Showing 291001 words to 294000 words out of 479911 words
Jikinta ne ya ƙara saki, ta cigaba da bacci, tana yi tana surutai, a hankali har ta yi shiru. Ya sake haskata da fitilar sa, irin innocent face ɗin jauhar ta bayyana a fuskar Nabila. A hankali ya zare hannunsa daga nata, ya yinƙura ya tashi ya fita daga ɗakin.
Washegari da safe, sai tunanin mafarkin da tayi jiya take yi, tana tunanin gaske ne, ko kuma kawai mafarki ne?.
Da safe ana ta zuwa dubata, wajen ƙarfe sha ɗaya Nasir ya zo, lokacin babu kowa kasancewar ranar aiki ce, sai baba magajiya. Suka gaisa, ya aiki baba magajiya ya rage saura daga shi sai Nabila a ɗakin.
Ya zauna daf da ita a kan gadon, yana kallonta ya ce "Sannu ya jikin?"
Ta amsa da "Jiki Alhamdilillah, da sauƙi, zuwa gobe in Allah ya kaimu nake so na tafi ma, i have a lot to do"
Ya ce "Well, tambayarki zan yi, kuma bana buƙatar ki yi mini ƙarya, saboda zargina ya tabatta gaskiya ne a kanki"
"Wane zargin?"
"Nabila kin san in da Viper yake, kina haɗuwa da shi!"
Ta kalleshi ta ƙura masa ido amma bata yi magana ba.
"Ina magana kina kallona, na samu rahoton an ganshi a A.I hospital, naje bamu sameshi ba, amma naga signing ɗin ki, kin je asibitin me ki ka je yi?"
"Ni ganin likita naje, ka daina zargina tun da baka da wata hujja, mai asibitin aka tura ni wurinsa follow up, saboda lokacin da aka sallame ni, bai zo ba"
"Ƙarya ki ke yi Nabila"
"Ni ba ƙarya nake yi ba, ka fara samo tabattaciyar hujja, kafin ka ƙaryata ni"
Ya jinjina kai ya ce "Zamu gani ai, bayan duk wannan abubuwan hujja ki ke so na kawo miki? Shikenan zamu gani, amma ki sani aikinki ba zai baki kariya ba, muddin aka kama ki da laifi, sunanki yar ta'adda kema, mai ɓoye mai laifi"
"Abun kunya ne ga hukumar yan sanda ace sun gagara kama mutum ɗaya, da yake iya yawonsa a cikin gari, sai ma a din ga bibiyar wanda bai ji ba, bai gani ba, ana yi masa baranaza" tsananin fusatar da yayi, ya sanya kawai ya tashi ya bar ta a ɗakin.
Ta dafe ƙirjinta, saboda yadda yake tsananin bugawa, ta yanke a ranta dole tayi gaggawar fara shari'ar Viper, kafin ta kammala ta ramma.
Ya fita babu jimawa, baba magajiya ta dawo, ta karɓi aron wayarta, ta shiga banɗaki, ta kira wayar Walid, Allah ya taimaketa ya ɗaga.
Ya ce "Barrister ashe tsausayi ne ya faru haka, ya jiki?"
"Jiki da sauƙi, meyake faruwa ne? Yayana ya ce mini ya samu labarin Viper ya je asibiti, ina yake ina fatan babu wata matsala?"
"Eh, Yana nan cikin ƙoshin lafiya mun koma gida ma, haɗuwa yayi da ɗan Indabo a matsayin likitan da ya duba shi, shi ne ya sanarwa security"
Ta ce "Haba dai? Likitan da ya duba shi kuma? Garin yaya dole mu ƙara taka tsantsan amma ba abun da ya faru?"
Walid ya ce "Babu abun da ya faru, mun bar Asibitin ma, muna gida"
"Dole na haɗu da shi, nan kusa Allah ya ƙara afuwa" ta katse wayar ƙirjinta na cigaba da bugawa.
***
Indabo yana ta sanya ran ya ga ta ina Abdul zai ɓullo, ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda matsalolin da suke kunno kai, ya rasa wanne yakamata ma ya fara ƙoƙarin kawarwa.
Kwanaki biyu kenan, ko ya nemi Abdul a waya, baya samunsa. Kuma bai sake zuwa gida ba, hakan ya ƙona wa Indabo rai fiye da kima.
Viper bai sake neman Nabila ba, ko a waya, dama bata saka rai ba, dan ta san bata gabansa, idan ta tashi, Walid take kira ta tambaye shi ya jikin Viper, tana ta neman hanyar da zata bi, ta samu ta ganshi, dan sosai Nasir yake sanya mata ido yanzu, ya hanata sakat duk motsinta a kan idonsa, kasancewar motarta tayi damage, an kaita garrage wurin gyara, hatta wurin aiki shi yake kaita, da farko ya so ya Abba ya hanata fitar ma, amma ta din ga kuka, taba nuna wa Abba cewa akwai shari'oin da suke buƙatar ta yi attending.
Bayan ya ajiyeta a wurin aiki aƙalla yayi mintuna talatin a tsaye, ko da zata fito, sai da ya samu ɗaya daga cikin security na wurin, ya lambar wayarsa, ya ce masa idan ya ga fitar Nabila ya kira shi ya gaya masa, ya kawo alheri yayi masa sannan ya tafi.
Nabila kuwa a office ta iske barrister Habib, ya shirya tsaf zai fita, ta shiga da sallama.
Ya amsa mata ya ce "Sannu Nabila, ya hannun?"
"Hannu Alhamdilillah, fita zaka yi ne?"
Ya ce "Eh, zan je shari'a ne"
Ta ce "Mu fita tare, magana nake son mu yi da kai" ya ce "To shikenan babu laifi" suka fita suka shiga motarsa suka fice.
Kamar mai aljanu, suna tafe a hanya, ta ce "Ya ajiyeta, tayi mantuwa, office zata koma, ya ce zai kaita ta ce masa a'a, ta fice ta hau napep.
Viper ya buɗe ƙofar gidan zai fita, ya ganta a tsaye tana shirin shiga, ta saka hannu ta ɗage niƙabinta, suka yi ido huɗu ya ɗan tsura mata ido, ta faɗa sosai.
Ta ce "Ya jiki, ka warware?"
"Mmm"
"Zuwa nayi mu ƙarasa tattaunawa, ka fara yi mini bayanin shaidun da kake da su a hannu, zan fara gudanar da shari'ar ka, zan cigaba da yi tare da ta ramma, kafin su halaka ni, accident ɗin nan, da nayi, takani aka so yi da mota, garin na kauce musu, nayi accident" ya tsura mata ido, tare da haɗiye wani abu a wuyansa.
(Alhamdilillah ala kulli halin, ina godiya sosai da sosai addu'oin da ku ka yi mini, bisa ga rashin lafiya da nayi, Ubangiji Allah ya bar zumunci na gode ƙwarai)
Ayshercool
08081012143
70
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cigaba yayi da kallonta, ita kuma ta kasa sake ɗaga idonta ta kalleshi.
Yanayinta ya nuna sosai akwai damuwa a tare da ita.
"Kin fasa cewar ba zaki tsaya mini ɗin ba kenan?"
Ta jinjina masa kai ta ce "Eh, idan ma na fasa, zuciyata ba zata nutsu ba, alƙawari ne da nayi, yakamata na cika, ko ba dan kowa ba, dan wadda aka kashe ba da hakkinta ba" tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba.
Ya jinjina kai, a hankali ya furta "Ina zuwa"
Ya koma cikin gidan, tana tsaye ta bi ƙofar da kallo, ya fito ɗauke da jaka a hannunsa, ya ce "Muje" ba tare da ta san in da zasu ba, ta bishi. Sai da suka yi nesa kaɗan da gidan, sannan ya ja ya tsaya ita ma ta tsaya.
Ya samu wuri ya zauna, yayi mata nuni, ita ma ta zauna, ta sauke tata jakar daga bayanta, hannunta ɗaya an naɗa mata bandeji, in da ta samu gocewar ƙashin, sai dai hannun rigarta ya rufe wurin.
Ta ciro system ɗin ta, ta ajiye ta ajiye wayarta.
Ya zuba mata ido, bai yi magana ba, sai da ta ɗan ɗago ta ce "Wace shaidar da wace shaidar ce da kai, and dan Allah kar ka ɓoye mini komai, saboda kar sai mun je kotu, wani abu da ban san da shi ba, ya taso daga baya".
"Me ki ke son sani?"
"Shaidunka, da ka ce kana da su"
Ya ɗan lumshe idanunsa, sannan ya buɗe ya ce "Madaki, duk na yi masa illa, sai kuma babban yaronsa lakwari, duk suna wurina"
"Garkuwa kayi da su kenan?"
"Kusan hakan"
"Laifi ne fa ka aikata yin hakan"
Ya tari numfashinta ya ce "In sake su kenan?"
Ta ɗaga idonta, amma taga kallonta yake yi.
Jikinta ya ƙara sanyi, maimakon ta mayar da hankali a kan abun da take yi, sai hannunta ma ya hau rawa, wata irin ƙaunarsa ta din ga fizgarta, ji tayi tamkar ta ɗurawa kanta zagi.
Ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon fuskar system ɗin ta. Ta takure jikinta, ƙamshin turaren sa da warin sigari suka cika mata hanci.
Murya na rawa ta ce "Viper"
"Mmm"
"Ka sha sigari ko?" Yayi shiru bai bata amsa ba.
"Kar ka bari lafiyarka ta taɓu bamu gama shari'ar nan ba, kuma kaga ya fara taɓa maka internal organs, an ce hantarka ta kumbura"
Yayi shiru bai yi magana ba, sai kallonta kawai da yake yi.
"Akwai abubuwa da yakamata ka gaya mini, amma kamar kana ɓoye mini, yakamata idan kana ɓoye mini ka gaya mini, kar wani abu ya bamu matsala daga baya"
Har ta fitar da ran zai yi magana ya ce "Kamar me?"
"Suwaye suke goge laifukan ka idan ka yi? Ranar da muka je gidanka, ya aka yi ka gane jami'an tsaro a fararen kaya, har muka tsere musu? Wannan rigar da ka yaga a asibiti ta mecece? Kuma me kake yi da wayata da kake connecting?"
Viper ya yi gyaran murya ya ce "Wasu tambayoyin ba su da alaƙa da abun da yake gabanmu, amma na gane jami'in tsaro a farin kaya, saboda ni tsohon mai laifi ne, ba lokacin na fara aikata laifi ba, dan haka duk wani nuƙu-nuƙun jami'in tsaro sai na gano shi. Rigar da ki ke magana a kai, bata da alaƙa da abun da zaki yi a court. Wayarki kuma ina connecting ina duba wasu location, da tura saƙonni. Mai goge laifukana kuma ban sani ba. Sai kuma me?"
Nabila ta ce "To shikenan, nan da kwanaki biyu zaka ji ni in Sha Allah, zan har haɗa abun da nake buƙata, saboda yayana ya sakani a gaba da yawa"
"Good luck" ya faɗa a takaice, tamkar ta kurma ihu, ko sannu ya jiki bai iya yi mata ba, dan takaici ta tattare system ɗin ta, ta yinƙura ta tashi ta ce "Sai anjima" ya jinjina kai.
Jiki a sanyaye take takawa, kamar mara karsashi, ya waiwaya yana kallonta, yadda take ɗaga hannunta tana saukewa, ya tabbatar masa da kuka take yi. Sai da yaji zuciyarsa ta motsa, shi gaba ɗaya tausayinta ma yake ji.
Tana tafe a titi, barrister Habib ya kirata, ta ɗaga ya ce "Nabila kina ina ne?"
"Meyafaru?"
"Wai yayanki yaje ɗaukar ki, an ce masa mun fita, ya kira ni, wai muna ina?"
Guntun tsaki ta ja, ta ce "Rabu da shi dan Allah"
"A'a kamar yaya na rabu da shi? Kina ina ne, ni ya addabe ni"
"Wani wuri naje, ina kan hanyata ta komawa gida, ina son ma ganinka urgent, amma sai Allah ya kaimu gobe"
Ya ce "To Allah ya kaimu"
Ta amsa da "Amin"
***
Naja'atu Bunkure ta dubi Indabo ta ce "A haka ana wannan yanayin zaka koma Abuja?"
"To idan ban koma ba yaya zan yi, matsaloli sai kuma cakuɗewa suke yi"
"Dole fa a nemo Abdul, kuma ta wani fannin rashin kashe yarinyar nan yayi amfani, amma kuma ya tafka shirme da hauka, dan me zai ɗauketa ya je ya ɓoye, kuma saboda wulaƙanci yaje har gidansu da kansa, dole fa a nemo Abdul ya fito da yarinyar nan"
"Kin san ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, kin san a haukan yaron nan ce mini yayi, wai idan ya auri yar party chairman bayan aure zan bari ya auri wadda yake so, kawai ya yi mini wannan maganar, ban sani ba ita yake nufi zai aura ko wata oho"
"Taɓɗijan, lallai Abdul wannan karon ya ɗebo ta da zafin gaske, wallahi sai an yi taka tsantsan kafin a warware wannan shirmen da yayi"
Indabo ya yakice gumi ya ce "Na rasa makama gaba ɗaya, ga rayuwarsa na cikin hatsari, ya haɗu da mai zamani, wai yaron da ake ta nema ido rufe, shi ne yake yawon sa har da zuwa asibiti, tsoro ma nake ji, kar Vipern yayi masa wani abun"
Naja ta ce "Yanzu neman Abdul, shi ne abu mafi a'ala, ina tsoron yayi wani abun da zai tona mana asiri"
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Ni ɗan da na haifa, nake ta fafutuka a kan rayuwarsa yake neman ya kware mini baya, saboda mace, aishikenan da ina da wata hanyar da zan fito da jafar, da ƙyale shi zan yi, idan abun da yake bi a jikin nata ya gundure shi, sai ya dawo hayyacinsa"
Bunkure ta kwashe da dariya ta ce "Barewa bata gudu...
A fusace ya kalleta, ta haɗiye dariyar, tana mazewa.
***
"Nabila ina ki ka je daga wurin aiki? An ce kun fita da barrister Habib, na kira shi ya ce ba kwa tare.
"Eh, uzuri ne ya kamani, na je prison ganin wanda nake karewa ne, ko yanzun ma kana zargin wurin Viper na je?" Kawai ya gyaɗa kai ya fita.
Ta kwanta ruf da ciki, ta buɗe wurin da ta ɓoye videon da ta yi wa Viper, ta din ga kallon hotunan da video, tana ƙara jin yadda ƙaunarsa take mamaye zuciyarta.
Ta yi shiru, bata taɓa zaton zata tsinci kanta a irin wannan yanayin ba, duk yadda take kallon kanta, a matsayin mai class taga namijin da ya ƙure wa ajinta gudu.
Ta dinga shafa fuskarsa, ta kan screen ɗin wayarta, ta lumshe ido tana tuno muryar sa, da a zahiri mai ban tsoro ce, amma a baɗini daɗin sauraro take yi mata, da sanya mata nutsuwa.
Ƙarfe takwas da rabi, tana ofishinta, tana jiran barrister Habib.
Yana isowa, ta tashi ta tafi, ya ce "Yar ƙwalisa, yaya aka yi ne? Ya hannu"
Ta zauna ta ce "Hannu Alhamdilillah, yaya Habib"
"Na'am ƙanwa Nabila"
"Kamar yadda baka gajiyawa da ni, na sake dawowa neman alfarma a wannan karon"
Habib ya ce "To Nabila, me ni ke so?"
"Wataƙila wannan ta zama alfarma ta ƙarshe zan neman a wurinka, duk da akwai haɗarin gaske, amma yanzu burikana biyu ne, bayan ganin bayan Bunkure foundation, sai wanke Viper daga zargin da ake yi masa"
Da sauri ya ce "Kamar yaya?"
"Kamar yadda nake gaya maka, bana nufin na sanyaka a matsala, kamar yadda ka taimakeni kwanaki a kansa, yanzu ma ina neman taimakonka, dan Allah"
"Nabila, wannan wasa da rai ne fa, ke ya aka yi ki ka san ba shi da laifi? Tayaya zakinkare mutumin da hukuma take nema ruwa a jallo?"
Nabila ta numfasa ta ce "Zaka ga ta yadda zan yi, ni dai haɗin kanka nake buƙata da taimakonka"
Ya girgiza kai ya ce "Nabila matana biyu fa da yara uku, haka kurum ki saka su zama zawarawa da marayu, na gaya miki case ɗin sa yayi involving manya haka kurum ki ja mana fitina muna zaman lafiya"
Cikin marairaice wa ta ce "Dan Allah yaya habib, ba zan bari sunanka ya fito ba, dan Allah copyn file ɗin sa nake so, da aka yi masa shari'a shikaɗai nake buƙata"
Ya ce "Taɓɗijan, ke kin san uban process ɗin da na bi, aka baki ki ka gani wancan lokacin, balle yanzu kicw copy ki ke so"
"Dan Allah ka taimake ni barrister Habib"
Yayi shiru sannan ya ce "Gaskiya sai kin bani lokaci, dan wanan aiki ne da yake buƙatar ɓoyayyiyar gwagwarmayar "
Cikin farinciki ta ce "Zaka nemo mini ɗin?
"Zan jarraba ne na gani idan zai yiwu, ba alƙawari nayi miki ba"
Ta miƙe cikin farinciki ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuriya"
Ya amsa mata da Amin.
***
Ramma tana ta gogewa Abdul labcourt ɗin sa, ya daɗe a tsaye yana kallonta, wani irin matsanancin tausayinta ne ya mamaye zuciyarsa.
Ya ƙarasa ya zauna ya ce "Rahama" ta ɗago ta kalleshi.
"Ina da masu gugu fa, kaiwa nake yi ayi mini, ki ke wahalar da kanki"
"Ka ce zaka yi tiyata, shiyasa nake goge maka"
Yayi murmushi ya ce "Ai ba da labcourt muke shiga tiyata ba, kayan tiyata daban suke"
Ta ce "Ok, duk da haka ka saka wani lokacin"
Ya jinjina kai ya ce "Rahama menene babban burinki a rayuwa ne?"
Ta sunkuyar da kai ta ce "Ka mayar da ni wurin mamana"
"Na san da wannan, zan mayar da ke, burinki na rayuwa?"
Ta ɗago idanu ta kalle shi ta ce "Babu"
Ya ce "Kamar yaya? Kowane ɗan Adam yana da buri da yake son cimma a rayuwarsa"
Rahama ta kashe socket, ta kalleshi ta ce "Wace rayuwar? Rayuwar da ka gama kassarawa wane buri ne yayi mini saura? Ka mayar da ni wurin mahaifiyata na ƙarasa rayuwata shikaɗai ne roƙona a gareka, amma ba ni da wani sauran buri da nake da shi, gaba ɗaya rayuwar ta fita daga raina, babu abun da yake burgeni yake bani sha'awa".
Abdul ya koma kusa da ita ya zauna, ya ɗan tsura mata ido, ita kuma ta kawar da kanta gefe ɗaya.
"Dukkanin mai rai baya fitar da rai, da cimma burikansa na rayuwa, na san ni ne musababbin rushewar naki, amma haryanzu ina dana sanin abun da na aikata, amma zan cika miki burinki Rahama, zaki koma makaranta kiyi karatu mai zurfi in dai muna tare in sha Allah, makaranta mai kyau zan mayar da ke, na gyara makarantun garinku, kuma an karɓi ƙudurin gyaran hanyarku, aiki yayi nisa na yi muku boreholes kamar yadda nayi miki alƙawari, idan aka kammala zan nuna miki"
Maimakon ta yi magana, kawai sai ta fashe da kuka.
Cikin damuwa ya ce "Rahama menene kuma?"
"Ni duk bana son wannan abubuwan, kawai na koma gidanmu na ƙarasa rayuwata, babu wani abu da zan zama a rayuwa da zai katange ni, daga tsangwamar da zan fuskanta a cikin al'umma, wannan ɗabi'a ce ta hausawa"
"Ina tabattar miki da idan muna tare, babu wanda zai tsangwame ki, wasu shirye shirye nake yi ne, da sun tabatta in sha Allah zamu je ki ga mama, amma babu maganar rabuwa tsakaninmu, ba sai na bar ki a tsakanin hausawan ba ma zau yi miki, ki daina damuwa Please bana so"
Wayarsa ce ta fara vibrating, ya ɗaga ya ce "Yeah Salim ya ake ciki ne?"
"Wai ina ka shiga ne? Mummy ta kira saifu a waya, wai an nemeka a waya an rasa, ya ce mini shi ma baya samunka a waya, ni kaina kwanana biyu kenan ina nemanka yanzun ma ban zaci zan sameka ba, nace bari na jarraba kiran wannan layin naka"
Abdul ya numfasa ya ce "Akwai damuwa ne Salim, mu haɗu a gidana na by pass"
"To shikenan, ka san nina har ta gaji da nemanka ita ma, har clubs ka daina zuwa, gidanka da take samunka ma yanzu baka zama, kuma ta daina samun wayarka, na ce mata kayi busy ne da shirye shiryen siyasarka"
Abdul ya ce "Manta da ita, zan je asibiti zan yi tiyata da daddare, idan na kammala ko kafin na tafi, sai mu yi magana sai mu haɗu"
"To shikenan, sai na ji ka"
***
Walid ne ya ƙarasa in da Viper yake a zaune a kan dutsen nan, yayi shiru