Showing 456001 words to 459000 words out of 479911 words
ba.
A zaman jinyar shi da ta yi sun ƙara shaƙuwa sosai, kuma ta rage jin kunyar shi, amma a yau da suka dawo gida za su kwana su kaɗai sai komai ya dawo mata sabo fil, musamman yadda yake ta rawar ƙafa a kanta, ta san mai ƙwatar ta sai Allah, dan ta fara ganin saɓanin abin da take tunani. Har za ta kwanta sai ta fasa ta zura hijabi ta fita parlour, ta san bai sha magungunansa ba, kuma idan ba ita ta ba shi ba bai zama lallai ya sha ba, dan tun da Allah ya sa ya daina shan ƙwayoyi, yake adawa da su, ko da kuwa ba shi da lafiya ne, ko warin magani ba ya so.
Tana fita shi ma yana fitowa daga ɗakin da yake facing nata, da sauri ta juya masa baya ganin daga shi sai gajeren wando ko singlet babu a jikinsa. Jin takunsa yana nufo ta ya sa ta yi ƙoƙarin komawa ɗakin a hanzarce, amma haƙanta bai cimma ruwa ba don cak ta ji ya ɗaga ta bayan ya damƙe ta. A ɗimauce tana zaro ido ta ce. "Na shiga uku! Don Allah ka yi haƙuri ka sauke ni, ka ga ba ka da lafiya kar ka fama ciwonka." Bai ce mata komai ba ya fara tafiya, ba ta da zaɓi wanda ya wuce ta riƙe shi don kar ta faɗi, hannunta ta sakala ta wuyansa ta zagaye bayansa da shi ta ƙanƙame shi, kamar bai ɗauki komai ba.
A tsakiyar parlourn ya zaunar da su tare da faɗin. "Ana so ana kaiwa kasuwa." Ɓata fuska ta yi tare da kawar da kanta ta ce. "Please Vi ka je ka saka riga kar sanyi ya shige ka." Karan hancinta ya ja tare da faɗin. "Na faɗa miki ni zafi nake ji, kin ƙi mun maganinsa ke kuma." A shagwaɓe ta ce. "To ai ni ban san wane irin zafi ne wannan ba, ga sanyin A.C amma idan kana so sai na yi maka firfita har ka yi bacci, ka yarda?" Gyaɗa mata kai ya yi tare da janyo ledar da ke gabansa, har lokacin tana jikinsa ya ƙi barin ta, ta tashi kamar yadda take ta ƙoƙari. Tun kafin ya buɗe ƙamshin ya daki hancinta, ya ware ya ɗauko yankan naman kazar ɗaya ya kai bakinta tare da faɗin. "Yau da kaina zan ba ki, tunda wancan karon ƙin ci ki ka yi, saboda ba kya so na, yanzu kuwa tun da zan kwana ina shan iskar fifitar da za ki mun, sai na baki da kaina." Murmushi ta yi cikin mamakin sabuwar lallaɓawar da yake yi mata ta buɗe bakin ya zira mata.
Shi ya yi ta ba ta a baki har ta ƙoshi, da ta ce ya ci sai ya ƙi ya ce shi ya ƙoshi, da ma tata ce ya siyo mata. Wani kallo ta yi masa ta ce. "Yaushe ma ka fita ka siyo?" Ya ce. "Order na yi aka kawo har gida." Ba ta kuma magana ba ta tattara ragowar ta kai kitchen, ta dawo ta gyara gurin.
Har lokacin yana zaune yana ta aikin kallon ta tana ta fama da hijabi, kamar mai takaba.
So take ta gudu ɗaki ta bar shi amma zuciyarta ta ƙi yarda da hakan, musamman a halin da yake ciki na rashin lafiya. Kusa da shi ya nuna mata ya ce ta zauna su yi magana, ba ta yi musu ba ta zauna, tare da tattara hankalinta wuri guda.
"Wai wannan hijabin na mene kamar wata mai takaba?"
Ido ta juya masa ta ce. "Sanyi nake ji ne."
"Ni ina jin zafi ke kuma kina jin sanyi, sammun naki na sammiki nawa sai duk mu daina ji." Ya yi maganar tare da cire hijabin ya ajiye a gefe. Dogon gashinta ya bayyana kasancewar babu dankwali a kanta. Idanunsa akan inda ya fi yawan takurawa da kallo a jikinta ya kai hannunsa ya fara shafa gashin a hankali, yadda gashin jauhar yake, mara yawa sai tsayi haka na Nabila yake, kuma ba baƙi ne ƙirin ba. Da sauri ta juya masa baya ta ce. "Ka daina ba ni kunya don Allah."
Ya ce "Ni fa ba wannan Nabilar na sani ba, a dawo mini da ta bayana mara tsoro da kunya, mai kallon cikin idanuwana, tana gasa mini magana yadda ta ga dama." Ya faɗa yana leƙa fuskarta.
Cikin rigima ta ce. "Kana nufin ban da kunya kenan ni mara kunya ce?"
Hannunsa ya zura a inda ba ta taɓa tsammani ba ya ce. "Mara kunyar dai nake son ki zama." Cikin ƙunƙuni na ce. "Kamar yadda ka zama ba."
"Oush!" Ya faɗa yana yarfe hannuwa. "Mene ne? Me ya faru?" Kafaɗarsa ya nuna mata bai ce komai ba.
A ruɗe ta ce. "Ciwo take maka? Ko ka fama ciwon ne?" Yamutsa fuska ya yi ya ce. "Har cikin ma duk suna mun ciwo." Yayi maganar yana nuna side ɗin cikin sa na dama.
Ba ta san lokacin da ta janyo shi jikinta ta fara shafa fatar bayansa cikin rarrashi ba, kamar za ta yi kuka ta ce. "Sannu, ko mu koma asibitin ne? Dama fa baka gama samun sauƙi ba ka ce, sai mun dawo gida" Girgiza mata kai ya yi yana ƙara shigewa jikinta. Cikin kulawa da tausayawa ta shafa kansa ta ce. "Bari na ɗauko magungunan ka sha to, sai mu je ka kwanta."
Kamar ƙwai haka ta dinga lallaɓa shi, shi kuma yana ƙara narkewa kamar gaske, ya ce mata nan da zafi can yana yi masa ciwo, har da hawayenta saboda tausayin shi.
Tare suka koma ɗakinta yana manne da ita, ta buɗe jakarta, ta ɗaukko ledar magungunan, ta din ga bashi ɗaya bayan ɗaya yana sha yana yamutsa fuska, ta rage haske ta lulluɓa masa bargon da yake kan gadon. Sai sannu take yi masa duk ta ruɗa kanta, ko kadan tunaninta bai kawo wayo yake yi mata ba, saboda duk lokacin da aka buɗe raunin za ayi masa dressing sai ta tausaya masa, saboda ramin da wurin yayi.
Sai da ta gama raɓe-raɓenta, ta din ga kai komo tsakanin ɗakin da falo, sai da tayi tunanin ya yi bacci, sannan taje ta raɓa ta kwanta, kamar mai hawa kan wuta, cike da matsanancin tsoro.
Shikam idonsa biyu, sai da ya tabbatar ta saki jikinta sosai yadda yake so sannan ya fara gudanar da ƙudurinsa. A firgice ta janye jikinta daga nasa, cikin rawar murya ta ce. "Vi rashin lafiyar kenan? Kana buƙatar bacci, ka kwanta ka yi Please." Ƙara janyo ta ya yi cikin wata irin murya ya ce. "Ni fa na warke, taki rashin lafiyar kawai nake yi." A tsorace na ce. "To ni ban da lafiyar ka ƙyale ni."
"A'a Abla, kar mu yi haka da ke, kar ki yi mini haka, kwana talatin da wani abu da aurenmu, kar mu yi haka da ke please"
Cikin rauni da tsoro ta ce "Ni dai a'a bana so." Ta faɗa cikin kuka, don sosai wani irin tsoro yake ƙara lulluɓe ta.
Tsayawa ya yi da abin da yake ya mayar da bakinsa kan kunnenta ya shiga hura mata iska, a hankali ta ji ta fara samun nutsuwa, ajiyar zuciya ta sauke ta koma hannunsa ta riƙe.
Jauhar ce ta shiga kai komo a cikin kwanyarsa, baiwar Allah babu sawa babu fitarwa, babu gardamar tsiya kamar Nabila.
"Abla" ya kira sunanta a hankali.
"Na'am"
"Amma ina alkawarin firfitar?"
Ta ce"Yana nan, sai ka yi bacci zan yi maka."
"Ba zan iya baccin ba ai"
Juyawa ta yi suna kallon juna ta ce. "Wai wacce irin iska ce wannan, ni fa kana ta sa ni a duhu." Yana shafa gefen wuyanta ya ce. "Shi yasa nake so na fito da ke haske amma kin ƙi.
"Vi"
"Mmm"
"Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga ni marainiya ce"
Ya ce "Menene haɗin aurena da maraicinki, nima marayan ne ai, sai fa na dangana da birnin tarayya"
"Wace birnin tarayyar kuma?"
Duk yadda ta so ƙwace kanta amma ta kasa, bisa tilas ta haƙura ta bar shi ya yi yadda yake so.
Sai dai jin abun nasa na gaske ne ya sa ta dawo hayyacinta ta saka masa kuka tare da doguwar magiya kamar wanda zai zari ranta.
Fuskarta da ta yi kaca-kaca da hawaye ya ƙura wa ido ta ɗan gutun hasken da ya rage a ɗakin yana jinjina taurin kai da tarin rigimarta, Jauhar ɗinsa mai sauƙin kai ce ta faɗo masa a rai, salihar baiwa kenan da sauri ya kawar da tunaninta, saboda alƙawarin da ya daukar wa kansa a wannan fagen ba zai taɓa yi wa Nabila maganarta ko ya yabe ta ba, a karan kansa ya ji duk da ƴar'uwarta ce amma ba za ta taɓa jin daɗi ba idan ya aikata hakan. Ba ya kuma so ta dinga jin haushin ta ko ta dinga kishinta kamar yadda ta ce masa yana sakawa ta ji a ranta. Amma da tabbas sai ya furta, ya yabawa yar madara.
Duk iya ƙoƙarinsa na ganin ya riƙe kansa amma ya kasa, juriyar da ya yi shekaru yana yi ya kasa yin ta a dare ɗaya, sosai yake da buƙatar iskar da ya yi shekaru bai shaƙe ta ba.
Sai da ya samu ɗin kuwa a daren ya samu sukuni, abin ya zo wa uwar gayyar a bazata.
Ƙarshen gadon ta koma tana sheshaheƙar kuka tare da takure kanta guri ɗaya, shiru ya yi yana sauraren ta, bai yi yunƙurin rarrashin ta ba.
Yadda ya tsallake Jauhar, bayan ya gama abin da Allah ya nufe shi da yi, saboda wata banzar poster indabo, Walid ya tafi neman magana, sai wani takaici ya mamaye zuciyar sa.
Wai yau shi ne zai je shimfiɗar aurensa, ya ɗauki wanka ya sha turare.
Wanda lokacin 'yar madara, wata ran da ƙaurin hayaƙinsa da komai idan ya dawo daga gantalinsa, komai dare wataran ma a buge, haka zai haye mata gado yana basarwa, shi a yi abin da yake so kawai. Daga baya sai ta dinga zama sai ta jira shi ya gama yawon ya dawo, ta lallaɓa shi cikin hikima, ta ce ita zai yi wa wankan, tun da ita ta saba wanka ba yau ba gobe kamar macen kunkuru kamar yadda yake faɗa.
Da haka zata lallaɓa shi, su yi brush ayi wanka a shafa turare, daga nan idan tana da wani ɗan abin kusa da bakan ta bashi, ba ta taɓa yi masa magana ba, a hankali kuma ya gane yake jin daɗin hakan, ya zamana ko ba ta saka shi ba, zai yi abin sa ya shafa turare sannan ya zo in da take.
Duk ranar da ta hana shi shan wani abu, ya je ya sha, sai ta sunsuna bakinsa, idan ta ji ƙauri, ranar ba zata saurare shi ba, sai dai yayi raragefensa ya gama. Jauhar ita ta mayar da shi ɗan gayu.
Kukan Abla ne ya dawo da shi hayyacinsa, da ta shafe lokaci tana yi, ba tare da ta gaji ba.
Ya mirgina kusa da ita ya yi ƙasa da bargon da ta lulluɓa har kanta. Cikin wani irin nishaɗi da ya cika masa zuciya haɗe da alhini ya ce. "Ablan Vi." Yadda ya yi maganar ya sa ta hadiye sauran kukan nata na zallar shagwaɓa ba tare da ta shirya ba.
"Kukan ya isa haka idan kuma ba ki gaji ba to."
Ya faɗa yana kwantar da kanta a kan ƙirjinsa, tare da bubbuga bayanta cikin rarrashi.
Baki ta tura tare da ƙara shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, rarrashin take buƙata da ma.
Tarairaya da kulawa kala-kala ya dinga nuna mata a daren tare da wata irin soyayya mai tsayawa a rai da wuyar mantawa, ita kuma ta dinga yi masa taɓara iri-iri.
Bayan sun yi wanka ta koma bacci, shi kuma ya jima ya kasa baccin, ya din ga jin tamkar ya aikata wani zunubi mai nauyin gaske, yau shi ne da wata macen daban, ba 'yar madararsa ba.
Duk zalama da ƙulafucin namiji da mace sama da ɗaya, bai taɓa jin haɗa jauhar da wata mace ba, amma Nabila wani sashi ce na jauhar, shiyasa ya bata wani gurbi a zuciyarsa, son Nabila son Jauhar ne, duk da ba ta raye.
Tabbas ya san ban da Nabila ya aura, babu wata mace da zata iya zama da shi, a hakan ma ya san Nabila na matuƙar ƙoƙarin yaƙi da zuciyarta a kan Jauhar, shi dai duk wanda zai zauna da shi, to dole ya so Jauhar, ko su raba gari, haryanzu babu mace mafi ƙololuwar daraja a ransa bayan mahaifiyarsa sai jauhar, ko mahaifiyarsa, ba ta yi masa tarbiyyar da jauhar ta yi masa ba.
A hankali ya furta "I miss you 'yar madara, may your gentle soul, rest in jannatul firdausi, may Allah subhanahu wata'ala grant you a highest rank in Janna" ya furta a hankali yana dafe saitin zuciyarsa, kamar yadda ya kan faru mafi yawan lokuta idan har ya tuna ta.
Ganin ya kasa baccin, ya sanya ya tashi ya sake ɗauro alwala ya koma ɗaya ɗakin ya tayar da salla.
Ya daɗe a sujuda, kawai yana nema mata gafarar Allah da rahamarsa, bai gushe ba idanunsa na zubar da hawaye, alkhairanta, na ci gaba da kai komo a cikin zuciyarsa.
Sai da ya idar ya gabatar da sauran addu'oi, na neman tsari, da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali a musayar da Allah ya yi masa.
Ya idar yayi shiru a kan dardumar, yana tunanin Jauhar kamar wata walƙiya ce, ko flashing da ta shigo rayuwarsa, dan kawai ta haska masa wasu abubuwa ta ɓace.
Ya daɗe a zaune, sannan ya tashi ya koma ɗaki ya kwanta.
Sai daf da Asuba bacci ya ɗauke shi, mafarki yayi gashi zaune a falo, Nabila na kujerar da take facing ɗin sa, suna ta hira cikin nishaɗi, sai ga Jauhar ta shigo, tana ta ƙamshin turaren da duk in da ya ji shi, sai ya yi tunanin zai ganta.
Ta zuba musu ruwa a kofuna, ta zauna a kusa da Nabila, tana kallon yadda Nabila ke magana cikin nishaɗi.
Murmushi take yi tana kallon Nabila, shi kuma yayi shiru yana bin Jauhar da kallo.
Da alama Nabila ba ta ganin Jauhar, amma jauhar sai kallon Nabilan take tana murmushi, alamar tana jin daɗin yadda Nabila ke cikin fara'a.
Viper take nuna wa Nabila tana murmushi.
"Vi an kusa idar da salla fa" muryar Nabila ta tashe shi.
A gida ya yi sallar asuba saboda ya makara, ita kuwa da ƙyar ya samu ta tashi ta yi sallar ta koma bacci.
Shi ma baccin yayi, saboda jiya bai samu isasshen bacci ba.
Naja'atu Bunkure kuwa tuni ta gurfana a gaban kuliya, bisa tarin zarge-zarge da ake yi mata. Ba ita kaɗai ba har da wasu daga cikin maƙarabbanta, da suka din ga gudanar da bunkure foundation.
Ta musanta tuhume-tuhumen da aka yi mata, kuma lauyoyinta suka nemi a bayar da belinta, amma fafur alƙalin nan yaƙi, ya aike da ita gidan gyaran tarbiyya da kuma gyaran hali, wato gidan yari.
Abin ya girmameta, tamkar zata zare ta haukace, wai yau ita ce, da ikonta da izzarta, aka aike da ita gidan kurku.
Babu alamar Indabo zai zo ya fitar da ita, haka aka sakata a cikin masu laifi.
Kamar mahaukaciya haka ta zama, tana tuna irin furucin da Nabila ta yi mata, ta tabbata sai da ta kaita ƙasa ta ga bayanta tukuna.
Wani irin abu mai tsananin ɗaci ta haɗiye ta ce "Kuskure mafi girma da muni, da Indabo zai tafka, shi ne watsar da ni ya wanke kansa, ya zame ya bar ni. Wallahi muddin haka ta tabatta, ko kurkukun bayan duniya aka kai ni, sai na yi maganinsa, ni zan kawo ƙarshen sa, ƙarshe mai muni da ban tsoro, ni ce dai-dai da kai Indabo, mu zuba mu gani, sai dai ayi mutuwar kasko".
Nabila ta riga Viper tashi, ta tafi ɗaya ɗakin, tayi wanka, dan kar ta dame shi da ɓuruntu ya tashi.
Ta shiga kitchen ta duba abin da yake akwai na girki, ta fara ƙoƙarin sarrafawa, ta dawo falo ta cigaba da karkaɗe karkaɗe.
Ta gama ta koma ɗaya bedroom ɗin, shi ma tana sake gyarawa, a nan ta ci karo da manyan frames, na hoton Viper da jauhar.
A hankali ta ɗauki ɗaya daga ciki tana gogewa, babu wanda zai ce ba ita ce a jiki ba.
Ta zubawa hoton ido, har ya shigo ba ta sani ba, sai daga baya ta razana jin motsi a bayanta.
"Me ki ke yi da wannan hoton, ki kula kar ki fasa mini hoto"
A sanyaye ta ce "Kallonta kawai nake yi"
"Ki na sonta ne" da sauri ta kalleshi ta ce "So kai, wallahi har cikin zuciyata nake jin matsananciyar ƙaunarta, haryanzu ina jin zafi da ɗacin rashin saninta a rayuwata, da tare muka tashi babu lallai na zama masifaffiya ko?" Tayi maganar tana kallonsa.
Dariya ya yi ya ce "Ai ke faɗa da tsiwa a jininki yake, ita kuma wannan haƙuri da kawaici ne a jininta, amma da ni da ita wa ki ka fi so?"
Ta nuna masa hoton jauhar, ya saka hannu ya karɓi hoton ya ce "Nima ita na fi so"
A sanyaye ta ce "Ko baka faɗa ba na sani, amma Vi dan Allah ba cin amana ne abin nan ba, haryanzu na kasa samun nutsuwa da auren nan, idan ina tuna wahalar da ta sha, sai na ga kamar na ci amanarta, da na fara sonka har na aureka" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye.
Ya rungumota jikinsa ya ce "Idan mafarkin da nayi gaskiya ne, to Jauhar tana murna da aurena da ke, kuma ta ji daɗin ganinki cikin farinciki"
"Vi"
"Mmm"
"Na san ba zan iya zama jauhar ba, ba kuma zan taɓa kamota ba, ba zan taɓa haɗa matsayina da nata a wurnka ba, amma dan Allah ko babu yawa ka sama mini space a zuciyarka, kar maraicin yayi mini yawa"
Wani irin tausayinta ya mamaye zuciyar sa ya ce "Ki na da naki space ɗin, ba zan bari maraici ya ci gaba da damunki ba, zan yi occupying spaces ɗin da suke cikin rayuwarki in sha Allah my abla"
A hankali ta yi ajiyar zuciya ta ce "Na gode sosai da sosai Vi, Allah ya bamu zaman lafiya"
Ya ce "Amin, yauwwa yakamata na yi comment akan fankar jiya, ita ma sanyinta ya yi, ba mai cutarwa ba ne ba"
Ƙwacewa ta yi daga