Showing 414001 words to 417000 words out of 479911 words
"Ko dan saboda wannan ai yakamata na fara saye sunan" tayi maganar tana nuna masa cikinta, da ya kai watanni shida ya fito sosai.
Murmushi yayi ya zira hannunsa cikin hijjabinta, ya shafa cikin nata.
"Ina fatan dai wurin awon babu wata matsala da babyn namu?"
Ta ce "Anty Nabila tana kula da ni sosai, tana kai ni awo"
"To ki na cin abincin da shan maganin dai ko?"
Ta jinjina kai ta ce "Eh, kawai dai ina son na ga ka fito ne, ina cikin damuwa tsareka a wurin nan"
Ya kalli wurin ya ce "Kar ki damu, ai na riga ma saba kuma ba wata wahala nake sha ba your excellency, kewarki nake tayi ne dai kawai, amma yaya zasu bar mu mu cigaba da zaman aurenmu?"
Ta rausayar da kai, ta ce "To gashi nan dai, ban san ya ake ciki ba, basu sake cewa komai ba. Ina son in roƙi Anty Nabila, ta ɗan ƙara lallaɓa mini su, amma nauyinta nake ji".
Ya ja hannunta suka zauna, ya ce "Ni zan roƙeta, ko sake durƙusawa zan yi a gabansu na basu haƙuri, ni dai su bar mini ke babyna, da ke jaririnmu mu rayu tare ko Rahamana?"
Ta jinjina masa kai, ta numfasa ta ce "To yaya yanayin abincin kana samu ka ci kuwa?"
"Eh mana, komai nawa normal kawai dai ina tsare ne, ki kwantar da hankalinki, ki rainar mana babynmu, ina fatan lokacin da zan fito yayi dai-dai da lokacin da zaki haihu, a karɓi haihuwar nan da ni. Na so ni zan kula da ke ayi rainon cikin nan da ni"
"To yaya zamu yi, kana naka Allah ya sa shi ne dai-dai, Allah ya fito mini da kai lafiya"
Abdul ya dafa kafaɗarta ya ce "Naki ne ni?" Ta jinjina masa kai cikin jin kunya tana murmushi.
"Naki ne ni rahama, ƙaddararmu ce ta zo mana a hagunce, amma mun gode masa Allah ya sassauta mana, ya sanya su barmu mu yi rayuwarmu ta aure"
Ta ce "Amin, bari ta zo ku gaisa, mu tafi, na san yanzu za su ce mu tafi"
Ya marairaice ya ce "Haba dai, kwata-kwata yaushe ku ka zo, ban gaji da ganinki ba, yayi maganar yana sumbatar goshinta.
Gandiroba ya ce "To sharokhan baban soyayya, lokaci yayi"
Abdul ya yi murmushi ya ce "Ai shi sharokhan na shi film ne, ni kuwa soyayya ce ta zahiri, dan haka ni na fi shi ma" yayi maganar yana dariya.
Nabila ce ta dawo, suka gaisa da Abdul, sai dai da ta ga farinciki a fuskokinsu, sai ta ji daɗi.
"Ina godiya sosai da sosai, rahama ta gaya mini yadda ki ke kula mini da ita da babyna, Allah ya saka miki da alkhairi"
Nabila ta ce "Amin, ai yi wa kai ne, rahama ƙanwata ce, ina jin daɗin ganinta cikin farinciki. Nayi mamakin yadda aka yi ka yi mata laifi kamar wannan kuma ka iya dasa soyayyarka a cikin zuciyarta. Meye sirrin ne?"
Yayi murmushi ya ce "Ita zaki tambaya ai"
Ramma ta harare shi ta ce "Ba wani sirri, ban da faɗa me ka iya?"
"Soyayya" ya bayar da amasa kai tsaye, da sai da ramma ta ji kamar ta nutse.
Suka yi dariya, ya sake cewa Nabila "Dan Allah na ga kamar ke kina tausaya mana, dan Allah ki rarrashi mama, ki ba ta haƙuri su bar mana aurenmu dan Allah"
Nabila ta sauke numfashi ta ce "To bani da ta cewa ne, idan na matsa yayanta hayayyaƙo mini zai yi, amma zan lallaɓa ta ɓangaren mama na cigaba da shawo kanta, in sha Allah komai zai wuce"
Ya ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi. Idan da wani abu ko kuɗi sun yi kaɗan, ayi mini magana"
Nabila ta ce "Kai wane irin kuɗi sun ƙare, wannan maƙudan kuɗi har haka, akwai kuɗi sosai in sha Allah ba wani abu"
Ya ce "To shikenan, muna godiya sosai barrister, babyna sai yaushe kuma?" Ramma ta galla masa harara, amma bai fasa ba, ya riƙe hijjabinta, ta waiwayo ta fizge ta na murguɗa masa baki.
Shafar sumar kansa ya yi, yana dariya, suka fice ita da Nabila.
Suna tafe a hanya, Nabila ta ce "Ramma har mamaki ku ke bani da ke da Abdul, dan Allah me Abdul ya yi miki, har ki ka fara sonsa, duk da girman laifin da ya aikata miki?"
Ramma ta jinjina kai ta ce "Na san da yawa ba za su fahimce ni ba, za a zata ko kwaɗayin wani abu ne na hannunsa, ko kuma wani abu nake yi wa, wanda ni har muka rabu ban san menene auren ba, kawai dai ina jin daɗin shiryuwar sa a dalilina. Kuma yana da wasu nagarta, wanda shi kansa bai san yana da ita ba. Da ya samu isashshiyar tarbiyya, ba zai yi wasu abubuwan ba.
Ya nuna tsantsar nadamarsa, gani nake idan na rabu da shi, zai iya koma wa ruwa, duk da da gaske, yake tuba a kan abubuwan da yake aikatawa. A matsayin ya aureni, ya tabattar mini da ya aure ni, babu irin zagi da rashin mutuncin da ban yi masa ba, amma ko a jikinsa, bai taɓa damunsa ba, kawai zai yi abin da ya ga dace yayi domin ya kyautata mini, ko na yaba ko na kushe bai dame shi ba.
Sannan daga halayensa masu kyau, yana da tausayi da taimako, mutum ne mai kyauta ta ban mamaki, kuma ya san aikinsa sosai da sosai, ina duba wannan abubuwan ne, amma ni kaina na san ta wani ɓangare kamar ban kyauta wa kaina da mama ba"
Nabila ta ce "Kar ki ce haka, wannan shi muke kira da jarrabawa, Allah ya jarabce ka ya ga yaya zaka yi? Bar ganin Abdul ba ya ji, wallahi sai ki ga saboda yawan kyautarsa da taimakonsa, ya sanya Allah ya din ga ji da shi, maybe shiyasa ya sanya tsautsayin nan a tsakaninku, domin ya rabauta ya tuba, yadda ya daina zina within shot period of time da ku ka zauna, ya cancanci a yaba masa daga ke har shi, ina fatan Allah ya tabattar da alkhairi a zamanku, ya sanya sanadin shiriyar sa kenan, idan Allah ya tabattar da zamanku, ki yi ƙoƙari ki rufa masa asiri, ki zauna da shi da zuciya ɗaya, ki yafe masa".
Ramma ta ce "In sha Allah Anty, na gode sosai da sosai, Allah ya nuna mana aurenku ke ma, da Yaya Al'amin"
Nabila ta kalleta ta ce "Da wa? Wannan yayan naki ai sai Jauhar ɗin, Allah ya bashi mace ta gari dai ba Nabila ba" Cikin mamaki Ramma ta ce "Amma Anty Nabila saboda me? Wallahi yana da kirki, yana da faɗa ne dai kawai"
"Wasu dalilai rahama, ki manta kawai, ba soyayya muke yi ba dama, kawai dai nima yayananne"
Jiki a sanyaye ta ce "A'a shi sonki yake yi"
"Yaya aka yi ki ka sani, shi ya gaya miki?"
"Ni a wa zai gaya mini, bai gaya mini ba, amma wasu lokutan irin kallon da Abdul yake yi mini, yake yi miki. Idan mutane sun kai goma a wuri, duk wanda zai yi magana ba zai damu ba, amma da kin fara magana, zai tattara nutsuwar sa da hankalinsa a kanki. Ko wani abin ki ke yi daban, yana kallonki ta ƙasan idonsa"
Kwashewa da dariya Nabila ta yi, ta ce "Kai rahama, haka ki ke saka masa ido kina kallonsa, ke duk a ina ki ka san hakan shi ne so?"
"Wurin doctor, amma Wallahi yana sonki"
"Daina rantsewa rahama, Viper mace ɗaya tak yake so a duniya, kuma yanzu ba ta raye, babu kuma macen da za ta iya maye gurbinta, dan haka ki manta kawai"
Rahama ta ce "Shikenan, tun da kin ce haka, amma ai kamarku ɗaya ita, kema yana sonki, ina ga dai ke ca ba kya sonsa kawai" Rahama tayi maganar cikin sanyin jiki sosai, dan tana son ta ga sun yi aure, dan sun dace sosai.
****
Abubuwa suka din ga damun Major, game da maganganun da Viper ya gaya masa, sai ya kasa haƙuri, ya kira Nasir ɗakinsa.
Ya dube shi sosai sannan ya ce "Nasir tambayarka zan yi, kuma ina so ka ji tsoron Allah, ka gaya mini gaskiya"
Ya ce "To Abba in sha Allah"
"Waye ya saka neman yaron nan da Nabila ta kare?"
Ya numfasa ya ce "Abba maitaimakin CP ne"
Abba ya ce "Da kuma wa?"
"Shikaɗai ne Abba"
"Gaskiya na ce ka gaya mini, waye ya baka kuɗi a matsayin cin hanci, ya ce lallai ka nemo shi? Kar ka yi mini ƙarya, ka san nima tsohon ma'aikaci ne"
"Ba kuɗi aka bani ba, senator ma'aruf Indabo ne"
"A kan me zai saka ka nemo masa wani ɗan daba, menene alaƙarsa da ɗan daba yana sanata?"
Nasir ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba Abba"
"Baka sani ba, kawai ka karɓa ka fara yi, Nasir idan baka ji tsoron Allah a kan aikinka ba, a tsiyace zaka shekara talatin kana wahala, ka gama aiki ka zama abin tausayi.
Na fara yadda wasu abubuwan kai ka ta'azzara su, kamar Nabila ta fika gaskiya".
"Abba mutumin fa ɗan daba ne, da yake zubar da jini, da aikata miyagun laifuka"
Major ya ce "To meyasa ba ku nemi kama shi a kan laifin da yake aikatawa ba, wani zai ja ka gefe ya kuma tunzuraka, ba tare da ka san abin da ya haɗa su ba, Nasir ka san aikinka kuwa? Kaga tashi ka je kawai jeka"
Ya buɗe baki zai yi magana major ya ce "Jeka ba zan sake magana da kai a yanzu ba, ina dai tunatar da kai muddin ka gauraya halal ɗinka da haram, babu in da zaka je wallahi. Kuma ka ji tsoron Allah, kar masu ƙarfi su din ga amfani da kai, a kan marasa ƙarfi, saboda kana saka wannan kakin lokaci ne" Sosai kunya ta kama Nasir, saboda yadda asirinsa yake nema ya tonu, na ya karɓi cin hanci, ya din ga matsawa Nabila da ƙoƙarin daƙileta a kan nata aikin.
***
Cikin dare hasken farin wata ya gauraye ko ina, Viper na tsaye a bakin window, yana shan sigari, hannunsa ɗaya yana kallon wayarsa, kwanaki shida kenan rabon da su yi waya ko ya sanyata a idonsa, babban mamakin da ta bashi, yadda ƙiri-ƙiri ya nuna mata yayi fushi, amma ko ta sake neman sa. Haka kurum ya ji ya ƙara fusata.
Ya harɗe ƙafarsa, yana ci gaba da shan sigarin, kawai sai watarana ta faɗo masa, Jauhar ta tsare shi a gida, ta hana shi fita ko ina, kuma ta bashi kara uku na sigari kawai.
Cikin dare ta yi bacci, ya tashi ya fita tsakar gida, ya shiga banɗakin tsakar gida, ya sha son ransa, ya daɗe hayaƙin ya ragu, sannan ya koma ɗakin ya kwanta.
Ashe tun da ya tashi ya fita, tana kallonsa, yana kwanciya ta tashi ta matso kusa da shi, ta saka hannu ta matsa bakinsa, ta sinsuna, dan ta tabbatar masa ta san me yayi, ba ta ce masa komai ba, ta juya ta kwanta.
Kamar wanda ta kama yana alfasha, yayi tsuru-tsuru, ya rasa me ma zai ce mata, kawai ya basar. Aka jima yana ƙoƙarin ya rungumeta, dan ya mantar da laifin da yayi, ta tashi ta bar masa gadon, ta yi alwala ta tayar da salla.
Asubar fari ba ta tashe shi ba, yaje masallaci ya dawo, a gida yayi azkar, ya din ga 'yan kame-kame, amma taƙi kula shi, har gari ya waye, sai da ya gaji ya ce "Ni fa guda uku na sha kawai ba da yawa ba"
Ta kalleshi ta ce "Me fa?"
"Sigarin" ta ɓata fuska ta ce "Hakan ya tabattar mini da zaka iya cin amanata wataran, ka yi abu ban sani ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ai uku ce kawai ba wata mai yawa ba, ki ke wani haɗe rai "
"To Allah ya baka haƙuri, na ga kamar na matsa maka" daga haka ta ci gaba da sabgarta.
Ranar ba ta hana shi fita ba, ya zauna bai fita ba, ko zata huce, har da yi mata aikin gida, amma ya kasa cewa ta yi haƙuri, ta tabbatar da ya sha jinin jikinsa, duk ya damu, amma ya kasa ba ta haƙuri. Duk sallolin ranar a jam'i ya yi su.
Kafin ya dawo daga sallar isha'i, ta sha kwalliya, yana dawowa ta rungunmi abin ta, kamar ba fushi tayi da shi ba, iya punishment ɗin nan da tayi masa, sai da ya ji kamar ya shekara a prison. Jauhar akwai iya dealing ta cikin ruwan sanyi, a lokacin babu wani abin da yake shakka irin yi mata laifi, saboda ta riga ta sanshi, ciki da bai ta san hanyoyin hukunta shi. Sakin guntuwar sigarin yayi, ya koma ɗaki ya kwanta ya cigaba da tunaninta.
Da haka wani nannauyan bacci ya ɗauke shi, sai dai kasancewar da ita ya kwanta a ransa, sai ya din ga mafarki da ita, mafarki mai cike da shauƙi da nishaɗi irin na ma'aurata.
"Master salla fa, zaka rasa sallar asuba." tayi maganar tana shafa sumar kansa.
Ƙanƙameta ya ƙara yi, yana tura kansa cikin wuyanta, da yake fitar da daddaɗan ƙamshin turaren da yake matuƙar son jin tashinsa daga jikinta.
"Viper wai ina zaka shiga a cikin pillown nan ne? Wai ko dai ka sha wani abu bamu lura ba, tun ɗazu fa muke tashinka, ka tashi mu yi salla dan Allah"
A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa ya ga hasken fitilar solar, ya haske ɗakin, sai a lokacin ya lura da ya ƙanƙame pillow.
Yayi miƙa tare da yin salati, ya kalli liti da yake tsaye a kan sa ya ce "Akwai gas ne?"
"A'a ɗan kaɗan ne sosai, sai an yi refiiling ma zamu iya dafa karin kumallo".
"Ɗora mini ruwa, ku yi sallarku zan yi wanka"
"Wai Viper meyake faruwa ne kwana biyun nan, ko ka fara dawowa bil adama ne? Ni ina cewa ka yi wa addini hidima meyake faruwa"
Ashar Viper ya yi masa, ba shiri liti ya ce "Allah ya baka haƙuri, ya ƙara lafiya"
Walid kuwa dariya yayi, ya ce "Allah ya ƙara, uban son jin ƙwaƙwaf".
Bayan sun karya Baba ya kira Viper a waya, ya ɗaga suka gaisa, ya ce "Aminullahi, dan Allah idan baka komai zuwa azahar ina son ganinka"
"To Baba in sha Allah zan zo, nan gidan zan zo na same ka?"
"Eh dan Allah"
"Zan zo in sha Allah"
"Yauwwa Allah ya yi maka albarka"
Viper ya amsa da Amin.
Ɓangaren Nabila ita ma kwanaki bakwan nan da suka yi, ba sa magana da Viper, abin ya dameta, ƙishirwar son ganinsa ta addabeta, ga ayyuka sun fara yi mata yawa, 'yat shaharar da tayi ta kwanan nan, ya sanya take ta samun cases ko ta ina.
Ban da masu nuna suna sonta, manyan mutane da suke sonta da aure.
Yau da mafarkin da tayi ta tashi a zuciyarta, mafarki tayi da mai kama da ita, wadda take da tabbacin jauhar ce.
Tana nuna mata inuwar mutumin da yake ɗaure cikin sarƙa a baya, yanzu babu sarƙar, sai dai daga yanayin inuwar tasa, kamar a galabaice yake, duk da babu sarƙar sai tangaɗi yake yi.
Tana murmushi ta cigaba da nuna mata shi, ta nufi in da take nuna mata, sai dai da ta waiwaya ba ta ganta ba, tana ƙoƙarin ƙarasawa in da mutumin yake, kawai ta farka daga baccin.
A hankali ta furta Viper, a gurguje ta shirya, tayi ta trying lambarsa, amma yaƙi ɗagawa, ta din ga jin ko me zai yi mata, yakamata ta kira shi, ta ji ya yake.
****
Ko da Viper ya je gidan su Jauhar, ya tarar da motoci a ƙofar gidan, bai damu da ko me ake yi ba, ya kira Baba ya ce masa gashi nan yana ƙofar gida.
Baba ya ce ya shiga kawai, ya ƙarasa ya shiga, babu wanda ya kula a mutanen gidan, sai hafsa da suka gaisa ya shiga ɗakin Baba.
Alhaji mu'azzam ya tarar, da Abbu, da kuma shi kansa Baban.
Gefe ya samu ya zauna a ƙasa ya gaishe su, sai dai da ya zo kan Abbu kamar an yi masa dole, haka ya gaishe shi.
"Ya gida ya ƙoƙarin Kuma?" Baba ya tambayi Viper.
"Lafiya ƙalau Alhamdilillah"
"Ina yan uwan naka?"
Viper ya ce "Su na gida, nikaɗai na zo".
Baba ya ce "babu laifi, Al'amin"
"Na'am Baba"
"Na san zaka yi mamakin kiranka da muka yi, babu tsammani da wuri haka.
To bakomai bane ya janyo, Nabila ta same ni, tayi mini wata magana ne, kuma nima naga hakan yakamata, duba da yadda abubuwa suka wakana.
Al'amin su iyaye, ba a fushi da su, kuma duk lalacewarsu iyaye ne, balle babu lalacewa a cikin iyaye, yakamata ka sasanta da mahaifinka, yanzu ina jauhar, ina mahaifiyarka, ina ɗan uwanka, ko da kuɗi ba zaka sake ganinsu a gidan duniya ba. Dan haka ka yi haƙuri, mun san mu masu laifi ne a wurinku, amma ku yi haƙuri a yafe ya wuce dan Allah ba dan halinmu ba".
Viper ya yi shiru, kamar mai nazari amma bai ce komai ba.
Abbu ya ce "Al'amin, nauyinka da nake ji, ya sanya na kasa nemanka gaba da gaba na nemi afuwarka, na san in dai dan halina ne, da abin da na aikata maka, ba zaka sake kallona a matsayin mahaifi ba, amma ba dan halina ba domin Allah.
A ƙaddarar rayuwarmu, na ɗauki darasi da dama, daga illar da mutum zai yi wa rayuwarsa, shi ne auren mace domin buƙatarsa kawai, ba tare da tunanin abin da gobe ka iya haifarwa ba.
Duk da ni a zatona dan gobenku na auri Rahila, amma ta ci amanata, kuma nima na san da laifina na rashin bibiya da tantance abin da take ɗora ni a kai, amma dan Allah ka yi haƙuri Al'amin, ka yafe mini ka dawo gida mu yi rayuwa a ɗan abin da yayi mini saura na rayuwata"
Alhaji mu'azzam ya ce "Viper, ka yi haƙuri dan Allah, duk wani abu da ya faru, ya wuce tun da bawan Allah nan shi yayi silar zuwanka duniya, kuma wani abin idan bai yi maka ba, wani yayi maka, yana cikin tashin hankali da damuwa sosai"
Viper ya numfasa ya ce "Ko a baya ni ban ƙi Abbu ba, ina matuƙar ƙawazucinsa da son kasancewa tare da shi, Abbu shi ne ya ƙi ni ya kore ni, amma tun da yanzu ya nemi na dawo shikenan, ya riga ya wuce. Amma ni a yanzu na girmi zaman gida, ba zan iya rabuwa da su Walid ba, sai na tabattar da rayuwarsu ta inganta suma, kamar yadda