Showing 363001 words to 366000 words out of 479911 words
domin ya yanke duk wata alaƙa tsakaninta da mahaifinta har abada.
Ta na yawan mafarki da wata mai kama da irinta sak suna wasa tare tun tana yarinya, idan ta farka tana jin tsananin ƙaunar yarinyar da suke wasan tare, idan ta gaya wa baba magajiya, sai ta ce mata shirmen mafarki ne da iskokanta.
Sai dai daga baya ta daina mafarki da ita, daga baya kuma bayan ta girma sosai, ta cigaba da mafarkinta, har cikin zuciyarta take jin matsananciyar ƙaunar wadda take gani a baccin nata. Sai dai yadda take ganinta daga baya bayan ta girma, cikin damuwa take ganinta, tana nuna mata inuwar wani mutum a cikin sarƙa.
Ta samu baba magajiya ta ce "Wai ni baba anya ba 'yan biyu ba ce ba? Yarinyar da nake mafarki ba ta girma ta zama kamar ni".
"A'a yan dozen ne ba biyu ba, gane-ganenki ne na makaran kanki, suke buɗe miki ido, dama ai tun kina yarinya ki ke yi" ta shiriritar da maganar.
Wataran suna camp, ta sake mafarki da yarinyar, tana kuka tana nun mata na cikin sarƙar, ta farka a razane sai ta ji kamar muryarta a zahiri tana kiran sunanta "Nabila" tsakiyar dare ta tashi zata fita, aka riƙeta da kyar.
Ta daina mafarkin mai kama da ita, sai inuwar wannan mutumin a cikin sarƙa, da take gani babu yau babu gobe a cikin baccinta.
Da kyar Nabila ta kalli Viper, ta na suffanto inuwar wanda take gani a cikin bacci.
Motsa bakinta take yi, tana son tayi magana, amma ta kasa ta ɗago hannunta da kyar tana nuna Viper, amma bakinta ya hau karkarwa.
Ayshercool
08081012143
87
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_GYARA SHINE MACE_*
*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327
*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,
Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍
Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍
Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃
Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata💃😍
Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃
Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃
Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima
KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻
Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi
Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu
Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra
Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa
Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka
*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻
07069711327 Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍
Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊
Bakin Nabila ya cigaba da karkarwa, idanunta suka fara ƙoƙarin kakkafewa.
Liti ya na tsaye daga baya a jikin bishiyar umbrella da take tsakar gidan, wani irin tausayin Nabila da jauhar har ma da Viper ya mamaye shi, har gara ma Viper, shi yanzu idan da sabo ya riga ya saba, ita kuwa an rabata da 'yat uwatta, an nesanta su da juna, kuma ta rasu ba su haɗu ba, sosai ya ji nadamar abubuwan da ya din ga yi wa Nabila.
A hankali Viper yake ɗan girgizata, yana kiran sunanta "Nabila, me yake damunki?"
Su Zakiyya da suke ɗaki kuwa, gaba ɗaya suka yi sak, dan sun san su ne kanwa uwar gamin abin da ya faru.
Baba ya miƙe hannu zai taɓa Nabila, major ya riƙe hannunsa ya ce "Bashir, haryanzu ina nan a kan bakana, babu kai babu abin da mairamu ta bari, ba zan taɓa baka Nabila ba, kuma ka cire a ranka Nabila ba 'yar ka ba ce ba"
"Yanzu maitama abin da ka yi kana ganin daidai ne? Baka gaya mini yarana biyu ba, ka kawo mini ɗaya ka nesanta ni da ɗaya? Zan iya ƙararka fa a kan abin da ka yi mini"
"Shut up! Ko kuma ni na yi ƙararka ba, da ka kashe mini 'yar uwa, ai dai na kawo maka ɗayar ko, ka aura wa ɗan daba ya kasheta, kai ka sani" Viper ya yinƙura da Nabila a hannunsa, sai wata irin miƙa take yi, ya nufi waje da ita.
Bayansa suka biyo, Bashir sai share hawaye yake yana kiran "Aminu ina zaka kaita ka tsaya na ga 'ya ta".
Cikin ɗaga murya, major yake yi wa Viper magana, a kan ya tsaya, Nasir kuwa kasa shan gaban Viper ya yi, gaba ɗaya suka bi shi. Sojan da ya kawo su, yana ganin Viper ya fito, ya buɗe masa mota, ya saka Nabila a ciki.
Saifu ya riƙe shi ya ce "Ina zaka kaita, dole fa ka tsaya a gama wannan tarzomar"
"Cika ni" Viper ya yi maganar yana kallon saifu. Saifu ya cika shi ya ja da baya.
Viper ya kalle su ya ce "Zan mayar da ita asibitin barrack, idan na bar muku ita a nan, zan iya yin laifi tun da tana ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne.
Walid taho mu yi gaba, su taho tare da liti"
"A'a shi dai su taho tare"
Zakiyya ta ce "To a tafi babu wata mace, mu tafi gaba ɗaya mana" kafin Viper ya bata amsa, Hafsa ta ture shi, ta shige cikin motar, yanayin yadda ta shiga kawai zaka gane kan babu daɗi.
Ya kalli saifu ya ce "Ka shiga ka riƙeta mu tafi"
Hafsa ta ƙanƙame Nabila, tana kuka ta ce "Yaya saifu, rannan ba ce muku naga Jauhar a asibiti ba, aka ce bani da hankali, to ai gashi yanzu ta dawo ba ta mutu ba"
Walid da Viper suna gaban mota, sai da Walid ya waiwayo gwanin ban tausayi, bai manta hafsa a da ba, yar gayu 'yar ƙwalisa, jawur da ita ta sha mai, amma yanzu duk ta koma baƙa ta firgice.
Har suka isa barrack, Nabila tana wannan miƙar bakinta yana rawa, viper ya ce a ƙarasa da su asibitin sojoji, saifu ya ce "Anya wannan abun ba aljanu ba ne?"
"Ba wani aljan" Viper ya faɗa a daƙile.
Sai dai suna isa, aka ɗauki Nabila aka shiga da ita, Viper ya yi wa ma'aikatan alama, da karba bari kowa ya shiga in da take.
Tafiya ce mai nisa sosai, daga gidan baban Nabila zuwa asibiti, amma har suka zo, jikinta a sandare yake, dai dai idan ta motsa tayi miƙa kawai.
Alluran bacci kawai aka yi mata, sai drip na babu gaira babu dalili, kusan ko ina a jijiyoyin hannunta akwai tabon hudar cannula.
Major ya fara tambayar ina aka kai masa 'ya, aka ce masa an hana kowa ya shiga in da take. Cikin hasala ya ce shi ma fa tsohon ma'aikaci ne kamar yadda yake gaya musu, dan me za ace ba zai shiga ba.
Aka ce masa ba bisa umarnin sojoji aka hana kowa shiga wurinta ba, bisa ga umarnin likitoci ne.
Baba ma ya ƙarasa tare da tijjani, yana kiran wayar saifu, dan ya gaya musu, a in da aka kwantar da Nabila, bayan su haɗu, saifu ya sanar masa an hana kowa shiga.
Baba bai damu da irin mugun kallon tsanar da major yake yi masa ba, babban burinsa kawai ya sake tozali da kyakywar fuskar 'yar sa, mai kama da jauhar Waliyiyya, kuma kamannin mairamu chubaɗo.
Walid ya kalli liti, da kamar ya koma kamar ɗan tsakon da ya faɗa ruwa, duk yayi tsuruu da shi, kamar mara gaskiya.
"Ya dai liti?"
"Walid zuciya da saurin fushi ba su yi ba"
"Meyafaru?"
"Yarinyar nan wani irin mugun tausayi ta bani, wallahi kamar na yi kuka, tabbas na daɗe da gane ba ita ce jauhar ba, tun da damu aka yi jana'izar ta, hausin abin da wancan banzan yayi mini mai ƙugu kamar an miƙo kare ta taga, da rashin kunyarta da shishishigi da take yi wa Viper, ya sanya na ji na tsaneta, haka kurum idan yana saurarenta, sai na ji kamar ya na cin amanar jauhar ne, ko bayan mutuwar ta, bai kamata ya kula wata mace ba"
"Abin da nayi ta nuna maka kenan liti, amma ka ƙi ganewa, kullum cikin yi mata rashin mutunci ka ke, ji maganganun da ka caɓa mata muna tafe a hanya. Ai a duniya idan zaka yi ƙiyayya ka yi ta sama-sama haka ma soyayya amma kawai ka je ka yi ta hantararta, ashe abin da yayi jauhar shi ya yi Nabila"
"Amma kamar su ta yi mugun ɓaci fa, ni fa na daɗe ina kokwanton idan ba fatalwar jauhar ba ce, halayensu da na din ga nazarta na fuskanci wannan sai a hankali, gaba ɗaya sun sha banban ta fuskar halayya, amma hatta muryarsu iri ɗaya, sai dai ta jauhar ta fi sanyi da nutsuwa, wannan kuwa tsabar tsiwa da masifa ce a cikin ta ta muryar, Allah sarki Allah ya jiƙan 'yar madara". Walid ya amsa da Amin.
Major kuwa ganin Bashir ya kafe ya nace, ya sanya ya Kalle shi ya ce "Bashir, ka kama hanyarka ka bar wurin nan, wallahi ko me zaka yi, ba zan ba ka Nabila ba, kar ma ka yi tunanin ayyana kanka a matsayin mahaifinta"
"Maitama babu in da zan je, har sai ya ta ta farfaɗo, kuma sai ka bani kayata na tafi da ita"
"Ita ma ka je ka aurawa ɗan daba ya kasheta kenan"
Bashir ya ce "Ko ma wa zan aurawa, 'ya ta ce, ina da iko a kan aba ta"
Saifu ne ya din ga ba su haƙuri, a kan su yi haƙuri su daina abin da suke yi.
Viper kuwa yana zaune a cikin ɗakin, da take tana bacci, yayi alwala ya gabatar da salla, sannan ya nemi wuri ya zauna yana danna wayarsa.
Ya ɗago ya kalleta jin ta yi tari, bacci take yi, amma yanayin fuskarta ya nuna ba daɗin baccin take ji ba sam.
Sosai Nabila take kama da jauhar, babu yadda za ayi ka ce ba mutum ɗaya ba ce ba, sai ka rayu da jauhar, ka dawo ka rayu da Nabila, zaka fuskanci su na da banbanci.
Amma mafi yawa they have so many things in common.
Ya mayar da kansa kan wayarsa, ya ci gaba da daddanawa, bai fargaba kawai ya ga ta tashi tsaye, ta fizge ƙarin ruwan, jini yana zubowa daga hannunta.
Da azama ya tashi, ganin idanunta a rufe ko gani ba ta yi, ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Shan gabanta ya yi ya ce "Ina zaki je?" Da kyar ta buɗe rinannun idanunta ta kalle shi, ta je uban tsaki, ta raɓa shi za ta wuce, amma ya riƙe ta, ya danne hannunta da yake zubar da jini.
Ya ce "Abla, menene? Meyake damunki?" Ta tsaya ƙyam sai rangaji take yi kamar wadda ta sha ta bugu, tana lumshe idanunta ta na buɗe su.
"Abla" ya sake kiranta a hankali.
Kamar wadda ta farka daga bacci ta kalle shi, ta ce "Mafarki ne ko, ai ba gaske ba ne ko?" Kan ya kai ga ba ta amsa, ta kalli kayan jikinsa, ta kalli na ta, ta shafa fuskarta, ai sai ta saka kuka, ta fara kiran Abba da ƙarfi, tana ƙoƙarin ture Viper tayi waje.
"Shikenan, ya isa ki nutusu, bari ayi masa magana ya shigo ki ganshi, amma mu je ki zauna tukuna" kamar mahaukaciya sabon kamu, haka Nabila ta din ga misbehaving.
Viper ya yi waya, ya ce a ba su damar su shigo su ganta.
Sai ga su duk sun shigo, ga hafsa saifu da Tijjani, major da Bashir na rige-rigen shigowa, sai kuma su liti da walid da Nasir.
Bin su ta din ga yi da kallo, Hafsa ta ƙarasa gaban gadon Nabila ta ce "Waliyiyya, sannu kin tashi? Ina ɗan jaririnki yake? Shikenan yau sai ki koma gidan Master, ku ci gaba da shan soyayya" ƙuri Nabila ta yi mata da ido, dan ba ta santa ba sai a ɗazu ta taɓa ganinta.
Major ya ce "Arfa, ya jikin naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
"Arfa Abba ne fa, ba ki gane ni ba ne?"
Bashir ya zagaya ta gefenta, yana ƙare mata kallo, cikin matsananciyar soyayya da ƙauna.
"Yarinyata, ki kalle ni, ni ne mahaifinki" yayi maganar cikin matsanancin rauni.
Nabila ta ɗaga kai, ta kalle shi sau ɗaya, ta kawar da kanta, tabbas ta ɗokanta da son ganin mahaifinta, ba irin alwashin da ba ta yi ba, na idan Allah ya sa yana raye, su ka haɗu, babu ruwanta da Al'ada sai ta rungume shi, ko a yaya yake, sai dai kash! Ba ta ji daɗin a yadda mahaifin na ta ya kasance ba, duk da ba ta san mahaifiyarta ba, amma uwa uwa ce, ba ta ji daɗin abin da ta ji game da tarihin zaman su ba.
Nasir ya ce "Nabila, ki yi magana mana"
Major ya sake cewa "Arfa, ki kalle ni mana? Meyake damunki?"
"Ni ku daina nuna ku na so na, ba kwa so na ba kwa ƙaunata, meyasa za ku yi mini haka? Ni menene laifina a tsakanin ku? Ace ina da 'yar uwa ban ganta ba, ba ta ganni ba har ta koma ga Allah, kun san me nake ji kuwa? Ban san uwata ba, 'yar uwata kuma ta mutu ban taɓa ganinta ba, duk ba kwa so na, kun fifita tsamin alaƙar ku a kai na, ta mutu fa ba zan ganta ba kenan. Abba tsananin son da ka ke yi wa 'yar uwakka ya sanya ka yanke wannan hukunci, ni yanzu ba ka yi tunanin a wane halin nake ciki ba, da na rayu kamar wata mujiya, ba wani ɗan uwa da zan ɗaga in kalla ya na so na tsakani da Allah" tayi maganar tana wani irin kuka mai matuƙar sauti.
"Shikenan da ban haɗu da Viper ba, ba zan san ina da 'yar uwa ba, Abba ka ɓoye mini, kai kuma babana, duk burin da na ci na in ganka, gwiwata ta yi sanyi, meyasa ka yi wa mahaifiyarmu haka, da ba ka yi haka ba, da babu lallai a raba ni da 'yar uwata, ban fa taɓa ganinta ba, shikenan ta tafi har abada"
Ta miƙe tsaye a kan gadon, tana neman hanyar sauka.
Viper ya ce "Meye haka ne ki ke yi? Ina kuma zaki je?"
"Ka kira mini sumayya dan Allah" tayi maganar cikin sigar magiya.
"Sumayya kuma? Me za ta yi miki?"
"Ni dai ka kirawo mini ita"
"Magariba ta yi, ba za a kirata ba sai da safe"
Likita ne ya dawo, ya ce duk a fita a ƙyaleta, a stage ɗin nan da take, za ta iya samun matsalar ƙwaƙwalwa, a ƙyaleta ta huta.
Matsananciyar nadama da jin kunya, suka mamaye Bashir yanzu shikenan Nabila ba ta farincikin ganinsa.
Shi ma major, damuwa ce ta mamaye ilahirin fuskarsa, wani irin dana sani yake yi, na raba Nabila da jauhar da ya yi, wato duk wayon bawa ƙaddara ta riga fata.
***
Gidan su jauhar, tun bayan da Zakiyya ta yaudari maman saifu, ta aurawa Alhaji mu'azzam Hafsa, dama haɗin kan na su ya lalace, kullum cikin faɗa da tashin hankali suke, sai ka ce ƙanan yara, gaba ɗaya tarbiyyar yaran sai a hankali, ba wanda yake ganin uwar wani da gashi sai tasa.
Bayan tafiyar su Major, Zakiyya ta ce "Ke kin ga wani ikon Allah, wallahi saura kaɗan na haukace, na ɗauka gamo na yi, yanzu duk tsawon wannan lokacin dama jauhar 'yan biyu ne?"
"Wallahi kuwa, abin da mamaki ba kaɗan ba, kuma wani ikon Allah, ba ya zancen uwar su, tun wancan lokacin"
Zakiyya ta ce "Eh, amma