Showing 384001 words to 387000 words out of 479911 words
ke, su ka je, Nabila ta ɗauki ramma ta ce za ta fara zuwa awo, maman ramma na matuƙar jin nauyin Nabila, dan haka ta ƙyaleta da ita.
Hatta likitan da zai yi mata awon, Abdul ne ya gaya musu wanda zai yi mata, dan kar a cutar da ita. Asibitin abokinsa ne, su na ta hira da sumaya, ramma ko uffan ba ta iya cewa, hankalinta kacokan ya na kan ya jikin Abdul, dan baban fatanta bai wuce yau ma Nabila ta kaita wurinsa ba.
Su na shiga wurin likitan, ta ga ya zuba mata ido, ko ƙiftawa ba ya yi.
Nabila haushi ya kamata, ta ce "Lafiya kuwa?"
Ya ce "Ahh lafiya ƙalau, wani cikin ki ka samu kenan?"
"Ban gane ba, matar abokin ka mu ka kawo, Abdul yasar da ya ce kai za ka yi mata awo"
Ya ce "Ok Allah sarki, Abdul yasar, ai ya haɗu da larura shi ma, gashi wai ba a zuwa dubiyarsa, ai mun yi mamaki yadda aka yi ya yi aure babu labari" yayi maganar cikin kame-kame ya na kallon Nabila.
Ganin ta haɗe rai, ya sanya ya ce "Wacece matar ta sa a cikin ku?" Yayi maganar yana kallon ta ita da sumayya.
Nabila ta nuna masa ramma, ya waro ido, Ganin ƙaramar yarinya, bai matsa da tambaya ba, ya ɗauki details ɗin ramma, ya tura su gwaje-gwaje.
Bayan sun dawo ya dudduba ya ce "Ya aka yi matar likita take fama da ƙarancin jini har haka, kuma ga shi ta ce ba ta iya bacci, menene yake damunta haka?"
Ya tattara hankali a kanta ya ce "Menene yake damunki ba kya iya bacci? Ko dan doctor ba shi da lafiya ne? Ki yi haƙuri zai warware, in sha Allah. Amma dan Allah ki din ga cin abinci yadda yakamata, ki sha magungunan ki, dan kanki ya daina ciwo, kuma ki din ga isashshen bacci, idan ba haka ba, jininki zai hau ki yi jijjiga ƙwaƙwalwarki ta taɓu"
Ramma ta jinjina masa kai, yayi counseling ɗin ta sosai, Su ka yi masa godiya, har sun miƙe, ya ce "Baiwar Allah dan Allah yi haƙuri, wai ba Zahra ba ce ba matar Al'amin, da yake ce miki 'yar madara? An ce ya kashe ki, ranar da ku ka zo nan, na ce washegari za ayi inducing ɗinki, kuma yanzu na ganki a raye"
Nabila ta yi masa wani marayan murmushi ta ce "Ba ni ba ce ba"
"Yaya za ki ce mini ba ke ba ce ba? Ki na ce master fa, ya na ce miki 'yar madara. Idan za ku zo awo, har da abokansa, wani Walid da wanenen na manta sunan su, ranar har ki ke cewa ya goya ki ba zaki iya tafiya ba kin gaji. Na yi miki scanic ya ce na gaya masa da wa ɗan yake kama ke ko shi? Baki gane ni ba, doctor muktar ne fa. A tsohon asibitina fa na gadon ƙaya da ku ke zuwa".
Nabila ta yi murmushi, hawayen idanunta ya gangaro. Ta ce "Ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo? Twin sister na ce, ba ni ba ce ba" sai kuma ya yi shiru ya na kallonta, ya ce "Ikon Allah, Amma ban taɓa ganin identical twins da kamaninsu ya ɓaci fiye da kima ba kamar ku, amma ban taɓa sanin ta na da twin sister ba, mu na hira da su sosai. Duk da mijinta ba shi da fara'a, amma muddin yaga na ba ta kulawa ta musamman sai ya saki jiki da ni ya yi ta mutunta mini.
Haryanzu ina mamakin yadda aka yi ya kashe ta duk da irin soyyayar nan da yake yi mata, kamar ya haɗiyeta.
Ga ta da sanyin hali, komai ta ce master yarinya mai haƙuri da girmama mutane"
Nabila ta katse shi, ta hanyar cewa "Bari mu je doctor, mun gode sosai da sosai".
Sai dai su na fita, ta saka musu kuka, Sumayya ta ce "Haba Nabila menene haka? Ya da kuka kuma"
"Wallahi sumayya duk lokacin da na tuna ban taɓa ganin jauhar ba, wallahi sabon baƙin ciki nake shiga, sai dai ina jin daɗin duk wanda na haɗu da shi, halinta na kirki yake gaya mini"
Ramma ta ce "Ki yi haƙuri ki daina kuka, mu yi mata addu'a, mama na yawan gaya mini, lokacin yaya Nura ya na da rai, kullum ya je sai ya bata labarinta, har ta na ce masa ya samo mata, za ta saka Yaya Aminu ya yi masa aure. Ana faɗar kyawawan halayenta, kamar dai yadda ki ke kema"
Duk da kuka Nabila take yi ta ce "Haba, dan Allah nima ina da kirki rahama? Za a iya faɗar alkhairina idan bana raye nima, ba za a din ga cewa masifaffiya ce ni ba?"
Ramma ta jinjina kai ta ce "Ki na da kirki sosai Anty Nabila, daga ke har Anty sumayya"
"Viper fa?" Shiru ramma ta yi ta na kallonta.
A tare Nabila da sumayya suka hau dariya, Ramma ma ta ɗan biye musu ta murmusa.
Nabila ta ce "Kar ki ƙullace shi, shi ma mutumin kirki ne, zuma ne kawai sai da wuta, ki yi ta banka masa addu'a, zamu shawo kansa in sha Allah.
***
Viper ya na kwance ya na ta juyi a kan katifa, ba kalar rarrashi da ban bakin da su Walid ba su yi masa ba, amma yayi shiru bai kula su ba. Ga wani malulun takaici da ya ƙule shi, Tun bayan da ya shiga iftila'in rashin Jauhar, babu wanda yake jin rarrashin sa ya na ratsa shi, kamar Nabila, gashi saboda wulaƙanci, ta na kallonsa, ya na kallonta, amma tayi banza da shi, ta hau motar da ake fita da ita saboda tsaron lafiyarta amma ta yi burus, duk da ta na kallonsa a ciki, kuma ta san ita suke jira.
Jin takaici ya cika masa zuciya, ya sanya ya tashi ya kunna sigari, ya koma gefe ya na ta busa hayaƙi a nutse, sai dai sam ya kasa samun sassauci a ransa.
Ya lumshe idanunsa, ya na hango jauhar.
Ta kalle shi, yadda ya zuba mata ido, ta na yi wa wani mayafi aikin bead.
"Mazajena ya aka yi ne?"
Guntun tsaki ya ja ya na daga kan doguwar kujera ya ce "Gaskiya na gaji, haba ke baki san me nake ji ba ne ba, wallahi kara uku na sigari ɗaya safe ɗaya rana da dare kamar wani magani, gaskiya yayi mini kaɗan, gaba ɗaya kin takura mini rayuwa kin hanani sukuni haka ake yi, ba sai ki bari na je na sha a waje ba, idan ma ba kya so na sha a gabanki ne ba" yayi maganar yana jin haushin kansa, yadda ta kirshe shi a gida, kamar wani ɗan ta wai ba zai fita ba, hadda ƙayyade masa iya adadin abin da zai sha"
Murmushi ta sakar masa, duk da faɗa yake yi, gashi dai ba ɗaure shi ta yi ba, amma ya na zaune ya na masifa, saboda ya san ya na fita ranar ba tausa ba hira, ba zata saurare shi ba sai ta wana shi.
Ta ƙarasa gaban kujerar ta na masa murmushi, ta na kallon yadda ya wani maze ya na kumbura, ba kuma iya rashin shan sigarin ne ya sanya yake ta faɗa babu gaira babu dalili ba, period take yi shi ne abin da ya ƙara sanya shi faɗan, yake cika ya na batsewa.
Ta shafi sumarsa ta na murmushi ta ce "Manya gatan wasa, tuba nake yi, kaina bisa wuyana, ban yi hakan dan takura walwalarka da nishaɗinka ba, lafiyarka nake yi wa. Ayi mini afuwa a daure a lallaɓa da kara ukun nan, zan soya maka wainar fulawa mai ɗan karen daɗi, fanka kuwa sai ka kasheta dan kanka, panel ɗin ya samu isasshen hasken rana, ba zaka kwana cikin zafi ba, za ka samu wadatacciyar iska, a maimakon sigarinka da na hanaka, ai ka na so ko?" Tunstirewa ya yi dariya ba tare da ya shirya ba, ya janyota jikinsa ya ce "Wai ke mai wayo ko?"
Ita ma dariyar ta yi ta ce "Ai na san ba faɗan sigarin kawai ka ke yi ba, tari idan ka yi master na san me ka ke nufi"
"Aishikenan, ɗaukko abin mayafin da na tayaki, ko kuma wani abun zan yi miki"
Ta ce "Inyee duk murnar fankar ce za a tayani aikin bead ɗin da ake watsar mini"
Ya ce "To kin yi wa kanki, na fasa tayakin"
"Bakomai zauna ka ci gaba da kallona, hakan ma ya wadatar da ni ɗan aljanna na"
Murmushi ne ya suɓuce wa Viper, lokaci guda ya na haɗiye hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa.
Ya saki sauran sigarin hannunsa, ya na sauke numfashi a hankali.
"Allah ban san dalilin da ya sanya ka karɓi jauhar, ka shigo da Nabila rayuwata ba, amma duk abin da ka yi dai-dai ne. Astagfirullah wa atubuilaihi Allah ya yi miki rahama ya sada ki da annabin rahama matata"
***
Gidan su Nabila kuwa tun da Nabila ta zo, aka yi wannan fashe-fashen, tonon sililin, gidan ya ƙara rikicewa, Zakiyya kamar ta tsine wa Hafsa faɗar abubuwan nan da ta yi. Faɗa da tashin hankali ya ƙara kacame wa a gidan, Baba kuma ya ƙaurace musu gaba ɗaya, ya daina shiga shirginsu, ya daina cin abincin su, ya din ga kaɗaice kansa daga shiga cikin su.
Wata irin sabuwar damuwa ta addabe shi, dana sani ta aure shi, ya din ga jin tamkar ya mayar da hannun agogo baya ya gyara wasu abubuwan da su ka shuɗe. Gaba ɗaya nauyin Nabila yake ji, gashi tun da ta tafi, ba ta sake waiwayarsa ba, gashi ya na matuƙar son ganinta, amma babu hali dan nauyinta yake ji, dan a zatonsa fushi ma take yi da shi. Gashi kamar yadda ta faɗa lallai akwai buƙatar samun daidaito a tsakaninsa da major.
***
Nabila ta gaji da yawa, kai tsaye gidan major ta wuce, ta saka mukulli ta buɗe ɗakinta, babu wanda ya kulata sai baba magajiya, tare su ka yi ta hirarsu, ta na ba ta labarin yadda shari'a ta kasance a falo.
Mama sai hararta take yi, tamkar idanunta, za su faɗi Nabila ko a jikinta.
Unexpected Nasir ya shigo ya tarar da ita a falo, duk ta rame sosai da sosai.
Kamar ya shareta ya wuce, sai kuma ya kasa, ya ce "Ashe an fara shari'ar?"
Kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta numfasa ta ce "Ai ba ashe ba ne DSP, tin da ka halarci shari'ar kai ma"
Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, to ayi dai mu gani"
"In sha Allah za ku ga alkhairi, muddin da jinin major Yusuf maitama a jikina, zan ci gaba da tsayawa a kan gaskiya, kuma zan yi nasara in sha Allah" ya kalleta ta basar ba ta kuma magana ba.
Nabila na ta son ta kira Viper, ta ji yaya yake, kuma ta bashi labarin likitan nan, amma ta basar da ta tuna da maganganun da ya caɓa mata.
Washegari da wuri ya tafi gidan madam Halima ya na muzurai, a zatonsa Nabila ta na can, amma madam ta ce "Ba ta dawo ba fa tun jiya, Nabila ta na wasa da rayuwarta, ba ta san a iya haɗarin da take ciki ba, an ba ta security amma abin da ta ga dama take yi"
Viper ya gyaɗa kai ya ce "Zan yi mata magana"
Ya duba wayarsa, ya duba location ɗin ta, ya ga ta na gidan Major.
Nabila kuwa da safe da ta shirya, ta je ta samu Abba ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama ta tashi ta fita.
Ƙarfe sha ɗaya na safe, ta na asibitin da Abdul yake kwance.
Cikin sa'a mahaifiyarsa ta na nan, ta na ganin Nabila ta tsuke fuska, ta na tambayarta uban me ya kawo ta.
Abdul ya ce "Mummy ki tsaya mu je menene mana?"
"Ba za a ji ɗin ba, uban me za ta zo da shi na alkhairi wannan"
Nabila ta numfasa ta ce "Magana ce mai muhimmanci na zo zan yi da kai"
Ya kalli Mummy ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ki bari mu yi maganar nan, bamu san ta zo da shi ba" tashi ta yi ta fice ta na tsaki.
Nabila ta ja kujera ta zauna, ta kalleshi ta ce "Ya jiki kuma?"
Ya amsa da "Alhamdilillah"
"Na biya wurin likita, ya ce ana samun improvement a ciwon naka, yanzu kuma damuwa ce ka saka a ranka tayi maka yawa. Ɓangaren rahama ma, na kaita awo wurin likitan da ka ce, a kaita"
Cikin sauri ya ce "Komai lafiya ko?"
"Ba na ce ba, tun da ta yi complain da cewar ba ta iya bacci, ga ciwon kai, jininta ya yi ƙasa saboda ba ta cin abinci"
Cikin damuwa ya ce "To meyasa?"
Nabila ta ce "Abu ɗaya ke damunku kai da ita, sai dai kafin mu zo nan, mu fara tattaunawa a kan tubalin dalilan matsalolin da suka yi wa muradinku ƙawanya.
Zan fara da yi maka tambayoyi ka bani amsa, ta haka ne kawai za mu kamo bakin zaren. Zamu yi magana ne a matsayin mutum da mutum, ba wai a matsayin lauya da mai laifi ba"
Ya jinjina kai ya ce "Ina jinki"
"Na san ka na cike da jin takaicin yadda Viper ya ƙara dagewa kai da fata, a kan lallai a hukuntaka, amma ka san Viper kafin yanzu?"
Ya gyaɗa kai ya ce "Na san shi, yaron mahaifina ne"
Nabila ta ce "Wane irin aiki yake yi masa?"
Ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Abin da ya shafi harkar daba ne"
Ta ce "Good, meyasa kai ba ka yi masa, duk da na san ka fi Viper morar mahaifinka, kai ya kai ka waje ka yi karatu shi kuma ya bashi ƙwaya da makami, ya bar shi a sake a cikin al'umma?
Ko kuma shi ba shi da ƙwaƙwalwar dai idan an biya masa kuɗin karatu, ba zai iya ba?"
Abdul ya yi shiru.
"Mahaifinka ya yi wa Viper laifukan da su su ka zama kanwa uwar gamin ruruta wutar ƙiyayyar da yake yi wa mahaifinka ce ta gangaro zuwa kanka.
Na san ka san meyafaru da Nura guduma zuwa yanzu, duk da ba abu ne mai daɗin da zan ta nanata shi ba, hakazalika ban sani ba ko ka san abin da mahaifinka ya yi wa Viper. A kan case ɗin Nura ya aika a kashe Viper, amma aka ɓuge da kashe matarsa, wadda take twin sister ɗina, kuma aka rufe shi shekara biyar da zargin shi ne ya kasheta" cikin tashin hankali da mamaki yake bin Nabila da kallo.
"Ta yaya ka ke tunanin Viper zai iya yafe wannan tozarci da aka yi masa, Ramma ƙanwace a wurinsa, ya na da dangantaka da ita ta ɓangaren uwa, shikaɗai ne yake tsaye a kansu, yake taimaka musu. Ya na ɗora alhakin mutuwar Nura a kansa, dan haka ya na jin dole yayi duk mai yiwuwa ya yi supporting ɗin su.
Ni ya damƙawa ragamar shari'ar rahama, kamar yadda ragamar ta sa shari'ar ma take hannuna. Da zafina har cikin zuciyata nake son na ga an hukuntaka, saboda abin da ka aikata ya tsaye mini. Ga rape, ga tozarta uwar yarinya, ka sace mata 'ya, ka yi amfani da dukiya wurin aurenta ta ƙarfin tsiya. Aka kama wani daban aka ɗora masa laifin, ƙarshe ma aka kashe shi, duk dan a kare ka. Banda waccan azzalumar matar mai rufe kura da fatar akuya da take zaluntar mutane, Naja bunkure wadda na yi wa kaina alƙawarin tona mata asiri. Sai dai abin da na gani ya bani mamaki, daga gareka da kuma rahama, na bibiyi wasu abubuwan da su ka faru babu saka hannunka.
Amma dagiyar da muke yi, kowa da gaskiyar sa, twins sister na ban taɓa ganinta ba, duk da wani labari ne daban, amma ko ba komai, na shigo cikin labarin nima.
Yanzu abin da nake so da kai, gaskiya ni na karaya, ka tattauna da lauyoyinka, mu yi zama na musamman a kai mu shari'a law, saboda ka samu sassauci ko yaya a hukunta ka dai hankalinsu ya kwanta, ina tunanin makomar Rahama da abin da yake cikinta, they really need you. Ka cire girman kai da duk wani abu, ka roƙi alfarmar Viper da mahaifiyar rahama, ita dan ta rahama a ƙyaleka ba sai an hukuntaka ba. Ta na ta yi mini magiyar a sassauta maka.
Amma ya ka gani"
Abdul ya ɗan yi shiru, ƙarshen ƙasƙanci dai ace ya durƙusawa Viper, yaron mahaifinsa da ba sa ga maciji ƙasƙantaccen ɗan daba, amma ba shi da wani zaɓi sama da hakan.
Ya numfasa ya ce "Na amince da hakan"
Ta ce "To Alhamdilillah, ba amincewarka ba kawai, ka tattauna da lauyoyinka. Ni kuma zan san yadda zan shawo kansa, a yi zaman tattaunawar ka san murɗaɗen mutum ne, da ba ya sarrafuwa cikin sauƙi, amma dai ka yi shawara"
Ya amsa da "Shikenan, na gode sosai da sosai, da ƙoƙarin da ki ke yi mana, dan Allah ki gaida mini da rahama, ki ce na ce dan Allah ta kula mini da lafiyar su, ta daure ta din ga cin abinci "
Nabila ta yi murmushi ta ce "In sha Allah"
***
Aka shafe sati guda, Nabila da Viper ba su haɗu ba, ta koma gidan major ta yi zamanta, mutanen gidan babu mai iya tanka mata.
Viper ya sha mamakin yadda Nabila ta watsar da shi gaba ɗaya, idan ya ɗaga waya kamar ya kirata sai ya fasa ya ga kamar ya faɗo. Ita kanta daurewa kawai take yi, ba ƙaramin azalzalarta zuciyarta take yi, a kan ta kira Viper ba, ko ta je in da yake ba, amma ta dake.
Lauyan Abdul ya kira Nabila a waya, ya sanar mata da sun amince ayi zaman sulhun.
Nabila ta na zaune a office ɗin ta, ta na tunanin yadda za ta shawo kan Viper a kan lamarin ramma.
Ta cire kayan jacket ɗin ta, daga ita sak dogon wando da shirt, ta ɗora ƙafafuwanta a kan tebur, ta ajiye popcorn a wata container, ta na ci kaɗan kaɗan ta na tunani.
Buɗe ƙofar ya yi ya shigo, tare da yin sallama ƙasa-ƙasa.
Ita ma a cikin ta amsa masa, ta ɗauke idanunta daga kansa, ta maze.
Har ya ƙarasa gaban teburinta, ba ta motsa ba.
Ya daddaki teburin, ta ɗago, ya kalli ƙafafuwanta ya kalleta.
So ta yi tayi burus da shi, sai dai ya yi mata kwarjini, ta sauke ƙafafuwanta, ta na yamutsa fuska.
Ya matso kanta ya tsaya, ya yi gyaran murya ya ce