Showing 336001 words to 339000 words out of 479911 words
ta istigfari, Allah ya yafe maka ya sassauta maka, bari na je waje" ya jinjina mata kai alamar to.
Ta fito ta tarar da su, ta kalli barrister Habib ta ce "Yaya, zamu je mu ga ɗaya daga shaidun da muke da su ne, gobe in Allah ya kaimu zamu je wurin jami'an tsaro"
Habib ya ce "To shikenan, jikinsa sa sauƙi amma?"
Ta jinjina kai alamar eh.
Sumayya ta ce "Ni dai sonake naga Vipern nan, amma Allah bai yi ba, zan koma ana nemana, amma Nabila na gaya miki mahaifin sa yana ta sintiri, yana so na haɗaki da shi, neman ɗansa yake ido rufe"
Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Ki rarrashe shi, yayi mana afuwa zuwa mu kammala shari'ar nan, Viper ba zai yadda su haɗu yanzu ba".
"Amma Arfa meke damunki ne? Ko wani abin suke yi miki da ba kya so?"
Nabila ta girgiza kai hawayen da ta ke ƙoƙarin tarewa, suka zubo mata.
Hankali a tashe Sumayya ta ce "Nabila menene?"
Nabila ta ja hannunta suka koma gefe, ta ce "Sumayya, matar Viper da aka kashe, ina kyautata zaton ina da alaƙa da ita"
Sumayya ta ce "Ta ina?"
"Yanzu na san ko na ce ya bani hotonta, ba zai bani ba, idan ki ga ganta rantsewa zaki yi, ki ce ni ce a jikin hoton"
"Ke Nabila bana son shirirta dan Allah, saboda soyayya ta rufe miki ido, har kin fara kalen dangi"
A hasale Nabila ta ce "Sumayya yaushe zaki din ga ɗaukar maganganuna serious ne? Kodayeke shikenan, daga baya idan komai ya bayyana, zaki gane idan ma ƙarya nake, idan ma gaskiya nake faɗa, ki je kiran da ake yi miki" Sumayya ta bi Nabila da kallo har ta bar wurin.
Suna tafe a hanya, Nabila take tunanin lokacin da take takurawa Nasir, tana tambayarsa me zata yi, wanda zai saka tayi suna sosai ta zama kamar bunkure, ya ce mata ta nemo masa Viper. Ta din ga bin yadda abubuwa suka din ga faruwa daki daki, ita kanta ta san ƙudura da ikon Allah ne kawai da ya ƙaddara sai ta haɗu da Viper. Da ta din ga lissafa rashin hankali da wautar da ta din ga yi, tana yawon nemansa, yana iƙirarin kasheta, amma tana nace tana bibiyarsa kamar mayya har zuwa wannan lokaci, abun lamari ne na Allah kawai.
"Amma daga can, yakamata muje ku gaisa da mahaifiyar ramma"
Ya ɗago ya kalli Nabila ya ce "Bana son haɗuwa da mutanen da na sani, suna yi mini kallon ɗan ta'adda"
Nabila ta girgiza kai ta ce "Ba kowa ne yake yi maka kallon hakan ba, abin da yakamata ne, mussaman da iftila'in nan ya faɗawa ramma" yayi shiru bai ce komai ba.
Har ɗakin da madaki yake aka kai su.
Tare da Viper suka shiga, suka tarar da shi a kwance, duk jikinsa sara da suka, da rauni, ɗakin sai wari yake yi. Babban abin da ya bawa Nabila mamaki bai wuce duk jikin madaki raunukan nan sun yi kore ba, maimakon ja, irin na ciwo. Hatta fuskarsa sara ne, kamanninsa sun sauya daga shi sai ɗan wando.
Nabila ta dubi jami'an tsaron da suke tsare da shi ta ce "Yanzu a haka yake? Ana duba shi kuwa?"
"Eh, likitoci na duba shi, yana da ciwon suga ne, dan haka wannan raunukan ba zasu warke ba, sai dai ayi ta treatment a haka".
"To wannan tayaya zamu je da shi kotu, yana magana ma tukuna?"
Madaki ya buɗe ido da kyar, yana kallonsu.
Viper yayi murmushi, dan ya san ba ciwon suga bane kawai, russia da yayi amfani da ita, wurin karya sihirin da yake amfani da shi ne ya janyo haka, duk wani rauni da ya ji, muddin da ƙarfe ne, ba zai warke ba. Wancan karon ma Viper shi yayi sponsoring yanke ƙafar madaki.
Viper ya ce "Ya kake kallonta, haryanzu kana tunanin wadda ka kashe ce ko? Nayi mamaki da na turo maka ita da farko, ka iya jurewa baka yi wani abu ba. Kodayeke namiji idan ya kai namiji, baya tsoro baya nuna gazawa.
Ina yi maka albishir da sai ka ruɓe a raye, kafin ka mutu, dan idan ka mutu yanzu hutu ne. Naka ƙarshen ya fi na kowa muni. Baka aikata alkhairi ba, baka bar wani baya mai kyau ba, babu ɗa babu jika, sai tarin zunubi da haƙoƙƙin mutane. Ga lokaci ya ƙure da zaka bi su yawon neman yafiya. Ka zo a banza zaka koma a wofi, ina fatan sunana da yake gadon bayanka ba zai ruɓe ba, zaka koma ga Allah da shi, duk da kome zan yi maka, ba zan huce zaluncin da ka yi mini kashi-kashi ba.
Da farko yayana, na biyu ubangidana, mafi muni kuma matata da ɗa na, wata shari'ar sai a lahira, duk abin da zan yi maka, ba zan bi wa yar madara hakkinta ba, Allahn da yayi ta shi zai saka mata" yayi maganar muryarsa na rawa. Madaki ya ƙure su da ido.
Nabila ta girgizawa Viper kai, cikin matsanancin tausayin sa, juyawa yayu yana haɗiye hawayen da yake shirin zubo masa.
"Vi, shaidar da muke da shi, ɗaya yana kwance ba zai ma taɓa yi mana amfani ba, ba magana zai yi ba, dole muna buƙatar wata ƙwaƙwƙwarar shaidar"
"Kamar wa kenan? Wa zamu samo?"
"Muna buƙatar, ko daga cikin maƙwabtanku, ko makamancin haka"
Viper ya ce "No, ki rabu da wannan mutanen, mu bari gobe in Allah ya kaimu sai mu ga yadda za ayi".
"Muna buƙatar iyayen jauhar a case ɗin nan"
"Meyasa?"
"Saboda shaidunmu su zama masu ƙarfi, bana son a ja shari'ar da yawa" yayi mata shiru bai sake cewa komai ba.
Nabila har system ɗin ta aka kawo mata daga wurin aiki, barrister Habib ya kawo mata.
Tayi mamakin yadda tun da ta kunna wayarta, daga gidansu babu wanda ya neme ta.
Dan haka ta kira Abba, sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga.
Ta ce "Abba ina wuni?"
"Lafiya ƙalau Nabila, yau kin tuna da ni kenan?"
"A'a Abba, wayar ba ta hannuna ne, yau aka bani ita"
"Kin ga abin da taurin kanki ya janyo mana ko? Ƙiri-ƙiri an ɗauke ki, an kai ki in da ban sani ba, da sunan an kauwwame ki, ban isa na ganki ba"
Cikin mamaki Nabila ta ce "To ai Abba Sumayya ta zo in da nake, barrister Habib ma haka, kuma dama na ce zan koma bakin aiki, ina son zan dawo gida"
"Ai kin ga da baki bijirewa umarnina na cigaba da kare mutumin banza ba, da ba ayi haka ba. Ki je Allah ya taimaka" ya kaste wayarsa. Nabila ta bi wayar da kallo, ta rasa abin yi gaba ɗaya.
Nasir kuwa ya kasa ya tsare, muddin Viper bai bayyana a gaban yan sanda ba, sai ya kama shi, ya ɗaura aniyar ko ta wani hali sai ya kai Nabila ƙasa da Viper, Viper yake son nuna wa iyakarsa, ko dan saboda wulaƙanci da gadarar da yayi masa.
****
Sumayya ce da safe ta buɗe gidan radiyo da safe, tana amsa gaishe-gaishe, masu sauraro suke tambayarta ina Nabila da gaske an yi garkuwa da ita.
Sumayya ta ce "Haƙiƙanin gaskiya, ba wanda yayi garkuwa da Nabila, yanayin jiki da jini, ayyuka sun yi mata yawa, kuma ba ta ɗan jin daɗi, dan haka da komai ya lafa za a ji ta dawo"
Message ɗin Nabila ta gani, a kan su haɗu a police station, tana son su zama witness, zasu je da Viper a ɗauki statement ɗin sa.
Sumayya ta riga su Nabila zuwa, da ita da murtala.
A wata irin zuƙeƙiyar mota aka kawo Nabila, da Viper da su Walid.
Nabila ce ta fara fitowa, su Walid ma suka fito.
Sumayya ta ce "Ki ka ce na zo da wuri, amma sai yanzu ku ka ƙaraso"
"Malama ba wani daɗewa fa muka yi ba, yaya murtala ina kwana"
Ya ce "Lafiya ƙalau, ya ki ke ya hidima" Alhamdilillah.
Sumayya ta ce "Ina Vipern ne? Wanne shi a nan?" Tayi maganar tana nuna su Liti.
Nabila ta yi murmushi ta ce "Wane mutum, yana cikin motar, sai ya gama mulkin zai fito"
"Kai ni nayi neman suna, naje na gaishe shi"
Nabila ta yi dariya ta ce "Idan yayi miki halin, zaki gane baki da wayo, ki bari zai fito da kansa.
Motar barrister Habib ma ta iso harabar wurin state CID ɗin, yayi parking ya fito, suka gaggaisa, amma madugun yana ƙame a cikin mota, yana kallon su ta cikin glass.
Can kuma da ya gama abin da Allah ya nufe shi da yi, ya fito daga motar.
Ƙaton tabon da yake gefen wuyansa ya tabattar wa Sumayya shi ne Viper, duk rawar ƙafar da take yi zata ga Viper yau, sai bakinta ya mutu, ta zubawa sarautar Allah ido.
Ɗan ƙarewa harabar wurin kallo yake yi, yana tuna adadin zuwansa wurin nan, tun jauhar na raye yake zuwa, da aka kasheta ma, nan aka kawo shi, aka din ga gana masa azaba.
Tinkis-tinkis, ya fara tafiya yana bayar da faɗi.
Barrister Habib ya miƙa masa hannu, suka gaisa ya ce "Ya jikin, an ce mana baka ji daɗi ba jiya"
Viper ya ce "Eh, ina ta fama da hanta, sai fatan Allah ya sa mu yi kyakywan ƙarshe"
Ɗan mama ya ce "A'a Master ba yanzu ba in sha Allah" Viper ya galla masa harara.
Liti ya ce "Wannan zaƙal zaƙal ɗin da ka ke yi, ba zai hana aci ubanka, a hukuntaka ba, gara ai maka hukunci a duniya, tun kan ka je lahira da laifin munafunci"
Nabila ta ce "Viper, ga yar uwata, sumayya T ladan"
Ya jinjina kai ya ce "Yarinyar indabo" yayi maganar yana mayar da hankalinsa kan Walid da yake yi masa magana.
Zata yi magana, Nabila ta hana sumayya magana.
Nasir ne ya shigo, wurin shima, da tasa tawagar, yana tafe ana sara masa, yana wani basarwa.
Sai da ya ɗan tsaya suka yi kallon kallo da Viper.
Sumayya ta kalli damtsensa na hagu, nan ma wani tabon ne, da alama an taɓa yi masa ɗinki a wurin, gefen kansa ma, ya wani shata kai ka zata aski ne aka yi masa a haka, amma sara ne. Kai da ganinsa ka san an sha gwagwarmaya.
Nabila ta ce "Vi, dan Allah na san kai ba mai magana bane, sai abin da na amince kayi magana zaka yi, banda hasala da saurin fushi dan girman Allah, kar ka yi wani abu da zaka janyo mana matsala Please".
Shafa ƙeyarsa yayi yana kallonta.
"Bamu da ƙarfi, bamu da tsumi bamu da dabara, sai a wurin Allah, muyi ta addu'a"
Ya jinjina mata kai, suna tafe, ya ga ta koma jauhar, lokacin da tayi belinsa da kyar, ta riƙo hannunsa suka bar wurin suna kuka.
Ɗan sandan ya kalle su ya ce "Waɗan nan fa?"
Nabila ta ce "Ni da wannan lauyoyin sa ne, wannan 'yan jarida ne, wannan kuma suna cikin shaidunmu"
Mutumin ya jinjina kai, can aka fito da lakwari, ya rame ya fita hayyacinsa tamkar lagwani, aka riƙo ƙugunsa, aka fito da shi.
Viper ya ƙure shi da ido, yana jin tamkar ya ƙwaci bindiga ya harbe shi.
Ɗan sandan ya kalli Viper ya ce "Ina tayaka murna, kotu ta hana kamaka, duk da ba a nan take ba, an danne bodari ta ka" yanayin zaman da Viper yayi, kai baka ce da shi ake magana ba.
"Meye cikakken sunanka?"
Nabila ta ce "Sunansa Al'amin Ibrahim"
Nasir da yake wurin ya ce "Bashi da baki ne?"
"Doka ta bashi damar yin shiru, lauyoyin sa su yi magana" ya kalli Nabila ta kalle shi.
Aka juya aka karɓi sunan lakwari ma.
"Menene ƙorafinka?"
Viper ya kalli Nabila, ta jinjina masa kai ya ja wasu second ya numfasa ya ce "Sun shiga gidana, da misalin ƙarfe uku saura na daren alhamis, shekaru shida da suka gabata, suka shaƙa mini abu, suka kashe matata, ta hanyar kayar da ita a kan cikinta, bayan sun bugar da ni".
Nasir ya ce "Amma shaidu sun tabattar da cewa kana ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, su ka sha ka kasheta"
Viper yayi shiru yana kallonsa, Nabila ta ce "Wane shaidun kenan? Nan ba zaman kotu muke yi ba, statement muke bayarwa"
Nasir ya kalli Nabila, tamkar an canzata zuwa wata daban ba Nabilansa ba, yadda take yi masa martani da zuciya.
"Meye haɗinka da su, da har suka shiga gidanka suka kashe maka mata?"
Viper ya nuna lakwari, ya ce "Shi zaka tambaya, ban san laifin da nayi musu ba"
Aka tambayi lakwari, amma lakwari ya kada baki ya ce "Viper ƙarya yake yi masa, ba su shiga gidansa ba, basu kashe masa mata ba"
Taka ya fara harzuƙa, amma Nabila ta dakatar da shi.
Walid ya ce "Yallaɓai, mune abokan harƙallar Viper, tare muke sha da fataucin wiwi, Viper ya kan sha ƙwayoyi amma ba ko yaushe ba, kuma mu abokansa da maƙwabtansa shaida ne, na matarsa ta saita shi a hanya, kafin su kasheta, dan kuwa a lokacin sai da Viper ya hana sayar da wasu kalar ƙwayoyi, a unguwar da yake da kewayenta".
Nasir ya kalli Walid ya ce "Ikon Allah, daina shaye-shaye fa ba abu ne mai sauƙin da ka ke tunanin, abu ne da zai daina farat ɗaya ba. Abu ne da yake buƙatar dogon lokaci, wani ma har da likitocin ƙwaƙwalwa kafin mutum ya daina, ta yaya zamu yarda da cewar Aminu ya daina shaye-shaye kuma bai yi shaye-shaye ba a wannan ranar?"
Liti ya ce "Sun je Asibiti da matarsa, ni na raka su, aka ce za a yi mata inducing, bamu koma gida ba sai bayan ƙarfe goma na dare, suka ajiyeni suka wuce gida a adaidaita sahun wani ɗan unguwarmu.
Viper bashi da wani wurin zuwa sai wurinmu, bashi da wasu abokai sama da mu, tare muke shaye-shaye, irin abu ɗaya muke sha, dan haka Viper baya cikin nutsuwar sa, bai yi shaye-shaye ba ranar, suna fargabar inducing da za ayi wa matarsa".
"Malam shi mai shaye-shaye, kullum yana buƙatar samun sauyi, da samun abin da zai bugar da shi, fiye da wanda yake amfani da shi, dan haka zai iya yiwuwa ya samu wani abun bai sanar muku ba"
"DSP Nasir, ya sunan abin da Viper ya sha ne ya bugu ya kashe matarsa?"
"Hodar iblis ce, aka haɗata da wasu sinadarai, kuma a binciken da muka yi, an taɓa kama shi da cocaine a gidansa"
"Tayaya karabutin ɗan daba zai iya ta'amalli da cocaine a ganshi a haka? Ina gwaje-gwajen likita da yayi, ya tabattar da cewar ya ga cocaine a jinin Viper? Ko kuwa kawai da ka ake cewa ya sha cocaine?"
"Wanda kuke tuhuma, bai amsa cewar shi ya aikata ba, kin san hakan dai-dai yake da baku da hujja"
Ɗan mama ya ce "Mu na da ita" gaba ɗaya suka kalle shi.
"Ina daga cikin yaran madaki tsageru, Viper ya taɓa illata ni, daga baya yayi mini nasiha, ya biya kuɗin da aka yi jinyata.
Kwangilar kisan Viper aka bawa su madaki, aka haɗa musu da abin da suka kashe shi, saboda sun ce ba zai mutu ta daɗi ba, saboda yana da ƙarfi sosai.
Da madaki, da lakwari, da wani ana ce masa ɗan fari, da gulafa, su huɗu su ne suka je gidan Viper. Kuma saka su aka yi, wani ne ya saka su".
"Waye wanin?"
"Ban sani ba, su za a tambaya, amma ina da hujja, duk da ɗan fari an kashe shi, amma gulafa lagos ya gudu bayan an biya shi kuɗin aikinsa"
Yan sandan suka ce "Ɗan mama ma ya shiga cikin suspect, tun da a gabansa aka shirya komai, bai sanar da hukuma ba"
A take Viper ya rikice ya ce "Ba zai yiwu ba, babu ruwan ɗan mama a cikin wannan maganar"
Ɗan mama ya ce "Oga Viper, kar ka damu, zan zama cikin shaidu"
Liti ma rikicewa yayi, ya ce "Ɗan mama wane irin shirme ne wannan kayi haka?"
Nabila ta ce "DSP, ba fa zaman kotu muka zo ba, bayar da statement muka zo yi"
"Ɗan sanda baya wasa da duk wani abu da zai iya zama hanya ce ta kama mai laifi, hanyar da kuka ɗauka ma, idan baki yi wasa ba, zata sadar da ku zuwa ga baƙar duhuwa"
Ɗan mama ya ce zai yi magana da Nabila, yayi mata raɗa a kunnnenta, hakan ya sanya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Na fahimta sosai, in sha Allah muke da nasara".
Sumayya kanta tayi mamakin yadda Nasir gaba ɗaya ya canza, muraran ya fito da adawar da yake yi da Nabila. Ta sake keɓewa da barrister Habib, suka yi rubuce-rubuce, suka gama bayar da statement, suka tashi suka fita harabar wurin.
Hankalin Viper ya ƙi kwanciya, ganin an kama ɗan mama, sai da Nabila tayi masa bayani, sannan ya ɗan samu nutsuwa.
Nabila na fitowa, Nasir ya sha gabanta ya ce "Ki zo ki wuce mu tafi gida"
Nabila ta kalle shi ta ce "Wane gidan kuma?"
"Gida nawa ne da mu? Ko kin zaɓi Abba ya cigaba da fushi da ke? Ki je wurin da ba wanda ya san in da ki ke? Abba ya iya yarda ki tafi wurin da bai sani ba, ya ƙyale ki da halinki, hakan duk bai dame ki ba?"
Nabila ta girgiza kai ta ce "Ko kaɗan, Abba baya fushi da ni, zigar da kake yi masa ne da kai da mahaifiyarka, ya sanya ya ɗauki zafi, amma na san yafi kowa fahimta ta, kuma zai fahimce ni. Kuma a barikin sojoji nake zaune, duk lokacin da ka buƙaci ganina zaka ganni, daga nan wurin aiki za a kai ni, barrister Habib sumayya, duk suna zuwa wurin da nake. Dan haka ka daina aibata ni, da cigaba da danganta ni da mummunar ɗabi'a, dan na san abin da ka ke yinƙurin yi kenan".
Viper ya ƙaraso in da suke tsaye, ya ce "Ga abokin aikinki nan, zaki iya bin sa ki je office, in sha Allah you are safe"
Ta jinjina masa kai ta ce "Zamu je mu ga ramma ma, daga nan na ji ina aka tsaya da batun kama mutumin nan, amma yakamata ka je ku gaisa da ita, kaga yarinyar ma, tun da kai yaya ne a wurinta, a yan uwanta babu wani wanda yake zuwa wurinta"
Viper ya ɗan gyaɗa kai ya sakar mata wani irin murmushi ya ce "Zan je in sha Allah, tun da ke ce lauyata, kuma lauyar su, abin da ki ka ce ai shi nake yi ko?" Sai da Nabila ta tsaya tana kallonsa, cikin mamaki.
Ya sake cewa "zaki iya tafiya, take care, my only hope" yayi maganar yana cigaba da yi mata murmushi, Nasir kuma ya sandare a wurin kamar katako.
Nabila ta ce "To daga nan ina zaka