Showing 243001 words to 246000 words out of 479911 words

Chapter 82 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6180

wani wanda yake da laƙanin karyewar asirin, sai shi wanda ya bashin, wanda yanzu ya mutu sai ɗan sa yanzu dan kuwa shi kansa ɗan ma bai san makarin asirin ba, dan haka sun yi mamakin yadda aka yi Viper ya samu.

Sun kamo hanyar dawowa kano, madaki ko iya magana baya yi, babu tunanin da yake yi, da ya wuce wani mataki zai ɗauka a kan Viper, dan kuwa karya asirin nan, dai-dai yake da karya alkadarinsa baki ɗaya.

Kiran P.A ne ya din ga shigowa wayar Madaki, sai da yayi da gaske sannan ya ɗaga, domin kuwa gaba ɗaya ransa a jagule yake saboda tashin hankali, da fargabar halin da zai shiga, idan aka fuskanci Alkadarinsa ya karye.

"Madaki, ina ka shiga ne, yau kwanaki kusan huɗu wayarka ba ta shiga, distinguish ya bayar da muhimmin aiki da kai kaɗai ne zaka iya yin sa"

Madaki ya yi ajiyar zuciya ya ce "Aikin menene?"

"Idan kana gari ka shigo"

Madaki ya ce "A'a, na ɗan yi wani balaguro ne"

"Duk in da ka ke ka dawo, honorable ya matsa a kan lallai a kama viper, yarinyar nan yake so a ɗaukko masa"

Madaki ya ce "Wace yarinyar kenan?"

"Wata lawyer ce, wadda na fara yi maka zancen nan"

Madaki yayi wani huci, ya ce "Bari na shigo garin, zan yi maka magana"

P.A ya ce "Wai madaki lafiya kuwa? Kamar ba ka da karsashi, meyake faruwa ne?"

"Basar ka ɗauke tunaninka a kan hakan, zan faso idan na shigo gari" ya katse kiran yayi shiru yana tunani, tabbas ta bakin Al'amin daga lokacin da suka ga ya daina yi musu amfani zasu watsar da shi.

***
Nabila ta kira layin Viper ya kai sau biyar, dan ta ji halin da yake ciki, amma ba a ɗagawa, har ta fitar da ran zai ɗaga ta ji an ɗaga wayar.

"Haba master, ka barni cikin zullumi da tunanin halin da kake ciki,  ka ƙi ɗaga wayata".

"Walid ne"

"Oga walid, yana ina dan Allah?"

"Gashi muna ta fama, jiki ya rikice gaba ɗaya".

Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wani abun ne ya same shi ne?"

"Ke zamu yi wa wannan tambayar, dan babu yadda bamu yi da shi ba, ya ce sai ya fita, wurinki zai zo, zai yi wani aiki, mun yi iya ƙoƙarin mu mu hana shi, amma ya ƙi saurarenmu, ko kin yi masa wani abu ne ki gaya mana dan Allah"

"Wallahi Allah kenan, ban yi masa komai ba, office ɗina ya zo ɗazu....

Walid ya katseta ya ce "Office kuma? Ya ce kiranki zai yi a waya ku haɗu"

"A'a zuwa yayi, yayi amfani da wayata da computer ta ta, daga nan ya ce zai ƙarasa mini labarin da ka fara bani, har gidansa muka je" ta yi wa walid bayanin yadda aka yi.

Walid ya ce "To ki tayamu addu'a, jiki ya rikice, ɗan sakewar da yayi kwana biyu, ta gushe ya koma yadda yake a da. Salla kawai yake yi a kwance tun da ya dawo, sai dafe ƙirjinsa yake yi yana haki".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Oga walid da ka ƙarasa mini labarin nan, duk da haka bata faru ba, da na san halin da zai shiga kenan, da ba zan takura masa ya gaya mini ba. Ubangiji Allah ya kawo masa mafita, Allah ya bashi lafiya, ba zai yiwu na fito yanzu ba, dan Allah ku kula da shi sosai. Zan zo in ga jikin nasa in sha Allah"

"Shikenan, Allah ya kawo ki" ya kaste wayar, yana kallon in da Viper yake kwance, hannunsa ɗaya a kan ƙirjinsa, yana ta sauke numfashi.

***
Duk wasu kalamai da Abdul yake tunanin idan yayi amfani da su, zai shawo kan ramma, yayi amma fafur taƙi saurarsa, ya kaɗa ya raya, amma taƙi saurarsa. Da ya addaba mata cikin tsawa ta ce "Wai me kake so ne Abdul, ai ban yi zaton mugun zaluncinka ya kai haka ba, ka yi mini fyaɗe an ɗora wa mutanen da suka taimaka mini sharri, wannan wace irin rayuwa ce?"

Ya sake kwantar murya ya ce "Ki fahimce ni dan Allah, zan yi duk iya ƙoƙarina a kan mutumin nan ya fita a sake shi, dan Allah ki daina ɗaga hankalinki"

"Dama dole ka ce haka mana, tun da kana ganin ko ta halin ƙaƙa, kuɗi zasu ƙwatar maka komai, baka tunanin mawuyacin halin da zaka jefa zukata, baka yi dacen hali ba ko kaɗan" taƙi sauraronsa, sai uban miyagun maganganu da ta din ga yaɓa masa.

***
Bacci ya gagari idanun Nabila, ta ga tamkar an ƙara wa daren tsawo, gashi ta kasa bacci, ƙarshe ta tashi tayi alwala ta tayar da nafila.

A gaggauce ta hana baba magajiya aikinta, ana idar da sallar asuba, ta shiga kitchen ta dafa abun da take buƙata, da duku-duku, ta ɗauki motarta ta fita.

Jin ƙarar mota ya sanya Nasir ɗaga labulensa ya duba, ya ga babu motarta, ya kalli agogo, hari sam bai gama waye ba, ya fara tambayar kansa ina tafi da wannan duku-dukun?.

Gudu ta din ga yi a titi, gani take yi tamkar kafin taje, wani abun ya same shi.

Gari yayi haske sosai tana hanya, ta ajiye motarta a wani wuri, ta fito ta tsaya ko zata samu abun hawa, amma bata samu ba, dan haka ta cigaba da tafiya da ƙafa, gabanta na ta tsananta faɗuwa sai addu'a take yi.

Ta sha tafiya sosai, sannan ta samu abun hawa ta hau, ya ƙarasa da ita.

Kasancewar da tafiya daga titi zuwa gidan da yake, haka ta din ga haɗawa har da gudu, har ta ƙarasa tana ta haki, ta shiga da sallama, ta ƙarasa ƙofar ɗakin, ɗan mama ta hango zaune a gaban Viper, yana ta rarraba ido, daga shi sai shi a gidan.

Ƙwayoyi ne a hannun Al'amin, gefe ga allura a cikin sirinji, amma sai haki yake yi mai ban tsoro.

Da sauri ta ƙarasa ɗakin, tana cewa "Wannan ƙwayoyin na menene?"

Kafin ta ƙarasa ya watsa su a bakinsa, babu ruwa yake ƙoƙarin haɗiyewa, ba ta san lokacin da cikin tsawa ta ce "Viper meye haka? Ƙwayoyin meye wannan kashe kanka ka ke son ka yi?"

Bai kulata ba, ya cigaba da ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai ya kasa saboda abun da yake ji ya tokare masa a wuyansa zuwa ƙirjinsa.

Matse bakinsa tayi iya ƙarfinta, tana girgiza masa kai "Kar ka haɗiye, wallahi hakan ba mafita ba ce ba, dan girman Allah ka zubo su daga bakinka" hankaɗeta yayi yana ta huci.

Ɗan mama ya ce "Ki daina zuwa in da yake, zai yi miki illa, wallahi aiken su Walid yayi, ni kuma yayi mini barazana da wuƙa, na samo masa kuma wanda ya watsa a bakinsa sun yi yawa, sun yi masa ƙarfi"

"To waye ce ka kawo masa, ba sai ka gaya wa Oga walid ba, ai ka san ba zai taɓa iya kisan kai ba"

Ta sake tunkarar Viper, sai haki yake yi mai haɗe da huci, tamkar kumurcin, yana motsa bakinsa a hankali, yana son haɗiye ƙwayoyin.

Bakinsa ta sake matsewa, idanunsa sai buɗewa suke yi suna lumshewa, wanda suka fara narkewa a bakinsa, sun fara rikita masa lissafi.

"Kalleni nan, ka fito da su na ce" tayi maganar tana zare masa ido.

Ya ɗago a hankali ya kalleta, ta ce "Ka zubo da su, kar ka haɗiye. So kake ka kashe kanka, idan ka kashe kanka, ɗan wuta zaka mutu, kuma ko ka je lahira ka mutu ɗan wuta, yar madara kuwa muna saka mata ran tana aljanna, kaga ba zaka ganta ba"

A galabice, ya buɗe bakinsa, yana zubo da ƙwayoyin da suka rage a bakinsa, yana ta haki.

Shammatarta yayi, ya ɗauki sirinjin da yake gefensa, ya caka mata a hannunta, wata irin ƙara tayi, cikin razani, dan ba ta yi tsammanin hakan ba.

Ɗan mama ya rikice, ya nufo su da sauri, Viper ya kalli in da ya caka mata sirinjin, ya kalli fuskarta yadda ta fara kuka, sai kuma ya ankare da abun da yayi.

Sai ya rikice, ya zare sirinjin ya jefar ya riƙeta ya ce  "Zahra, me nayi miki? Yi haƙuri, na daina shan komai, ai nayi miki alƙawari" yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannunsa fuskarta, ya share mata hawaye.

Walid ne suka shigo tare da liti, suka nufo su, liti ce wa yake "Me ki ka yi masa?"

Viper ya yinƙura ya tashi, amma ya yanke jiki ya faɗi.

Suka rufu a kansa, suka ɗaga shi da kyar, Nabila ta gaya wa Walid a halin da ta zo ta same shi.

Walid ya kalli ɗan mama, cikin tsananin ɓacin rai, ɗan mama ya ce "Nifa bani na kawo masa ba, wallahi ɗaukko masa kawai ya saka nayi, ban san a ina ya samo abun sa ba"

Suka mayar da hankali a kan Viper, sai dai ba maye kawai yake yi ba, suma yayi, ga numfashinsa iya ƙirjinsa yake.

Nabila ta ce "Dole fa a kai shi asibiti, ko da hakan yana nufin a kama mu ne baki ɗaya, lafiyar sa ita ce mafi muhimmanci a wannan lokacin"

Walid ya ce "Haka ne, amma wani asibiti zamu kai shi?"

Liti ya ce "Akwai wani asibiti a can bayan gari sosai, sai dai na kuɗi ne, ina ga kamar can zai fi zama safe"

Nabila ta basu mukullin motarta, ta gaya musu a in da take.

Liti ya karɓa ya tashi ya fita.

Nabila kallonsa take cike da tausayawa, namijin gaske ne, sai dai ta wata fuskar yana da raunin zuciya sosai.

Da liti ya kawo motar, suka yi kama kama, suka ɗauke shi, suka shafo tafiyar nan da shi, suka fito titi.

Liti ne yake jan su a motar, ɗan mama da Viper da walid suna baya.

Asibiti ne mai kyau, sai dai ya yi nisa da gari sosai da sosai.

Ganin halin da yake ciki yasa suka karɓe shi da gaggawa, Nabila ta tambayi ya tsarin Asibitin yake, da payment ɗin, aka ce su bari, a fara ceto ransa tukuna.
Da aka tambayi sunan Al'amin, sai Walid ya ce "A saka masa Muhammad Nura"

Liti ya ce "Meyasa baka bayar da normal sunansa ba"

Ya bashi amsa da "Saboda tsaro"

A kan oxygen aka fara ɗora shi, saboda numfashinsa, sannan aka fara sauran ƙoƙari a kansa.

Walid kallonta kawai yake yi, yadda take a rikice cike da tashin hankali, babu ma alamar tana fargabar a kamata ko wani ya ganshi, ta uzzurawa likita da tambayoyi.

Likitan yayi mata bayanin yadda Jinin Al'amin ya hau, ga bugun da zuciyar sa take yi, fiye da kima kamar yadda ECG ɗin sa ya nuna, he's at very risk of having heart attack.

"Subhanallah, dan Allah doctor kayi ƙoƙarin ka, na san Allah ne mai komai, amma dan Allah ka taimaka"

"In sha Allah zamu yi iya a ƙoƙarin mu a kai"

Tayi masa godiya, ta tafi reception ita da litu, suka gaisa da cashier ta tambayi, me za su yi depositing, na patient ɗin su da aka yi admitting?.

Ya tambayi sunan mara lafiyan, liti ya gaya masa, ya duba cikin system ɗin gabansa ya kalle su ya ce "Ai an biya"

Suka kalli juna da ita da liti, liti ya ce "Malam ka duba sosai, ɗazu muka shigo fa, aka ce mu bari a fara bashi taimakon gaggawa, ka duba ko masu irin sunan biyu ne".

"Shikaɗai ne me irin sunan da aka yi admitting yau, Al'amin Ibrahim"

Suka kalli juna da Nabila, liti ya ce "Mu sunan mara lafiyanmu Muhammad Nura"

"Wanda ya biya kuɗin, sunan da ya bamu kenan, ba shi ne na ɗaki mai lamba 2 ba? Al'amin Ibrahim ya ce mana, ya turo kuɗi ya ce ayi masa duk abun da yakamata".

Ayshercool
08081012143

59
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Nabila ta ce "Malam ya za ayi mu kawo mara lafiya, mu zo kuma ace mana wani ya biya  kuɗinmu, dama haka ake yi, wannan wane irin abu ne, ka gaya mana bills ɗinmu mu biya, mu bamu san kowa ba"

Ya girgiza mata kai ya ce "No ma, ba zan karɓi kuɗinku ba, na gaya miki an riga an biya"

"Waye ya biya?"

Liti ya ce "Kai bana son nuƙu-nuƙu, wanene ya biya kuɗin?"

"Nima ban sani ba, management ne suka turo mini receipt, aka ce kar mu karɓi kuɗinku, an yi settling bills ɗin"

Nabila ta ce "Suwaye management ɗin?" Yayi shiru yana kallonta.

"Malam kayi mini magana, ka tsare ni da ido, suwaye management ɗin? Suwaye suka biya kuɗin?"

Liti ya ce "Ki yi magana a hankali, kar ki janyo hankalin mutane kanmu"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ana bibiyarmu, wanda yake wannan abubuwan ya san duk wani motsi da muke yi"

Liti ya jinjina kai ya ce "Nima nayi wannan tunanin"

Nabila ta ce "Mu koma wurinsa, kafin mu san abun yi" suka koma in da suka baro Al'amin da walid da ɗan mama.

Walid na ganin su ya ce "Yaya? Nawa ne kuɗin?"

Nabila ta ce "Kar ka damu, an biya"

Tayi maganar tana zama a gefen Viper, ta tsurawa fuskarsa ido, kawai tuno yadda ya din ga kuka ta din ga yi, gaba ɗaya jikinta ya ƙara sanyi.

Walid ya ce "Ba zaki ga likita ba, wurin da ya caka miki allura?"

Ta girgiza kai ta ce "Bakomai, ni yanzu ta lafiyarsa nake yi"

"Amma yakamata ki koma wurin aiki fa, ai muna tare muna kula da shi"

"No, ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba, ba zan iya aikin ba, bari na jira naga abun da hali zai yi"

Likita ya sake shigowa, yana duba Al'amin.

Ya ce "Alhamdilillah, ina ga ya samu bacci, dan ya farfaɗo daga suman"

Nabila ta ce "Masha Allah" ji tayi ya taɓa hannunta, ta kalli hannunsa, ya yi mata alama ta matso.

Ta matsa ta kai kunnenta saitin bakinsa, a hankali ya ce "Ki gaya masa a cire mini wannan abun na hancina bana so".

"Haba master, baka ga yadda kake numfashi da kyar bane ba? Dan ya taimaka maka aka saka maka shi, dan Allah ka yi haƙuri ka ji, Allah ya baka lafiya"

Ya sake cewa "Ki ce musu bana iya bacci, yayi mini abun da zan yi bacci, kaina zai tarwatse"ta ɗago ta kalli likitan ta ce "Doctor, ya ce dan Allah ayi masa allurar bacci, so yake yayi bacci baya iya bacci"

Likitan ya ce "Ai mun yi masa, kuma da jinin ya sauka zak yi bacci mai yawa mai daɗi in sha Allah"

Ta sake sunkuyawa, zata yi masa magana ya ce "Bana son baccin, ba na son jinin ya sauka, bani da rabon sake yin su, Allah ya nuna mini ranar da zan bi matata"

Babu wanda yake iya jin abun da yake faɗa, sai ita, muryarta na rawa take yi masa magana a hankali cikin nutsuwa.

"Haba Al'amin, mai babban suna, shikenan bawa ba zai yi imani da ƙaddara ba, tun da ka fuskanci kurakuran da ka yi a baya, ba sai mu nutsu mu nemi mafita ba, yanzu idan ka mutu maƙiyanka sun ci galaba a kanka kenan fa.
Dan Allah ina roƙonka ka janye wannan fatan da ka ke yi, kuma in dai muna tare in sha Allah zaka yi bacci mai daɗi mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali trust me.
Wallahi i feel your pain, bani na tsinci kaina a halin da ka ke ciki ba, but ina jin zafi a zuciyata, in sha Allah you won't cry alone, an cutar da kai, in sha Allah kuma sai in da ƙarfina ya ƙare a kan ƙwato maka hakkinka, in sha Allah sai nayi sanadin dawo da farincikin ka.
Amma sai ka yi haƙuri, ka yi haƙuri, kayi haƙuri na san da wahala, da ciwo, an yi maka illa, amma ina roƙonka a wannan karon kar ka jinkirta tuba, mu yi ta addu'a, Allah ya taimake mu, ka kwantar da hankalinka ka yi haƙuri, Allah da kansa ya rarrashi masu haƙuri a cikin Alqur'ani"

Yayi shiru yana sauraren Nabila, hawaye yana bin gefen fuskarsa.

"Madam ya kuma kike kuka, mu da muke son hankalinsa ya kwanta, jininsa ya sauka?"

Liti ya ce "Rabu da shi doctor, kukan shi ne samun afuwarsa, mun gode sosai da ƙoƙarin ku.

Cikin kalaman hikima, da tausasawa, ta cigaba da yi wa Viper nasiha, tare da bashi ƙwarin gwiwa, a kan cigaba da haƙuri, da kuma Addu'a.

Har bayan azahar, Viper bai gama frafaɗowa ba, haka Nabila ta haƙura ta tafi gida, bayan ta ajiye musu abincin da ta zo da shi.

Sai magariba ta isa gida, Allah ya sa Abba baya nan, balle ta sha tuhuma.

Message ne ya shigo wayarta, ta ɗauka ta duba.

"Arfa dan Allah kar ki yi mini mummunar fassara, ki tsaya ki saurare ni mu yi magana, kin ƙi ɗaga wayata, hankalina a tashe yake, amma ki bani dama nayi miki bayani, dan girman Allah"

Har jikin Nabila yayi sanyi, kamar ta yarda da maganar Sumayya, sai kuma ta fasa, tayi mata reply da "No peace for wicked person, kar ki sake tunanin zan yarda da maganarki" ta saka lambar a busy, ta cigaba da sabgar gabanta.

Ta idar da sallar isha'i, tana zaune tana cin abinci, kawai Nasir ya faɗo ɗakin, babu ko sallama. Ta ɗaga kai ta kalle shi, amma bata ce masa uffan ba.

"Arfa"

"Na'am yaya"

"Ina ki ka je yau?" Ta ɗaga ido ta kalleshi ta ce "Meyasa kake tambayata?"

"Ki bani amsa kawai"

Cikin ko in kula ta ce "Wurin aiki"

"Ƙarya ki ke yi, me ya kai motarki hanyar ungoggo?"

Ta ajiye cokalin ta ce "Haba DSP, mutum nawa ne suke da vibe a birnin kano?"

"Ya ina magana kina nema ki raina mini hankali, wurin aikinki an ce baki je ba"

"Amma yaya ka san aikina ba na zama wuri ɗaya bane ba, yaya ka ke yi mini tmbaya kamar ka ritsa ƴar ta'adda ne? Wataƙila harkar aiki ne ta kaini wurin, bibiyata kake yi kenan? Ko kuwa meyafaru ko rashin yadda ya shiga tsakaninmu ne?"

Ya sauke numfashi ya ce "Gaba ɗaya kwanan nan kin canza Arfa, na je Division ɗin ungoggo kan wani case, a hanya na ga motarki, dan lambar motarki ce"

"Abokin aikina ne ya ari motar, suka fita, ta sa ta samu matsala. Sannan kuma ni ban canza ba, kai ne dai ka canza mini kwanan nan, ni ban san me nayi maka ba, duk ka tsane ni, ka daina goyon bayan gaskiya, ni na fara tsoron ko kaima ka fara karɓar cin hanci" tayi maganar tana ƙaƙalo kukan kissa.

Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "No ki fahimce ni, ke ɗin ce yanzu dole sai ana saka miki ido, kar wani abun cutarwa ya samar mini ke,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login