Showing 192001 words to 195000 words out of 479911 words
a dalilina? Ba zan sake gangancin da na yi a baya ba, dole a saki liti, in dai kai kaina zai saka a sake shi"
"Is a minus case, dole zai fita, amma bama buƙatar a sake kama ka, ka gane mana, dole mu shirya ɗaukar fansar ka"
Viper ya sake kallon Walid ya ce "Sai na kashe yarinyar nan fa"
"Indabo yakamata ka kashe da Madaki, wani tunanin yakamata ka yi a kan wannan yarinyar ba wannan ba"
"Tarko aka yi mini da ita, ko ba ka gani?"
Walid ya girgiza kai ya ce "Haryanzu bamu da tababcin hakan, amma ba ka da wani sharhi ko tunani a kanta?"
"Babu, idan na sake ganinta kuma sai dai wata ba ita ba" ya bashi amsa kai tsaye.
"Shikenan, yanzu dai zan fita in ga me za ayi a sako mana liti".
Viper yayi shiru bai ce masa komai ba, sai da ya yinƙura zai tashi, Al'amin ya riƙe shi. Walid ya juyo ya kalleshi ya ce "Ina alƙawarin da ka yi mini?"
Walid ya ce "Ina sane, haryanzu kayan ba su sauka bane ba, ka san yanzu hanyar akwai tsaro sosai ba irin na da bane ba"
"Bani wanda ka kwashe ka fita"
Cikin damuwa walid ya ce "Wai dan mai zamani so ka ke yi sai ka haukace ne gaba ɗaya hankalinka zai kwanta, wannan uban ƙwayoyin da ka ke jibgaw kanka ba abun da suke yi maka, jikinka duk ya riga ya bujire, ka yi haƙuri mu bi a sannu"
"Mai laya.....
Walid ya ce "Mai zamani"
"Ka yi mini abun da nake so, ai na riga na daɗe da gama haukacewa, ka bani idan na cigaba da zubawa na san za su yi mini"
Walid ya girgiza kai ya ce "Da za su yi maka, da tuni sun yi, ka yi haƙuri ka bani lokaci"
Al'amin ya waro masa idanunsa ya ce "Ka fara kaini bango, baku san fa me nake ji ba, bana bacci, ƙwaƙwalwata so take ta tarwatse, sonake komai ya shafe daga cikin kaina, ko da hakan yana nufin zan haukace"
"Fansar ta ka fa"
"Zan ɗauka"
Walid ya yinƙura zai fice ya bar Al'amin, amma ya sake riƙe shi, Walid yana ƙoƙarin ƙwacewa, hakan ya ƙara tunzura Al'amin, ya fara ƙoƙarin shaƙe Walid.
Babu yadda Walid ya iya, duk da yadda Al'amin yake zuba wa kansa kayan maye, amma yafi ƙarfin sa, ya dunƙule hannu, ya daki jijiyar wuyan Al'amin, ya silale ya faɗi ƙasa.
Yayi sauri ya durƙusa a kansa, ya ga Al'amin yana ta ƙifta idanunsa, bai kai ga suman ba, jikinsa ya saki gaba ɗaya.
Walid ya dafe kai yayi shiru, abubuwa na neman su ƙwace musu, gashi alamu sun fara nuna ƙwaƙwalwar Al'amin na nema ta fara taɓuwa.
Ya dafa kafaɗar Al'amin ya ce "Ka ƙara bamu lokaci ɗan uwa, zamu kawo ƙarshen komai, da yardar Allah" ya tashi ya fice.
***
Abba da magajiya sai anty, su ne suka yi ta ɗawainiya da Nabila, har ta ɗan samun nutsuwa, take ta uban bacci, tana tsaka da baccin sumayya ta zo, dan jiya hankali a tashe ta kwana, ta jirata har ta gaji, taje can wurin aikinta an ba ta je ba, ta zo gida an ce ba ta zo ba, ga lambobinta ba sa shiga, ta din ga fargabar Allah ya sa ba su indabo ne suka yi mata wani abun ba, gashi suka din ga kiranta suna tambayarta ta gaya musu me suka tattauna da Nabila.
Yanayin da ta ga Nabila, ya tsoratata, gaba ɗaya kamar ba ita ba, duk ta yi wani iri.
Cikin ikon Allah ta farka daga nannauyan baccin da ya kwasheta, da sumayya ta fara tozali, cikin kulawa sumayya ta ce "Sannu" ta jinjina mata kai kawai.
Duk shegen surutu irin na Nabila, sai bakin ya mutu, ta kasa cewa kowa uffan.
Sai da suka kaɗaice, sannan sumayya ta ce "Nabila ki yi magana mana, meyafaru da ke? Kiran me ki ka yi mini kina so mu haɗu? Kuma na neme ki na rasa jiya, yau kuma na ganki a haka ko wani abun ne ya faru?"
Nabila ta ƙura mata ido, yanzu ita ta ina za ta fara yi wa Sumayya bayani ma, wataƙila idan ta bata labarin abun da ya faru ma ƙaryata ta zata yi, ta ce mata ba ta da hankali, ta san babu lallai ta bata goyon baya, a kan abun da take niyyar yi. Ba wannan ba shi kansa Nasir idan ya dawo, ta ina za ta bi ta warware mugun ƙullin da tayi, muddin ta yarda aka kama Viper a sanadinta, ta zama azzaluma duk da ba ta ji ƙarashen labarin ba, amma yin hakan shiga hakkinsa ne.
Sumayya duk yadda ta kaɗa ta raya, fafur Nabila taƙi cewa komai, hasali ma zancen zuci ta din ga yi taƙi kulata.
Abba ya din ga yi wa Nabila faɗan yawo ba ɗankwali, jin kaɗe-kaɗe da kuma yawan kwalliya.
Walida ta shigo da waya a hannunta, ta miƙawa Nabila ta ce "Gashi Yaya ne zai yi magana da ke"
Nabila ta girgiza mata kai, ba zata karɓa ba.
"Me zan ce masa to?"
Sumayya ta karɓi wayar suka gaisa da Nasir ta ce "Yaya mutuniyar jikin ba daɗi, taƙi magana ma gaba ɗaya, ka yi haƙuri ko zuwa anjima mu gani idan zata yi"
Ya ce "Shikenan, hanklina ne a tashe, ban ji ɗuriyarta ba ai, na sake kira anjima". Suka yi sallama ta kashe wayar.
***
Kwanaki kusan uku ramma na fama da jikinta, kafin ta ɗan ji ƙwari, a kwanaki ukun nan, Abdul bai kulata ba, zai dai ba ta abinci ya bata magani, sai a kwana na uku da ya ga yi ƙwari, har tana salla.
Tun da rana ta fara ganin take-takensa dan haka hanklinta ya ƙi kwanciya, da daddare ta kasa bacci sam, aikuwa kamar yadda ta yi tsammani, sai gashi ya shigo ɗakin, yana miƙa yan kallonta. Cikin hanzari ta tashi tsaye. Ya mayar da ƙofar ya rufe ya ce "Ina zaki ne?"
Ta hau ja da baya, ya nufota gadan-gadan kawai ta ciro wuƙar yanka fruit, ta ce "Wallahi ka taɓani sai na caka maka, sai na kasheka azzalumi mara imani kawai"
Ya ce "Ohh wow, in ajiyeki ina ciyar da ke, ki ɗauki wuƙa ki ce zaki kashe ni, ni da ki ka samu ban kashe ki ba? Dole na canza taku.
Ya danƙota sai ga wuƙar a hannunta, amma ta kasa yi masa komai da ita, ba ta wuƙar yake yi ba, ya fara ƙoƙarin yi mata abun da ya saba, taƙi sakin wuƙar, garin kokowar ƙwatar kanta ya yanke shi da wuƙar hannunsa. Sakin wuƙar ta yi ta ce "Na shiga uku" ya tsaya yana kallonta, hannunsa na zubar da jini.
Tayi sauri ta saka hannunta, ta danne wurin da yake ta zubar da jinin, ta ga hakan ba zai yi ba, ta kama rigar jikinta tana dannewa tana cewa "Ka yi haƙuri" ya ƙura mata ido, gaba ɗaya sai ta rikice.
"Ni zaki kashe ko?"
"A'a ba kasheka zan yi ba, sonake kawai ka ji tsoro ka ƙyaleni, ka yi haƙuri" ya fizge hannunsa ya fice, ta samu wuri ta zauna hankalinta rabi a tashe, rabi kuma tana gode wa Allah da ya saka ya ƙyaleta.
Nabila ta warware, sai dai gaba ɗaya walwalarta ta ragu sosai da sosai, ba ta iya bacci, tunaninta da lissafinta kawai yaya zata ɓullowa lamarin.
Ta sake ɗaukko wayarsa tana jujjuyawa, ta tuna abun da Walid ya ce mata "Sai dai ki je shi ya ƙarasa miki"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Dole zan je, zan neme shi, sai na ji ƙarshen labarin, for now dole na tsayar da aikin DSP, na kamo bakin zaren nan, dan gudun kar a haihu a ragaya.
Ranar monday ta kunna wayarta, ta shirya ta ce wurin aiki zata tafi, ana ta zancen Nasir zai dawo, sai dai ko a jikinta, dan ba ta shi take yi ba, ta shirya ta fice.
Da ƙafarta take ta tafiya, dan kar ta hau abun hawa tayi saurin zuwa wurin aiki, ba ta gama tunanin da take son yi ba, wataƙila ko za ta samu mafita a haka.
Kamar an ce ta waiwaya, ta ga wata baƙar mota, na ta bin ta sannu a hankali, tun da ta fito titi kuma ta ga motar, ta basar ta cigaba da tafiya, bayan wasu mintuna ta ƙara waiwayawa ta ga motar still tana bin ta.
Tsayawa tayi ta juya ta nufi motar, sai aka tsaya aka yi parking aka daina bin ta, glasses ɗin motar tint ne, dan haka ba ta ganin na ciki. Ta ƙarasa ta hau ƙwanƙwasa glass ɗin, amma ba a sauke ba.
Ta gaji ta tari abun hawa, ta tafi.
Ta shiga reception kenan, ta tarar da wasu matasan mata su biyu, a cikin tashin hankali.
Ba ta damu ba ta wuce su, ta tafi office ɗin ta, ta ajiye kayanta ta sake fita harabar wurin, ta gansu a tsaye suna kuka.
Har ta gota su ta dawo, ta kallesu ta ce "Lafiya kuwa?"
Ɗayar ta ce mata "sannu"
Nabila ta ce "Yauwwa meyafaru ne?"
"Dama babanmu aka yi wa sharri, an kai shi wurin 'yan sanda ma, wai kotu za a kai shi, an ce mu ɗaukar masa lawya mai zaman kansa, mun ji ba zamu iya ba, abun da tsada sosai"
Nabila ta ce "Sharrin me?"
"Gadi yake yi a wani gida, sai ɗan wan matar gidan ya yi wa mai aikinta fyaɗe ya gudu, su suka fara kaita asibiti, da shi mai wankin gidan, shi ne daga baya aka kama su, wai su ne suka yi mata"
Nabila ta yi shiru tana nazarin maganar ta kalli ɗayar ta ce "Yayata kin tabatta, ba na shiga case ɗin mutumin da ba shi da gaskiya, kar na yi bincike na tarar da saɓanin abun da ku ka gaya mini"
"Wallahi ba ƙarya muka yi miki ba"
Ta ce "Well, yanzu ina da tarin ayyuka a office ɗina, personally zan taimaka muku, ku zo gobe in Allah ya kaimu ƙarfe tara na safe, zamu je wurin mahaifin naku, na ga abun da zan iya yi a kai"
Godiya suka din ga yi mata, tamkar za su durƙusa mata, yanayinsu kawai ya nuna suna fama da matsin rayuwa.
Ta so haɗuwa da barrister Habib, amma bai shigo ba, ya tafi gudanar da wasu shari'oi dan haka ta zauna ta gudanar da nata ayyukan.
Sha biyu na cika, ta ɗauki jakarta ta fita, kiran Nasir ya shigo wayarta, kamar ta share, sai ta ɗaga tayi sallama.
"Barrister, kina office ne na biyo?"
"Ka dawo kenan?"
Ya ce "Eh ina cikin kano"
Nabila ta ce "No, zan yi wata shri'a ne, ka je gida ka huta na kusa dawowa nima" ba ta jira mai zai ce ba, ta saka wayar a Flight mode, ta tari abun hawa, ta nufi unguwar da Viper yake.
Ayshercool
08081012143
47
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Suna tafe a hanya, Nabila na ta saƙe-saƙe daban daban a cikin ranta, har suka iso dai-dai in da ta sauka wancan zuwan, ta sallami mai napep ɗin, ya din ga kallonta yana tunanin ita kuwa me za ta yi a irin wannan wurin haka ranar tsaka.
"Malam lafiya, ka tafi mana" ya ce "To, tafiyar zan yi" ya ja baburinsa ya tafi.
Sannu a hankali ta bi waccan hanyar da Walid ya bi da ita wancan karon, amma ta kasa gane hanyar da suka bi, balle ta gano gidan.
Ta din ga nausawa cikin wurin, tana bulayi, amma ko rabin gano hanyar ba ta yi ba, gashi ta fara gajiya ga rana tana yi.
Sosai take bulayi, tana sake nausawa wani wurin, amma sai ta ga ta ɓulla wani wurin daban.
"Ke baiwar Allah" ta ji muryar wani a bayanta, ta waiwayo tana kallon mutumin, sanye da uniform ka security.
"Me ki ke yi a nan wurin rana tsaka haka?"
Ta ce "Dan Allah malam wani gida nake nema"
Ya kalleta ya ce "Gida a nan kuma?"
Ta ce "Eh"
"Gida fa ki ka ce?"
"Eh wani ƙaramin gida ne, rannan na zo ma amma hanya ta ɓace mini" ya girgiza kai ya ce a'a babu wani gida a nan haka, duk kamfanunnunka ne, sai gonaki, can kuma idan ki ka bu dutse ne, daji zaki shiga dan haka babu wani gida a nan"
Nabila ta ce 'Malam akwai gida a nan haka, na je gidan fa"
Cikin tsawa ya ce "Ke babu wani gida a nan, ki bar wurin nan tun ban sakar miki karnuka ba, ko na kama ki na haɗaki da jami'an tsaro"
Ta ƙare masa kallo ta ce "Ni zaka saka a kama, na yi maka kama da ɓarauniya ne?"
Ya ce "To wa ya sani, yanzu ai ɓarayi ne kawai ɓata gari ba, kuma ba a goshi ake ganin ɓata garin ba, ta cigaba da ƙarewa wurin kallo, ba ta ga hanyar gidan ba" ta ja guntun tsaki ta juya ta fara tafiya, sai mamaki take yi, tabbas gidan a nan haka yake, amma ya aka yi haka ta faru?
Haka ta koma ba tare da ta gane wurin ba.
Tun daga haraba yake murmushi, kamar bakinsa zai yage, cikin ƙarfin hali ta ƙaƙalo murmushin ita ma, ta ƙarasa ta ce "Welcome home DSP" ya miƙa mata hannu, ta miƙa masa na ta suka gaisa ya ce "I really miss you barrister"
"Me too, ya aiki?"
"Aiki Alhamdilillah, daga shekranjiya zuwa yau duk ina cikin damuwa, an ce ba ki da lafiya, ba kya ɗaga wayata"
Ta ce "Ka san ni ɗin ce a lallaɓa, auren zamani, yau da lafiya gobe babu, bari na je na yi wanka na ci abinci"
Ya ce "Take your time, ki huta sosai zuwa yamma, zan je office ne, zan ga mutumin da aka kama, aka ce ya san in da Viper yake, kan na dawo ki bani abun da ki ka ce" dammm! Ƙirjinta ya buga, amma ta maze ta ce "Ok bye bye, sai ka dawo" ya ɗaga mata hannu ta shiga cikin gidan.
Sai yanzu ta tuna tayi alƙawarin gaya masa wani abu idan ya dawo, wanda dama wayar Viper take son ba shi, wanda a yanzu ko me za'ayi mata ba zata miƙa wayar nan ba, sai ta ji ƙarshen labarin nan.
Tana wanka tana zancen zuci, idan ta ce za ta yi wa Nasir bayani, ba ta da wata cikakkiyar hujja, da za ta sanya ya fuskanci in da ta dosa, kuma sai ta tonawa kanta asiri na cewa ta haɗu da Viper.
***
Ɓangaren ramma kuwa, tun da ta yanki Abdul da wuƙa, ba ta sake ganinsa ba, har gari ya waye, duk abun duniya ya ishe ta, wai ita ta yi wa mutum illa da wuƙa har ya zubar da jini.
'sai me, ke kin manta abubuwan da ya aikata miki?' wata zuciyar ta tambayeta.
'Duk da haka, da kuma na caka masa in da zai mutu fa?" Ta tambayi kanta.
Ta buɗe falon, ta fito da rigarsa sai towel da ta ɗaura, ta rufe jikinta da ɗan kwalin kayanta, ta fito falon ba kowa.
Solomon ya fito zai shirya abinci a kan dining, ta ce masa "Ina kwana?"
Cikin gurɓatacciyar hausarsa ya amsa mata, ta ce "Yana ina?" Yayi mata saroro ba ya jin hausa.
"Kai ba ka jin hausa ne? No hausa?" Ya jinjina mata kai tare da yin murmushi.
Hausa da turanci take haɗawa, tana tambayar sa ina wannan mutumin, mai gidan nan?"
Turancin nata ya bashi dariya, da turanci ya ce mata bai kwana a gida ba.
"Ina ya tafi?"
Ya ce "Ba a tambayarsa in da ya tafi" tayi ajiyar zuciya ta kalli, kwanukan abincin ta ce "Duk kai ka ke dafa wannan? A ina ka iya girki?"
Ya ce "Catering school na yi, tun ina ƙarami kuma, ina taimakawa mamana wurin yin girki, tana sayar da abinci"
Ramma ta ce "Ka san koko?"
Ya yi shiru yana kallonta, kwatanta masa ta shiga yi, yayi dariya ya ce "Pap" ta ce "Eh, shi ka din ga yi mini turancin ƙanana yadda zan gane"
Yayi dariya ya ce "Ai normal turanci ne, kawai dai pidging ne" a dai-dai lokacin Abdul ya shigo falon, ya tarar da ramma a tsaye, tana magana da solomon tana murmushi.
Wani abu ne ya tokare masa wuya, suka ɗago suna kallonsa, tana ganinsa ta haɗa fuska, ta din ga satar kallon hannunsa, da ya naɗe da bandeji.
"Solomon, yaushe na zama sa'anka da zan ajiye yarinya ka din ga hira da ita? Kai ka ajiyeta? So kuna shirya yadda za ta gudu kenan?" Da sauri solomon ya girgiza kai ya ce "Ba zan taɓa cin amanarka ba sir, abu ta tambayeni nake ba ta amsa"
"Babu ruwanka da ita, idan tambayar ce ta tambaye ni"
Ya jinjina kai. "Bar wurin nan" da sauri ya bar wurin.
Ya ƙarasa dining ɗin, zai zauna ramma ta tashi. "Zauna ina zaki je? Haɗa mini abinci in karya"
Cikin tsananin takaici take bin sa da ido. "Zaki haɗa mini, ko sai na turmusheki na yi breakfast ɗin da ke, 'yar dabar ƙauye kawai, ki na 'ya mace kina ɗaukar wuƙa".
"Ni ba 'yar daba ba ce ba, kare kaina nayi yinƙurin yi daga mugu irinka mara imani"
Ya ɗora ƙafarsa a kan dining ya ce "Na ji, haɗa mini, ko kuma wallahi na yi abun da na ce"
Tuni hawaye ya cika mata ido, ta haɗa masa tea, da doyar ta tura masa gabansa, ta tashi zata tafi ya riƙota, ya ɗaga mata hannunsa na dama, wanda a nan ta yanke shi, ya ce "Da wani hannun zan ci?" Ta tsaya tana kallonsa.
"Oya feed me, tun da kin riga kin yi wa hannun illa, idan ba haka ba kin san condition ɗin" babu kalar tsinuwa da zagin da ba ta yi masa a zuciyarta ba.
Cike da ƙwarewa a fannin iya rashin mutunci da bariki, haka yake haɗawa da hannun ta idan ta bashi a bakin, yana wani ƙare mata kallo. Sai ƙanƙame jikinta take yi, gaba ɗaya wani iri take jin ta.
Ya cinye doyar ya ce ta ƙara masa, a ranta ta ce "Shege jaki"
Lomar ƙarshe, ya riƙe hannunta, da yatsunta a bakinsa, kokowar ƙwacewa take yi, amma ya riƙe su a bakinsa yana yi mata kallon 'yan iska a cewarta. Ba ta san lokacin da ta dunƙule ɗaya hannun nata ta ɗirka masa duka a kafaɗarsa ba, ɗan dukan da babu in da ya je, ya saki yatsun yana murmushi, da ƙoƙarin tauna sauran doyar, wani irin mugun kallo take yi masa, tare da goge yatsunta a jikin rigar jikinta, ba ta fargaba ya