Showing 471001 words to 474000 words out of 479911 words

Chapter 158 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6075

da ya haramta shi a kan kansa, sannan ya sanya shi abin haramtawa a tsakaninmu, ke ki ka biya mini wannan hadisin, ni babu wani abu da za a gaya mini yanzu na ji sanyi, ina tausaya masa haɗuwarsa da Allah"

Jiki a sanyaye ramma ta ce "Ka yi gaskiya, amma yanzu ai ba mutuwar yayi ba"

Ya kalleta fuskarsa duk hawaye ya ce "Kin san hukuncin ace an kama mutum da irin abin da aka kama shi da shi a ƙasa mai tsarki? Muddin suka tabattar hukuncin kisa ne" gaba ɗaya sai ta rasa me ma za ta ce. Har ga Allah Abdul ya bata tausayi, amma ita ba ta ji ta damu ba ko kaɗan, albarkacin Abdul ɗin ne ma bai sanya ta ce Allah ya ƙara a zuciyarta ba.


****

Hafsa ta biyo Alhaji mu'azzam, domin kawo ziyara gida, sai dai ta tsorata da yadda ta ga jikin mama ya ƙara tsananta, ta zama wata irin miskiniya abin tsoro.

Sai dai ta tsorata da ganin ita ma tata mahaifiyar ta yi wata irin muguwar rama, gashi duk kauɗinta yanzu ba ta son yin magana.
Ga zaman ɗaki, cikin mamaki take tambayarta ko lafiya?

Ta fashe da kuka take gaya wa Hafsa abin da yake faruwa.


Tayi shiru sannan ta ce "Ikon Allah, kin ga kaɗan daga illar biye-biye anty, yanzu an ce Anty Rahila tana gidan masu rangwamen hankali, ni na fara yin ciwon hauka a sanadin shaye-shaye, ke ma kuma ga alamu"

Ta waro ido ta ce "Hauka kuma?"

"Eh matsalar ƙwaƙwalwa, wannan alamomi ne na depression"

"Wallahi na yarda da maganarki, wasu lokutan ji nake kamar na fita da gudu ina ihu, duniyar tayi mini zafi, amma ni sai nake tunanin ko matar nan ce duk da tana kwance, ta haɗa kai da yaranta suke banko mini asiri"

Hafsa ta katseta ta ce "Mama babu wanda yake banko miki wani asiri, ganin Jauhar da mahaifiyarta da ki ke yawan yi, yana alamta miki, kin tafka mummunan laifi a rayuwarki, da babu lallai sun yafe miki, gashi ba sa duniyar. Shawara ɗaya zan baki, ki din ga yi musu addu'a, sannan ki dage da istigfari kuma ki daure, ki nemi afuwar Baba, sannan ki nemi afuwar ɗan uwanta babansu Nabila, da ita kanta Nabilan, tun da duk su na da alaƙa da su, idan ki na so ki samu nutsuwa. Sai kuma mu dangana da asibiti ki fara ganin likita"

"Tabɗijan, kawai kuma sai na je ina cewa wani su yafe mini, da na yi musu me? Wallahi ba zani ba"

Cikin takaici da mamaki, take bin Antyn da kallo, ta ce "Ba zaki ba Anty, sai abin da ya samu babar su Shahida ya same ki tukuna?"

"Ya daɗe bai same nin ba, ba zani ba, ni na san asiri kawai ake yi mini, kuma ni dai-dai nake da kowane mara mutunci" Duk yadda hafsa ta so ganar da ita, ta rufe idonta taƙi ganewa.

"To mu je asibiti, tun da nima kin ga da haka na warke, da aka din ga kai ni Asibiti"

"Ba zani ba shi ma, ni na san maganin matsalata" haka Hafsa ta ƙyaleta, dan babu yadda ta iya da ita".


Washegarin zuwanta ta tafi gidan Nabila, tayi sa'a Sumayya ma tana can, haɗuwar ta su ta yi musu daɗi, sai dai a kallon farko ta ga Nabila ta rame sosai, ba ta yi magana ba, Nabila nata nuƙu-nuƙu da hijjabi, amma sai da Hafsa ta gano ta.

"Abla, wai me ki ke ɓoyewa ne? Duk ɓoyonki ana gani ai"

Kunya ta kama Nabila ta ce "Ake gane me?"

"Ɗan baban mana"

Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Ai na gaya mata ana gani, taƙi yadda, mai cewa sai ta yi good 2yrs a gidan miji, kafin ta ɗau ciki, amma farawa da bisimillah"

Hafsa ta kwashe da dariya ta ce "Ai kura ta san gidan mai babban sanda, ai ita ta san in da za ta iya cewa, sai ta shekara biyun ba ta haihu ba, ba dai a gidan Viper ba"

Nabila ta ce "Baku da aikin yi ne, ulcer ce ta kumbura mini ciki"

"Viper dai yayi ajiya, shi ya kumbura miki cikin" Hafsa tayi maganar tana dariya.

"Ku da Allah, kuna munafuncin mijina a gabana, wanda idan yana nan, ko tarin kirki ba zaku iya ba, a ƙyale mini shi kar a saka ya ƙware, yana can yana aiki, kuna nan ku na gulmarsa"

Hafsa ta ce "Ke abin alkhairi ne ai, Ubangiji Allah ya inganta miki ƙanwata, ya rabaku lafiya"

"Amin Anty hafsyna"

Sumayya ta ce "Shahida ma na ga kamar an gamu"

Hafsa ta ce "Nima ma gani, ai na je gidanta"

Nabila tayi dariya ta ce "Mijinta ce mini yayi baya son saka ido mura take yi" suka yi ta hirarsu gwanin sha'awa, hafsa ta ce "Dan Allah ku tayani da addu'a, nima Ubangiji Allah ya sa ina da rabon ganin jinina a duniya, ni haryanzu shiru" suka yi ta kwantar mata da hankali da yi mata fatan alkhairi.

Aka koma maganar bikin Sumayya, Hafsa na ta ƙara nanata mata, kar ta kuskura ta je ta sha wani abu da ba ta san menene ba, alhalin ga likitar mata.

Nabila ta ce "In dai ki na son daga shiga kema ki ɗaukko magana, ki riƙe wa kayan likitar mata wuta, zaki gane baki da wayo, laulayi is not your mate "

Hafsa ta ce "Rabu da ita, ta ji da assignment ɗin da Viper ya bata"

Nabila na daga kwance a kan cinyar Sumayya ta ce "Wuta balbal idan aka ƙira sunan mijina"

"An faɗa Aminu Viper, mai zamani"

"Ku da Allah"

Nabila ta dage ta din ga lallaɓa hafsa, sai da ta kira Alhaji mu'azzam, suka kwana a gidan.

Ita dai kaf 'ya'yan babansu, da aka nuna mata, babu wanda take jin tana so, kamar hafsa, ita dai tana ƙaunarta sosai.

Sai kuma suka koma hirar ƙalubalen rayuwar gidan auren, tare da ba wa junansu shawarwarin da za su fishshe su.


Kwana biyun da suka yi mata ta ji daɗi sosai, bayan tafiyarsu zaman kaɗaicin ya ci gaba da damunta.

Babu tsammani taga Viper ya dawo, aikuwa ta ji daɗin hakan.

"Vi ya na ganka ka dawo yau?"

"Shi ne lokacin da aka ce ki fara zuwa awo, ina lissafe ni ai"

Tun daga Abuja ya taho mata da amala, saboda ya san tana sonta, aikuwa ta ji daɗin amalar nan.

Ta ci kaɗan ta ga tayi awa biyu ba ta yi amanta ba, aikuwa ta rufar mata, ta cinye tas.
Kwana tayi amai, ba ta yi baccin kirki ba.

Da safe ya buga wa Abdul waya, ya ce masa zai kawo Nabila asibiti, ya ce masa to.

Abdul ya yi mamki, ganin cikin Nabila wata huɗu, amma ya ɗago sosai.

Suka gaggaisa, ya yi mata sannu.

Viper ya ce "Ya ƙanwata?"

"Tana gida sun yi hutu, ga saƙo ma ta bani, wai na kawowa yayarta" yayi maganar yana nuna musu fulas ɗin abinci.

"Ko menene a ciki, in dai yaji yayi yawa ba zaki ci ba, bar rawar jiki" yayi maganar yana harar Nabila.

Tashi Nabila ta yi, ta buɗe flask ɗin, ƙamshin miyar jajjage ya daki hancint, tayi maza ta rufe dan da alama miyar mai yaji ce.

Abdul ya ce "Ina ce mata zaku zo, ta zaunar da ni sai na taho miki da abinci"

Viper ya ce "Duk in da muka je, har rawar jiki take ace mata ga abinci, kamar ba na ba ta abinci a gida"

"Bana ƙoshi ne" tayi maganar tana dariya.

Abdul ya ce "Maybe na gidanta ba ta iya ci, idan suna irin wannan halin sai haƙuri ai"

Viper ya ce "Haka ne, amma ya na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?"

Bai ɓoyewa Viper ba, ya gaya masa komai, Viper ya ce "Irin haka sai haƙuri, kuma ka ci gaba da addu'a, kuma kai ka kiyaye aikata makamantan laifukan da ya aikata"

Kalaman Viper dai babu tausayawa ga Indabo, amma rarrashi ne ga Abdul.

Ɗakin scanic suka tafi, bayan an yi wa Nabila gwaje-gwajen masu ciki.

Viper yana tsaye a kan Nabila, yana riƙe da hannunta.

Abdul yake gaya wa Viper, doctor Muktar ya tafi ƙaro karatu malesia.

Abdul yana cikin maganar ya yi murmushi, ya kalli Viper ya ce "Congratulations bani goron Albishir"

"Albishir ɗin me? Bayan dama can na san da akwai cikin?"

Abdul ya ce "Ba zan faɗa ba ne, sai ka bani tukuici"

Viper ya ce "Faɗi sai a baka"

"Naƙi wayon, kawo kawai"

Viper ya yi murmushi ya zaro dubu ɗaya ya ajiye masa ya ce "Faɗi idan yayi mini sai na ƙara maka"

Abdul ya ce "Ai kai ne mayar da tukuicin, ai albishir ɗin namu ne gaba ɗaya. Twins ce dama ita ai ko?" Viper ya jinjina masa kai.

"So congratulations, babynta biyu ne a cikinta, twins ne yaran"

Waro ido Viper ya yi yana kallon screen ɗin injin scanic ɗin, tamkar zai gane menene a jiki.
Jikinsa ya hau wata irin tsuma ya ce "Dan Allah da gaske ka ke ko da wasa?"

"Yaya zan yi maka wasa da abu mai muhimmanci har haka? Wallahi da gaske nake, twins ne, kuma duk su na cikin ƙoshin lafiya"

Viper ya miƙe ya yi sujudar godiya ga Allah, ya miƙe ya rasa me ma zai yi ko ya ce.

Ya kwance agogon hannunsa, ya ajiyewa Abdul, ya zaro ɗaya daga zobensa na azurfa shi ma ya ajiye masa.

Ya fara laluba aljihunsa, Abdul ya ce "Haba Viper, yanzu mun zama ɗaya sirikina ne fa kai, ina tayaka murna, Allah ya inganta ya raba lafiya, amma ku yi shiru kar wanda aka gaya wa biyu ne. Ga agogonka da zobenka ba zan karɓa ba"

Viper ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar mu yi haka da kai, yarana biyu na rasa, ɗaya aka yi ɓarinsa, ɗaya kuma bai ma zo duniyar ba, yanzu Allah ya haɗa mini biyu. Na ma rasa wane irin farinciki zan yi ne, ba kai ka bani ba, saƙon kawai ka gaya mini, amma ba ka ji zuciyata ba, Alhamdilillah ala kulli halin.
Na rasa jauhar, ga Nabila, na rasa yarana ya bani biyu Allah Alhamdilillah. Yayi maganar yana goge ƙwalla.

Jikin Abdul ya yi sanyi, da ya tuna babansa ne silar ajalin matar Viper.

Ya tuna lokacin da yake yi wa Viper kallon ɗan jagaliya, ɗan maula ƙasƙantaccen mutum da yake zuwa maula wurin mahaifinsa, yau gashi Allah ya canza komai, ya nutsu ya zama mai bayar da gudummawa ga al'umma.

Ya ƙarasa ya ɗago Nabila, yana mata sannu.

"Abincina" tayi maganar kamar ƙaramar yarinya tana kallonsa.

"Ai dole ma a ɗaukko abincin nan Abla"

"Kuma ka gaya musu su daina damuna, ko in ƙi haifarsu"

Cikin murmushinsa da yake ƙara masa kyau ya ce "Za su daina in sha Allah"

Abdul ya ci gaba da yi musu fatan alkhairi, da taya su murna.



Tun da suka koma gida, duk in da Nabila ta yi sai ya bi ta da kallo, yana tunanin yara biyu ne a cikinta.

Addu'a ya din ga yi, Allah ya sa yana rabon da ganin yaran, tare da yi musu fatan shiriya tun kafin su zo duniya, da fatan Allah ya sa kar laifukan da ya aikata su shafi yaransa.


Nabila tunani ta din ga yi, na abin da za ta yi, da zai wayar wa da al'umma kai, a kan muhimmancin neman 'yancinsu, da ƙirƙiro abubuwan da za su taimaka wurin ƴaƙi da harkar daba da shaye-shaye da kuma bangar siyasa.

Yanayin shirin bikin Sumayya da suke yi, ya hanata zama su tattauna yadda yakamata, ta na son ta yi magana da Viper ma, domin za ta so goyon bayansa ɗari bisa ɗari a kan abin da take ƙudurin yi ɗin.


Aka yi taron bikin sumayya lafiya, aka gama lafiya, ita ma mijinta mutum ne mai rufin asiri, ya na da mace ɗaya da yara uku, cousin ɗin Alhaji mu'azzam ne, shi ne ya haɗa shi da ita ma.

Major yana ta mitar Nabila kwana biyu ba ta zuwa gaishe shi, ya kirata ya ce mata shi zai zo ya ganta, amma ta ce masa ba ta nan, sai dare zata dawo.

Bayan sallar isha'i kuwa sai gashi shi da Anty, tun da suka zo ta manne a wuri ɗaya ta ƙi tashi.

Viper ya yi wa Major zancen rabon gadon Jauhar, za a sayar da kayanta, Nabila ta ce ba ta son kaya.

Abba ya ce "Ni idan an yi wa kayan kuɗi a bani na saya, sai mu bayar sadaka Allah ya kai mata ladan".

Viper ya ce "Ita ma ta ce kuɗin, ayi wani abu da su, Allah ya kai ladan kabarin Jauhar"

Major ya ce "Hakan ma yayi kyau, amma a ajiye wani abu da za a din ga tunawa da ita dai"

"Eh in sha Allah, ko ma muje gidan tare, sai na yi wa Baba magana muje a duba"

Major ya ce "Duk yadda ka yi yayi, Allah ya saka maka da alkhairi kai ma, Allah kuma ya ƙara bamu haƙurin rashin Jauhar da mahaifiyarta"

Har suka gama abin da za su yi, Nabila taƙi yi musu rakiya, sai Viper ne ya raka su, suna tafe a hanya Major yake mitar Nabila duk ta zama so silent, ko dai akwai wani ne da take ɓoyewa.

Anty ta ce "Ciki ne fa da ita, take ta wannan nuƙu-nuƙun"

"Kaii ciki, tun yanzu?"

Anty ta ce "Ahh ikon Allah, wata nawa da yin auren?"

"Lallai Major, wato Arfa ce 'ya, mu a shekara nawa muka haihu?"

Ya ce "Ai ku tun zamanin baya ne, ita kuwa kamar yayi wuri, haryanzu ƙanƙantarta nake gani"

"Shekara ashirin da shida?"

"Eh mana, rainon ciki akwai wahala, kin ga ita ga ba uwa, ku ba tayi sakewar da za ta tunkaroku da wannan maganar ba, balle ma idan wani abin ne ku taimaka mata ba, bari na koma gida, zan kirata a waya, ko da wani abu da take buƙata"

Waro ido ta yi ta ce "Sai ka tambayeta a kan cikin?"

"To shi ne me? Ni uwar ni ne uban, ai cikin halak ne, mijinta ba mazauni ba ne ba, cikin fari ba ta san kan komai ba"

"Amma ai ka bari mu mu tambayeta ko"

"Tsakaninki da Allah yaushe rabonki da ita, ban da yau da na ce ki zo ki rako ni wurinta? Ni ba abin kunya ne a wurina ba, idan ta kama na dawo da ita gida, gani gata magajiya ta din ga kula mini da ita, ba ruwanku" Anty ta ja bakinta ta tsuke, dan ba ta ga tsari a hakan ba.

Aikuwa kamar yadda ya faɗa, hakan aka yi, bayan ya koma gida ya kira Nabila yake tambayarta. Kasa ba shi amsa tayi, ta ji tamkar ta nutse a wurin, saboda kunya.
"Idan kin san akwai matsala, ni sai na yi wa mijin naki magana, idan baya gari ki taho gida, ko na turo miki magajiya, ta din ga kula da ke"

"Abba yana kula da ni, baba Magajiya kuma yakamata ace zuwa yanzu ta huta ita ma, ina iya yin komai ma"

"Kin tabatta?"

"Eh Abba"

"Arfa ba na son kawaicin nan naki, Ni babu kunya a tsakanina da ke, baki da uwa a raye, kar ki bari wani abu ya shige miki duhu, idan ba zaki iya kirana a waya ba, ki yi mini message kin ji ko?"

"To Abba"

"Allah ne mai komai, amma ba zan so ki sha wahalar da mahaifiyarki ta sha ba"

"In sha Allah"

Ya ce "Yauwwa, sai da safe, ki gaida mijin naki, Allah ya yi muku albarka gaba ɗaya"

"Amin mun gode, ayi wa Anty ya ta je gida" ta kashe wayar, Viper ya na kusa da ita, ya na saurarenta.

"Abla" ta waiwayo ta ce "Na'am"

"Kowane dangi, idan aka samu irin Abba ko guda ɗaya ne, mai jajircewa a kan zumunci, ba tare da kallon ɗora wa kansa ɗawainiya ne ba, da an rage wani abin. Mutum ne mai zafi, amma jajirtacce ya san abin da yake yi. Ke kaɗai sadaƙatul jariya ce a gare shi ko bayan ransa. Banda ladan zumunci hatta taimakon da ki ke yi wa al'umma yana da lada. Kin tsayawa dattijon nan babu ko sisi, kin tsaya wa rahama, kin tsaya mini duk babu ko sisi, kin siffantu da wasu daga cikin kyawawan ɗabi'unsa, da shi da Alhaji mu'zzam, da Walid da liti, mutane ne da al'umma ke buƙatar irin su."

Nabila ta ɓata fuska ta ce "Ban da liti dai"

"Haba masoyiyya, ya fa baki haƙuri. Wallahi Abdallah mutumin kirki ne fiye da yadda ki ke zato, kawai dai mutum ne da babu ruwansa da kara, zai yi abin da yake so ne, ko yayi maka daɗi ko ya kashe ka, bai damu ba"

"Ai na ga alama, ni fa ban taɓa zaton ya na barkwanci ba, ranar da na fara ganinsa, a tal'udu wurin da yake sayar da katin waya, amma kayan maye yake sayarwa, sai da na tsorata.
Babu alamar ɗigon imani a tattare da shi, sai fa da ya ce sai ya kashe ni, idan na sake zuwa"

"Wallahi ba haka yake ba, sharrin ƙwaya ne kawai da kayan maye, Allah dai ya ƙara shirya mu, rayuwa duk ta fi yi mana daɗi a yanzu. Mutane kowa yana sonmu, yana son haɗa alaƙa da mu, har ana ɗora mana wasu nauye-nauye.
Duk a baya, mu kanmu bamu jin cewa, a duniyar da mutane suke muke, hango duniyarmu muke yi daban, saboda kowa kallon mutane marasa amfani yake yi mana. Marigayiyya ce ta fara ƙoƙarin ankarar da mu, muhimmancinmu a cikin al'umma."

Nabila ta jinjina kai ta ce"Jauhar ta yi namijin ƙoƙari ƙwarai da gaske, kuma in sha Allah, yana daga cikin abin da na ƙudurce a zuciyata, ci gaba da yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ta hanyar nuna wa wanda suka tsinci kansu a harkar, su ma 'ya'ya ne, kuma akwai amfanin da za su yi wa al'umma.
Ina son da ni da kai, sa sumayya, barrister Habib, da wanda suka kamata, mu ga abin yi, idan ta kama ko ƙungiya ce mu kafa, ko mutane goma ne suka shiryu a sanadinmu, mun yi nasara"

"Duk a bar wannan maganar, sai Allah ya saka kin sauka lafiya, sai ayi ta, tunani mai kyau sosai da sosai. Sumayyan nan taki ma 'yar aljanna ce da yardar Allah, na ga tana yinki saboda Allah"

"Ko ba Sumayya ba, ba ka ga Abba ne yayi waliccin aurenta ba ma, ƙawar amana kenan, ina alfahari da ita"

Haka Viper suka ci gaba da tattaunawa da shi da abar ƙaunarsa.


Kwanci tashi asarar mai rai, cikin Nabila ya yi watanni shida, amma kamar zata haihu a lokacin, saboda girma, hakan ya saka ta daina fita gaba ɗaya, saboda nauyin cikin.

Shahida kuwa matar Walid, ta fita nauyi, dan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login