Showing 231001 words to 234000 words out of 479911 words

Chapter 78 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6131

na ci maka mutunci" cikin sauri ya fice, yana sake kiran rahama, a ransa yake jin sai dai ayi wadda za ayi, ko da kuwa hakan yana nufin bayyanawa duniya ramma ne.

***
Yana tsaye a jikin bishiya, ya juya wa hanyar da take tahowa baya, yayi crossing ƙafarsa, hannunsa ɗaya riƙe da taba, ɗaya kuma yana danna wayarsa. Daga bayansa kawai, sai mutum ya so ya juyo ya ga fuskar sa, suffarsa ta ƙaƙƙarfan namiji duk a bayyane, saboda yadda damtsensa yake a murɗe, ya cika hannun shirt ɗin sa, hannunsa ɗaya kuma ya sha ɗinki. Rigar ja sai dogon wandonsa baƙi.

"You are under arrest, officer ku kama shi" ko motsi bai yi ba, balle ya waiwayo, ta zagaya ta gefen bishiyar, tana leƙa fuskarsa, ya ɗaga kai ya kalleta ta ce "Kai baka jin tsoro ne?, ba ka ji tsoro ba da na ce you are under arrest" ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Tsoro?"

Ta ce "Eh mana"

"Hmm" kawai ya ce, ya zuƙi sigarinsa, ya kawar da kansa gefe, ya din ga sakin hayaƙin, in a passionate way"

Ta zuba masa ido, komai nasa na daban ne, kuma na musamman.

"Wurinka na zo"

Ya ɗaga mata idonsa da girarsa ɗaya alamar yana jinta, hakan ya sanya ta ɗan diririce.

Ya samu wuri ya zauna, ita ma ta zauna, ta kalleshi ta ce "Sannu ya hannunka? Na ga da sauƙi ma baka da ƙan jiki" ya kalli ciwon, ya basar, ya sake zuƙar sigarinsa.

Yana sakin hayaƙin, ta fara tari, ya kashe sigarin a jikin bishiyar, ya ce "Ina jinki".

Tayi gyaran murya ta ce "Raina ma fa babu daɗi, shari'ar nan da nake yi, so suke su yi mink fin ƙarfi, na fara sarewa kuma hope ɗin iyalin mutumin duk a kaina yake, ni da na gansu ma sai in ji zan yi kuka" tayi maganar tana goge hawayenta.

"Ohh, a haka za a tsaya mini? Idan bamu yi nasara ba, sai mu zauna mu yi kuka?" Ta girgiza kai ta ce "A'a zamu yi nasara in sha Allah, shaidar fa da na gabatar babbar shaida ce, wani ya turo mini voice na maman Yarinyar, tana kuka ta ce a taimaka mata, amma wanda ya turo ɗin yayi blocking ɗina, sai kuma aka ajiye mini wannan a office ɗin" tayi maganar tana ciro file ɗin tarihin Naja bunkure ta miƙa masa daga cikin jakarta ta goyo.

Ya karɓi file ɗin ya fara dubawa, ya miƙa mata hannunsa, ya ce "Bani wayarki" ta ce "Wayata?" Yayi shiru yana kallont, dan ba zai maimaita ba.

Ta ciro ta cire password ta miƙa masa, ya karɓa yana dannawa.

Ta zura kai tana leƙa wayar, ta ce "Me kake nema a wayar?" Ya janye wayar ya cigaba da dannawa.

Kiran Nasir ne ya shigo, ya miƙe mata dan ta ɗaga, ta girgiza masa kai ta ce "Rabu da shi"

"Ki ɗaga ki gaya masa muna tare, ba nemana yake yi ba?"

Ta kalleshi ta ce "Ga wayar nan a hannunka, ka ɗaga ka gaya masa" kafin ta rufe bakinta, ya yi accepting call ɗin, ya kai wayar kunnensa.


Ayshercool
08081012143

56
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Wata irin zabura Nabila tayi, ta kai hannunta zata karɓe wayar, amma ya riƙe hannunta yana kallonta, girgiza masa kai tayi da sigar magiya tana kallonsa.

"Hello. Hello, Arfa" muryar Nasir ta fito rangaɗau a wayar.

Viper ya ɗaga idonsa yana kallon ƙwayar idonta, ga mugun riƙon da ya yi wa hannunta da take jin tamkar zai ɓalle.

"Arfa kina ina ne? Hello kina ji na?"

Kallon da Viper yake yi mata, gaba ɗaya sai ta rikice, ga kusancin da suke da shi, ta ƙara rikicewa. Kasa daurewa tayi ta ce "Wayyo hannuna"

"Nabila, menene? Kina ina ne?"

Al'amin ya sakar mata hannunta, ya katse kiran, ta ja da baya tana murza hannunta tana ƙifta ido.

"Amm meye ma sunan naki?"

Ta kalleshi tana turɓuna fuska ta ce " 'yar madara"

Cikin sauri ya kalleta ya ce "Iyee?"

"To idan ban kai 'yar madara ba, ka din ga ce mini 'yar suga, ko mazarƙwaila" tayi maganar tana cigaba da murza hannunta.

"Baki shiryawa wannan ranar ba, ki ka yi gammon ɗaukar abun da baki san a ina zaki sauke ba?"

Ta gyara zamanta ta ce "Nayi mana, ai shi ramin ƙarya ƙurarre ne. Amma yau  da ka gaya wa DSP muna tare, da ka gama kashe ni da raina, ban gama da aikin gabana ba, ka sake ɓallo mini ruwa.
Zaman kotun nan na yau ya bani haushi, Alƙalin alamu sun nuna side zai ɗauka, gashi dattijon nan ya musa ya ce ba shi bane ba, sun kafa hujja da shi ne, wai lokacin da abun ya faru daga shi sai ita, kuma ita da shi da wata mai aiki ne, amma har gidan ɗayar  naje ban same ta ba.
Su kawo ita rammar kotu, ba su kawota ba, ba su da wata tabbatacciyar shaida, recording ɗin da na gabatar, an soke an ce sai dai uwar taje da kanta, ni na rasa me ma zan yi wallahi" tayi maganar cikin matsananciyar damuwa.

Ya nuna mata file ɗin hannunsa ya ce "Waye ya baki wannan?"

"Ban san waye ba, a kan teburina kawai na ganshi da safe" ya cigaba da daddana wayarta, ba tare da ya kalleta ba ya ce "Kin ɗauki hotona, dan ki nuna wa yayanki ya kama ni?"

Ta kalli wayar hannunsa, ta ce "Ai nayi hiding ɗin hoton, ya aka yi ka buɗe?"

Ya sake kallonta ya ce "Me kike da hotona?"

Nabila ta ce "Saboda in din ga kallonka, ina jin daɗi, askin nan da aka yi maka kayi mini kyau sosai da sosai ne" tayi maganar tana murmushi.

"Amm, amma dan Allah ina ka tafi, naji su Oga walid sun ce, ɓata kayi, wai ranar da muka rabu ina ka tafi? Can ka koma ko? A can aka ji maka ciwon nan. Na tsorata da naga an yanki cinyar wani, da sun ganni nima kasheni za su yi ko?"

Gyaɗa kai yayi, ya ce "Kina da system?"

"Eh tana gida amma" ya cigaba da danna wayarta.

"Wai dama kana magana haka? Baka taɓa yi mini doguwar magana ba sai yau. Hmmm da tabon wuƙarka da ka yi mini zan koma ga Allah, ka kusa fa kashe ni ranar farko da muka haɗu, ban san laifin da nayi maka ba ka kusa kashe ni. Amma dai yau ba ka sha komai ba ko? Naga yau ka yi mini kirki" jefa mata wayarta yayi ya tashi tsaye, ya ce "Ki kula da kanki, ana bibiyar ki, ana bibiyar wayar da ki ke yi da wata sumayya, akwai alamar tana bin diddigin abubuwan da ki ke yi, ko kuma ana bibiya bata sani ba". Ta tashi tana zare ido ta ce "Sumayyan?"

"Wanda yake bibiyarki, shi ya turo miki wannan voice ɗin, ya baki tarihin bunkure, duk da bai baki complete ba. Yana bibiyar ki ko dan ya taimake ki, ko kuma yana da manufar da yake son cimma, dan haka ki kula"

Ta dafe ƙirji ta ce "Amma meyasa za a din ga bibiyata da sumayya? To wa ka ke tunanin yana bibiyata? Ka yi mini bayani sosai da sosai to me ma nayi za a bibiye ni?. Ya cigaba da tafiya bai bata amsa ba, tabi bayansa tana cigaba da magana.

Ya tsaya cak, ya waiwayo ya kalleta, tsayawa tayi ita ma, tana kallonsa tana jiran taji mai zai ce?.

"Kin haɗu da Indabo?"

Shiru ta yi, sai kuma ta waro ido ta ja da baya, ta ce "Wai indabo ɗan siyasar nan, shi ne dai na cikin labarinka? Na ganshi a wurin aikin su sumayya, subhanallah shiyasa tun a ganin farko da nayi masa naji na tsane shi".

"Ya ganki?" "Eh, sai dai ban kula shi ba. Ai ni bai sanni ba, nima kuma ranar na fara ganinsa, sunansa kawai nake ji, amma menene?"

Ya girgiza kai ya ce "Shikenan" ya cigaba da tafiya.

Ta sake bin sa tana ɗan haɗawa da gudu, saboda saurinsa ya fi nata sosai, "To ka yi mini bayani, ni menene haɗina da shi to?"

"Babu, ki je ki mayar da hankali a kan wannan case ɗin, idan kin yi wining sai ki dawo, kar na sake ganinki a wurin nan"

Cikin rashin fahimta ta ce "To amma"

"Take your way, ki tafi na ce" yayi maganar yana nuna mata hanya, ƙyam ta tsaya tana kallonsa, mamaki ne ya cika shi, tsawar da yayi mata ko a jikinta, ta tsare shi da idanunta masu matuƙar haske, yanayin yadda take abubuwan ta, ya sake tabattar masa da akwai sangarta a tare da Nabila.

Ya juya ya tafi, ita kuma ta tsaya cak, tabi bayansa da kallo, tafiyarsa kawai gwanin burgewa, tafiya yake yi cike da ƙasaita, da bayyanar da ƙarfin da yake da shi, sai dai shi bai san yana hakan ba, har ya ƙulewa ganinta, sannan ta juya ta fara tafiya.

Sai yanzu take wasu lissafe-lissafe, tabbas sumayya ta canza, sun rage yin waya sosai yanzu, kuma ba ta kiranta da layinta sosai yanzu, kenan da gaske haɗa baki aka yi Sumayya a bibiyeta? To waye yake bibiyar ta ta? Farar motar nan ce ya faɗo mata a rai.

"To idan kuma an san ina zuwa nan fa, aka tona mini asiri, ina zuwa wurin mai laifi da ake nema ruwa a jallo. Wace amsar zan bayar na kare kaina?.

"Wai me ma ya aike ni tun farko? Ina zaman zamana" tana tafe a hanya, wani irin ciwon kai ya saukar mata, da kyar ta ƙarasa gida.

***
A kwance Abdul ya tarar da ramma, cikin damuwa ya ce "Rahama ya aka yi baki da lafiya, har na fita baki gaya mini ba?"

Ta yamutsa fuska ta ce "Na zata zan warke ne, ba sai na sha magani ba"

"Wannan ai ganganci ne, ko dai ciki ne?"

Da sauri ta ce "A'uzibillah, Allah ya yi mini tsari, ai kai ma ka san ba shi bane ba"

"Duk da haka, sai na gwada" first aid drower ɗin sa ya buɗe, yayi mata gwaje-gwaje, babu ciki sai malaria.

"Rahama, wurin nan babu sauro a ina ki ka samo malaria kuma?"

Ta kalleshi ta ce "A jikinka"

Yayi murmushi, ya haɗa allurai, zai saka mata cannula, ta hau kuka wai ba ta so.

"Rahama kina wahalar da ni, yanzu alluran baki zan yi ki shanye ko kuwa?"

"Ni hannunka da zafi gaskiya, ka samo wani yayi mini" ya harareta ya ce "Wani wa? Babu wani mahaluki da zai ganar mini jikinki a doron duniyar nan, ina kallon shi"

"Eh amma ai kai ka iya kallon na wasu"

"Duk cikin aiki ne, kuma ki yi mini shiru nayi aikina, ko na caccaka miki allurar har a baki"

Ya saka mata cannula, yayi mata allurai, ya saka mata ruwa, da duk ya ajiye su a gidan, saboda ramma.

Ya rungumeta a jikinsa, yana shafa saman cannulan, ɗaya hannun kuma yana matsa jikinta a hankali.

Ya zubawa hannunta ido, daga lokacin da ya ɗaukkota zuwa yanzu, ta canza sosai da sosai, fatarta tayi kyau, tayi haske. Ramma ba wani shahararren kyau ne da ita ba, amma yana jinta a kusa da zuciyar sa, duk da ba wani shiri suke yi ba, duk in da ya tafi tana ransa.

Bai taɓa raping ɗin mace ba, sai a kan ramma, hakazalika bai taɓa tarayya da virgin ba sai ita. Bai taɓa jin kunya da dana sanin wani rashin mutunci da ya yi ba, sai a kan abun da yayi musu, yanzu kuma uwa uba, ɓatan mahaifiyarta, bai san me zai ce mata ba, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya gano in da take.

Yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Sannu, kan ya daina ciwo?"

"A'a, amma Alhamdilillah ya rage"

"Masha Allah, ki bani labarin ƙauyenku mana, zan cika alƙawari, na yi magana da ɗan majalisar ku, lokacin da naje Abuja, zai shigar da ƙudurin hanyar ku, burtsatse ma da ki ka ce, ina jiran injiniyoyi su gama lissafi su turo mini, za ayi muku guda uku" ta tashi zaune ta kalleshi ta ce "Da gaske dan Allah?"

Ya jinjina mata kai yana murmushi, itama murmushin ta yi, ta ce "Yan garinmu za su ji daɗi, mun gode Allah ya saka da alkhairi, mun gode sosai, yan garinmu mun daɗe muna koken rashin hanyar nan, amma ba ayi mana ba, mun gode"

"Yau ba Allah ya isan?"

"Ai wancan abun da ka yi mini daban, wannan ma daban, amma Allah ya isa tana nan"

Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki yafe mini mana sweetheart "

Ramma ta ce "Ka mayar da ni wurin mahaifiyata, ka nemi afuwarta, amma haryanzu a zuciyata ban ji zan iya yafe maka ba, daga kai har anty maijidda, da wannan bayahudiyar matar"

Yayi shiru ya sunkuyar da kai, zuciyarsa babu daɗi, ta ɗaga kai ta kalli fuskar sa, ta ce "Oho, ba zaka bani tausayi ba, ka tuba ga Allah ka gyara halayenka, dan ka samu kyakkyawar makoma. Ka cigaba hannun ya fara zafi" bai ce mata uffan ba, ya cigaba da shafa mata hannun.

Ta saka ɗaya hannun ta juyo da fuskarsa, taga idanunsa sun yi ja, sun bayyanar da tsantsar damuwa.

"To meye kuma?" Ya girgiza kai alamar babu komai.

"Ka tabattar?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Shikenan, to kayi haƙuri dai, ni gaskiyata na gaya maka, baka san zafin abun da ka yi mini bane, amma naga kamar ka ji haushi"

"Meyasa zan ji haushi, carbi zan sayo ki zauna ki yi ta jan Allah ya isan son ranki" ta murguɗa masa baki, ta kawar da kanta gefe.

***
Madaki ya zuba wa cinyarsa ido, yadda ciwon da Viper ya ji masa yayi wani irin mugun rami, maimakon ya yi ja ma, sai ya koma yayi kore, wasu irin jijiyoyi duk suka ɗaɗɗaga a gefen ciwon, ƙafar ta ƙara riƙewa, ba ya iya takata sai dai ya dinga jirgata.

Ya kalli babban amintaccen yaronsa ya ce "Lakwari, ciwon nan fa cigaba yake yi, kenan ta tabatta alkadarina ya karye?"

"Nima na gani maigida, kaga ana ta saka maganin, amma sai cigaba yake yi. Ba zamu yi saurin yanke hukunci ba, mu bi dare kawai, muyi makabeli mu ɓace mu yanka gabas, mu koma in da aka fara, ya duba mana, idan da wani abu da za a yi a kai, idan ba haka ba, mai zamani ya yi maka muguwar illa, kuma yana sane yayi hakan".

Madaki ya jinjina kai ya ce "Haka ne, babban abun da ya bani mamaki, bai wuce wanda suka zo suka ɗauke shi ba, ban san suwaye ba. Ta tabbata yana da waɗanda suke goge laifukan da yake aikatawa, yakamata na sanar da indabo"

Lakwari ya ce "Haka ne, amma mu fara neman mafita, a karya dafin nan da ya saka maka, kafin duk wata magana ta biyo baya".

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan".

***
Sumayya da murtala ne a zaune a gaban MD sun yi fiƙi-fiƙi da idanu, gefe ga lawisa a zaune.

"Abun da ku ke yi, da kai da sumayya ya fara yawa a wurin nan, ko dai ku bi tsarikanmu, da abun da muka ce dan cigaban tashar nan, ko kuma ku ajiye mana aikinmu. Duk jajircewarku akwai waɗanda suka fiku. Gashi kun saka hankalin mutane gaba ɗaya ya yo kanmu, saboda recording ɗin da ku ka saki a duniya da yake bayyanar da zargi ga Naja'atu Bunkure, wands duniya kowa ya shida mutuniyar kirki ce, mai yi wa mutane hidima".

Murtala ya ce "Tuba muke, muna neman afuwa in sha Allah ba zamu sake ba"

"Daga kai har ita, wannan ne karo na biyu da kuka aikata mana laifuka, muna ƙyaleku, na uku kora ce. Yanzu dole mu san yadda zamu yi mu gyara wannan shirmen da kuka yi" Murtala yayi ta bayar da haƙuri, sumayya kuwa fafur ta yi shiru, taƙi cewa komai.

Sun fito daga ofishin MD, tana hura hanci, ta tarar da Nabila.

Sumayya ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita, ta ce "Ke kuma daga ina? Kin je kin haɗa kai da Uncle murtala, mun saka recording ɗin da yayi miki, a kan shari'ar nan, yanzu aka gama sauke mana kwandon jaraba a ka.

Nabila ta ƙurawa sumayya ido, ta ce "Sumy why?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Don't mind me, mota fa ta iso, na zo na sanar miki"

Ihun farinciki sumayya tayi ta ce "Are you serious, ko kuma jirgani ki ke yi?"

"Da gaske nake, amma Abba ya ce ba zan hau ba, sai driving licence ɗina ya zama ready, kin san shi da ƙa'ida"

Cikin farinciki ta ce "Alhamdilillah, summa Alhamdilillah yawo ba kama ƙafar yaro, Allah ya saka wa Abba da alkhairi, uban marayu mai uban ma goyawa yake yi. Amma dan Allah arfat ki kula, ki san in da zaki din ga zuwa, banda rigima da faɗa da mutane a titi" ta din ga kallon sumayya, da son tabattar da abun da Viper ya gaya mata, yanzu sai ayi amfani da ita, a cutar da ita, sam ta kasa yarda gaba ɗaya.

Wada M karofi ne ya kira Nabila a waya, ta ɗaga ta ce "Hello sir"

"My beautiful angel, ya kike yau bamu gaisa ba gaba ɗaya, kin ƙi bari mu haɗu, gashi na koma wurin aiki"

Ta ɗan kashe murya ta ce "Ba haka bane ranka ya daɗe, ka san aikin namu ne babu zama, amma very soon zaka zo har gida mu gaisa" yayi murmushi ya ce "To shikenan, na san maybe kina wurin aiki, da daddare zamu yi waya in sha Allah"

"Ok Allah ya kaimu, ka kula da kanka sosai, kar ka yi aiki ka gaji da yawa"

Yayi dariya ya ce "Thank you my dear"

Sumayya ta ce "Ohh wa kuma ake yaudara, wa aka kwaso mana?" Nabila ta bata labarin wada M karofi.

Sumayya ta ce "Allah ya sa shi ne mijin, kakarmu ta yanke saƙa, kin san waye mutumin nan kuwa Arfa? Allah ya tsaga miki farinjinin manyan mutane, kar ki yi mana buƙulu dan Allah".

Nabila ta tashi ta ce "Taɓ gaskiya ba na son shi, ki zo gida kiga motarmu"

Sumayya ta ce "Dolena" Nabila tayi mata sallama ta fito, zuciyarta na cigaba da wasi-wasi a kan Sumayya, har ga Allah tana ƙaunar sumayya har cikin zuciyarta, ta kasa yadda da abun da Viper ya gaya mata.

Nabila na tafiya aka kira Sumayya a waya, ta ɗaga tayi shiru.

"Sumayya meyasa ki ke wasa da rayuwar ki, da ta ƙawar taki ne? Bayan ɗan waken zagaye da ki ke yi,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login