Showing 453001 words to 456000 words out of 479911 words

Chapter 152 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6036

kuwa ba wuri ɗaya aka kaita da su Indabo ba, ita Kano aka yo da ita, domin ta fara Fuskantar tuhuma ta farko, da ake yi mata a kano, amma shiru babu alamar za ayi belinta, jami'an tsaro suka tabbatar mata da cewa a gaban kotu za a gurfanar da ita.

Abokan aikinta da suka kai mata ziyara, suka tabattar mata da cewa an bayar da belin indabo, daga majiya mai ƙarfi, kuma ba a sanar da cewa an kama shi ba, ita ce kaɗai labarin kamata ya cika media.

Abin ya ɗaure mata kai sosai da sosai, sai dai ta yi masa uzuri, ta ƙara masa kwanaki, ko zai waiwayota ya sanya a bayar da belinta.

Washegari da sassafe Nabila da Hafsa tare da Alhaji Mu'azzam, suka tafi wurin Viper.

Ko da su ka je, Nabila da Hafsa ne suka shiga, shi kuma Alhaji mu'azzam ya tsaya a wani office.

Suka tarar an buɗe wurin raunin Viper ana dressing.

Da sauri Nabila ta ƙarasa, ta zauna ta gefen sa tana yi masa sannu, cikin kulawa da tausayawa.

Ya langaɓo kansa jikinta ya ce "Washh da zafi" sai ta sake rikicewa cikin tausayawa ta ce "Sannu Vi, dan Allah doctor ka yi masa a hankali"

Likitan ya ce "Ba wani zafi, tun ɗazu nake durje ciwon, bai ce da zafi ba sai da ki ka zo"

Viper ya ce "Abla zafi, da zafi yake yi mini"

Hafsa kuwa riƙe baki tayi, tana kallon ikon Allah, da wani ne ya gaya mata zata ce an zabga mata ƙarya ne, kodayeke ba abin mamaki bane, ko a baya Jauhar yana sakin jiki da ita. Nabila kuwa ta sake rikicewa ta ce "Dan Allah ciwon nan ya wanku haka a ƙyale shi"

Likitan kasancewar sa, bahaushe ne ya ce "Sai dai ya yi kukan jini, sai na cuɗe shi sosai"

Marairaicewa Nabila ta yi kawai ta saka kuka, domin ramin da taga wurin harbin yayi, kuma a haka likitan yana cewa wai bashi da ƙan jiki, wurin ya ciko.

"Ke da wasa nake yi fa, ba wani zafi kawai ina son in ga kina kula da ni ne"

"You are just pretending, amma na san da zafi"

Yayi murmushi ya ce "Idan muka koma gida, ke zaki ci gaba da yi mini dressing ɗin fa"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya ba, kuka zan ta yi" Viper yana kallo Hafsa ta silale ta bar ɗakin, bayan ta ajiye kayan abincin hannunta.

"Zafin shigar bullet ɗin, bai kai zafin ƙiyayyar da ki ka nuna mini ba, ya taɓa zuciyata sosai"

Ta marairaice ta ce "Am sorry Vi, dan Allah ka daina tunawa mana" dai-dai lokacin likitan ya kammala nananɗe masa hannun ya ce "Gashi nan maza ki haɗiye shi madam" Nabila ta yi murmushi, sai a lokacin ta farga Hafsa ba ta nan, ta ce "Kai, tare fa muka shigo da hafsa, tana ina?"

"Ta fita tun ɗazu, taga abin naki ba na ƙare bane ba" yayi maganar yana janyota jikinsa.

Ta tura baki ta ce "Ni da suka din ga soyayya a gabana ya na yi, ko kunyata ba sa ji"

"Mhmm su su na can su na soyayya, ke ki na takaicin an yi miki auren dole"

Tashi ta yi daga jikinsa, saboda da lafiyayyen hannun, yake ƙoƙarin fara lalubeta, ta ce "Bari na baka abinci ka karya, yaya ka kwana da jikin?"

"Jikina Alhamdilillah, yau zan fita ma na zagaya, na ji sauƙi sosai da sosai"

Tana cikin haɗa masa breakfast, Alhaji mu'azzam ya shigo tare da Hafsa.

Suka duba jikin Viper, Alhaji mu'azzam ya ce "Minista zai zo dubaka anjima in sha Allah"

Viper ya ce "Ni ɗin?"

"Eh kai fa" ya kalli Nabila ta kalle shi.

Ta ce "Yallaɓai, Viper ministan tsaro zai zo ya duba?"

Alhaji mu'azzam ya ce "Ni ma ba ƙaramin ministan bane, ai komai sila ne Nabila, kuma idan Allah ya yi niyyar yi maka wani abu, ko da sai ka sha baƙar wahala, kan ka same shi, sai ya baka abin nan.
Da gudunmawarsa ɗari bisa ɗari na din ga gudanar da wasu abubuwan, na taimaka wa rayuwarka.
In sha Allah kukan da ki ke yi na sha wahala, zai zame masa alkhairi, dan na yi masa bayaninsa sosai da sosai, kuma mussaman saboda kai ya kira ya ce lallai ayi bincike a wanke ka, dan haka ka kwantar da hankalinka in sha Allah babu abin da zai faru da kai sai alkhairi, wahalar da ka sha, ba zata taɓa tafiya a banza ba in sha Allah"

Shi dai Viper jin abin yake kamar ba gaske ba, bayan sun gama, Alhaji mu'azzam suka tafi, suka bar Nabila, da zummar da yamma za a zo a ɗauke ta.

Viper zuciyarsa ya din ga kaiwa nesa, kasancewar sa da daga shi Nabila, saiti yana neman ya ƙwace masa, duk da a da yana iya sarrafa kansa yadda yakamata.

Ya ja ta suka fita yawo, idan suka haɗu da na ƙasa da shi, su sara masa, idan na sama da shi ne, ya sara musu.

Duk da gargaɗin da Viper ya yi wa Walid, amma sai da ya gaya wa Liti, abin da yake faruwa, ƙarshe sai da suka yi video call da shi, sannan hankalinsu ya kwanta.

Sai da aka kwana huɗu, sannan Alhaji mu'azzam ya zo tare da ministan tsaro, kamar yadda ya sanar da Viper zai zo duba shi, ba kuma shikaɗai ba, har da babban hafsin soja na ƙasa, da wasu daga manyan shugabannin rukunin sojoji masu irin aiki irin na Viper.

Yana zaune a kan gadonsa, Nabila na kan kujera, suka shigo, ta tashi tsaye tana kallon su, sai da ta gansu tare da Alhaji mu'zzam, sannan ta ɗan nutsu.

Yana zuwa ya miƙa wa Viper hannu, sai da ya ɗan yi jimm, sannan ya miƙa masa suka gaisa.

"Finally, yau gani ga Viper, ya ci sunansa Viper, yayi kalar mazaje" yayi maganar yana murmushi.

Ɗaya daga sojojin ya ce "He's very intelligent, and hardworking man, da taimakon team ɗin sa, mun daƙila hare-hare masu yawa, yana taimakawa rundunar tsaro sosai da sosai"

Ya jinjina kai ya ce "Na ji daɗi sosai da sosai, duk da ta wani fannin mun aikata laifi, na cireka daga prison, aka yi maka horo na musamman, amma da wata ɓarnar gara wata, na ji labarin duk abin da ya sameka, hakan ya sanya na ƙara samun ƙwarin gwiwar saka hannu a taimaki rayuwar ka, duk da ka bamu wahala da farko, dan sai da na ce, idan zaka bayar da matsala gara a kasheka, amma Kankarofi ya dage, ya ce a bika a hankali.
Ina jimanta abin da ya same ka, Allah ya baka lafiya, sannan zan san abin da zamu yi maka, mu ƙara ɗaga darajarka a gidan soja, you are brave man Al'amin, the entire nation is proud of you. Ka yi abin da ya dace, sauran kuma ko su hukunta masu laifin, ko su bar su, wannan kuma su da Allah ne, get well soon my man" yayi maganar yana dukan kafaɗar Viper.

Alhaji mu'azzam ya ce "Ga kuma madam ɗin sa fa, his lioness wife, barrister Nabila, yarinyar da nake baka labari, mutuniyar Naja'atu Bunkure"

"Kai, to ai na ganta yarinya ƙarama"

"Eh yarinya mai kasada ba, su suka assasa lallai ayi wa Indabo kiranye, amma aka daƙile su, ai nan Abuja zata dawo, ku nema mata gurbi gaskiya, a din ga matsawa matasanmu, suna gwada mana tasu baiwar, hatta cheif judge ya san da ita, amma ita ba ta sani ba"

Shugaban hafsin Sojojin ya ce "Tabbas ƙasarmu Nigeria tana da nagarttun matasa, wanda za a basu dama, zasu kawo gayar a abubuwa da yawa. Kamar history ɗin Viper da na duba, da tun tasowarsa, ya samu abin da ya dace, to da tabbas a irin ƙwaƙwalwarsa, da wataƙila shi ne a kujerata, ya zama matashi mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe rundunar tsaro ta Nigeria, na yaba da basirarsa nesa ba kusa ba"

Nabila ta ji daɗin yabon da Viper ya samu, bakinta har kunne, bayan fitarsu ba ta san lokacin da ta rungume shi ba, tana ta yi wa Allah godiya.

Ta ce "Ka ga abin da na gaya maka ko? Dama lokuta da dama, Allah yana jarraba bawansa, kafin ya yi masa wata baiwa, Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya ƙara ɗaukaka Vi"

Murmushi kawai ya yi mata, shi dai baya fatan ace za ayi masa wani babban matsayi, saboda yana da 'yan adawa a cikin jami'an tsaron, gani suke kamar akwai wani fifiko na musamman da ake ba shi.

Bayan tafiyar baƙin, shugaban sojojin yake cewa kankarofi, yana yi wa Nabila kallon sani, tana kama da wani tsohon ubnagidansa a sojoji, major Yusuf maitama.

Kankarofi ya ce "Ai 'yar sa ce"

Ya ce "In dai jarumta ce da taurin zuciya, ba ta yar a ƙasa ba"

Minista ya ce yana son a saka sunan Viper, cikin sabbin naɗe-naɗen da za ayi na sojoji, a yi wa manyan ritire.

Shugaban ɓangaren su Viper ya ce "Amma sir, lokaci bai yi ba ayi masa wannan muƙamin fa"

"Eh a banza ma, ana saka waɗanda ba su cancanta ba, dan haka a saka mini sunansa, dan ya cancanta" ya ja bakinsa ya tsuke, domin kuwa kujerar da za a ɗora Viper, daga ita sai tasa.

A daddafe Viper yayi kwana tara, ranar na goma ya ce a gidansa zai kwana, ya din ga zuwa dressing ɗin, ya gaji da zaman Asibiti.

Nabila ma ta ji daɗin hakan, dan kuwa ta gaji da sintirin nan, babu wanda suka gayawa halin da ake ciki, a 'yan uwa, duk Major ya samu labari, ya kira Viper ya din ga faɗa a kan meyasa ba su faɗa ba, Nabila ta kaee shi, ta ce masa basa son tayar wa mutane hankali ne.

Allah ya taimake su, an daƙile yaɗuwar labarin ƙaryar cewar Viper ɗan ta'adda ne.

Nabila tana ta yi wa Viper santin gidan, ɗan ƙarami mai kyau, hafsa har gidan ta rakata, ta tayata suka yi 'yan gyare-gyare, komai akwai a gidan na furnitures da na buƙatu.
Sai dai komai na maza ne, sai da hafsa ta tafi gida, ta aiko mata da wasu abubuwan.

Nabila tana ta tsokanarsa, wai gidan gwauro.

Ya kalleta ya ce "Gidan gwauro ko, zaki ga gidan gwauro, yau zan mayar da shi na magidanci"

Sai kuma tayi ɗif, ta sha jinin jikinta.


*GA MASU JIRAN DOCUMENT, ZA SU IYA PAYMENT YANZU, FEW PAGES YA RAGE, ONGOING PAGES NE 500 COMPLETE DOCUMENT KUMA 1K. VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK
SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143

Ayshercool
08081012143
Ayshercool
08081012143

Wani irin miskilin murmushi yayi, tare da gyara zamansa a kan doguwar kujera.
Nabila ta ɗan saki jikinta, duba da yadda haryanzu hannunsa da saura, bai gama warkewa ba, amma ya ci gaba da yi mata wani irin murmushi da shikaɗai ya san ma'anarsa, ƙarshe jikinta ya koma zauna tare da kwantar da kansa a jikinta.

Suna yin sallar isha'i Nabila ta sulale daga parlour ta shiga ɗaya daga cikin bedrooms ɗin gidan, don ta ga al'amuran na Viper yau suna ƙoƙarin girmar tunaninta.

Ajiyar zuciya ta sauke cikin mayar da numfashi tare da bin jikinta da ke ƙamshinsa da kallo, guntun murmushi ta yi ta shige toilet, bayan ta yi wanka ta ɗauro towel ta sanya hijjabi ta fito, ta ɗauko kayan da Hafsah ta aiko mata da su.

Kayan turarurruka ne, masu ƙamshin gaske, da kayan wurin maman dr., Dan tana ɗagawa, taga sticker jikinsu.

Kiran hafsa ta yi a waya, hafsa ta ɗaga tare da faɗin "Nabilatu, ya kawo miki kayan?"

"Wannan kayan watsewar waye zai yi amfani da su?"

"Ke mana, malama ki yi abin da ya dace please, a sha amarci lafiya" ta katse wayar tana murmushi.

Nabila ta girgiza kai, ta ci gaba da dudduba kayan, kasancewar ba a shirye ta taho Abuja ba, hafsa duk ta haɗo mata kayan sakawa da na bacci.
Humra kawai ta ɗauka saboda yadda ƙamshinta ya daki hancinta tun kafin ta buɗe murfin, ta ɗaga hijab ɗin ta shafe jikinta da ita tana lumshe ido saboda daɗin ƙamshin kamar ƙara shi ake, sassanya ƙamshi ne, mai ratsa zuciya. Lokaci ɗaya ɗakin ya buɗaɗe gabaɗaya da ƙamshin.

Tana ɗaga ɓingilallun kayan baccin da Hafsan ta haɗo mata da su Viper ya turo ƙofa ya shigo, da sauri ta yi ƙasa da kayan cikin faɗuwar gaba tana ɓoyewa kamar mara gaskiya, a hanzarce ta  fara mayar wa cikin jakar da ta ciro su, a ranta tana faɗin. 'Wa zai saka wannan abun kamar matacin koko?.'

Bai ce mata komai ba ya jingina a jikin ƙofa tare da zuba wa bayanta ido, kasa juyowa ta yi ta fuskance shi, saboda wata irin kunya da tsoron shi da suke ƙara cika mata zuciya.

A hankali ya taka ya ƙarasa inda take ya tsugunna a daf da ita, yana jin yadda ƙamshinta yake ƙoƙarin zauta shi, lumshe idonsa ya yi cikin wata irin murya da ba ta san yana da ita ba ya ce. "Haka ake jinya da ma a tafi a bar mara lafiya shi kaɗai?" Kanta a ƙasa ta ce. "To ai na ga ka warke, kuma ni bacci nake ji, tun da na zo Abuja ban yi isashshen bacci ba." Shirun da ta ji bai kuma magana ba ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi, wani irin kallo da ya burkita mata zuciya ta ga yana bin ta da shi wanda ya sa ta ji wani bakon al'amari a jikinta. Ƙoƙarin janye idonta ta yi amma ya hana ta, ta hanyar kama haɓarta ya ɗaga fuskarta tare da saka idanunsa da suka ƙanƙance a cikin nata.

Ba za ta iya jure tasirin abubuwan da take gani daga idanunsa suna shiga cikin nata ba, hakan ya sa ta lumshe natan da sauri tare da ƙoƙarin ƙwace fuskarta.

"Ina Ablata mai tsiwa ta tafi ne?"
Ya faɗa yana ƙara matsar da fuskarsa daf da tata.

A ruɗe ta janye jikinta baya, kamar za ta yi kuka ta ce. "Ban da lafiya ni fa, kuma na faɗa maka bacci nake ji, haba Vi." Guntun murmushi ya yi ya zauna da kyau a kusa da ita har jikinsu na gogar na juna, idanunsa akan ƙirjinta da ke ɗagawa saboda bugun da zuciyarta take yi mata ya ce. "Faɗa mini me kike tsoro ne? Ni ban gane firgicin duk na mene ne ba fa?" Baki ta tura masa cikin kunya ba ta ce komai ba.
Ɗanyatsansa ya saka ya fara zagaye lip ɗinta da su, tsit ta yi ba ta hana shi ba sai ma lumshe ido da ta yi, a hankali ya kwantar da kanta akan kafaɗarsa mara ciwon, tare da saka hannu ya zagaye ƙugunta da shi.

Bakinsa ya kai kunnenta kamar mai raɗa ya ce. "Uhmmm, ƙamshin nan daɗi, kamar na dawwama ina shaƙar shi." Ya ƙarashe maganar yana shinshina wuyanta ta jikin hijjabin. Da sauri ta ture shi ganin yana ƙoƙarin ɗaga hijab ɗin jikinta, ga shi babu komai a jikinta sai towel, shi ma tana ji ya kunce ɗazu, hijab ɗin ne kawai rufin asirinta ga shi yana ƙoƙarin bankaɗa mata shi.

Kara naniƙar ta ya yi yana sassauke mata numfashi a fuska, gabaɗaya ya burkice mata kamar ba shi ba, ko son kallon fuskarsa ba ta yi saboda yadda idanunsa suka canza kala, ta lura kuma ƙamshin jikinta ne ya ƙara tunzura shi, ganin yana ƙoƙarin wuce gona da iri ta danne tarin tsoron da ke ranta don ta alamar sai ta haɗa da dabara za ta samu ta ƙwaci kanta, cikin kulawa ta ce.

"Vi"

"Uhmm.."
Ya amsa mata a ƙasan maƙoshi.

"Magungunanka fa, na san ba ka sha ba, kar lokaci ya ƙure."

Bai ce komai ba ya zare jikinsa a hankali ya kwanta a kan carpet ɗin da suke kai yana mayar da numfashi, wani irin yanayi yake ji da zai iya cewa rabonsa da shi, tun lokacin babyn robarsa, yadda jikinta yake rawa ne kawai ya sa ya ƙyale ta.

"Ka tashi mu je ka sha." Ta faɗa a shagwaɓe.

Kallon ta ya yi, da sauri ta yi ƙasa da kanta.

"Magani ba zai yi mini maganin abin da yake damuna ba, don haka yau ba zan sha magani ba, fanka nake so." Ya faɗa a sanyaye kamar wanda aka yiwa duka.
Da mamaki ta ce. "Fanka kuma?" Gyaɗa mata kai ya yi tare da lumshe idonsa.

"Ina jin zafi sosai."
Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana lumshe ido.

Cikin rashin fahimta ta ce. "Wai wacce fanka kake magana ne, bayan ga A.C "

"Taki kawai nake son sha, za ki ba ni?"

Ya sake faɗa tare da ɗage mata gira.
Ta jinjina masa kai cikin wasi-wasi, dan ba ta san meyake nufi ba.

"Kin tabbatar Abla?" Ya ƙara tambayar ta. Ta ɗaga masa kai, kamar ƙadangaruwa.
Tashi zaune ya yi yana ci gaba da bin ta da kallon da ba ta so ya ce. "Na gaji da ganin wannan abun, ina ta son na cire kuma kin hana ni, ki cire da kanki." Yayi maganar yana nuna mata hijjabin jikinta.

Ƙara tukukuye shi a jikinta ta yi ta ce. "Ina ruwanka da abuna, don Allah ka koma ɗakinka ka bar ni na yi baccina."

"Ni ko nake da ruwa da shi tunda ya hana ni rawar gaban hantsi. Ni yaushe ma ki ka fara saka hijjabi ne abla, haka ki ke yawonki fa da"

Waro ido ta yi ta ce "Haba Vi, wannan shaidar zaka yi mini, wallahi ka san dama can ina saka hijjabi, idan ba dogwayen riguna ba, ina saka hijjabi.

"To na ji, amma yanzu cire wannan"

Ba ta kula shi ta miƙe da sauri tana riƙe towel ɗin ta nufi hanyar toilet, shi ma bai kuma magana ba ya tashi ya fice.
Dafe ƙirji ta yi tana sakin ajiyar zuciya, tambayar kanta ta shiga yi anya kuwa wannan viper ɗin da ta sani ne? Gabaɗaya ya canza mata, kamar ba shi ne mai wannan muzuran da tsare gida ba, ga shi sai wani narke mata yake kamar wani jariri, kallon hannunta da ya dinga jagwalgwalawa ta yi tare da sakin murmushi, kamar har yanzu yana cikin nasa haka take ji.

"I love you so much my Vi."  Ta furta a hankali, ashe duk wannan maziyar ya iya kalamai da tausasawa haka?

Ta faɗa tana ɗora hannun a kan ƙirjinta tare da lumshe ido, tana jin yadda zuciyarta take bugawa.

Gudun kar ya ƙara dawowa ya same ta a haka ya sa ta fita ta shirya cikin wata doguwar riga a cikin kayan  mara nauyi, don ba za ta iya saka ɗaya rigar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login