, ta ci gaba da kallon Nabila, ta na ƙoƙarin gano dalilin da ya sanya za ace mata ba jauhar ba ce ba.

Baba da kansa ya fito ya tari Nabila, har zuwa ƙaton falonsa, ta zauna su ka sake gaisawa, babu kunya Zakiyya da maman saifu su ka biyo bayanta har ɗakin su ma.

Su ma ta gaishe su, su ka amsa su na kallon ta kamar baƙuwar halitta.

"Ya ki ke aikin naki?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah"

"Ina ɗaya 'yar ta wa?"

Nabila ta ce "Ta na wurin aiki, ni ma zuwa nan ɗin faɗo mini kawai ya yi na taho"

Ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne, yaushe za ki kammala aikin ne, ki dawo ki zauna tare da ni, in dinga kallonki ina jin daɗi tare da ɗebe mini kewar jauhar"

"Baba ko na kammala, zan zo dai na ɗan yauta maka amma ba zan iya dawowa gidan nan na zauna ba, idan na dawo nan gaba ɗaya Abba fa?. Na zo ne na nemi bakin zaren saita tarwatsatsiyar alaƙar da cikinku babu wanda yayi tunanin gyarata duk a sanadiyyar hawa dokin zuciya da ku ka yi.
Baba, kai mahaifina ne, major kuma rayuwata ne, kuma ka san waye shi, a fannin tsatstsauran ra'ayi da kafiya, a wannan karon ya sake ɗaukar zafi da yin fushin da har ya nemi ko dai na rabu da kai, da shari'ar mijin jauhar, ko kuma babu ni babu shi, saboda ya na ganin jauhar ba ta samu kyakywar rayuwa daga gareka ba, ka aurar da ita ga ɗan daba, wanda ya yi ajalinta.
Tabbas na rayu dogon zamani, cike da muradin son sanin waye mahaifina, sai dai gaba ɗaya na sare, gwiwata ta yi sanyi, tun bayan da na saurari labarin abin da ya faru.
Sai dai hakan ba zai hanani sauke hakkina a matsayina na 'ya ba, yanzu warware mini wasu abubuwan, zai taimaka mini a kan shari'ar nan, kuma ya taimaka mini wurin wanke ka a wurin Abba. Dan Allah ka fahimce ni, ba wai ina fatan na ƙure ke ba ne ba, mafita nake nema,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login