Showing 468001 words to 471000 words out of 479911 words
musamman a cikin zukatansu, duk da a ƙarƙashin zuciyar ramma, ta na jiyo raɗaɗi da zafin rasa mutuncinta, da kuma rayuwar da ta yi, ita ba karuwa ba ita ba mai aure ba. Amma ba ta fatan sake tayar da wannan maganar, dan ta yi masa alƙawarin komai ya riga ya wuce, domin yanzu Abdul gaba ɗaya tausayi yake bata.
Da safe Nabila suna Video call da Viper, ko saukkowa ba ta yi daga kan gado ba, ta kira shi ta gaishe shi.
Ya zuba mata ido ya ce "Fito daga bargon sai mu gaisa" ta fito ta tashi zaune ta ce "Good morning Vi"
"Morning darling, ya aiki ya gidan kuma"
Cikin shagwaɓa ta ce "Am missing you"
"Next week zan shigo in sha Allah, ni kaina ina kewarki like crazy, kin rame ma fa, ya aka yi ne?"
"Hidimar tariyar ramma ce da na yi ta zirga-zirga, jiya dai ta tare Alhamdilillah "
Viper ya ce "Masha Allah, an sha gwagwarmaya Allah ya zaunar da su lafiya ina fatan dai maman ba ta ɗaga hankalinta ba?"
"Ba ta ɗaga ba, baka ga gidan rahama ba, har lefe yayi mata, ka ga rawar kai, sai dai babu kowa daga danginsa"
"Tun da dai shi ya ji ya gani, aishikenan ina yi musu fatan alkhairi, yaron ma ni tausayinsa nake ji, a idonsa zaka ga yadda yake ƙaunarta. A yadda na san shi yaro ne ɗan gata mai ji da kansa. Tun da na ga ya sauke yana magiyar a bar masa rahama, na gane lallai yana son ta"
Nabila ta ce "Vi ba dai son girma ba, wai yaro, mijin rammar ne yaro?"
"Ban girme shi ba?"
Cikin dariya ta ce "To kuma sai ka ce masa yaro?"
"Eh mana, an gaya miki ni na yau ne, na kama hanyar 40yrs fa"
Tayi dariya ta ce "Sannu dattijo"
"Eh faɗi ki ƙara beb, Allah ya sa ki samo mana baby da wuri, kin ga na kama hanyar tsufa, in ga babyna, gashi ke ki na can ni ina nan, da mun ƙara effort kuma mu yi ta addu'a"
Ta tura baki ta ce "Duk effort ɗin da saka bai isa ba sai ka saka wani? You won't kill me"
Ya ƙanƙance idanunsa ya na kallonta, yana yi mata wani miskilin murmushi.
"Menene kuma?" Ta tambaye shi a shagwaɓe.
"Maganarki ce ta bani dariya, Abbu ma fa end of this month zai angwance in sha Allah"
Waro ido Nabila ta yi ta ce "Aure zai yi?"
Ya ce "Eh mana, za a ɗaura aurensu da maman ramma in sha Allah, ni na nemi ya aureta, ita ma ta fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali"
"Au kai ka bashi shawara ya yi wa maman Shahida kishiya, na ji daɗi amma ta wani fannin, baka tunanin yadda zamansu zai kasance da maman Shahida, gata ba ta da cikakken hankali?"
Viper ya ce "Wacece ita da ba za ayi mata kishiya ba, haifarsa tayi?"
"A'a Allah ya baka haƙuri, na ga haryanzu akwai wani abu a ranka, game da matar nan, yakamata komai ya wuce"
"An gaya miki kowa irinki ne, wallahi ba zan taɓa yafewa matar nan ba har abada, ina ɗaga mata ƙafa ne kawai saboda 'yar uwata, amma ko da me take yawo ba zan yafe mata ba, ke sai anjima ma kin ɓata mini rai"
"Allah ya baka haƙuri " bai jirata ba ya kashe wayar sa.
Hafsa ta fara shiga damuwa, tun da ta koma gidan Alhaji mu'azzam, ko canza date na period ɗin ta ba ta taɓa samu ba, ta duƙufa da addu'a Allah ya sa tana da rabon samun haihuwa a rayuwarta, gashi kusan kullum sai Anty ta kirata tana tambayarta, ko ta samu ciki, har abin ya fara ba ta haushi.
Sosai Abdul yake nuna wa ramma soyayya da kulawa, sai dai ta fara fuskantar ƙalubale daga dangin Abdul, babu wanda ya zo tariyarta, amma suka fara zuwa wai ganin 'yar ƙauyen da ta yi wa Abdul asiri.
Abbu kuwa gidan da zai ajiye maman ramma daban, ba zai haɗata da Rahila ba.
Sai dai tun da ya sanar mata da zai yi aure, hauka ya ƙaru tuburan, kamar ta yi masa duka saboda azabar kishi, har da iƙirarin zata cinna musu wuta a cikin gidan.
Viper ya zo gida hutu, ya samu labarin abin da matar Abbu ta ce, ya ce sai ta koma gidansu an nema mata magani ta dawo, ba za ta ƙona masa uba ba, ace ba ta da hankali, idan ba haka ba ruwansa da haukanta, zai saka a fitar da ita daga gidan ta ƙarfin tsiya.
Har gida Shahida ta zo tana kuka, ta na bawa Viper haƙuri, a kan yayi haƙuri, idan ta fita babu in za ta je.
Viper ya ce "Shahida ba ina ƙoƙarin tozarta mahaifiyarki ba ne ba, amma da alama haryanzu karatun da duniya ta yi mata ba ta ɗauke shi ba, amma ki yi haƙuri daga ke sai mahaifina ku ka rage mini, idan ta ƙona shi ban san ya zan yi ba. Idan ba haka ba kuma a kaita asibitin masu rangwamen hankali, har sai ta warke.
Shahida ta yarda da hakan, dan ita ma gani take, larurar ta mahaifiyar ta ta, ƙara gaba take yi. Abbun ma ya amince a kan a kaita asibitin ƙwaƙwalwa. Bayan kaita kuma su ka ce gado za su bata, har sai ta warke, a can zata zauna.
Indabo hankalinsa ya kwanta sosai, jin ya zarta wata guda, yana zaune lafiya a ƙasa mai tsarki, ya miƙe ƙafa ya ɗora da tsula tsiyarsa.
Nan gida Nigeria kuma aka ce, Indabo ya je neman lafiya ne, bashi da lafiya, amma duk wasu allowances ɗin sa suna shiga account ɗin sa.
Wajen ƙarfe sha ɗaya, ya farka da kyar, kansa yana yi masa wani irin nauyi, ya duba ɗakin ya nemi yarinyar da ya kwana da ita ya rasa.
Ya tashi da kyar yana dube-dube, duk ta kwashe masa abubuwa masu muhimmanci ta gudu da su.
Ya duba gefen da ta kwanta, ya ga wani ƙaramin note.
"Ina mai farincikin sanar da kai, samun saƙon Naja'tu Bunkure, ta ce ayi maka fatan girbar abin da ka shuka, a nan duniya da ma can in da zaka"
Yana bankaɗa pillown da ta kwanta, ya tarar da ɗaurin hodar iblis, kafin ya yi wani yinƙuri, ya ji ana buga ƙofar ɗakinsa.
Ayshercool
08081012143
https://chat.whatsapp.com/CHMyWTRhDYe8tdSLnXsezq
Kunaneman group din dazakuringa sarin kayan kitchen afarashin sari yanda duyanda zaku karade kasuwa bazakusamu kasa d farashinmuba!!! Kuyi joining a mai nono kitchen utensils and household domin siyan dai dai ko sari dukkanin kayanmu available ne kuma farashi daidai aljihunku siyan nagari....maida kudi gida...gaskiya d amana sune takenmu!!!
Ɓoye hodar ya yi, gabansa na tsananta faɗuwa ya nufi ƙofar ɗakin, yana tambayar waye?. Shiru ba a bashi amsa ba, aka ci gaba da bubbuga ƙofar.
Ya buɗe ƙofar, yana buɗewa aka hankaɗo ƙofar, jami'an tsaro suka shigo cikin ɗakin, aka hau caje ɗakin.
Ba ma wadda ya buɗe suka gano ba, wata jaka suka ɗaukko, ana zazzageta sai ga miyagun ƙwayoyi da hodar iblis a ciki.
Rantse rantse indabo ya fara, cikin matsanancin tashin hankali, ya rasa ma me zai ce, suka saka masa ankwa, suka ingiza ƙeyarsa suka tafi da shi.
****
Nabila na ta rawar ƙafar shirin bikin Sumayya, sai dai jikinta gaba ɗaya babu daɗi, wani irin nauyi jikinta yake yi mata ga kasala.
Shahara da ɗaukakar da ta yi, ya sanya take samun manya manyan case, amma yanayin ɗawainiyar aure, ya sanya ta fara sarewa, gaba ɗaya jin ta take ba a dai-dai ba.
Suka shirya ita da Viper ta kai shi gidan ramma, ta ji daɗi sosai da sosai da zuwansu, dan ranar Abdul ma bai fita ba, da ta gaya masa za su zo.
Abincin da ramma ta yi, Nabila ta ce ba ta ci, wai ta dafa mata indomie ta cika attaruhu ta bata.
Ramma ta yi murmushi, ta ce mata to, ta dafa ta bata, ta ji daɗin indomien sosai da sosai, dan a gida ba ta iya cin abinci.
A hanyar komawa gida, ta saka Viper ya saya mata ƙosai, suka je gida ta dirarwa ƙosan nan, ta din ga ci da yaji tana suɗar baki.
Ya dawo daga sallar isha'i, ya tarar ta kashingiɗa, tana ta lasar lemon tsami.
"Abla, idan ki ka ce mini cikin ki yana ciwo, ko kuma ulcer, ko saurararki ba zan yi ba, kalli yadda ki ke azabtar da kanki da yaji, ina kallonki har da barbaɗa yaji a kam man ƙosai kina lasa, yanzu kuma kina shan lemon tsami ko?"
"Vi dan Allah kar ka yi mini baki mana"
"Ni dai na gaya miki ne"
Aikuwa hakan ce ta faru, kwana ta yi tana yawon banɗaki, atini ya sakota a gaba, ga amai. Yana kallonta ya yi mata banza ya sha baccinsa da daddare.
Da safe ma da kyar ta yi masa breakfast, almajirinta ta aika chemist ya sayo mata ruwan gishiri da suga ta haɗa tana sha. Gaɓoɓinta duk suka sage, wunin ranar ta kasa cin komai, indomien da ramma ta ba ta ce kawai take dawo mata.
Cikin dare yana jin motsinta, tana ta sintirin toilet, har ya basar sai ta bashi tausayi, yadda gari yayi tsit sai kakarin amanta kamar zata amayar da kayan cikinta.
Ya je ya sameta a zaune dirshen a banɗaki, duk ta fita hayyacinta. Dolensa ya fita ya bugawa maƙwabcinsa ƙofa yana da abin hawa suka tafi da Nabila Asibiti.
Kwantar da ita aka yi, fatarta duk ta bushe ta zama dehydrated, leɓenta ma ya bushe sosai.
Abinka da farin mutum, sai tayi busu-busu kamar korarriya.
Ga tausayinta ga dariya ta bashi, iya sintirin banɗakin da ta sha ma, ya isheta punishment.
"Abla ko a sayo ƙosan ne?" Murguɗa masa baki ta yi, ta lumshe idanunta, saboda har a lokacin cikinta hautsunawa yake yi.
Da safe Abdul ya shigo, yana ward round kawai ya ga su Viper.
Ya ce "Ya aka yi ba a kirawo ni ba? Daga tafiyarku shekranjiya har jikinta yayi haka?"
Viper ya ce "Eh, likitan da muka tarar yayi mata duk abin da ya kamata ai, ba ta ji ne, ka ga gobe ba ta kuma ba, ba zata ci abinci ba, sai ta zabga yaji, abincinma sai ta gama zaɓe-zaɓe, ko ba komai ai ta hanamu bacci, in da na ji daɗi ta ji a jikinta ai, nan ɗin ne yafi mana kusa shiyasa kawai muka yo nan"
Abdul ya yi murmushi ya ce "Gaskiya yakamata a tausaya mata, wataƙila baby ne ya saka take hakan, bari na yi reviewing ɗin ta" ita dai ba ta san me ake yi ba, bacci ya sake ɗaukar ta.
Gwajin farko ya tabattar da Nabila na ɗauke da juna biyu, dama Viper jikinsa ya bashi, sai dai bai tabattar ba ya bar abin a zuciyarsa.
Abdul ya ce "Ka ga babynka ne ya sakata cin yaji, ka ke mata dariya".
Cikin farinciki Viper ya ce "Har da rigimarta, da kafirin kwaɗayinta"
Ya rasa in da zai saka kansa dan murna, shi yana ta farinciki, Nabila na fama da kanta, atini ya tsaya amma jiki babu ƙwari.
Sai yamma aka sallame su, Abdul ya ɗauke su a mota zai kai su gida.
Duk in da aka tsaya sai ta ce Viper ya saya mata abu, duk sai dai ya kashe kuɗin jikinsa.
Tun da suka koma gida kuma, Nabila ta kwanta laulayi sosai da sosai, ba ta cin komai, amai ya sakata a gaba, ga zazzaɓin dare. Jauhar ta yi laulayi ita ma, amma Nabila ta fita laulayi nesa ba kusa ba, ko fita ta daina yi, sai lokaci lokaci.
Viper ne yake ta kula da ita, yana roƙon Allah ya kare masa ita da abin da yake cikinta su rabu lafiya.
Ya sanya yana da rabon ganin ɗan sa a duniya.
Sosai Viper yake ba ta mamaki, mutum ne mai tausayi, sai lallaɓata yake yi.
Ranar wata juma'a, aka ɗaura auren Abbu da maman ramma, hakan ya yi wa Viper daɗi sosai da sosai, su Major, Baba duk sun halarta, a wurin ɗaurin auren Major ya haɗu da mahaifin liti.
Classmates ɗin sa ne, tare suka yi karatu, tun lokacin secondary school, sun yi zaman mutunci, ɗakinsu ɗaya kuma kwanarsu ɗaya, tare suke komai.
Rashin wayar hannu a wancan lokacin ya sanya zumuncin na su bai ɗore ba, nan hira ta wanzu tsakaninsu, hirar yaushe rabo, da hirar ƙalubale da kuma nasarorin da suka samu a rayuwa.
Rahila tana ji tana gani, aka ajiyeta a gidan masu rangwamen hankali, Abbu kuma ya yi aurensa.
'yan kwanakin nan, kusan kullum idan Zakiyya ta kwanta bacci, sai ta yi mafarki da Chubaɗo, hannunta rungume da jarirai guda biyu, ɗanyen haihuwa, ƙafafuwanta duk jini, tana kallonta tana kuka.
Tun da ta rasu, ba ta taɓa mafarki da ita ba sai a wannan lokacin, da fari ta maze ta basar da mafarkin, amma kuma ta ci gaba da yin sa a kai a kai, har ya zamana tana yi mata gizo a zahiri.
Abu kamar wasa, ba iya ita take gani ba, wasu lokutan har da jauhar, idan ta hange su, su na zaune su na cin abinci, da sun hangota sai su nufota.
Kafin wani lokaci, ta yi wata irin rama, abin duniya ya isheta, ta kasa gaya wa kowa halin da take ciki, ba ta iya cin abinci, ga wata irin fargaba da faɗuwar gaba, sai ta din ga ganin kamar ita ma mutuwa za ta yi a kowane lokaci.
Gaba ɗaya ta ji duniya tayi mata zafi, ba ta son komai, ba ta jin daɗin komai, ta tsangwami kanta kuma ta kasa gaya wa kowa halin da ake ciki, gashi tana murna yanzu miji ya zama nata, tun da mama na kwance tana jinya, amma ita ma ta kasa jin daɗin rayuwar gaba ɗaya.
Kafin Viper ya auri Nabila, kallon mace mai son jiki yake yi mata, kai ba ka ce ta iya wani abu ba, saboda yadda take a sangarce, amma sai ya ga abin da ba haka ba, sam ba ta son ƙazanta, idan ya rage mata aikin gida ya fita, idan ya dawo a hakan zai tarar ta lallaɓa jikinta, ta gyara ko ina, har ma ta yi girki.
Kayansa za ta saka a inji ta wanke ta shanya, su bushe ta bayar a goge masa.
Sosai yake jin tausayinta, gashi lokacin komawarsa bakin aiki yayi.
Cikin kulawa ya ce "Abla ko dai tare zamu tafi ne, ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba saboda yanayin jikin nan naki"
"Komawa zaka yi, babu wani abu da zai faru in sha Allah"
"Yanzu ko a gidanku, babu wani wanda za a baki, ya zo ya tayaki zama?"
Tayi murmushi ta ce "Maraicin kenan Vi, ba sai na gayyaci kowa ba, na san ba bani za su yi ba, Sumayya ce dai ta ce mini za ta zo idan ka tafi, kar ka damu zan iya zamana"
Cikin kulawa ta ce "Abla ba kya cin abinci ai, duk kin yi wani iri" yayi maganar yana shafa wuyanta. Langaɓe masa ta sake yi, daurewa kawai take yi ne, dan kar ya ƙara shiga damuwa, dan kuwa har kuka take ɓuya tayi, ganin yadda ba ta iya cin abinci, kullum cikin amai take.
Shi kansa Viper sai da ya tambayi Abdul, ko akwai maganin da za a bata ta daina aman nan, ya ce masa sai dai ayi haƙuri, lokaci ne zata daina.
Lokaci lokaci, ramma sai ta yi girki, ta ba wa Abdul ya biya ya kai wa Nabila.
Har Viper ya tafi, hankalinsa yana kan Nabila da ya bari, Sumayya ta kan zo ta ɗan tayata zama ta kwanar mata biyu, ita kanta tana jin tausayin Nabila dan wani irin wahalallen laulayi take yi.
Sai dai duk da halin da take ciki, kasancewar 'yar dagiya ce, bai hanata kasawa tare da tsarewa ba, a duk lokacin da za a gabatar da shari'ar Naja'atu Bunkure ba.
Dan ranar farko da Bunkure ta ga Nabila, sai da haɗuwarsu ta farko ta dawo mata, bayan gama saurara Shari'a sai da Nabilan ta bita, ta ce "Allon kwaikwayona, ina fatan a yanzu kin tabattar da Allah ne mai yi, babu ruwansa lokacin da ya so, zai iya ɗaukko na can ƙasan da ba a iya hango shi, ya ɗaukaka shi sai kowa ya ji shi, hakazalika ya ɗaukko na can saman ya kai shi ƙasa, sai kowa ya manta da shi.
Ba zan ci gaba da bibiyar shari'arki dan fatan na ga bayanki ba, sam, na gama nawa tun da na kai ki ƙasa, na bayyana wa duniya wacece ke, zan bibiya ne saboda hakkin mutane da kuma jinin 'yar uwata da ki ka ce ya tafi a banza" Bunkure ba ta iya mayar da martani ba, aka zunkuɗata cikin motar masu laifi, aka tafi da ita.
*****
Duk ƙumbiya-ƙumbiyar da ake yi, da ƙoƙarin rufe abin da ya faru, sai da abun ɓoye ya bayyana na kama Indabo da miyagun ƙwayoyi a ƙasa mai tsarki.
Ramma tana zaune a falo, tana assignment, Abdul ya shigo babu ko sallama, ya wuce ɗaki.
Ta bi bayansa tana faɗin "Yau kuma waye ya taɓo mini bokan turai" idanunsa ne suka tabbatar mata akwai damuwa gagaruma.
"Doctor meyafaru kuma? Wani abin ne ya faru?"
Ya haɗiye wani abu mai ɗaci, ya dubeta ya ce "Daddy aka kama a Saudiyya"
Ramma ta ce "Subhanallah, me ya yi aka kama shi?"
"Da miyagun ƙwayoyi aka kama shi, abin takaici wai a ƙasa mai tsarki"
Ramma ta ce "Subhanallah, abin bai yi daɗi ba. Addu'a ce yanzu ya kamata ayi, Ubangiji Allah ya fitar da shi"
Ya kalli ramma idonsa fal hawaye ya ce "Allah ya fitar da shi how? Saudiyya ba fa Nigeria ba ce ba, duk laifukan da yake aikatawa ba su isa ba, sai ya tsallaka ƙasa mai tsarki?. Har tsoro nake ji, ko idan ya koma ga Allah idan na roƙa masa rahama Allah zai karɓa? Tarin mutanen da zalunta saboda kujerar nam, a ina zai gansu ya nemi afuwarsu? Ni iyayena ne jarrabawata, da ina da iko, da ban zo a tsatsonsa ba"
Cikin kulawa ramma ta fara rarrashin da bai kai zuciyarta ba ta ce "Doctor, ba a yanke tsammani da rahamar Allah, kuma shi mai rahama ne, dole a roƙa masa rahama tun da musulmi ne"
"Amma kin san Allah baya yafe hakkin wani a kan wani ko? Yau ko tuba yayi ya daina laifukan da yake yi, waɗanda ya zalunta fa wasu ba sa duniyar nan, sun bar ta, a wurin wa zai nemi yafiyar? Mutanen da ya dasawa damuwa da baƙin ciki su na da yawa fa.
Allah mai rahama ne da jin ƙai, amma sai