Showing 360001 words to 363000 words out of 479911 words
suka din ga zunɗenta, wai kwaɗayi ne da zunubin Jibo, duk ya janyo mata.
Yara maimakon su din ga girma, sai suka din ga yanƙwanewa, duk suka lalace kamar yaran aljanu, gashi wasu lokutan tayi ta shirme, ba ta iya gane meyake faruwa saboda jijjigar da tayi, gashi kullum cikin haki take, ga jego kuma babu cikakkiyar kulawa. Yara kuwa kullum cikin amai da gudawa suke, da tari da sarƙewar numfashi, sai dai a basu jiƙe-jiƙe da hayaƙi, aikuwa suka ci-gaba da tsula gudawa ba ƙaƙƙautawa.
Sai da suka yi wata biyar, kwatsam Allah ya kawo maitama garin, dan shi kansa bai san da mutuwar ramata ba, sayayya yayi ya zo ya gaisheta, dan duk da baffa ya rasu, ba zai manta da alkhairi da kuma hidimar da tayi da chubaɗo ba. Ya shafe watanni baya ƙasar, an tura su yaƙi can libiya, dan matansa ma sun fara tunanin ko an kashe shi a can, shiyasa bai samu ya je yaga chubaɗo ba, fatansa dama daga nan jalingo ya kwana biyu ya tafi Bauchi ya ga Chubaɗo.
Sai dai abin da ya tarar ya ɗaga masa hankali, mairamu ta koma baƙa, da ta ganshi ma sai da ta ɗan yi shiru sannan ta tuna shi.
"Mairamu shi Bashir ɗin ne ya turo ki riga ki zo ki yi jego?" Ta girgiza masa kai.
"Ki yi mini bayanin, menene ya faru, kan na zane ki"
Cikin rawar murya, ta gaya masa komai tiryan-tiryan, ba ƙaramin mamaki ne ya kama shi ba, abin kamar almara ya din ga tunanin anya Bashir yana hayyacinsa.
Ya ɗauketa da yaran ya nemi a garin wata ta raka su asibiti, dan ya san za a kwantar da su, amma aka rasa mai yadda, ya ɗauke su zuwa asibiti, sai dai kwananta biyu a asibitin, aka tura su Gombe, saboda zuciyarta ta taɓu, tun lokacin tana da ciki.
Ya sha faɗa sosai a wurin ma'aikatan lafiyan, suka din ga cewa a haka kamar yana da ilimi amma yayi wannan shirmen, aka yi sake tamowa ta kama yara ƙanana, ita kanta uwar yunwa ce a jikinta, ga complication na jijjiga da suka gano, bayan sun yi mata tambayoyi, ga kuma zuciya ta taɓu.
Shi dai bai ce komai ba, aka basu kwanciya.
Shi ne yake kwana da chubaɗo, da taimakon nurses yake kula da ita, suka ce lallai ya samo mata mace, jinya dole sai da mace.
Ya rasa yadda zai yi, ya koma garin da ya fara karatu, su sun samu cigaba sosai, ya ce a samo masa wadda zata yi masa jiyyar ƙanwarsa ya biyata, aka samu wata 'yar dagaci, da aurenta ya mutu mai suna magajiya, ta ce ita ko kyauta za ta yi, ba ta manta ɗawainiyar da ya din ga yi da mahaifinsu ba.
A haka ya daddafa, ya koma can gidansa, ya sanar da matansa abin da yake faruwa, Allah ya sauwwaƙe kawai suka yi masa, ba tare da wata tayi karar bin sa ta duba mairamu ba.
Ya ɗaukko babban ɗansa Nasir, ya taho da shi, ya zo ya duba mairamu, da jariranta, da suka yi masa kyau a ido duk da ba su da lafiya.
Abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, ɗayar kamar ba zata yi rai ba, ga shi chubaɗo na fama da kanta, ga rainon yara marasa lafiya. Suka wayi gari ɗaya ko numfashi ba ta iya yi, aka saka mata oxygen, ƙarin ruwa sai da aka aske mata gashin kanta, sannan aka saka, jininta ma da za'yi gwaji, ta mararta aka samu jinin.
Aka bawa maitama ɗayar aka ce ya kaita wani asibiti, ita ma a saka mata oxygen nan space ya ƙare, ita ma kuma tana buƙata.
Yana tafe a mota, baƙin ciki da takaicin abin da bashir yayi masa ya hana shi sukuni, kamar ya jefa yarinyar ta taga, gaba ɗaya ya ji haushin yaran yake ji, ya din ga dana sanin rashin jin maganar baffa.
Kawai zuciya ta ɗebe shi, ya canza akalar motarsa, ya nufi Bauchi.
Yana tafe a hanya, yarinyar babu kuka, babu komai, sai shan hannunta da take yi, duk da tana ta haki. Bai manta ba haka uwar ma aka yi ta fama da tana jaririya, amma aka ƙi kaita Asibiti. Yana tuƙi yana yi yana kallonta, tayi bacci ta tashi, ta sha hannunta, ko uffan sai da ya tsaya ya sai ruwa ya bata.
Saboda tsabar masifa da wahala, yaran da ya kai su fara zama, amma suna kwance duk yunwa da zawo ya cinye su. Ya ja tsaki a fili.
Har ƙofar gidan ya isa, cikin matsananciyar sa'a, da ya aika aka yi masa sallama da Bashir ya ga ya fito yana gari, sai da ya ga maitama, sannan ya tuna da wata halitta wai ita mairamu.
"Ka bani kunya ka bani mamaki Bashir, meye ribar abin da ka aikata ka wulaƙanta mini 'yar uwa, ka tozarta ta? ta haihu a wulaƙance, ka ci amanata, amma na bar ka da Allah, ga wannan nan, ita ce mai alamar zata rayu shima wataƙila, yar ka ce na kawo maka, yar uwata ba zata mutu tana yi maka wahala kana gefe ba, kana tsula rashin mutunci.
Kuma, ka gaya mini menene matsayar aurenku a yanzu? Tun da ta ce baka saketa ba"
Bashir ya kalli maitama, ya kalli yarinyar da take ta bacci, ya ce "Na saki mairamu, Saki ɗaya Allah ya haɗa kowa da rabonsa, 'ya ta kuma na karɓa Allah ya raya mini"
Cikin tashin hankali ya kalli Bashir ya ce "Ka saketa, ba sakin ne ya bani haushi ba, amma laifin me tayi maka?" Bashir ya girgiza kai alamar babu.
Maitama ya haɗiye yawu mai matuƙar zafi da ɗaci, ya so ya sanar masa yaran biyu ne, amma sai ya kasa saboda tsananin mamaki. Kuma ya san wadda ya baro, wannan yarinyar kafin ya koma ta rasu, saboda ta galabaita da yawa, dan haka ya ga babu amfani gaya masa, ya ce "Na gode Bashir da wannan tukuici, ya taka ce dama, an bar maka halak malak, zan nesan ta ka da mairamu nesantawa ta har abada, kuma in sha Allah duk wani sukuni da nutsuwa da ake samu da walwala a sanadin aure ba zaka same shi ba, kai da Allah da ni da zuriyarmu ba zaka sake ganin ire-iren mu ba, in sha Allah zamu ƙaddara babu wata alaƙa, ko wani abu da ya jiɓanceka a rayuwarmu" A hankli yarinyar ta buɗe idanunta, ta ƙura wa maitama, sai kuma ta wangale masa dadashinta tana dariya, tare da jan numfashin ta da kyar.
Maitama ya juya ya nufi motarsa, yana jin tamkar ya fasa ihu, Bashir kuwa ji yayi sakin mairamu kamar ya saukewa kansa wani nauyi ne, ya shiga da yarinyar gida, cike da ƙaunarta.
Bashir yana tafe a mota, kawai tausayin mairamu ya lulluɓe shi, sai kuma ya din ga tunanin da ya sani, bai ɗauki yarinyar nan ya bashi ba, ita menene laifinta, dariyar nan da ta yi masa, sai ta tsaye masa a ƙirjinsa, ya kasa mantawa, ganin ita ma a galabaicen take, ya sanya ya din ga addu'a Allah ya sa yarinyar ta mutu, dukkansu ma su mutu kowa ya rasa, shikenan babu sauran alaƙa a tsakanin sa da Bashir.
Yana komawa da daddare, aka din ga tambayarsa ina Husna take, ya jikinta, dan dama Hassana da hussaina kawai ake ce musu, a asibitin, ta ce ba ta san sunan su ba. Dan ita wannan yaran kawai take cewa, kasancewar su yaran fari.
Mairamu na kan gado na fama da ƙarin jini, ta ji nurses na tambayar "Ya jikin haussaina"
Mairamu ta ce "A'a, ba ita ba ce, babbar ce ya tafi da ita, ƙaramar tana nan"
"Allah ya yi mata rasuwa a hanya, har an binneta ma, shiyasa ban dawo da wuri ba"
Duk da ƙirjinta ya buga da ƙarfi, amma ta dake, a matsayin ta na bafulatana, bai kamata ta nuna damuwa a kan ɗan fari ba.
Maitama ya sha mamaki, da ya ga jaririyar da ya bari ta fara farfaɗowa, bai taɓa tunanin zata ƙara mintuna talatin ba ta mutu ba. Da an tambayi ranar da aka haife su, nawa ga wata, sai mairamu ta ce ba ta sani ba, ita dai ta san ranar arfa ne.
Maitama ya tambayeta, ainihin sunan da za a saka wa jaririyar.
Ta ce duk sunan da ya saka shikenan, kasancewar yana son sunan Nabila, sai ya saka mata Nabila, ya ce "Tun da ranar arfa aka haife ta bari mu saka mata sunan 'yan gayu, arfa"
Tsananin tausayin Nabila da wahalar da ta sha, ya sanya ya fara yi mata wata irin soyayya, da fari ba dan tafi jigata ba, ya so ace ya haɗa har ita ya kai wa uban su, shi ya kula da ƙanwarsa, tun da ba shi da mutunci, amma idan ya tuna yadda yarinyar da ya baro, ta kalleshi har da ƙarfin hali dariya, sai ya ji babu daɗi a ransa.
Hutunsa ya riga ya ƙare, dan haka ya ɗauki chubaɗo, ya tafi da su illori, in da yake aiki a lokacin.
Ya mayar da ita asibitin sojoji, sai dai ya lura da yadda idan chubaɗo ta zauna take yawan shiru, ta saka damuwa a ranta sosai.
Cikin kulawa ya ce "Mairamu, ke da ake fatan ki samu lafiya, menene kuma na tunani da saka damuwa a rau?"
Ta ce "Bakomai, yarinyar nan har ta mutu, babanta bai taɓa ganinta ba, ina ga ko shi ma mutuwa yayi ba a sani ba" duk tsananin kunya irin ta ta, hakan ya tabattar masa da damuwar rashin 'yar ta ne da kewar mijinta yake damunta, haka yayi ta rarrashinta, ƙasan zuciyarsa yana jin, ba zai iya yafe wa Bashir ba.
Aka sallame su, suka koma gida, baba magajiya ke yi wa arfa komai, da taimakon Nasir, da kullum yana liƙe da arfa, yana raino.
Sai a lokacin ya yi wa Nabila hakika, sai dai an hana mairamu cin jan nama a lokacin.
Yayi mata suturu, ya yi wa Nabila kayan sakawa masu kyau na zamani.
Sai da babar Nasir ta magantu a kan "Wai dan Allah ina uban yarinyar nan, da ka ke ta wahala, tun da ka dawo da su, bai zo ya duba ta ba, ai hakkinsa ne"
Ya bata amsa da ba ta da uba, ni ne uban.
Can Bauchi kuwa, Bashir matansa sai ganinsa suka yi da jaririya, suka tambaye shi wannan ƙarmasashiyar 'yar fa a ina ya samo ta.
"'yar wurin waccan yarinyar ce, yanzu yayanta ya kawo mini ita, dan ya tura mini takaici, ni nama manta da ita gaba ɗaya, na karɓi kayata ina son abata".
"To kai ya zaka yi da jaririya, saboda rashin mutunci da zalunci, sai a ɗaukko wannan yar mitsitsiyar yarinyar, duk a tsotse ta kusa mutuwa a kawo maka, kai amma mairamu azzaluma ce, kalli ƙashin haƙarƙarin yarinyar, kamar fara sai uban fari da gashi kamar horo".
Ya sake gyara ta a cikin zani, ya kalli Zakiyya ya ce "Zakiyya, ko ke zaki shayar da ita, tun da kin ga shayarwa ki ke yi"
Ta buga tsalle ta ce "Wallahi ba zata ba wa 'yar mayu nononta ba, wannan yarinyar abar tsoro, ta tsotse mini jini a banza, wallahi ba zan bayar ba"
Uwargidan ta ce "Dama ni ban haihu kwanan nan ba, dan haka bani da abun bata, ban da jakanci irin na mutumin daji, kawai ku wofantar da jaririya haka, Allah wadaran naka ya lalace"
Ƙarshe sai azare ya koma, aka kaita Asibiti, aka lalubi mai shayarwa a dangi, sai dai danginsa ba ƙaramin zagi suka yi wa su chubaɗo ba, bayan da ya gaya musu rabuwa suka yi aka dawo da yarinyar.
Wadda ta karɓi 'yar ta ce 'Kai kuwa basiru, me yarinyar nan tayi maka, ka saketa? Duk haƙurinta da biyayyarta" yayi shiru, dan shi kansa ba shi da amsar tambayar da ta yi masa.
Illori, arfa ta murmure tsaf, idan maitama yana yi mata wasa, yayi ta ce mata gawa taƙi rami, chubaɗo ta gaji, ta ce wa magajiya, dan Allah ta ce wa hammanta, ko za aje a duba ko baban yaran mutuwa yayi, ko wani abin ne ya same shi.
Da ta gaya masa, sai ce mata yayi babu buƙatar hakan, dan ba zai iya kallon mairamu, ya bata saƙon sakin da Bashir yayi mata ba.
Har Arfa tayi watanni tara, mairamu na jinya, matan maitama suka ɗora mata tsana, baya ta tasu sam, komai chubaɗo komai ita, magajiya kuwa ta ji daɗin zama, ta zauna tare da su, ta ci-gaba da rainon Nabila cikin soyayya da ƙauna.
Dare ɗaya chubaɗo ta tashi numfashi ya sarƙe, suka ɗiba suka yi asibiti, kwananta biyu a asibiti ta daina magana, ta kasa tashi.
Hankalin maitama ya ƙi kwanciya, ya rasa abin da yake yi masa daɗi, ya rikice ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Kwana na biyar, ya zo dubata, ta buɗe idonta, ta kalle shi, ta miƙa masa hannu, ya kama hannun nata, ya durƙusa a gaban ta, ta ce "Nabila" karon farko da ta kira sunanta.
Sai kuma ta sake ce wa "Bashir" shi ma karon farko da ta kira sunan sa a rayuwarta, "Allah ya sa 'ya ta ta samu lafiya, ka ɗaukko mini ita"
A hankali ta lumshe idanunta, ya zata bacci tayi, ashe tafiyar kenan.
Ga shi namiji, ga shi soja, amma ya kasa jarumta, ya rikice tamkar hankalinsa zai gushe, ya ji mutuwar chubaɗo, fiye da yadda ya ji mutuwar iyayensa.
Bayan rasuwar ta, ya yi niyyar sallamar magajiya, amma matan suka nuna masa ba zasu riƙe Nabila ba, kai tsaye babar Nasir ya fara danƙarawa saki, baba magajiya ta yi ta bashi haƙuri, ta ce zata ci gaba da zama ta kula da Nabila.
Bayan wani lokaci ya haɗu da wani ɗan garin su Bashir, yake gaya masa ai kwanaki wata 'yar wurinsa mara lafiya ma ta rasu, hakan ya saka maitama zata ko jaririyar nan ce, amma yar wurin zakiyya ce da take shayarwa taƙi haɗawa da Nabila, ta mutu.
Ya ƙallafa soyayyar Nabila a ransa, gani yake yi tamkar chubaɗo ce, ga pneumonia ta koma mata Asma, bai yi mamaki ba, dan dama larurar mairamu ce. Hakan ya ƙara sanya wa yake kaffa-kaffa da ita.
Gashi saboda yawo tsakanin dazuzzukan barrack a garuruwa, da maitama yake yawo da su saboda wurin aiki, Nabila ta kwashi aljanu, dan dama ba ta jin magana ko kaɗan, hakan ya ƙara mata baƙin jini a gidan, gashi ba ta taɓuwa. fitinar Nabila ta mussaman ce, saboda larurarta, ga tsalle-tsalle, da iface-iface da an taɓa ta ba wuya ta faɗi, ko kuma asma ta tashi. Ba ta aikin fari balle na baƙi.
Da ta isa shiga secondary school, ta ce ita boarding take so, babu yadda maitama bai yi da ita ba, ta dage ta ce ita sai boarding. Haka aka kaita boarding jss1 cikin ƙedaren arna ƙabilu, a ajinsu ta haɗu da sumayya, ita kaɗaice bahaushiya musulma. sai ya sanar musu larurarta, saboda kar a samu matsala.
Da farko faɗa suka fara yi, daga baya ya zama ƙawance, sumayya ba ta da hayaniya, Nabila kuwa akwai fitina da neman magana.
Mahaifinta ya rasu, coustom ne a hatsarin mota, wan mahaifinta ne ya kawo ta boarding, idan aka yi hutu kamar kar su rabu, Sumayya a mayar da ita Kano, Nabila kuma tana nan garin su na Bayelsa lokacin, Maitama ya zama major.
Ya saba da ƙanin mahaifin Sumayya, wataran idan hutunsu ba yawa, a gidan su Nabila take zama, komai tare yake yi musu.
A makarantar akwai tsirarun musulmai, da malamin da yake kai koyar da su ilimin addini.
Idan an yi hutu ma, akwai malamin da yake zuwa gida, koyar da Nabila karatu.
Nabila ta ce ita ma soja take son zama, Abba ya ce ba ta isa ba, har kuka ta yi, wai ita a lallai sai ta zama soja, ga samarin inyamuran nan, suka yi mata caaa lokacin da ta zama budurwa.
Abba ya ce ba zata yi soja ba, ta ce law zata yi.
Suka haɗa kai da sumayya, wai Benin zasu tafi jami'a, Abba ya ce bai yarda ba, saboda ba ta da cikakkiyar lafiya. Tun suna sakandare idan ciwo ya tayar wa Nabila, sumayya ce take jinyarta.
Ganin ya hanata zama soja, yanzu kuma ta kawo issue na ga makarantar da take so, ya ƙyaleta, ita ma sumayya ɗan uwan babanta yana ta ƙoƙari, ya ce sumayya ba zata je Benin ba, major ya lallaɓa shi, ya ce su yi musu addu'a.
Ɓangaren Bashir kuwa, jaririyar sa ya saka mata fatima jauhar, kamar ba shi da wata 'ya sai ita, Allah ya jarrabe shi da son yarinyar nan.
Ana yayeta ya je ya ɗaukko ta, cike da makirci, mama ta karɓa ta ce ita zata riƙe, saboda ta ƙara samun fada a wurinsa, dan kuwa ya ƙara samun rufin asiri lokacin, dan sun koma kano ma, yana ƙoƙarin barin aiki ma.
Bawa aiki da kasuwanci muhimmanci, haɗi da sakaci da ibada, sallolin farilla kawai ake samun yi, babu azkar da neman tsari, hakan ya sanya matan Bashir samun damar ci gaba da yi masa asiri, kowacce so take ace babu ya ita.
A ƙarƙashin zuciyarsa yake jin wani irin nauyi a cikin zuciyarsa, kamar akwai wani babban bashi a kansa, da yakamata ace ya sauke, amma ya rasa menene.
Bashir yayi aure-aure, amma su zakiyya na hana su zama, su kansu mugunta suke yi wa kansu, amma sun kasa galaba a kan junansu.
A wayance, tun jauhar tana ƙaramar yarinya, take fuskantar izaya kala-kala, amma Bashir ba ya iya magana, duk da yana matuƙar tausayin jauhar.
Bai taɓa zancen kaita wurin babarta ba, ko kaita garin su ba, sai dai hoton ta, da ya nuna mata.
Nabila ta kammala makaranta, jin zasu koma kano, kamar ta taka rawa, dan tana tunanin rabuwa da Sumayya, saboda shaƙuwar da take tsakanin su.
A Kano tayi bautar ƙasa, ta fara aiki, duk da ba wani zama take a gidan major ba, ta tashi ana nuna mata ƙiyayya muraran a gidan, daga baya ta fuskanci major ba shi ya haifeta ba, dan haka ta saka shi a gaba, da tambayar ina babanta, tun da ya ce mamanta ta mutu, sai dai ta kan fuskanci mummunan ɓacin rai, a duk lokacin da ta tambaye shi.
Tun tana yarinya, major ya gargaɗi Magajiya da Nasir, a kan kar a kuskura, Nabila ta san cewa su biyu aka haifa, duk da ya samu labarin mutuwar ɗayar, kuma yayi mummunan gargaɗi a kan yi wa Nabila duk wani zance da ya danganci mahaifinta,