Showing 162001 words to 165000 words out of 479911 words
ba zan manta da su yaya walid ba, duk da suna taimakawa wurin ƙara ingizaka a shaye-shaye, amma sun tsaya tare da ni a lokacin da kow yake ganin idan ya taimaka mini zai kwana a ciki"
Ya ce "Allah sarki 'yar madara, ba na son in ga kina kukan nan ne, ko kina yi wa 'yan sanda magana, suna wani yanƙwana mini ke, raina ɓaci yake yi shiyasa na ce kar a sake kawo ki".
Ta ce "Gashi ya wuce, duk da lokacin gani nake kamar ba zai wuce ɗin ba"
Ta tashi ta shiga ɗaki, ta dawo ta tarar da robar alawar madarar da take sayarwa, a gefensa bakinsa kuma yana ta tauna, ta ɗaga robar ta ce "Alawata ka ke sha ko?"
"Eh, ta guda uku na sha sittin, a rage mini naira goma hamsin kenan"
Sororo take kallonsa, "To ai ba a jikina ake tatso madarar ba, da zan sayar da ita ashirin ashirin, naira hamsin ce fa duk ɗaya "
Ya waro ido ya ce "Ki ji tsoron Allah, har na sha ta ɗari da hamsin, gaskiya saba'in zan bayar".
Abun da yake so ya gani ɗin ta fara, shagwaɓa tana cewa sai ya biya ta.
"Gaskiya bani da kuɗi yanzu, zo ki shanye abarki" ya fito mata da harshen sa.
Ta harare shi ta ce "Bana so, kuma idan na zo yi maka wanki na tsinci kuɗi, sun zama nawa"
"Eh ai dama kin saba kwashe mini 'yan canjina, da kayan cajina shiyasa ki ke yi mini wanki ba dan Allah ki ke yi ba" ya tashi kamar zai tafi, amma ya riƙeta, yayi kissing ɗin ta, ya ce "To kin ga tare muka shanye, yanzu talatin ma zan baki" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya ɗora mata a wuyanta ya ce "Gashi nan, uwar son kuɗi"
"Ai talatin ka ce zaka bani, saura dubu ɗaya, dubu uku yakamata ka bani"
Ya ce "Biyoni ɗaki ki karɓa"
Ta ce "A'a na yafe maka sauran, amma kar ka sake"
Sosai wani bond mai ƙarfin gaske ya shiga tsakaninta da shi, har mamakinsa take yi, duk da mai hali baya fasawa, idan miskilancinsa ya motsa, ko kuma ya cake, ba ya sarrafuwa ta daɗi, amma haka take jurewa. Ga babban abun da yake ci mata tuwo a ƙwarya yanzu, wasu lokutan idan ya dawo daga shaye-shayen sa, da ƙaurinsa da komai yake zuwar mata, gashi ba abu ne mai sauƙi ba, ta nuna masa hakan ba, dole sai ta cikin hikima da dabara.
Haka zata zauna, komai daren da zai yi sai ta jira dawowarsa, ta saka shi yayi wanka, ya canza kaya.
Yau bayan ya bar ɗakinta, bayan ta idar da salla ta je ta same shi, a zaune a kan katifa.
Ta ɗauki kwalin sigarin gabansa, ta ciro guda uku ta bashi ta ce "Wannan ta isa, kar a sha sama da haka dan Allah"
"Bani in je ƙofar gida in sha"
Ta ce "A'a ai shan nake so ka rage sosai da sosai, wannan ta isa"
Ya juya mata baya ya shanye, tana zaune tana jiransa, ta bubbuɗe window, saboda hayaƙin ya fita.
Jira yake ta fita ya kuma kunna wata, amma ta cire masa shirt ɗin jikinsa, ta ce ya kwanta, ya kwanta yana jiran ta fita, amma ta kwanta a jikinsa, a hankali ta din ga karanto azkar ɗin safiya.
Babbar salla na ta ƙaratowa, jauhar hada-hadar neman kuɗi, ta cigaba da kankama, Al'amin bai taɓa saka ido a kan abun da take samu ba, dan yanzu iya ƙoƙarin sa yake yi, ya yi cefanensa, duk da kuɗin da take ɗan samu, in dai ya ji kuɗi a jikinsa, a kaso ɗari tamanin, ita zai kashewa, bai fi ya ƙarar da kaso ashirin ba, goma ya rabar goma ya yi shaye-shaye.
Idan ta fuskanci da kuɗi a hannunsa, ta din ga lallaɓa shi kenan, ayi wani abu mai muhimmanci, idan ba haka ba, ba zai sai abubuwan da suka fi buƙata ba.
Kuma babbar hanyar samun kuɗinsa, wurin Indabo, ya din ga tatsarsa kamar mai, duk da yana samun hanyoyin samun kuɗi yanzu, tun da kakar siyasa ce.
Ana jibi salla, ya ba wa jauhar kuɗi, wai tayi kitson salla ita ma, ta je ayi mata zane a hannunta.
Ta dawo ta tarar da kaya a kan gadonta, ta zazzage taga kaya na alfarma duk an ɗinka su, har da takalmi da turare.
Mamaki ya cikata, yana dawowa ta fito falo ta ce "Master kayan waye a kan gadona?"
"Na kishiyarki ne"
"Wace kishiyata?"
"Ban sani ba, ko ina da wata matar ne bayan ke"
Gaba ɗaya ta rikice ta ce "Master wai nawa ne Gaba ɗaya?"
Ya ce "Naki ne babyn roba"
Har ƙasa jauhar ta durƙusa tana yi masa godiya, ta rasa ma wace kalar godiya za ta yi masa, har da matse ƙwalla.
"Ni ba irin wannan godiyar nake so ba, a sheƙa mini girki, a yi wa fankata caji, in sha iska sosai" sunkuyar da kai ta yi, cikin matsananciyar jin kunya.
"Allah ya ƙarawa fankata gudu, tana ba da iska sassanya, ƙarfin gudunta, bai sanya tana bada iska mai cutarwa ba"
"Amm bari na je na yi jajjage" ta juya ta nufi ɗaki.
"Dama a ɗaki a jajjagen" ko waiwayowa ba ta yi ba, ta shige.
Ranar idin babbar salla ma, tare suka tafi sallar idi.
Ta sha kwalliya, tayi kyau sosai da sosai, a abun da bai fi wata guda ba, ta yi ƙiba fatarta ta ƙara fresh.
Ta sha ɗaurin ɗan kwali, hannunta yayi kyau da zanen lalle ja da baƙi. Su liti suka din ga kiransa a waya, suna jiransa, yaƙi fita, sai da suka zo har gida sannan suka fita da shi, bayan sun kwashi wainar masa da sinasir da miyar agushi.
Bayan la'asar sosai, ya dawo gida da nama kaya guda, har da karfatar sa, ga kayan ciki da uban nama.
Kamar tayi kuka ta ce "Master, aiki daf da magariba ya zan yi?"
"Ke da aiki ba ya yi miki wahala, ɗan wannan aikin zaki yi raki?".
"To aikuwa sai ka tayani, kuma ba ka sayo itace ba"
Ya kalleta ya ce "Ba a yi a gas, an hanaki shiga hayaƙi".
"Gas ɗin dubu nawa za a zuba? Dole sai a itace"
Ya kalli naman, ya ce "Ki shiga ciki, bari na aika nura ya sayo itacen, su walid suna waje, sai su shigo mu yayyanka"
Ƙarshe dai hayaƙin da ba ya so, sai da ta shiga, har sha biyun dare suna aiki ita da shi.
Duk da haka aikin bai ƙare ba, sai washegari, ta ce masa tana son zuwa gida, ya ce sai ta gama yi masa kwalliyar salla kan ta fita.
Ya samu dambun nama da cin-cin, ya din ga tumurmusa, jauhar ta ce "Ni ban gane wannan lamarin ba, gaskiya rabawa za ayi. Kana ta ci idan cikinka ya ɓaci babu ruwana".
"Ke ki ke da ruwa kuwa".
Sai huɗu ga salla, sannan ya bari ta je gida, ya kaita da kansa.
Aka yi sa'a Hafsa ma ta je gidan, tun da ta jauhar ta je, suke kallonta da kayan jikinta.
Sai da mama ta magantu ta ce "Jauhar wannan leshin fa?"
"Mama kayan salla ne"
"Kin san kuɗin leshin nan kuwa?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a shi ne ya kawo mini"
Ta kalleta ta ce "Wai sana'ar me yake yi haka ne?"
Tayi murmushi ta ce "Yana sana'oin sa, kuma kin san yana tare da 'yan siyasa".
Hafsa ta din ga kallon jauhar, yadda take komai nata cikin walwala, kamar ba ta da wata damuwa, duk da tana auren ɗan daba.
Bayan jauhar ta ba su nama, dambun nma da cincin, aka din ga gaya wa jauhar, ai mijin hafsa rago ya kawo.
Ta ce "Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi" Duk yadda Hafsa ta so mazewa, sai da yanayin ta ya nuna akwai damuwa.
Sai yamma Al'amin ya dawo, ya ce ta fito su tafi, babu yadda ba ta yi da shi ba, amma ya ce ba zai shiga ba.
Gidansu ma da ya kaita, a waje ya tsaya, a gurguje jauhar ta shiga ta gaisa da Rahila, ta bata naman sallar sai dai ita ma, kayan jauhar kawai take kallo.
Ana gama bikin salla, aka shiga hada-hadar zaɓe.
Hankalin jauhar ya kasa kwanciya, saboda yawan shige da ficen da yake yi yawa.
Yau ake zaɓen sanatoci, dan haka tun kan ta tashi daga bacci ya fice.
Har yamma shiru bai dawo ba, kuma wayarsa ba ta shiga.
Gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, jikinta ya din ga bata akwai matsala, har bayan magariba bai dawo ba.
Jin ana knocking ɗin gate, gabanta ya faɗi, ta saka hijjabi ta fito, ta ga Nura guduma a tsaye ta ce "Yaya wannan karon me kuma yayi?"
Ya ce "Ki sako hijjabinki mu tafi"
"Mu tafi ina?"
"Asibiti!"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un!"
Ayshercool
08081012143.
40
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Muryarta na rawa ta ce "Meyafaru? Wani abun ne ya same shi, ko ya yi wa wani?"
Ya ce "Ni ma ban sani ba, oga walid ne ya ce "In zo mu tafi tare "
Jikinta a sanyaye, ta kulle gidan, ta bi Nura guduma suka tafi, suna tafe tana ta addu'a a ranta.
Wani private clinic suka je, emergency suka nufa, ana ta kai komo da matasa, da aka ji wa raunuka daga wurare daban-daban na harkar zaɓe, kasancewar an yi tarzoma sosai da sosai a wasu wuraren, kuma nan asibitin ne mafi kusa.
Da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wani irin yammmm haka jikinta yake yi mata, saboda tsoro da tashin hankali.
A ƙofar wani ɗaki, ta tarar da Walid hankalinsa a tashe, yana kaiwa yana komowa.
"Yaya walid, meyasame shi? Ko mutuwa yayi?"
Walid ya ce "Ki nutsu ba mutuwa yayi ba, yana ta kiran sunanki ne kafin mu zo nan".
"To meya same shi, yana ina?"
Ganin likita ya fito daga ɗakin da yake facing ɗin su, ya sanya ta saka kai ta shiga ita ma.
Gigicewa ta yi, ganin Wuƙa a kwiɓin Al'amin a tsaye tsororo, jini baya zuba, amma tana jikinsa, ga gefen kansa, an naɗe shi da bandeji. An saka masa oxygen, gefe ga oxymetre na reading vitals ɗin sa.
Cikin kuka ta ce" Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka? Waye yayi masa haka, Master dan Allah ka tashi, kar ku ce mini mutuwa yayi" tayi maganar tana rirriƙe hannunsa cikin tsananin tashin hankali.
Kukan jauhar ya janyo hankalin likitoci, da m'aikatan jinya, suka ce meyasa aka bari ta shiga?
Da ƙyar aka fito da jauhar ana rarrashinta, aka tabattar mata da yana da rai, tiyata za a shiga da shi a cire masa wuƙar, sai a duba kansa.
Cikin tashin hankali ta ce "Dan Allah likita zai rayu?"
"In sha Allah, da kun biya kuɗin za a shiga da shi"
Ta kalli Walid ta ce "Yaya Walid, nawa ne kuɗin?"
Walid ya ce "Kuɗin da yawa, P.A ɗin Indabo muke kira, su biya kuɗin, hannunmu kuɗin ba za su kai ba ayi masa aikin"
"Ka gani ko? Sun ma ƙi ɗaga wayar, su suna can hankalinsu a kwance, suna jiran sakamakon zaɓe, ni kuma an kassara shi, wannan tashinsa ai sai Allah"
Liti ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah zai tashi"
"Nawa ne kuɗin?"
"Da ɗan yawa, ki bari kawai"
Ta girgiza kai ta ce "Ni ku gaya mini dan Allah, a nema tun da wuri, wuƙa ce fa a cikinsa" tayi maganar tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.
Suka din ga rarrashinta, amma taƙi saurarsu, Liti ya ce "Bari na yi gaggawa na je na samu wannan banzan mutumin P.A, ko dai a san yadda za ayi a biya, wallahi ko mu jiƙa musu aiki"
Jauhar kamar za ta yi hauka, ƙarfin Addu'a ne kawai ya saka mata nutsuwa, ta din ga kaiwa tana komowa, gashi an ce ba zata sake shiga ta ganshi ba.
Jauhar ba ta san yadda aka yi ba, liti da Nura guduma suka dawo da kuɗi, suka biya.
Ake ce ana buƙatar jini, dan da yiwuwar ana cire wuƙar, jini ya ɓalle.
Haka suka din ga zirga-zirga, jauhar itakaɗai a cikin su, babu wani daga danginsa, babu daga nata.
Nura guduma ne ya bayar da jininsa, dan shi ne yayi dai-dai da na Al'amin, aka shiga da shi tiyata.
Hawaye suka kasa barin idanunta, zuciyarta ta din ga wani irin zafi, ba ta taɓa tsanar wani abu ba, tsana mai muni sai yau duk da ba ta taɓa ganin indabo ba, tsananin haushinsa take ji, dan shi ne musababbin wannan tashin hankalin.
Ta kai ta kawo, ta tsuguna tayi kuka, aka shafe sama da awa guda, ba a fito da shi ba, tayi alwala ta shimfiɗa ɗan kwalinta, ta tayar da salla, sai dai tana cikin sallar sai ta hau wasi-wasi, da tunanin me zai faru ta kasa nutsuwa.
Babu tsammani likitocin suka fara fitowa, dan team ɗin tiyatar sun kai su biyar, gaba ɗaya suka nufe su, suna tambayar yaya?.
Jagoran tiyatar ya ce "Alhamdilillah, an cire wuƙar, kamar yadda muka yi tsammani ya zubar da jini sosai, amma an saka masa jini, zamu kai shi ɗakin hutu, amma ba ma son a din ga shiga ana fita da sunan dubiya, kafin a kai shi ɗakin hutun, za a yi masa hoton kai, duk da saran da aka yi masa a ka bai yi zurfi ba, amma akwai buƙatar a duba".
"Alhamdilillah ala kulli halin, Doctor mun gode Allah ya saka muku da alkhairi, ya jiƙan magabatanku, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya ku bar aiki lafiya, ka da Allah ya wulakanta rayuwarku bayan ajiye aiki".
Cikin farinciki suka din ga amsar addu'a jauhar, da Amin, tare da ba ta ƙwarin gwiwa a kan zai tashi ya warware gaba ɗaya.
Bayan an yo hoton, suka tabattar da babu internal injury, jauhar ta zauna ta zuba masa ido, ga jini yana shiga jikinsa a hankali.
Walid ya ce "Ina ganin ki koma gida, ko ni sai na kwana da shi a nan, kin ga idan ya tashi ba abun da zaki iya yi masa"
"A'a idan na koma ba zan iya zama bama, hankalina ba zai kwanta ba, ni kawai ku bar ni".
"To ai dole sai da namiji, ko zaki iya ɗaga shi, idan yana buƙatar hakan?"
Cikin ƙwarin gwiwa ta jinjina kai alamar eh.
Duk da alhini da suke ciki, sai da suka yi murmushi.
Walid ya ce "Bakomai, ki kwana da shi, sai na kwanta a waje ni, idan ana buƙatar wani abun sai ki kira ni, yanzu bari na sayo wani abun, ki ci".
"Bana jin yunwa"
Haka suka kwana da Al'amin, amma bai farfaɗo ba.
Ta din ga kallon wayarta, tana tunanin wa za ta kira, kamata yayi ace tana da wanda za ta kira, a kawo mata abun da zata buƙata saboda zaman asibiti, amma ta san ko za ayi mata sai an yanƙwanata ko gaya mata maganar da zata ɓata mata rai.
Kwana suka yi likitoci na kaiwa da komowa a kansa, ƙarfe shida ta kira Abbu a waya, ya dawo daga masallaci kenan, ya ga kiran jauhar. Ya ɗaga a nitse suka gaisa.
Ta gaya masa abun da ya faru, dumm ƙirjinsa ya buga, duk da ba wannan ne karon farko da Al'amin yake kai kansa in da ake cutar da shi ba.
Abbu ya ce "Shikenan, ki yi haƙuri ki daina kuka, in sha Allah zan zo asibitin, daina kukan haka yarinyar kirki".
Rahila da bacci take yi, sama-sama take jin sa ta ce "Lafiya, kai da waye?"
"Matar Al'amin ce, wai suna asibiti an caka masa wuƙa a ciki jiya a wurin zaɓe"
"Kai amma ka tsorata ni, shi ne ka ke ta rafka wannan salatin haka? Yau ya fara zuwa ayi masa illa a yawonsa? Dan Allah ka kwantar da hankalinka"
Ya kalleta ya ce "Wuƙa a cikin sa fa aka ce mini, waya sani ma ko mutuwa yayi, Rahila Al'amin fa ɗa na ne, ba shi nake ƙi ba miyagun ɗabi'unsa ne ba na so"
"Lallai kam na ga Alama, Allah ya bar soyayya" ta juya ta cigaba da bacci.
Ƙarfe shidan, Nura guduma ya zo Asibitin, Walid ya saka ya raka jauhar gida, ta ɗebo kaya.
Suka tafi, jikinta duk a sanyaye.
"Dan Allah Nura kana ganin zai tashi?"
Ya ce "Eh mana, in sha Allah, shi fa master ɗan baiwa ne, bar ganin abun da yake yi, yana da sa'a sosai da sosai in sha Allah zai tashi "
"Amma ya aka yi aka yi masa haka?"
"Wallahi ban sani ba, wai dai husuma ce ta tashi a wurin tattar sakamakon ƙananan hukumomi, amma ban san shi ya aka yi hakan ta faru ba"
Jauhar ta ce "Allah ya sa ya tashi ya warke"
Ya amsa mata da "Amin"
Ko da taje gida, ta ɗebo kaya suka koma, Alluran da aka yi masa sun fara sakinsa, ya na 'yan maganganu a hankali.
Ban da 'yar madara babu abun da yake kira, ta je ta zauna a kusa da shi, ta riƙe hannunsa, ta kifa kai tana kuka mai ban tausayi.
"Gaskiya ƙanwa idan baki daina kukan nan ba sai kin tafi gida, duk muna jin abun da ki ke ji, daurewa muke yi, ba gashi yana magana ba ya kusa dawowa duka"
Ta girgiza kai "Yaya walid ba ka san me nake ji bane"
"Mun sani, amma ki yi haƙuri"
Abbu ne yayi sallama, wanda jauhar ba ta taɓa tsammani ba, ta dai gaya masa ne kawai, kar ace ba ta faɗa ba.
Da sauri ta tashi ta durƙusa ƙasa tana gaishe shi ya ce "Jauhar sannu ya mai jikin?"
"Jiki da sauƙi Alhamdilillah"
Su Walid ma duk suka gaishe shi.
Ya ƙarasa gaban gadon, ya ƙura masa ido, ya ce "Ya aka yi abun ya faru"
Tayi sauri ta ce "Zai dawo gida ne wasu suka yi masa haka da daddare"
Kallon da su liti suka yi mata, ya sanya Abbu gane ƙarya take yi.
"Yanzu ya ake ciki to?"
Walid ya ce "An yi aiki an cire wuƙar"
Ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah, Allah ya tashi kafaɗunsa"
Suka amsa da "Amin"
'yar madara da yake ta maimaitawa ya sanya Abbu cewa "Wace 'yar madara kuma?".
Gaba ɗaya suka kalli Jauhar, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.
Abbu ya yi murmushi ya ce "Ikon Allah"
Nurse ta shigo, ta ba su takarda a sayo magani.
Abbu ya bayar da kuɗi aka sayo, ya din ga yi wa jauhar nasiha a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta, dan har a lokacin tana kuka.
Sai dai wata nustuwa ta saukar masa, ganin Al'amin yayu ƙalau da shi.
Har azahar suna tare da Abbu, daga bisani, ya ajiyewa jauhar kuɗi, ya ce "Duk yadda ake ciki su kira shi.
Liti ne ya fita waje, ya kira P.A