Showing 465001 words to 468000 words out of 479911 words

Chapter 156 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6157

aka dawo, shi ne rufin asirinki, kuma sai hankalinki ya fi kwanciya, amma ki yi tunani a kai"

Bayan tafiyarsa ta din ga tunani, ƙarshe dai maganar tayi ta cin ta, take gaya wa ramma.

"Amma na ji daɗi mama, babu abin da zamu cewa yaya Aminu sai Allah ya saka da alkhairi, da har ya ce ki auri mahaifinsa"

"Ramma ni gani nake yi abin bai yi tsari ba, goɗai-goɗai da ni na hau yin aure?"

"Mama ai mu ma sai mun fi jin daɗi ace ki na da aure, aure security ne, dan Allah ki amince kar ki ce a'a"

Ta ce "Ai abin ne sai a hankali, amma zan yi addu'a dai"

"To sai mu tayaki addu'ar, kin ga nan gidan ma, bamu sani ba ko Daddy zai yi amfani da abin sa, kin ga ya yi mana ƙoƙari, kalli shi yake ciyar da mu, yake yi mana komai, kin ga kuma yau da gobe sai Allah. Amma idan aure ki ka yi ai mijin ba zai gaji ba, tun da hakkinsa ne" shiru ta yi tana kallon ramma, tabbas maganganunta haka suke, ita ba ma tayi wannan tunanin ba, dan haka ta ce "Kuma fa da gaskiyar ki rahama, amma ni duk na fi son na ga kin tare tukuna a naki ɗakin"

"Eh, ya ce babansa ya bar ƙasar, ya kuma gama gyara in da zamu zauna, ya canza shawara yanzu, wai zan tare amma fa har kayan ɗakin duk ya saka"

Mama ta ce "Ai ni wannan mijin naki, rigimarsa ta yi yawa, na ma daina ce masa ya bari, Allah ya taimaka" ramma a zuciyarta ta amsa da Amin.


Nabila kuwa fafur ta daina sauraren Viper, duk rarrashin da ya so yi mata, fafur taƙi tsayawa ta saurare shi.

Zata dafa abinci ta bashi, da duk wani abu da yakamata ta yi masa, amma ba ta zama in da yake, babu hira babu duk wani abu na soyayya da take yi masa.

Duk yadda yake murnar hutun da ya samu, zai zo su samu isasshen lokacin da zai bata kulawa da soyaya, amma komai ya ɓaci.
Zaman gidan ma ya daina yi masa daɗi ko kaɗan, duk ɗaukinsa da son kasancewa da ita, yanzu fargabar tunkararta ma yake yi, dan sam babu fuskar hakan, sai yayi ta maza yake iya tunkararta, shi ma sai dai yayi kiɗansa da rawarsa shikaɗai.

Sosai yake jin tausayinta, sai dai taƙi ba shi damar ya fahimtar da ita abin da yake son ta sani.

'yan gidan Nabila su suka zo mata wuni, har da Walida da baba magajiya, dama bata saka ran ganin Sauda ba, har da Anty.
Ta ji daɗin zuwan na su, kuma babu wanda ya fuskanci tana da damuwa, suka wuni suka yi wasa da dariya, sai da ta ji kamar kar su tafi.

Abu kamar wasa, Viper ya daina cin abincin Nabila, idan ma ta ajiye ba zai ci ba, ya koma kwana a ɗaya ɗakin, hakan ya saka a jere kwana biyu baya kwana a gida ba ma ta sani ba, sai kwana na uku, da bata ganshi a gidan ba, wunin ranar.

Bayan magariba sai ga Walid, ta yi masa maraba ta karɓe shi hannu bibbiyu, bayan sun gaisa ya ce "Barrister, meyafaru ne tsakaninki da mai zamani, muna murna an yi aure komai kuma zai wuce, shi ma zai samu nutsuwa yanzu ya ji daɗin rayuwa kuma sai a fara rigima?"

"Wani abin ya ce na yi masa?"

"Bai faɗa ba, amma alamu sun nuna, kamar a gidan da muka zauna yake kwana, me yayi zafi haka?"

Cikin mamaki ta kalle shi ta ce "Kwana kuma? A can yake kwana?"

"Wallahi Nabila da gaske nake yi miki"

Kawai ta fashe da kuka ta ce "To ni ya zan yi ne? Duk iya ƙoƙarina baya gani, Jauhar ce kawai a ransa, ni ba ni da wani gurbi a zuciyarsa. Zuciya ce fa a ƙirjina, ina son 'yar uwata, amma abin da yake yi mini yayi yawa. Muna tare da daddare har ya kwanta ya ce mini fita zai yi, sai ji na yi kuna waya, wai gidan da suka zauna ya tafi, a wannan daren ni bani da amfani kenan? Ba zan hana shi tuna Jauhar ba, amma ni fa? Kodayeke dama ni na ce ina son shi, dole na jure duk abin da zan gani"

Walid ya ce "Subhanallah, kuskuren fahimta ne Nabila, tun yamma muka yi magana da shi, ya ce mini ya ji wani wa'azi, an ce gado nauyi ne a kan mamaci, har sai an raba ake sauke masa wannan nauyin.
Shi ne ya ce mini tun da kema gaki, kina cikin magadanta, zai je ya duba gidan, yayi magana da su Baba, ina ga tun zuwan da ku ka yi, bai sake zuwa ba.
Da safen ma, da muka yi magana ce mini yayi abin ne yake ta damunsa, ya kasa bacci, ya ji bai kyauta ba ace tsawon wannan shekarun ba a sauke wa Jauhar nauyi ba, kuma baba bai yi masa magana ba, kawai ya fita a daren, ya je ya sake dudduba gidan, ba wai dan baki da amfani ba ne ba Nabila.
Wallahi kulawar da ki ka samu, Jauhar ba ta sameta daga gare shi ba shi fa yanzu duk wannan abin da yake yi, ihu ne bayan hari kawai, amma wallahi yana sonki Nabila.
Kin san sunanki da nasa ya hargitsa ya fitar da sunan da yake kiranki da shi Abla? Ki din ga yi masa uzuri, a hankali zai daina, zamansa da Jauhar ba abu ne da zai manta lokaci guda ba, yarinyar ta sha wahala ne sosai, kuma ba ta wani more shi ba, an kashe ta a dalilinsa. Da bakinsa yake faɗar ki na da haƙuri matuƙa da kawaici, amma ina ƙara baki haƙuri, dan Allah ku sasanta"

Tayi ajiyar zuciya, ta jinjina kai ta ce "Wallahi ina yi masa uzuri, shi ma ai ya sani amma In sha Allah zan ƙara, na gode sosai da sosai "

"Yauwwa Nabila, ai wallahi tun da ya ce mini wai kin goyi bayan soyayyar liti da ƙanwarki na sara miki, ba ki da riƙo, kuma ki na da haƙuri sosai da sosai, Allah ya baku zaman lafiya ya ƙara muku fahimta juna"

Ta amsa da Amin, tayi ta masa godiya, ya tafi.

Kamar ta kira Viper a waya, sai ta ƙyale shi, sai da gari ya waye, tayi girki ta shirya ta fita.

*****
Cikin matsanancin tsoro da fargaba, indabo ya sauka a airport, yana ta tunanin abin da ka iya faruwa, na sharrin da Bunkure ka iya ƙulla masa.

Sai dai ya ga ya wuce airport lafiya, babu abin da ya faru, har ya isa masaukinsa, bai haɗu da wata matsala ba.

Ya kira abokansa ya sanar musu takardar da Bunkure ta aiko masa da ita, suka bashi ƙarfin gwiwar ka da ya damu, barazana ce kawai ba wani abu ba, yayi zamansa zuwa lokacin da komai zai daidaita.

Kankarofi kuwa yana ta campaign ɗin sa, na takarar sanata, kujerar da Indabo yake kai.

Kuma yana ta ci gaba da samun karɓuwa ta kowace kusurwa.
Jidda ƙanwar indabo kuma tana ta nacin sai ta koma ɗakinta.

***
Kamar daga sama haka Viper ya ji sallamar Nabila, sai dai bai iya amsa mata ba, cikin ɗakin ta shiga, aikuwa ta same shi a zaune a kan katifa.

A ranta take mamakin halinsa, daga samun saɓani yayi yaji, ƙasan zuciyarta, take addu'a Allah ya sa bai sha wani abu ba.

Ba ta ce masa komai ba, ta ajiye flask ɗin, ta ƙarasa kusa da shi ta zauna, bai kulata ba, ta saka hannunta ɗaya a bayansa, ɗaya kuma ta juyo fuskarsa ya kalleta, ta marairaice ta ce "Na zo biko ne, am sorry Vi, son da nake yi maka ne ya janyo komai, kuma tunanin da nake yi, ba ni da matsayi a wurinka ne ya sanya nake shiga damuwa, but am sorry" bai yi magana ba ya ci gaba da tsareta da idanunsa.

Ta shafa fuskarsa ta ce "Talk please" kamar gunki yaƙi magana.

"Please talk Vi"

"I love you" yayi maganar yana tsareta da ido.

Idonta ne ya ciko da hawaye ta ce "And you mean it?" ya jinjina mata kai alamar eh.

Rungume shi ta yi, hawayen farinciki na zubowa daga idanunta, gadon bayansa take shafawa zuwa kansa ta ce "Dama zaka iya bani gurbi a zuciyarka?"

"Na daɗe da baki Abla, baki yadda da kanki bane ba, shiyasa ki ke ganin kamar ba da gaske nake ba. Tashin hankalin da na shiga, da na ji an ce gado nauyi ne, ya sanya na kasa jurewa na tafi a daren, communication gap aka samu a tsakanin mu, dole mu zama masu saurarar juna da yi wa juna uzuri domin zaman auremu ya ɗore kuma ya yi daɗi.
Na yadda ke ba Jauhar ba ce ba, kuma ina ƙoƙarin na rayu da ke a Nabilanki, amma sai kin yadda da kanki, kin kuma rage zargi.
Abla ina yawan gaya miki Al'amin ba butulu bane ba, bana manta halacci komai ƙanƙantarsa kuwa. Balle ke naki da ceto raina, hankalina kacokan ki ka yi, rayuwarki ki ka saka a hatsari mai ban tsoro ki ka ceto ni, tayaya zan zama butulu, a ɗakin nan na kusa ajalinki, amma bai hanaki ci gaba da bibiyata ba, wane irin butulu ne ni da zan kasa buɗa miki zuciyata ki shiga? Ki manta da matsayin Jauhar a zuciyata, ki kalli kanki ke ɗaya kawai, wasu lokutan wasa nake yi miki a wasu abubuwan, amma tun da ba kya so, in sha Allah na daina, amma ina ƙaunar 'yar sugar, wannan kalaman ko 'yar madara ban taɓa gaya wa ba, sau ɗaya na taɓa furta wa jauhar ina sonta a rayuwata, daren da za a kasheta, amma ke ba na son na maimaita wannan kuskuren ina sonki Nabilatul arfa, Ablana kuma 'yar sugana"
Ita kanta ba ta san takamaimai kukan me take yi ba, ya ci gaba da rarrashinta, da duk kalaman da shi kansa bai san ya iya su ba, tare da ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa.

A hankali ta ce "Vi ba fa a gida muke ba"

"Eh, ai ke ki ka ɓata mana honeymoon a gida, sai mu yi a nan"

"Honeymoon a kango?" Tayi maganar tana murmushi, bai san lokacin da ya tuntsure da dariya ba, ya tashi zaune yana kallonta ya ce "Gidan gwaurontakar namu ne kango?"

Tana daga kwance ta yi murmushi ta ce "Kogon da macijina ya din ga ɓuya ba"

Ya gyaɗa kai ya ce "Ke ce jarumar da ki ka samawa wannan maciji 'yanci, ya ci gaba da rayuwa da cikakken 'yanci.
Abla a lokacin da ake nemana ruwa a jallo, ba ki duba kamani tare da ke barazana ne a gareki ba, ba kya lissafa wannan, 'yanci kawa ki ke nema mini, na bar kogon da yake tamkar kurku a gare ni, wai duk tayaya zan manta wannan ne?" Ya ƙarasa maganar yana kwanciya a jikinta.

Ta rungume shi sosai, tana sauke numfashi.

A nan suka karya, hankalinsu kwance kamar su na gida, su ke gudanar da soyayyar su.

Har Dutsen da ta kan je ta same shi, su ka je, ta din ga tuna masa wasu abubuwa da suka din ga faruwa, suna nishaɗi.

Har yamma suna can, sannan suka tafi gida.

Viper ya tambaye ta, a raba kayan jauhar a bata, ko a sayar a raba kuɗi kawai a bata.

"Ba zan iya amfani da kayanta ba"

Dumm ya ji a ƙirjinsa, amma ya daure ya ce "Meyasa?"

"Zan daɗe ina kallon kayan ina tunata"

Ya ce "Ko dai kishin ne?"

"Ko kaɗan, rayuwarta da yadda ta rasu, ba zai taɓa barin ƙwaƙwalwata da zuciyata ba, ba zan iya amfani da kayan jauhar ba, rashin haɗuwa da jauhar a rayuwata wani miki ne za ba zai taɓa warkewa daga zuciyata ba. Idan ma an raba, ayi amfani da abin da na samu a sai wani abu da ladan amfani da shi zai isketa da mahaifiyarmu a makwancinsu"

"Shikenan, zan yi magana da  Abba abin da ya ce shikenan"

Gidan Major kuwa, Mama ta takurawa Nasir a kan ya auri 'yar ƙawarta da take so ya aura tuntuni.

Aka fara shirye-shiryen biki, aka yi masa transfer a wurin aiki, zuwa kudancin Najeriya, kuma aka rage masa matsayi sosai da sosai a in da aka kai shi.

Walida kuma sosai suke soyayya da liti, dan kuwa akwai shi da shiga rai.

Sosai Viper yake ƙara ganin kimar Nabila, saboda rashin riƙonta, maganar bikin Sumayya ita ma ta taso, Nabila su na ta shirye-shirye.

Viper sai da ya samu Liti, shi ma ya ja masa kunne, a kan abubuwan da yake yi wa Nabila.

Nabila ta sake komawa duba mama, an sallamota daga asibiti tana gida, sai dai wata irin wahalalliyar jinya take yi, gaba ɗaya yaran babu mai tausayinta.

Har gidan su Shahida ta je, ta zazzagaya ta sada zumunci.

Bayan ta dawo, ta tarar da Viper yana ta mita.

Ta ce "Meyafaru ne?"

"Kuɗin da muke rabawa na ribarmu, na wurin shayin nan, wai ba za su bani ba, wurin refilling ɗin gas, Walid zai din ga zama idan ya dawo daga kasuwa, zai din ga zama".

Ta ce "To menene a ciki, idea ce mai kyau"

"To ai ni kuɗi nake so, harkar bikin nan na kashe kuɗi sosai, na sakankance na saka rai, suka ɓullo da wannan maganar"

Ta ce "Vi ai idea ce mai kyau, zaman haka ka dogara da aikin gwamanti kawai, ba zai yiwu ba, gashi shiru an ce za ayi maka ƙarin girma amma haryanzu shiru"

"Wannan ƙarin girman duk matsala ne"

"A'a ina fatan mu samu ci gaba, a kan komai"

Cikin ikon Allah aka saka ranar tarewar ramma, kuma maman ta amince da batun auren baban Viper.

Nabila ta mayar da hankali wurin gyara ramma ma, ta biya kuɗin yi mata gyaran jiki, sannan ta saka maman yusuf likitan mata haɗata.

Viper ya yi ta mita, saboda Nabila ta koma aiki, haka abubuwa suka yi wa Nabila yawa, zama matar gida babu sauƙi ga komawa aiki.

A haka lokacin hutun Viper ya cika, zai koma bakin aiki.

Daga shi har ita kamar su cinye juna, dan tun bayan da suka shirya, yake ta ƙoƙarin kare duk wani abu da zai sanya ta ji babu daɗi, ita ma daga nata ɓangaren tana ta ƙoƙarin kiyaye abubuwan da zai janyo su samu saɓani.

Tun dare ta haɗa masa jakarsa, ta yi masa snacks, ta yi masa cincin da dambun nama, yadda zai daɗe yana amfani da shi.

Sun sha soyayya ranar, kamar kar su rabu.

Da safe wurin ƙarfe goma, ya tafi duk sai ta ji babu daɗi, gidan yayi mata wani iri.


Kwanan Viper biyu da tafiya, Walid ya rako liti har gida, ya zo ba wa Nabila haƙuri.

Nabila ta ce "Da zan riƙe abin da ka yi mini a raina, hatta alaƙarka da Vi sai na rabata, duk da tasirin shekarun da ku ka yi tare. Kawai da ka din ga iya bakinka, wani idan ka cutar da shi da harshenka, har abada duk aikin alkhairin da zaka yi masa, ba zai shafe tasirin abin da ka gaya masa ba, Allah ya shiryeka" duk da ya ji haushin kausasan maganganun da tayi amfani da su a kansa, amma ya danne.

Bayan sun fito yake cewa Walid "Yanzu da gaske sai ta raba alaƙata da Viper, duk tsawon lokacin da muka ɗauka tare?"

Walid ya ce "Macece fa, wallahi sai ta raba"

"Kai ƙarya ne ba zai yiwu ba, ba wata mace"

"Galibinmu uban meye ya koro mu daga gidan iyayenmu, idan ba tasirin kaidin mace ba, ka daina cika baki malam"

Sai kuma ya ce "Kai haka ne fa, to Allah ya kyauta"

Nabila ta samu labarin mutuwar Madaki, ya mutu an rasa wanda zai zo ya karɓi gawarsa, ga jikinsa babu ta in da za a saɓa shi ayi masa wankan gawa, saboda duk ya ruɓe, haka aka yafa masa ruwa aka binne shi.

Da Nabila suka yi waya da Viper, ta din ga godewa Allah, da Allah ya dawo da su hanya madaidaiciya lokaci bai ƙure musu ba.


Nabila ta kai wa madam Halima ma ziyara, dan sai da ta kwana biyu a wajenta, Viper ya bata damar hakan.
Nabila ba zata taɓa mantawa da matar nan ba.

Aka gama shiri tsaf, ramma ta tare a gidan Abdul, a lokacin tana cikin hutun makaranta.

Gidan ramma ya yi kyau sosai da sosai, ana gobe zata tare ya sanar wa mummynsa, a lokacin Anty Jidda tana gidan.

Ta ce "Abdul ka yi asara, 'yar matsiyata talakawa da suka tagayyara rayuwarka, yau ita ka bi kake wannan rawar kan a kanta"

Abdul ya ce "Anty Jidda ban yi asara ba, gyara kuskurena na yi, kuma ke ma yakamata ki nemi yafiyar ramma, abin da ya faru da ita a gidanki, amma ki ka nuna halin ko in kula, ba zan gaji da sarawa Alhaji mu'azzam kankarofi ba, ya cika uba, kuma ni abin da yayi mini taimakona yayi"

Mummy ta ce "Jidda ba fa zai gane ba, a kan yarinyar nan zai iya ci miki mutunci ma, ai ni na cire hannuna daga kan Abdul na saka masa ido, kina kallo halin da mahaifinsa ya tsinci kansa a ciki wanda har saka hannunsa bai dame shi ba, ya haɗa kai da abokan adawar ubansa ba abin da ya dame shi".

Jidda ta ce "Amma kuwa Abdul ka yi asara"

"Wallahi ban yi asara ba, tun da kema abokin adawar ta sa ki ka aura ai"

Duk da bai ji daɗin abin da ta faɗa ba, amma yana Addu'ar Allah ya sa kar furucin mahaifiyarsa yayi tasiri a kan aurensa.

Hankalinsa kwance ya kasance da ramma, cikin jin daɗi da farinciki, saboda yadda yake ji a yanzu yana da cikakkiyar dama a kan matarsa.

Babban abin da ya basu mamaki, har da akwati bakwai na lefen ramma, suka tarar a gidan.


Store ɗin ta na abinci shaƙe da abinci, duk wani abin buƙata da na amfani ya saka mata.

Kafin ta tare ta sha nasiha, kuma sai da aka yi walima sannan ta tare.

Ko sabon ango fil bai kai Abdul rawar ƙafa ba yau, a baya duk da auren ramma yake yi, ya kan ji kamar yana wani abu ba dai-dai ba, amma yanzu hankalinsa kwance, kasancewar duniya yanzu ta san ramma matarsa ce.

Daren bai gushe ba, sai Abdul yana nanata wa ramma, irin matuƙar ƙaunar da yake yi mata, tare da neman afuwarta a kan abubuwan da suka faru a baya.

Duk daga shi har ita ba baƙin juna bane ba, amma daren yau ɗin ya ƙara zama na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login