Showing 438001 words to 441000 words out of 479911 words

Chapter 147 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6174

yayi. Amma muddin ku ka ci gaba da takura mini, a kan rabuwa da rahama, zan bar gidan nan gaba ɗaya. Allah ne ya tashi kama ni, ya sanya na keta mata haddi ya jarrabe ni da son ta. Allah ne ha so ni da rahama, na haɗu da rahama, kuma shigowarta rayuwata ta zo mini da tarin alkhairi, ni duk abin da suka yi mini, ban ji haushi ba, domin kuwa ma sassauta mini suka yi, dan Allah ku bar ni na ji da zafin da zuciyata take yi mini dan Allah" yayi maganar yana haɗa hannayensa alamar magiya.

Har Mummy za ta yi magana, Indabo ya ɗaga mata hannu, Abdul ya wuce yana share hawaye, yana jin zuciyarsa na wani irin zafi saboda tuna wasu abubuwan.



*****
Viper ya tafi tare da Abbu ya duba ramma a asibiti. Abbu sun yi hira sosai, dan sai da hirar ta tuna masa da marigayiyya matarsa babbar su Viper zahra'u.

Abdul yana ta zarya a kan rahama, baya damuwa da shan ƙamshin da mama take yi masa, hatta medications ɗin ta, shi yake serving.
Duk abin da ake buƙata haka yake yi mata, baya nuna gazawa, dama yana zuwa mama ke bar musu ɗakin.

Ranar da Abbu ya zo duba ramma, Nabila ma tana nan, yana ankare da su daga ita har Viper, babu wanda yake kula wani, yayi musu shiru bai ce musu komai ba.

Sai da Ramma ta kwana biyar a asibiti, sannan Abdul ya yadda a sallameta, babu wani abu da yake damunta, ta samu sauƙi sosai da sosai.


Nabila na zaune a ɗakinta, a kan gado, ta baje takardu tana duddubawa tana nazarin shari'oin da take da su.
Abba yayi sallama a ɗakinta, ta amsa masa ta miƙe tana faɗin "Abba Allah ya sa ba laifi nayi ba?"

"Saboda kin saba da aikata laifuffuka ba" ta ɗan yi murmushi.

Ya zauna a gefen gadonsa ya ce "Maganganu ne da ni nake son mu yi" yayi maganar yana kallon jikin wardrobe ɗin ta, duk ta liƙe shi da hoton maciji da stickers na Viper.

Ta ce "To Abba ina jinka"

"Yanayin alaƙarki da ɗan uwanki Nasir, dan Allah ina son komai ya wuce, ba na son gabar da ku ke yi sam"

"Abba ba gaba nake da shi ba, kawai ika mamakin yadda ya din ga kware mini baya ne, yana haɗa ni da kai"

Major ya ce "Na sani Arfa, amma Nasir ba ƙashin yarwa bane, kin san kowane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, kuma abin da ya aikata shi ake kira da rauni, irin na ɗan Adam"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Haka ne"

"Yauwwa dan Allah ya wuce ki yi haƙuri"

"To Abba, in sha Allah ya wuce, Allah ya yafe mana baki ɗaya, yanzu ka yarda gaskiyar da ka tarbiyyantar da ni a kai a kanta nake dagewa, shiyasa wasu lokutan ake ganina kamar mara ji, ko mara ɗa'a ko"

Yayi dariya ya ce "Na yarda, Allah ya ci gaba da dafa miki"

Ta amsa da "Amin"

"Abu na gaba, babanki ya ce na gaya miki, An tsayar da ranar auren sisternki, ƙarshe watan nan, za a sake ɗaura aure, ta koma gidan tsohon mijinta, Alhaji mu'azzam"

Nabila cikin farinciki ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, na ji daɗi sosai da sosai nayi farinciki, Allah ya sanya musu albarka ya daidaita su" ya amsa da "Amin, to ke ya naki batun ne? Kin ce ba kya son yaron nan, babansa sai magiya yake yi yana roƙo, ga Sumayya mamanta ta yi mini magana, wani ya fito ya ce shi kuɗin aure zai kawo, ke kuma kin ja bakinki kin yi shiru, baban yaron nan ya damu lallai a ba wa ɗan sa ke"

Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Haryanzu Abbu bai haƙura ba? Wallahi ina jin nauyinsa sosai da sosai, amma ba zan iya auren Vi ba"

"Meye kuma vi?"

"Au Al'amin"

"Haryanzu yana shaye-shayen ne da harkar daba?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, ai yanzu soja ne, kuma yana zuwa asibitin ƙwaƙwalwa, duk ya rage yin wasu abubuwan, kawai dai ba na son sa ne"

"Ita kuma wallpaper ɗinki, da wannan liƙe-liƙen na ɗakinki, duk cikin tsanar ta sa ne?"

Cikin jin kunya ta ce "A'a Abba, kawai dai ina sakawa ne, a lokacin ina da hope na ganin na saka kotu ta wanke shi daga zargi"

Abba ya tashi ya ce "Gaskiya ne, to ni dai duk hukuncin da babanki ya yanke ba ni da ta cewa, tun da na ga shi ma yana yin yaron, ni na fita sai na dawo"

"A dawo lafiya"

"Allah ya sa"

*****
Rahila ta ɗaga hankalinta sosai, ganin da gaske Walid da ba shi da komai zai aura wa Shahida, babu irin zagin da ba ta yi wa shahida ba, amma tayi bore ta ce ba ta so, amma Shahida ta ce ita ta ji ta gani.

Abbu ya ce "Ke dama ban isa sa ke ba, Shahida kuwa 'ya ta ce, dan haka ina da ikon zartar da duk wani hukunci a kan ta, idan bai yi miki ba, zaki iya tattara kayanki ki ƙara gaba, dan albarkacin ta kawai ki ke ci ki ke zaune a gidan nan" haka suka yi faɗa kaca-kaca, ƙarshe Shahida sai komawa tayi cikin ɗaki tana kuka.

Da daddare da Viper ya je gidan, ya ga Shahida kamar ba ta walwala, yake tambayarta ko lafiya.

Cikin damuwa ta ce "Dan Allah yaya, ka roƙa mini Abbu, na ji ya ce saboda ni mama take zaune a cikin gidan nan, dan Allah ka ba shi haƙuri, na san tun ba yau ba, yana matuƙar haƙuri da ita, amma dan Allah yayi haƙuri, ba ta da cikakkiyar lafiya kuma idan ya rabu da ita, babu in da za ta je, dan Allah yayi haƙuri"

Viper ya ce "Kar ki damu, barazana yake yi mata, kin san shi da tausayi, da kuma fushi wasu lokutan, amma in sha Allah ba zai rabu da ita, duk a kan maganar aurenki ne ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Ba zigaki nake ki bijire mata ba, amma ki samu miji irin Walid, sai kin daɗe kina tonawa, tun da ki ka ga Abbu ya amince shi ma, ba mutumin banza bane ba"

Shahida ta ce "Haka ne Yaya, ni dan Allah ma ka yi masa magana, wai ba zai yadda a bashi aurena, kuma a bashi wurin zama ba, wai haya zai kama, kuma ya dage sai ya yi mini kayan lefe ko babu yawa. Naga ba ƙarfi ne da shi ba, kuma ni ina duk abin buƙata. Budurwa ce ni ba bazawara ba, amma yaƙi yadda"

"Muhsin bai yarda da gazawa ba, wannan wata aƙida ce da muke da ita, ko zamu yi a raina, mun fi son mu ƙoƙarta, amma ki kwantar da hankalinki, zan yi magana da shi in sha Allah, kuma da mun kammala shiri, ba jira zamu tsaya ba da an kawo kuɗin aure lokaci za a tsayar, duk abin da ki ke buƙata ki gaya mini"

Shahida ta amsa da "To yaya in sha Allah "

Wasa-wasa girma ya hau kan Viper, ɓangaren ramma shi ne, haka gidansu, ga liti ga Walid, kowa Viper.


Al'amin sai da ya fara tausayawa Abdul, Abdul bai furta a bashi ramma ba, amma yadda yake sintiri kullum a tafe, ya ƙara tabattar da gaisuwa yake gami da roƙon iri, a kan a bashi matarsa.

Ita kanta mama ta ɗan fara saukkowa, ta zuba musu ido. Dan kuwa duk da jaririn ya mutu, sai da ya yanka san da ya saya ya ce idan ta haihu za ayi mata amfani da shi.

Duk da kayan da take da su, sai da yayi mata sayayya fal, na kayan sakawa.

Ranar da ya kawo, ta din ga yi masa godiya, ya tambayeta, me take so ta karanta zai yi processing komawarta makaranta.

"Nurse nake son zama"

Yayi murmushi ya ce "Shikenan, sai mu ƙarfafi asibitocinmu, mu kula da su sosai da sosai, amma rahama zaki dawo gidana sai ki yi karatun?"

Ramma ta ce "Ai ka san wannan ba maganata ba ce ba, maganar mama ce da yaya Aminu, amma kuma idan na dawo gidanka ai ba zan samu yin karatun ba, an ce ba a ɗaukar masu ciki"

Abdul ya ce "No, sai mu yi planing zuwa lokacin da zaki kammala"

Ta ce "Anya kuwa, yadda ka ke son yara, kar in je ka canza shawara"

"Haba rahama, kin fi kowa sanin halina, ni ɗan Adam ne, amma ban fiye yi wa mutum ƙarya ba dan ya yarda da ni, duk son yarana dolena na jure, kema na ga na inganta rayuwarki na kafa ki"

"To ka bari yaya Aminu ya dawo, ya koma wurin aiki ne, amma ka fara yi wa Daddy magana tukuna"

"Waye daddyn?"

"Alhaji mu'azzam mana, ko da nayi aiki a gidansa, ai haka ake ce masa"

"To shikenan, zan yi masa magana in sha Allah, kin san za a mayar da aurensa da yayar Nabila Hafsa".

"Ai ban santa ba, ni lokacin anty Jidda na fara aiki a gidan"

Abdul ya ce "Ok haka ne, ta koma gida ma, wai sai ya saketa duk a kan case ɗin mu, ni kowa ya ƙarata, a bar mini matata kawai"

Tayi murmushi suka cigaba da hira.


Nabila sai da tayi ta rarrashin Hafsa, a kan tayi haƙuri ta koma gidan Alhaji mu'azzam, dan fafur cewa tayi ba ta sonsa.
Kasancewar duk ƙarshen wata, sai tayi sayayya taje ta gaida Baba, hakan ya saka sun shaƙu sosai da hafsa, sai dai sauran mutanen gidan babu ruwanta da su, idan aka cire saifu, shi ma suna gaisawa.

Tare suka ta shirye-shirye, Hafsa tana cewa ita babu wani gyara da zata yi, lokacin da aka yi na farin ma, bai yi mata amfani ba balle yanzu.
Amma Nabila da taimakon sumayya suka ce, sai ta yi gyara da da yanzu ba ɗaya bane ba, zamani ya riga ya canza.

A lokacin Shahida ma Walid ya kai kuɗin aure, kuma Hafsa ƙawar Shahida ce, kasancewar iyayensu aminai ne. Watanni biyar aka saka, saboda babu yadda Viper bai yi da Walid ba, ya dage ya ce shi sai yayi mata lefe ko yaya yake, kuma sai ya kama gida. Shi ba ruwansa da bazawara ce, ba zai so ace shi aurensa na fari, ace ya naɗe hannu komai sai dai ayi masa ba.
Viper ya ce masa ya gyara nasa gidan, su zauna sai ya din ga biyansa kuɗin hayar.
Walid ya ce "Ai sakankancewa zan yi, na san naka ne, idan ma ban biya hayar ba, ba zaka damu ba, kuma zan ta damuwa gidan zai din ga tuna mini ƙanwata Jauhar, kuma kai a ina zaka zauna, idan ka yi naka auren?"

Viper ya ce "Ina da wurin zama ai ni, ko ka ƙi, ina wani gidan, na ji ba zan saka maka hannu ba, ka gyara shi da kanka, kayi lefen, amma ba zaka kama haya ba gaskiya ba"

Da kyar Walid ya amince da hakan, sai dai Liti ya zage kamar kayan lefensa zai tara, kuma Nabila suke turawa kuɗi take haɗa kayan, ita kanta Shahidan ba ta san da haka ba"

Sai dai daga Hafsa har Shahida sun dawo daga rakiyar iyayensu, na shirmen bin bokaye, domin sun tabattar da ba hanya ce mai ɓullewa ba.

Kasancewar Sumayya na ta'amalli da mutane daban-daban, a dalilin harkar aikinta, ya sanya ta nemi lambar maman dr., Domin haɗawa Alhaji mu'azzam da kuma ango Walid amayarsa. Tun da ita mace duk in da take sai da gyara. Kuma masu iya magana suka ce, idan kana da kyau ka ƙara wanka.
A cikin wata gudan nan, ba ƙaramin kyau Hafsat tayi ba, sai sheƙi tayi gwanin sha'awa, duk da ba ta da jiki, amma maman dr. Ta tsatsota, ta cika tayi fam, tayi ƙiba dai-dai misali, amma duk lokacin da Alhaji mu'zzam ya zo sai sun yi faɗa. Gashi can gidansa uwargidansa ta sako shi a gaba a kan ya ce zai dawo da hafsa, rashin mutunci na yau daban na gobe daban, gaba ɗaya ta ƙaurace masa, yadda Jidda ma ta fita, so take ta rayu itakaɗai a gidanta, shi kuma ya ce bata isa ba, yana da wadata da lafiyar da zai auri mace fiye da ɗaya.
Ya din ga ganin tamkar ranaku ba sa sauri, duk lokacin da ya je wurinta, da kyar yake saita nutsuwarsa, saboda kyan da tayi, da wani irin sihirtaccen ƙamshi da take yi. (Domin gyara da kankaro naku mutuncin kuma a naku gidajen auren, ku garzaya ku tuntuɓi maman dr. Likktar mata domin kar ayi babu ku 07069711327)


Viper yana zaune yana duba status ɗin sa na waya, yana son ya halarci ɗaurin auren hafsa, dan haka yana saka ran ana idar da sallar asuba zai nufo Kano, duk da ɗaurin auren na azahar ne sai an saukko daga masallaci.

Status ɗin Nabila da ya yi muting ya shiga, na farko Addu'a ce, kamar yadda ya zame mata ɗabi'a, yawan sanya addu'oi da shot videos na malamai.
Na gaba kuma, videonta ne, an yi mata lalle ja da baƙi, sumayya tana cewa our dear barrister marasa galihu, jin ki yafi ganinki, our anti serious beb" ta kwaɓe fuska tana harar Sumayya.

Ɗaya Videon kuma, Ita da sumayya ne da amarya hafsa, da wasu daga cikin yayyen su mata.

Haushi ne ya kama shi, ya san wataƙila duk mazan da suke cikin wayarta sun ga status ɗin, doguwar riga ce a jikinta, ta ɗora mayafinta a kanta, shigarta decent amma shi abin da idonsa yake gani, gani yake kowama ya gani.

A irin fitinarta, duk abin da Hafsa take amfani da shi na gyara, sai ta ce sai ta sammata.

Nabila kuwa tana saurar tashar su Sumayya, At the same time tana chatting, Sumayya na shirye-shiryen rufe tashar, ta fara sanar da ɗaurin auren hafsa, sannan ta ambaci na Nabila da Al'amin, a babban masallacin juma'a na BUK wanda za a ɗaura bayan an idar da sallar juma'a.


Ayshercool
08081012143

105
Miƙewa Nabila ta yi tsaye, tana tunanin kamar ba ta ji sosai ba.

"Wane irin wasan banza ne haka sumayya take yi mini?" Tayi maganar tana mamaki.

Wayar Sumayyan ta hau kira, amma wayarta a kashe, jikinta na rawa ta fito falo, amma ta tarar kowa ya kwanta, ko ina a rufe.

Ta koma ta hau kiran Umman Sumayya, amma ita ma ta ta wayar a kashe.

Ta saka wa zuciyarta zolaya ce kawai Sumayya take yi mata, dan tun da aka yi musu lallae take cewa tayi kyau kamar ranar tarewa a gidan Viper.

Sai dai wannan ya wuce wasa, ta rasa meyakamata tayi, ta din ga fatan Allah ya sa mafarki ne ba gaske ba.

Gaba ɗaya ta kasa bacci, sai dai yadda ta kasa baccin nan, haka Nasir ya kasa, da yayi juyi ya kalli invitation ɗin auren Nabila, sai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, cike da baƙin ciki da damuwa.

Ya so Nabila tun tana 'yar ƙarama, tun tana yawo ba riga, ba ta san ciwon kanta ba, yana matuƙar tausayinta, yana taya major ƙaunarta, saboda maraicinta, ga rashin lafiya ga kuma ƙiyayyar da mutanen gida suke yi mata.
Wahalarta babu wadda bai sha ba, kaita makaranta, yawon visiting kaita Asibiti idan Major baya nan, duk wata gudunmawa da ya san zai iya bayarwa domin ta ji daɗi yana yin su.
Duk rashin jin ta da karaɗinta baya damunsa, babban burnsa ya ganta tana cikin faranciki, mussaman idan yayi la'akari da hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da suka yi magana a kan kula da maraya, idan ya tuna mamanta ta rasu, ba ta san waye babanta ba, sai matsanancin tausayinsa ya ƙara shigarta.

Bayan Major ba ta da wasu da yadda da su take ƙaunar su, sama da shi da Sumayya, koma Yaya Nasir ko Sumayya, duk wata wauta da taɓara da zata yi, baya gajiya, da hakan matsanancin son ta ya shiga ransa, sai dai mama ta riga tayi masa kandagarki da Allah ya isa a kan Nabila, tsawon lokacin nan baya iya kula kowacce mace, saboda Nabila, sai dai duk wannan son da yake yi mata, lokaci ɗaya kuɗi suka rufe masa ido, ya tafka mummunan kuskuren da ya rushe waccan kyakkyawar alaƙar da take tsakaninsu, har ta kai tana yi masa kallon maƙiyinta a yanzu.

Da Asuba Viper ya nufo Kano, Abbu ya kira shi a waya, suka gaisa ya ce "Ka taho ɗin ne, zaka halarci ɗaurin auren?"

"Eh in sha Allah Abbu, ai ina hanya ma, na biyo sojoji mun taho"

"Akwai kuɗi a wurinka ne?"

Viper ya ce "Eh, amma kamar nawa?"

Abbu ya ce "Dubu ɗari biyu"

"Eh ba za a rasa ba"

"To da ka dawo ka taho gida da kuɗin, ina son ganinka"

"To in sha Allah, ina nan tafe"

"Allah ya kawo mini kai lafiya"

Viper ya yi murmushi ya ajiye wayar.

Sai dai babu daɗewa Walid ma ya kira shi, ya ɗaga ya ce "Mazaje ya ne?"

Walid ya ce "Mai zamani"

"Mai laya?"

"Za ka zo ɗaurin auren yayar Nabila ne?"

"Eh in sha Allah"

Walid ya ce "To ka yi sauri"

"Me zaka bani, ba sai bayan juma'a ne ɗaurin auren ba?"

"Eh kawai dai ka yi sauri"

Viper ya ce "To aiko mini da fuka-fukai na tashi sama"

Walid ya yi dariya ya ce "To in dai zaka yi sauri ai shikenan"



*****

Wayewar garin Allah, Ana idar da sallar asuba, Nabila ta tafi ɗakin Abba, ta tarar bai ma dawo daga masallaci ba, ta samu wuri ta zauna tana jiran dawowarsa.

Yana yin sallama ta tashi tsaye, ta ce "Abba, ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?"

"Abba ni fa ban yi bacci ba, Sumayya ce ta yi mini wani wasan banza da ya ɗaga mini hankali, wallahi ido biyu na kwana cikin zullumi da fargaba, na zata mafarki ne ma zan farka, amma dai na ga gaske ne"

Ya zauna yana faɗin "Subhanallah, wane irin wasa ne haka, da ya hana barrister bacci?"

"Ɗaurin auren hafsa ta sanar, kuma sai na ji ta faɗi sunana da na Viper, wai za a ɗaura mana aure"

Major ya ce "Ikon Allah, kuma kin kira wayarta?"

Ta ce "N kirata wayar a kashe, na kira ta Umma ma, amma ba ta shiga duka"

Abba ya jinjina kai ya ce "Abin da mamaki gaskiya, bai kamata ta yi miki wannan wasan ba gaskiya, amma ki je ki samu ki yi bacci, na san da wasa take yi miki, wurin ƙarfe goma sai ki shirya ki tafi can gidan naku wurin bikin, na ji Antynki da su Magajiya duk suma za su je"

Ta ce "To Abba" sai ta ji ƙwarin gwiwa, ta je ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login