Showing 396001 words to 399000 words out of 479911 words

Chapter 133 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6108

Alhamdilillah ko iya haka na samu raguwar wata azabar da nake ji".


***
Rahama ta kasa bacci, ta kasa cin abinci, nan Nabila ta ƙara tabattar da soyayya bala'i ce wani lokacin. Duk wannan bala'in da ake yi a kanta, ita hankalinta ya na kan mijinta.

Haka Nabila ta yi ta aikin rarrashinta. Washegari ta kashe wayoyinta, ta ɗauki ramma aka kai su prison.
Sai dai aka sanar musu, Abdul ba zai iya fitowa ba, Albarkacin ID card na aiki, da yadda Nabila ta fara tashe, aka ba su damar shiga cikin prison har ɗakin da Abdul yake.

"Subhanallah" ramma ta furta, ganinsa a kwance ruf da ciki, bayansa a farfashe saboda bulalar alƙali da ya sha.

Ta ƙarasa in da yake da sauri, ya ɗago da kyar, jikinsa ya na karkarwa saboda zazzaɓi, Abdul zai iya cewa da wayonsa babu wanda ya taɓa dukansa, amma yanzu ga shi ya sha duka, hakan ya haifar masa da zazzafan zazzaɓi.

"Abdul" ta faɗa a raunane ta na kuka.

"Rahama zafi, bayana kamar ana ƙona ni"

"Ka yi haƙuri Abdul, dan Allah ka yi haƙuri, ban ma san me zan ce ba" tayi maganar cikin kuka.

"Ai an sassauta mini, ta wani fannin na ji daɗi da wuri zan fito in sha Allah, ni zan karɓi haihuwar ki da kaina" yayi maganar yana kwanciya a jikinta.

Ta haɗiye yawu mai zafi, ta ce "Abdul da sun bi ta tawa, da na daɗe da furta musu na yafe maka, babu yadda mu ka iya, ƙaddaramu ce ta zo a haka. Amma ka yi haƙuri na yi maka alƙawarin duk rintsi idan ka fito in sha Allah mu na tare"

Ya ɗago da kyar ya kalle ta ya ce "Are you sure, kar ki saka mini rai fa"

"Na tabattar in sha Allah"

"Wallahi ina sonki sosai rahama"

Nabila ta na tsaye ta na kallon ikon Allah.

****
Viper ya na ta shiri zai je wani aiki na musamman cikin sirri, wayarsa ta fara ringing, bai damu da duba waye ba kawai ya ɗaga.

"Aminu Viper"

"Ma'aruf Indabo" ya amsa masa kai tsaye.

Indabo ya ce "Ban yi mamakin saurin ɗaukar muryata da ka yi ba, kai a nan ka dage ka haɗa kai da kankarofi a kan lallai sai kun ga bayana, yanzu ka kafe kai da fata, saboda yar matsiyata ƙanwar Nura guduma, an kai mini ɗa gidan yari, to bari murna karenka ya kama Zaki mai zamani. Za a sake ni daga ɗaurin talalar da aka yi mini, sannan ka shirya abubuwan da ka iya biyo baya da ba ka yi tsammani ba. Za a ci gaba da zaman kotu a kan shari'ar matarka, amma ka sani reshe ka iya juyewa da mujiya, ka tsammaci abin da ba ka taɓa zatonsa ba a kotu".

"Gargaɗi ka ke yi mini? Ko alhinin kar asirinku ya tonu a kotu, idan gargaɗi ka ke yi mini kar na kama sunanka, ka kwantar hankalinka, ai an san da wuyan biri ake ɗaure shi a ƙugu, kai tsaye waɗanda su ka kashe matata kawai za a hukunta, sannan ka din ga sassauta lafazinka idan ka na magana da ni, saboda ni ke da makami mai linzamin ƙarasa tarwatsa rayuwar iyalinka, idan ka ƙi ji ba ka ƙi gani ba. Na san babu abin da za ayi maka ko da kuwa an ambaci da saka hannunka a ta'addancin da aka yi mini. Zan yi dragging ɗin ka zuwa kogon da ramina yake ne, na yi ta azabtar da kai da dafina, zuwa abin da hali zai yi. Amma ina P.A ɗinka yake ne? Kwana biyu ba a ganin gilmawarsa yakamata ka yi tunani a kan wannan" ƙit ya kashe wayar.

Ayshercool
08081012143

94
Viper ya ɗan ja lokaci ya na kallon wayarsa, ya na tunanin mai indabo yake shiryawa, da har ya samu ƙwarin gwiwar kiransa ya na yi masa surutan iska. Kodayake bai kamata ya ce surutan iska ba, domin kuwa a rashin imani irin na indabo babu abin da ba zai iya aikatawa ba.

Lambar Nabila ya yi ta kira, amma a kashe ba ta shiga, dan haka ya haƙura ya ci gaba da shirin fita.

Ramma ta yinƙura ta ce "Bari mu tafi, na san ba dan albarkacin Anty Nabila ba, babu yadda za ayi a bari na shigo har na ganka, Allah ya baka lafiya ya baka ikon cin jarrabawar nan. Ba an hukuntaka da an tsaneka bane ba, ina fatan tuban da ka yi ya zama taubatan nasuha, kuma wahalar nan Allah ya sa ta zame mana kaffara baki ɗaya mijina" ya ɗago ya kalleta ya ce "Kai, rahama baki taɓa kirana da sunan da na ji yayi tasiri har cikin zuciyata kamar yau ba, da har nake jin eh lallai kin yafe mini ba. Yanzu kin yadda ni mijinki ne?"

Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Ai zamantowarka mijina tuntuni na yarda da wannan, da ban yadda wannan cikin ya samu ba" murmushi ne ya suɓuce masa, ta tashi ita ma ta na murmushin, ta fita daga ɗakin har ta fice ya na daga ruf da ciki ya na kallonta, duk wannan wahalar da yake sha, ko sau ɗaya bai ji wani abu daga son da yake yi mata ya ragu daga zuciyar sa ba.

***
Nabila ta biya ta ajiye ramma a gida, sai dai ramma ta fuskanci mama ta sassauta fushin da take yi da ita, saboda ta ɗan samu sassauci saboda hukunta Abdul da ta ga an yi.

Barrack Nabila ta koma, dan ita kanta ta ɗan tsorata da musayar yawu da su ka yi da Najar bunkure, dan ta san ba imani ta cika ba, amma da ta tuna da furucinta na cewar Jinin jauhar ya tafi a banza, sai wani nannauyan abu ya soki ƙirjinta.

Kusan da ciwon mara ta wuni, daurewa kawai take yi, su ka ci abincin dare tare da madam Halima, ta na ta ba wa Nabila labarin yadda aka kashe mijinta, da yadda ta zama soja.

Nabila ta ce "Taɓ sannu da ƙoƙari Mummy"

Madam ta ce "Daughter ke ma fa za ki iya zama sojan nan, ki zama military lawyer. Ga Mijinki soja na musamman ke ma haka"

Ta kalleta ta ce "Waye mijin nawa?"

"Ahh Viper mana"

Nabila ta ce "Taɓ ba zan iya ba, gara na auri civilian irina, ni fa idan ki ka ɗauke tsiwa daga nesa nesa, ko gadin ƙofa ba zan iya balle wani soja, ko 'yar agaji ba iyawa zan yi ba. Da ne da bani da hankali na ce wa Abba soja zan zama, ya ce ban isa ba, daga baya na fuskanci da na zama sojan, ba za ayi abin arziki ba"

Madam ta ce "Haba dai, kar ki bayar da ni mana, and kuma ba soyayya ku ke yi da Viper ba, ba shi ne zai aure ki ba?"

"In ji wa? Mijin sister na ne fa"

"Ehenn your sister is late, and ba haramun bane a addinin musulunci, soyayya fa ku ke yi ina kallonku"

Nabila ta ɓata fuska ta ce "Mummy ba ki gani dai-dai ba, ni fa marata ce take ciwo, gashi zuciyata sai tashi take yi kamar zan yi amai"

Madam ta ce "Sannu, ko za ki je ki kwanta?"

Abu kamar wasa Nabila ta gagara bacci, sai da madam ta kaita clinic, aka yi mata allurai ta dawo ta kwanta.

Cikin dare madam Halima ta tashi ta na sallar dare, ta din ga jin ringing ɗin wayar Nabila a falo, ta fito ta kashe, ta ga Vi snake.

Ta ɗaga ta ce "Snake ka ke kiran yarinyata cikin dare haka me za ta yi maka?"

Viper ya yi murmushi ya ce "Important issue ne shiyasa na kirata"

"Salon ka hanata bacci, ba ta jin daɗi ne, bamu daɗe da dawowa daga clinic ba, ta samu bacci menstrual cramps ne yake damunta, ta na ta ciwon mara ta sha allurai dai, har da kuka dan sangarta. This your wife is not brave at all, lazy citizen"

Murmushi Viper ya yi ya ce "Thank God ke ki ka faɗa ba ni ba, ayi mata sannu sai da safe".

"To shikenan sai anjima" ta kashe mata wayar ta ajiye.

Da safe ta ga Nabila ta shiryo cikin uniform ta ce "Kin ji sauƙi za ki iya zuwa aikin ne?"

Nabila ta ce "Eh Mummy, da sauƙi sosai"

Ta ce "To Alhamdilillah, come and have your breakfast".

"I have no appetite, zan samu wani abu na ci, zan haɗu da Joseph a bakin gate, zan tafi". Suka yi sallama Nabila ta fita.

Babu shari'ar da za ta halarta, dan haka ta na office ɗin ta, ta na ta aiki, zuwa ƙarfe sha ɗaya na safe, ta ji yunwa ta addabeta, ta ajiye aikin ta fita.

Ta fita babu daɗewa sai ga Viper ya zo.

Ya tarar ba ta nan, amma yadda ta bar ƙaramar wayarta da jakarta ya tabbatar masa da ba nisa tayi ba.

Ya ƙarasa gaban teburin, ta ajiye cake ga kofin tea da madara da milo, da alama tea za ta sha, ya janyo drowern teburin, nan ma ya iske gugguru da tarkacen alawoyi. Ya girgiza kai, a dai-dai lokacin ta buɗe Office ɗin ta shigo, hannunta riƙe da leda.

Ta ce "Binciken me ka ke yi mini waye ya baka iznin shigo mini office ma?" Tayi maganar tana ƙarasawa.

Ya ɗago ya kalleta ta ga idanunsa jawurrr.

"Ba ciwon mara aka ce ki na yi ba, amma ki ke cin wannan kayan zaƙin?" Yayi maganar ya na tsareta da idanunsa.

"Waye ya ce ina ciwon mara?" Tayi maganar ta na zaro ido.

"Madam, na kira jiya da daddare ta ce kun je asibiti, and yanzu kalli tarkacen abin da ki ke ci, ko tausayin kanki ba kya ji. Duk ranar da ki ka zo haihuwa zaki yi bayanin wannan zaƙin da ki ke ci ba yau ba gobe saboda basir"

Murmushi ta yi ta ce "Ba sai in zan haihun ba, adopting ɗin baby kawai zan yi, banda haihuwa dan tsoro nake ji, akwai wahala, idan ma zan haihu irin ɗayan nan is ok"

"Saboda ke haka aka yi miki? Ko kuma dan ke ki ka tsara wa kanki rayuwa?"

Ta ce "No ai yarjejeniya za mu yi da babyna kafin mu yi aure, banda haihuwa" ƙura mata ido yayi, ya na lumshe su a hankali.

Ta ce "Bari na wuce, kai ma sai na sammaka, ko ya aka yi ma ka san cin zaƙi na saka basir.....

Kan ta ƙarasa maganar ya ce "Am once married"

Ta ce "Eh haka ne, matsa na wuce to, bobon zan sammaka ko za ka ci gugguru. Wato bincike ma ka yi mini, duk ka kwaso mini kaya, ka ajiye a kan tebur" tahowa yayi zai faɗo a jikinta, ta ja baya kaɗan a tsorace. Ya dafe teburin ya na sauke numfashi.

Jiki a sanyaye ta ce "Vi" ya ɗago jajayen idanunsa a wahalce ya kalleta.

"Again? Me ka je ka sha ne? Na za ta ka daina gaba ɗaya, sai abin da ba a rasa ba. Ka yi shaye-shaye kuma ka taho hanya ba ka tsoro wani abu ya sameka? Me aka yi maka ma ka je ka sha kayan maye? Waye ya ɓata maka rai"

Ya kuma jan numfashin, ya na lumshe ido.

A hankali ya ce "Am so much thirsty, ina shan baƙar wahala, saboda daina ta'amalli da kayan maye. Idan ƙishirwar shan ta taso mini, sai na ji kamar zan bar duniya idan ban sha ba, is not that easy rabuwa da shaye-shaye" yayi maganar kamar zai faɗi ya na lumshe ido.

"Me ka sha?" Ta tambaye shi cikin damuwa.

Fito mata da dogon harshensa ya yi, duk ragowar farin ƙwayar da ya sha.

Ta ce "Guda nawa ka sha?"

Ya ɗago mata yatsunsa guda uku.

Ya ce "Uku ne kawai, ban sake yi wa kaina allura ba ai, tun da ki ka shigo rayuwata, ki ka bani ƙwarin gwiwa da tabbacin zan iya sake rayuwa kamar kowa.
Kin san da ba sa ɗaukata, yanzun ma ban yi tunanin za su ɗauke ni ba, sai da na zo nan gabanki, kawai su ka fara ɗibata, dole sai sun tona mini asiri" yayi maganar yana murmushi tare da layi.

Ta numfasa ta ce "Muje ga kujera ka kwanta" juyawa ya yi yana neman kujerar, ta riƙe hannunsa, har kan kujerar.

Ya hau ya kwanta a kai, ya na lumshe ido.

Ta kalle shi ta ce "Idan ka sake shan kayan maye, sai na gaya wa 'yar madara, dan ka san ba ta mutu ta barka a kan wannan tafarkin ba"

Ya ce "A'a Abla"

"Idan ka kuma sha sai na gaya mata, duk ka ɓata mini rai ban ji daɗin ganinka a haka ba. Kamar ma na yi kuka wallahi"

"Sorry ba zan sake ba in sha Allah" yayi maganar bacci nannauya ya na kwashe shi.

Ta tashi ta koma kan teburinta, dan cin abinci, ta na yi ta na gudanar da aikinta, ƙarshe ta ture system ɗin ta kifa kanta ta hau bacci, domin daren jiya ba ta samu isasshen bacci ba, saboda ciwo.

***
"Yaron nan ya fara bani tsoro, wai tambayata yake yi, in da P.A yake, ina tsoron kar na je ya san wani abu fa"

"Indabo, ka kwantar da hankalinka, babu abin da ya sani, kuma babu abin da zai faru, kawai zunzurutun barazana ce"

Indabo ya girgiza kai ya ce "Babu lallai barazana ce, shegen yaro ne fiye da yadda ka ke tunani. Ga waɗancan asararrun jarababbun yaran sun sako ni a gaba, yanzu Kanon nake son shiga amma har fargabar hakan nake ji, amma hakanan zan je na gano Abdul.
Wallahi zaman prsion ɗin Jafar bai ɗaga mini hankali ba, kamar na Abdul. Gidajen yarin Nigeria da babu gyara, babu kula a haka yaron nan yake rayuwa, wai a haka an yi masa sassauci saboda wata banzar yarinya, kodayeke ko ma menene shi ne ya janyo wa kansa ai"

Mutumin ya ce "Ka yi haƙuri distinguish, yaran namu ne ka haife su, amma ba ka haifi halinsu ba, kuma duk kankarofi ne kanwa uwar gami, tun da shi ne yake amfani da ƙarfin ikonsa, ya hana ruwa gudu ko ta ko ina"

Cikin takaici Inadabo ya ce "Could you imagine Alhaji Sada, yaron nan kuɗin da ake tuhumar nan tawa a kai, ware su aka yi saboda campaign ɗin sa, amma saboda sakarci wai ya tattare kuɗin a kan tsinanniyar yarinya 'yar ƙauye, kuma hakan bai yi musu ba, sai da suka kai shi gidan yari, har da duka. Shi kansa alƙalin ba zan bar shi ba dan uwatar. Wani baƙin ciki da takaici da maimuna take gaya mini, wai yarinyar ciki ne da ita, ta cewa Abdul a zubar wai ba za a zubar ba, gaba ɗaya mutuncina da kimar siyasata ya zube, ban da Abdul ɗa na ne, da sai na yi masa aiken da babu dawowa. Amma ina nan ina shiri, Sai an kashe banzan yaron nan Viper, duk wata fitina shi ne yake ƙara kunnota. Gashi yarinyar nan 'yar jarida twins ɗin matarsa ce, daga rahotannin da na samu. Shiyasa farkon ganina da ita na tsorata, na saka aka yi mini bincike a kanta, amma gaba ɗaya nasabarta ba ta yi alaƙa da shi ko waccan matar ta sa da aka kashe ba. Saboda mugun rainin wayo, shi ma wancan wawan, wai ya na bincike amma a gidansu yarinyar na haɗuwa da Viper bai sani ba, shi ma sai na ɗauki mataki a kansa"

Honorable Sada ya ce "Duk dai ka yi haƙuri ka kwantar da hankalinka, ai mun gama shirya komai, aiwatarwa ce ta rage. Kuma muna da tabbacin za a sami mafita"

Indabo ya jinjina kai da alamar gamsuwa da maganganun honorable Sada.

***
Barrister Habib ne ya shiga office ɗin Nabila, ya tarar da Viper a miƙe a kan kujera ya na bacci, Nabila kuma ta kifa kai ta a kan tebur ta na bacci.

Gaba ɗaya sai ya ji babu daɗi, wani irin matsanancin kishi ya na taso masa, duk da ya san ko da me yake yawo, Viper ya fi ƙarfin yayi takara da shi, duk haryanzu bai gane in da suka dosa ba, daga ita har Vipern, amma kusancinsu yayi yawa.

Ya ja da baya ya mayar da ƙofar ya rufe, ya na rufewa Viper kuma ya buɗe idonsa, ya bi ƙofar da kallo, ya mayar da idonsa kan Nabila da take baccinta a nutse, kamar ta samu gado.

Ya daɗe ya na kallonta, sak 'yar madararsa yake gani, duk da akwai tarin banbancin halaye tsakanin Nabila da jauhar, amma akwai abubuwan ta da suke burge shi, she's very straightforward, very silly and arrogant.

A hankali ya tashi ya kalli agogo, ya fice yaje ya yi salla, har ya dawo Nabila bacci take yi, kodayeke ba abin mamaki bane ba, ko lokacin da yana tare da jauhar, idan tana period kamar mai laulayin ciki, bacci ciye-ciye da saurin kuka.

Ya daddaki teburin da ta kwantar da kanta, amma shiru ba ta motsa ba, "Ke wani daren za ayi miki ne?" Still ba ta motsa ba.

Bayanta ya zagaya ya ja kujerar da take kai baya kamar za ta faɗi, razana tayi tare da yin wani ɗan marayan ihu.

Ya ƙura mata ido ya ce "Ki tashi haka mu yi maganar da ta kawo ni"

"Na ji amma ka ajiye ni mana kar na faɗi"

A hankali ya mayar da kujerar, amma ya sunkuyo ta bayanta dai-dai kunnenta, kamar zai yi magana, sai kuma yayi shiru, ta din ga jin saukar numfashin sa a jikinta.

Kame jikinta tayi, ta ce "Bari na wanke fuskata, sai mu yi maganar" ta tashi ta nufi toilet.

Ta dawo ta zauna ta kalleshi ta ce "Ka watstsake?" Ya ɗaga mata gira.

Ta ce "Alright, ina jin ka, meyafaru?"

"Inadabo ya kira ni jiya, kuma tabbas tun da ya kira ni, akwai abin da ya taka yake jin ƙwarin gwiwa, har ya kira ni, amma menene shirinki ke yanzu?"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Alhamdilillah, dai-dai gwargwado muna da abin da ya sauwwaƙa, Bunkure na ta dragging ne to sai ta faɗi ɓarnar da ka aikata a baya"

"Nabila ba fa zan koma prison ba" yayi maganar very serious.

Ta waro ido, sai kuma ta ɓata fuska "Nabila kuma garangatsau ba Ablan"

"Am very serious, kin san masifar gidan yari, ba fa zan koma ba"

Nabila ta ce "Easy, in sha Allah ba abin da zai mayar da kai prsion, amma Vi"

Ya kalleta. Ta kwantar da murya ta ce "Ina ganin yakamata mu fara zuwa kana ganin likitan ƙwaƙwalwa sab...

Haɗiye maganar ta yi, saboda ganin kallon da ya yi mata.

"Kallon mahaukaci ki ke yi mini kenan?"

Da sauri

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login