Showing 189001 words to 192000 words out of 479911 words
je makaranta.
Wurin shayin Al'amin kuwa, wasu irin kuɗi ne suke shiga suna fita, dan tun safe ake aikin ɗorawa da saukewa, ya zama chamber matasa sosai da sosai, duk da suna sayar da kayan shaye-shayen su a wurin, ba sa cutar Al'amin shi kuma ba ya yi musu mugunta.
Da safe su yi shayi, da rana indomie shayi, taliya haka suke wuni saye da sayarwar abinci.
Juahar sun gama haɗa kayan haihuwa, dan washegari ne ya kama ranar da za su je ayi mata inducing, tana ta jin tsoro yana kwantar mata da hankali.
Ta ce "Master"
Ya ce "Mmm"
"Ka ji sai motsi yake yi, kamar ya san gobe in Allah ya kaimu za a fara inducing ɗin nan"
Ya ce "Ya ƙagu ya ga daddynsa, Nuradeenin daddy, in sha Allah sunan Nura zan saka, kamar yadda na yi masa alƙawari".
Ta ce "Allah ya jiƙan Yaya Nura ya sa ya huta"
Ya ce "Amin".
Cikin shagwaɓa ta ce "Amma a gabanka zan haihu master, tsoro nake ji, an ce haihuwa akwai wahala fa"
"Ba wata wahala in sha Allah, ina kusa da ke, ina yi miki addu'a zaki haihu, Ni zai fara gani kafin ya ganki " yayi maganar yana sumbatar cikin nata.
"Ni dai na fuskanci ba a so na, ta babynka kawai ka ke yi" tayi maganar cikin shagwaɓa.
"Ni na isa? Dukkanku ina sonku madarata"
"Ba wani, ni baka taɓa cewa kana so na ba".
Yayi murmushi ya ce "Amma kina gani a aikace ai".
"Baka taɓa faɗa ba"
Yayi dariya ya ce "Ai ke da ruwan zinari aka rubuta sunanki a zuciyata. Ina sonki madarata, ina ƙaunarki ƙauna mai tsanani ya fi ubban shadidan"
Ta ce "Wayyo Allah daɗi. Wallahi har cikin tsakiyar zuciyata na ji kalaman nan, ba ka taɓa gaya mini ba, ka cigaba da gaya mini, da daɗi"
Ya ƙara rungumeta ya ce "I love you madarata"
"I love you too babyna, kuma baban babyna, masterna abun ƙaunata"
Har mamakin irin kalaman soyayyar da suka din ga musaya take yi, da ba ta taɓa tsammanin jin su daga bakin mastern ba.
Cikin matsanancin shauƙin so da ƙauna, suka kasance cikin farin ciki. Suka yi wanka, ya rungumota daga toilet tana takawa a hankali da ƙaton cikinta a gaba.
Ya taimaka mata, ta saka rigar bacci, sannan suka kwanta, ta kwanta a jikinsa, tayi balance da ta motsa sai yayi mata sannu.
Wani irin nannauyan bacci ne yayi awon gaba da ita.
Ji tayi kamar ana kokowa a falo, ta laluba ba ta ga Al'amin ba, ga wani irin ƙaurin taba ya cika ko ina.
Hasken fitila ta hango an kunna ƙwan falo, ta saukko ta fito falon tayi arba da wasu matasa hannunsu riƙe da miyagun makamai, madaki ta fara ganewa gabanta ya faɗi.
Sun rirriƙe Al'amin, suna shaƙa masa wani abu, jikinsa ya saki yana ta layi.
Madaki ya bushe da dariya ya ce "Ka ce baka ji, dama ka ce da ni da kai sai wani ya kawo ƙarshen wani, to ni zan kawo naka ƙarshen yau ina dodon da kake taƙama da shi? Duk da zuwan ba nawa bane ba, na uban gidanka ne Indabo, amma ya jaddada mini in tabattar ka tafi da wani mugun miki a zuciyarka".
Cikin tashin hankali jauhar ta janyo jikinta ta nufi in da Al'amin yake tana kiran sunan sa "Al'amin me ka yi musu ne? Dan Allah ku yi haƙuri mana".
Al'amin ko harshensa ya kasa motsawa, balle wata gaɓa ta jikinsa.
Madaki ya riƙo gashin jauhar, ya kalleta ya ce "Yanzu kin zama ragowa, ni kuma ba zan ɗana abun da yake ragowar maƙiyina ba, gashi kin zama cuus" ta riƙe ƙasan gashinta da Madaki ya riƙe.
Cike da mugunta, ya saka ƙafa ya kawashe na jauhar ta gaba ya saketa, ta faɗi a kan cikinta, ta ƙwala wata irin razananiyar ƙara ta ce "Ya Allah, Ya Allah, Ya Allah" ta faɗa sau uku, take jini ya fara malala daga jikinta, harshen ta kawai take motsawa a hankali tana kiran sunan Allah, ta din ga ɗaga hannunta tana son kiran sunan Al'amin. Ya ƙura mata ido yana kallon ta, cikin buguwa da mutuwar jiki, tun tana ƙoƙarin magana a hankali har ta daina motsi.
Madaki ya samu wani ƙarfe ya bugawa Al'amin a ka, shi ma suka sake shi a wurin.
Ayshercool
08081012143.
46
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Wayar Walid ce ta fara ringing, yayi shiru ya cirota daga aljihunsa ya kara a kunnensa ya ce "Ya aka yi?"
"Oga walid ka yi sauri ka dawo dan Allah, ya fara dawowa hayyacinsa, kar ya dawo gaba ɗaya ka san ba zan iya da shi ba".
Walid ya ce "Gani nan, ka yi iya ƙoƙarinka, kar ka kuskura ya fita, idan ya fita akwai ƙura ka sani, gani nan zuwa" ya katse wayar ya sakata aljihunsa, ya kalli matasan ya ce "Ku mayar da ita kawai" ya juya zai tafi.
Cikin azama Nabila da idanunta suka yi ja saboda kuka ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, kar ka tafi, ka ƙarasa mini labarin nan, yaya aka yi Viper ya tafi prsion? Shi aka ɗorawa kisan matarsa? Ta mutu ne ma ko kuwa yaya aka yi, ya kuma aka yi ya fito yanzu? Ni abubuwa da yawa ban gama fahimtar su ba, sun cukurkuɗe mini sun shige mini duhu, dan Allah kar ka tafi baka ƙarasa mini ba"
Walid ya ce "Ba zan ƙarasa ba ɗin, ba dai ke mara mutunci ba, na ɗauka haɗuwarki da shi, zai zama alkhairi amma ki ka yi mana halinku na mata, laifina ne da na kawo masa ke, Al'amin ya daɗe da cire mata a rayuwarsa, sai zuwan jauhar cikin rayuwarsa daga kawo ki a tashin farko kin mayar mana da hannun agogo baya, Viper ba zai taɓa zama ya bar liti a tsare ba, saboda shi ɗan halak ne"
Cikin matsananciyar damuwa ta ce "Na ji, na yi kuskure amma dan Allah ka yi haƙuri ka ƙarasa mini"
"Ba zan ƙarasa ba, ki je shi ya ƙarasa miki"
Cikin hanzari ta sake tarar Walid ta ce "Dan Allah ka sake yi mini jagora, ka kai ni wurinsa na nemi afuwarsa, na yi kuskure kaina ne ya riga ya gama kullewa na faɗawa lamuran a gaggauce cikin duhun kai, amma a shirye nake na gayara kuskuren da nayi"
Walid ya ƙare mata kallo ya ce "Kin riga kin aikata abun da ba zai gyaru ba, kuma kar ki sake yin gangancin zuwa in da yake, idan ba haka ba, ko bai kashe ki ba ni zan kashe ki. Ku ɓatar da ita daga gabana".
Suka saka Nabila a gaba, suka tasa ƙeyarta zuwa cikin napep ɗin da suka kawota, tana ta kallon walid tana yi masa magiya, amma suka ja babur ɗin suka tafi da ita.
Suka mayar da ita hanyar law firm ɗin su, suka bata wayarta suka tafi, wani abun hawan ta tare, ta nufi gida, zuciyarta sai bugawa dake da sauri da sauri, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, ga matsanancin tausayin Al'amin da ya mamaye zuciyarta, lallai an yi wa rayuwarsa yankan ƙauna mafi munin da har ya mutu ba zai manta da shi ba.
A falo magajiya take ce mata sumayya ta zo har gida tana nemanta, duk an kira layukanta ba sa shiga, ko akwai matsala ne, gashi yau ta daɗe sosai ba ta dawo ba.
Ai har baba magajiya ta gama maganarta, ba ta fuskanci komai ba, ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa, wayarta na ta ringing ta duba, missed calls ɗin sumayya sun fi ashirin, ga na Nasir, ban da barrister Habib, ta kashe wayar, ta cillata kan gado, ta shiga banɗaki tayi alwala ta fito ta yi sallar azahar da la'asar.
A kan daddumar ma haɗa kai da gwiwa ta yi, ta din ga kuka, za ta iya cewa tun da ta buɗe ido a duniya, ba ta ji labari mai ban tausayi da tsayawa a zuciya ba kamar na Al'amin.
"Why Nabila kin yi garaje, why would you judge the book, according to cover? Why?" Ta tambayi kanta cikin tsananin takaicin abun da ta aikata.
Ta kifa kanta a kan gadonta, wani abu tsananin ɗaci yana yi mata zafi a tsakanin ƙirjinta. Gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, wani mugun haushin kanta ya isheta.
"Ko yaya yake ji a zuciyarsa yanzu? Dole ya zama bugagge gaba ɗaya, amma idan aka bar shi ya cigaba a haka, to tabbas zai haukace, amma yanzu yaya za ayi na samu ƙarashen labarin nan? Ta haihun ko mutuwa tayi, kuma wa ya kashe aka kai shi prison? Wait, to yaya ma aka yi aka sake shi daga prison ɗin, yana yawonsa idan ya ga dama har ya je yayi ɓarna, kuma still a haka wai nansa ake yi. Wai wannan wane irin lamari ne mai sarƙaƙiya haka? Kar na je na haukace a banza mana" tayi maganar kamar za ta haukace ɗin.
Ta cigaba da sintiri, tana ƙirga yatsunta, tana lissafi.
"Kai dole na samo ƙarashen labarin nan, ko da kuwa me zai yi mini, ko dai wanda ya fara ya ƙarasa mini, ko kuma shi Vipern ya ƙarasa mini, no matter how and what it takes sai na ji ƙarshen labarin nan, kuma sai na yi wani abu a kai. Haba dan Allah What a pitful life of his? Kai, to ita meye nata ma da za ayi mata haka? Me ta yi she don't deserve this at all" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta.
Bugun ƙofar ɗakinta ake yi, amma ko gezau, da ta gaji da jin bugun ma, sai ta tashi ta tafi banɗaki, ta rufe ƙofa ta kunna fanfo, ta cigaba da kuka da tunani.
Ƙarfe takwas na dare Abba ya dawo gida, Nabila ya fara tambaya tana ina, Mama ta yamutsa baki ta ce "Ta dawo"
Ya jinjina kai, ya tafi sashensa, har ya fara cin abincin dare, ya ajiye cokalin ya kalli mama ya ce "Kirawo mini ita, ina ga ba ta san na dawo ba"
Haushi ya ƙule mama, ta tashi ta fita, ta je ɗakin Nabila, ta tarar da ƙofarta a rufe, ta din ga jijjiga ƙofar tana bugawa, amma ba ta buɗe ba.
Magajiya ta ce "Hajiya tun da ta dawo fa ta rufe kanta a ɗaki, taƙi buɗe wa, ba yadda ban yi ba taƙi buɗewa"
Mama ta yi tsaki, ta koma ta ce wa Abba, "To ka ji tun da ta dawo, ta rufe ƙofa taƙi buɗewa"
"Kuma lafiyarta ƙalau?"
"Ƙalau take, tsagwaron iskanci ne"
Ya girgiza kai ya ce "No, ko an ɓata mata rai ne, a wurin aiki ko a gida, ƙyaleta na ganta da safe na ji menene, ko kuma rigimar ce ta motsa" yayi maganar yana murmushi. Wani malolon takaici, ya ƙule mama, yadda yake lallaɓa Nabila, yana bin ta kamar wata uwarsa.
***
Abdul kuwa ganin ramma taƙi mayar da hankali ta ci abinci, hakan ba ƙaramin ƙular da shi yayi ba.
Ita kuwa jikinta ne babu daɗi, ga kewar gidansu, tana tunanin mama, ga baƙin cikin abun da yake aikata mata, gashi ya sakata a gaba duk sai ta kasa cin abincin.
Tana cikin zancen zuci, ta ji hannunsa a kan fusarta, ta tsorata ta ja da baya, ya tsuke fuska ya ce "Meye haka ne?" Ya buɗe idonta, ya ga she's still pale.
"Solomon" ya ƙwalawa kukunsa kira.
Solomon ya fito tare da cewa "Yes sir"
"Kana da kayan miya ko?"
Solomon ya jinjina kai alamar eh.
"Kawo mini tumaturi manya guda uku, da wuƙa ka haɗo mini da Apple ja guda biyu"
Ya ce "Ok sir" ya cigaba da kallon ramma, da ta ajiye cokalin, ta hau jan rigarsa da take jikinta, tana rufe ƙafafuwanta.
Mintuna kaɗan solomon ya dawo, da plate biyu, ɗaya ɗauke da tumatir, ɗaya kuma Apple sai ƙaramar wuƙa guda ɗaya.
Ya karɓa, ya matsa kusa da ita, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan cinyoyinta, ta ɗago cikin rauni idanunta sun tara hawayen takaici, ya yanka tumatirin ya miƙo mata. Ta tsaya tana kallonsa tana kallon tumaturin.
Miƙa mata yayi bakinta, ta kawar da kanta ta ce "Ni ba zan iya cin tumatur a haka ba"
"Zaki karɓa ko sai na burma miki wuƙar nan a ciki?" Yayi mata maganar cikin tsawa. A tsorace ta buɗe baki, ya din ga bata tumaturin nan, tana taunawa da kyar.
A zatonta zai bata tuffar, ta washe bakinta da ta ci tumatur, amma ya hau yanka tuffar yana ci, yana yi mata tauna a fuska, yana kallonta ga ƙafarsa a kan cinyoyinta da tayi musu nauyi.
Ya gama cin Apple ɗin sa, ya taɓa wuyanta ya ji babu zazzaɓi, ya ce "Haryanzu kina zubar da jinin ne sosai?" Tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, ya harzuƙa ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari, ya ga ba ta motsa ba, sai hawaye da yake bin kuncinta.
Ya janye ƙafarsa daga kan cinyarta, ya ce "Ki cigaba da ina yi miki magana kina kallona, ki yi mini banza kashe ki zan yi a banza" tayi shiru ba ta tanka masa ba.
Jin ana knocking ɗin ƙofar falon, ya sanya ya tashi tsaye, ya ce "Tashi ki tafi ɗaki, za a shigo". Ga mamakinsa ko gezau ba ta yi ba, ta cigaba da zama tana zubar da hawaye.
Zuba mata ido yayi, cike da tsananin mamakin shegen taurin kai a wurin kucakar 'yar ƙauyen yarinyar.
Tashi tsaye yayi, ya fizgi hannunta, amma ta faɗi a wurin, saboda dama jikin babu ƙwari, ga jiri tana ta fama.
Ya durƙusa ya ɗauke ta, ya nufi bedroom ɗin da ita, a bakin ƙofa ya dungurar da ita ta ciki, ya ja ƙofar ya rufe, ya koma ya buɗe ƙofar falon.
Wata matashiyar budurwa ce a tsaye, sanye cikin doguwar rigar material, sai hula a kanta, hannunta riƙe da Jakarta.
"Ko wata ce a ciki ne? Ina ta bugu amma baka buɗe ba?" Bai yi magana ba, ya bata hanya, ta shigo ta ajiye jakarta ta nemi wuri za ta zauna ta ce "Abdul, staining ɗin jini nake gani a kan kujerar nan"
Cikin ko in kula ya ce "And so?"
"Mace ka kawo gidan nan?"
"Eh, akwai magana ne?"
Cikin takaici ta ce "Abdul don't try me, ka sanni ka san halina, ba zai yiwu nayi dumping guys ɗina just because of you ba, and ka din ga rough play da ni ba"
Yayi murmushi ya ce "Nina, ki na da matsala, saif ne ya yanke hannu da wuƙa, yana cin Apple, yayi bleeding sosai, amma ba abun da ki ke tunani bane ba" tayi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa ko kai fa, har hankalina ya tashi, i so much miss you" tayi maganar tana rungume shi.
Gaba ɗaya sai ya ji banbarakwai, kamar ranar ya fara rungumeta, haka ya lallaɓata suka tafi ɗaya ɗakin sheƙe ayarsu, sai dai hankalinsa na kan ramma, kuma gaba ɗaya ya ji bai samu abun da ya samu a tattare da 'yar ƙaramar baƙauyyiyar yarinyar ba.
Duk yadda ya so mazewa, sai sa Nina ta fuskanci hankalinsa a ba a kanta yake ba da tayi magana sai ya ce mata ba shi da lafiya ne.
***
Har washegari, Nabila ba ta ci abinci ba, ta dai buɗe ƙofar cikin dare da zafi ya isheta, ta fara numfashi da ƙyar.
Ta ɗaukko wayar Viper, ta din ga kallo, kamar shi ne a gabanta, ta rintse idanunta tana tuno kamanninsa, a zahiri suffarsa ta ban tsoro ce, amma a baɗini abun tausayi ne.
Ƙarfe takwas na safe, yaran gidan na ta zuwa gaida Abba, sai da sauda ta shigo ta gaishe shi, ya ce "Sauda duba mini Arfa ko ta buɗe ƙofar, ki ce mata ina bata haƙuri idan laifi nayi mata, da ya sanya tun jiya ba ta neme ni ba, yau kuma ba ta zo ta gaishe ni ba" Sauda ta tashi, ranta a ɓace ta tsani yadda Abba yake sakata a shirgin Nabila ta girmeta gashi ba shiri suke yi ba, amma ayi ta zubar mata da girmanta.
Ta je ta tura ƙofar ɗakin taga ta buɗe, taga Nabila a kwance a kan gado, ta kwanta a kan hannunta, ta murɗe jikinta.
"Ke! Malama ki taso Abba yana kiranki" sai dai shiru Nabilan ba ta motsa ba.
Walida ce ta shigo ɗakin tana faɗin ta ga dama ta buɗe ɗakin kenan, sai dai tana ganin irin kwanciyar da Nabila tayi ta ja ta tsaya.
A fusace sauda ta tafi ta ɗala mata duka Walida ta ce "Yaya sauda kina ganin irin kwanciyar da tayi, da ƙyar idan ba iskokai za ta yi ba" da sauri Sauda ta ja da baya ta ce "Taɓ wallahi ba zata dake ni a banza ba" Nabila ta saka hannayenta, ta toshe kunnuwanta dan ta daina jin maganar su.
Sauda ta koma ta gaya wa Abba, cewar Nabila iskokai ta tayar.
Abba ya taso yana yi wa sauda faɗa, a kan cewa ya hana cewa Nabila tana da da iskokai, takura ce kawai ba ta so da ɓacin rai.
Ya ƙarasa ɗakin yana kiran sunan Nabila.
Ya ɗagota daga kwanciyar da ta yi, jikinta yayi wani irin mahaukacin zafi, har wani huci take yi.
Idanunta sun kumbura sun yi suntum, ga wani irin ja da suka yi, ga wasu irin siraran jijiyoyi da suka kwanta a saman goshinta.
Sai da Abba ya razana da yanayin da ya ganta, "Arfa, meyasame ki haka? Meyake yi miki ciwo"
Ta buɗe baki za ta yi magana, amma bakin ya din ga karkarwa ta kasa furta komai, hawaye ya din ga bin gefen idonta.
Ya kalli walida ya ce "Bani bedsheet a rufe mata jikinta" ta duba ta ɗaukko masa, ya rufe wa arfa jikinta, ya din ga tofa mata addu'a.
Wani abu mai nauyi, ya tokare mata ƙirji, ya hana numfashinta fita yadda yakamata, a ƙalla Abba ya kai awanni biyu, yana yi mata addu'a yana tofa mata, sai bin sa take yi da ido, amma ta kasa magana, sai can wani irin nananuyan bacci ya ɗauke ta, dan ba ta yi bacci ba jiya gaba ɗaya.
***
Walid ne yake ta kokowa da Al'amin, a kan lallai sai ya fita ya kai kansa wurin 'yan sanda, a sakar masa liti, shi a kama shi, amma kafin nan sai ya fara kashe Nabila.
"Ita wannan da tayi maka abun da bai taka kara ya karya ba zaka kashe, ko kuma zaka fuskanci indabo da madaki ne ka bar maganar wannan ƙaramar alhakin?".
Viper ya ɗaga rinanun idanunsa jawur da su ya ce "Zuwa yaushe? Zuwa yaushe mutane za su daina cutuwa