Showing 270001 words to 273000 words out of 479911 words

Chapter 91 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6037

hakan?"

"Ka fi ni sanin wa nake magana a kai indabo, mukiyaye abun da zai zubar mana da mutunci a idon duniya a matsayin mu na 'yan siyasa kuma sirikai da ni da kai, ba zan lamunci wani mummunan abu ya same ta ba, mu cigaba da yaƙar juna ta ƙarƙashin ƙasa kar duniya ta ji wannan labarin ka kiyaye"
***
Madaki ne ya lallaɓo ya fito daga cikin ɗakin da yake, yana ta kiran wayar lakwari, amma taƙi shiga.

Walid ya gani a tsaye, yana kallonsa, ya tsaya cak, suna kallon kallo.

Walid ya yi murmushi ya ce "Duk ƙoƙarin da ka yi, ka gaza ɓoye mamakinka na ganina madaki, wannan da uban gayyar ka gani sai yaya kenan?".

"Meya kawo ka wurina?"

"Ahh ai ba abun faɗa bane ba, zuwa na yi na duba ya yanayin jikinka yake? Ni na hana mai zamani zuwa wurinka, da yazo nan da wani zancen ake yi ba wannan ba.
Zuwa yanzu na san kana mamakin ina lakwari, kuma ya aka yi muka san in da kake? Lakwari dai Macijin nan mai ban tsoro viper, ya saya shi a cikin raminsa, sannan indabo yanzu ba ta taka yake yi ba, dan haka yanzu zaɓi ya rage gareka kafin mai zamani ya waiwayo gareka, ko dai ka fita ka nemi madafa, waɗanda ka zalunta su ƙarasa ka, ko kuma yunwa da wannan ruɓaɓiyar ƙafar taka su ƙarasaka a wurin nan.
Ba zaka yi wa mai zamani wani amfani ba, saboda ya riga ya gama da kai, iya hakan nan da ya barka azaba ce mai zaman kanta, sannan ka sani, duk in da ka motsa ka tafi, yana sane da in da ka ke, ɗaukar fansa cikin ruwan sanyi" ya ƙarasa maganar yana ciro wata zabgegiyar wuƙa daga ƙugunsa.

Madaki ya zaro ido ya ce "Kar ka matso in da nake, kar ka zo in da nake" yayi maganar yana dakatar da walid, dan idan yayi kyakykyawan yinƙuri, ji yake kamar naman cinyarsa zai zaftare ya faɗi.

Babu tausayi, Walida ya kwarfe shi, ya danne shi a ƙasa, ya zana masa V a gadon bayansa da wuƙar hannunsa.

Ya ce "Ka ce labarin Viper ba zai cika ba, sai an ambaceka, to kai kuma har ka ƙarƙare rayuwarka kana dakonsa da alhakinsa a kanka da gadon bayanka. Ka shirya a kowane lokaci zamu iya yi wa waɗanda ka zalunta cunenka. Kuma ina yi maka Albishir da hukuma ta kama tabar wiwinka da ƙwayoyi, baka ga tsuntsu ba ka ga tarko madaki"

***
Nabila ce tsaye a falo, tana yi wa Nasir magiya.

"Dan Allah Dsp ka bani wayoyina, ina buƙatar cigaba da amfani da su, ga ayyukana a ciki, amma ka riƙe mini waya da system ka hana ni"

Ya kalle ta ya ce "Ba dai da wayoyin ki ke janyo wa kanki matsala ba, kin yi sallama da su, ba zaki sake riƙe waya a gidan nan ba, and beside gaba ɗaya ni ban yarda da ke ba, akwai abun da ki ke aikatawa wanda ki ke ɓoyewa".

"Dan Allah ni ka bani wayoyina, ya za ayi ka karɓe mini kayan aikina, yaya wai meyasa ka ke yi mini haka ne?"

"Ni ki ke ɗagawa murya haka?"

"To ka bani mana"

Abba ne ya shigo falo ya ce "Haba arfa, daga farfaɗowarki daga ciwon ki ke ta ɗaga murya har haka, sai numfashin ya sake samun matsala"

"Abba kayan aikina ya ɗauke mini, ka ce ya bani wayata da system ɗina"

Mama a ƙule ta ce "Dan ubanka ka bata kayanta, ƙannanka babu wanda ya isa yayi maka abun da take yi maka, da sun motsa sai hantara da zagi, amma kalli abun da take yi maka"

Abba ya ce "Tsaya, Nasir meyasa zaka kaeɓe mata kaya ka hanata?"

"Abba nayi seizing wayoyinta ne for a while, da su take amfani take janyo mana magana, haryanzu ba a tabattar da musababbin tashin wutar nan ba, amma zai iya yiwuwa saboda abubuwan da take yi ake neman sabauta rayuwarta".

Abba ya ce "Haka ne, kana da gaskiya, amma ka yi haƙuri ka bata, ke kuma ki kiyaye da abubuwan da zaki din ga aikatawa da wayar nan, idan ba haka da kaina zan ƙwace su aikin ma ki daina yin sa. Bi shi ya baki kayanki"

Nasir ya numfasa, yayi gaba ta bi bayansa, ya ɗaukko ya miƙa mata yana kallon idonta cike da tuhuma.

"Wuƙa garin tone-tone take tono wuƙar yanka kanta, yaya, ina martabaka da martaba zumuncin da yake tsakanina da kai. Bana son harkar aiki ta zama tangarɗa ga wannan alaƙa da na lissafa maka, bayani ne nake yi maka da manyan baƙaƙe a kan farar takarda, sai dai ba zaka gane nufina a yanzu ba, ko dai ka bari a haka, ko kuma lokaci ya zo da fassarar da ba ita kake buƙata ba, ina fatan idan lokacin ya zo, zaka tuna wannan bayanin nawa, kuma ba zaka ga abun a bazata ba".

Ayshercool
08081012143

65
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Cikin rashin fahimta, yake bin ta da ido, sai dai tamkar soko, har tayi maganar ta gama, bai iya tofa mata uffan ba, har tayi ta gama ta karɓi wayoyinta da system tayi tafiyarta ɗaki.

Ɗakin ta rufe, ta shiga duba call logs ɗin ta, amma kaf ba ta ga kiran Viper ba, wani irin takaci ne ya turnuƙe ta, wato duk siraɗin nan da ta tsallake da kyar, bai kirata ba, balle ya ji a wane hali take ciki.

'To idan kuma bai san abun da ya faru ba fa?' ta tambayi kanta. Ta basar ta ce bari ta jira zuwa gobe, taga ko zai kira wayar.

Ƙasan zuciyarta kuma ta din ga hamdala da Allah ya sa bai kira ɗin ba, dan da ya kira Nasir zai ɗaga ne, kuma ba abun da yayi masa zafi, zai iya gaya masa waye, idan ya tambayi waye.

***

"Naja wai ko ke ki ka saka aka yi wa yarinyar nan wani abu ne?"

"Wace yarinyar?"

"Barrister nan? Karofi ya kira ni yana yi mini kashedi, ina tsoron Allah ina tsoron shu'umancin mutumin nan"

Naja ta ce "Eh, ni na saka aka yi mata haka, dan so nayi ma ta mutu, na ga kai ka ƙi mayar da hankali ka yi abun da yakamata, ba zai yiwu ta tona mini asiri a banza ba, mutuncina ya zube a idon duniya ba. Ba a taɓa samun wanda ya yi yinƙurin kawo mini tangarɗa ba, ka ƙyale shi ka ke jan ƙafa a kansa ba, sai a kan wannan yarinyar"

A fusace Indabo ya ce "wai meyasa ki ke haka ne Naja? Duk iya ƙoƙarin da nake yi a kan lamarin nan? Na gaya miki zata iya zama tarkon da zan kama Viper, kuma ina amfani da ita wurin yi wa yayanta barazana yake yi wa umarnina biyyaya, lokaci ɗaya karofi ya bijiro, yake yi mini gargaɗi a kanta, wai sonta yake yi, wataƙila ma yi yake yi dan kawai ya muzanta ni. Amma gaba gaɗi babu shawara, kin je kin aikata abu, kin saka yana ta kiran wayata yana nema ya tozarta ni"

"Nifa ban yi danasanin abun da nayi ba, kuma zan cigaba da bibiyarta sai na ga bayanta, ban damu da abun da zai biyo baya ba muddin zan tsira, kar ka manta kai ka koyar da ni hakan" ta kaste wayar tana jan guntun tsaki.

***
A gurguje Abdul ya yi breakfast a wurin ramma, yayi mata sallama ya fice.
Bayan fitarsa ta daɗe tana kuka, kamar zuciyarta ta fashe haka take ji, saboda damuwa da tashin hankali, tun tana lissafin adadin kwanakinta a wurin Abdul, har ta karaya lissafi ya ƙwace mata, tana matuƙar son sanin halin da mahafiyarta ke ciki. Ta sha attempting ta saka wuƙa ta kashe Abdul, amma sai ta kasa, ita kanta ta sha yinƙurin kashe kanta, amma tuna makomarta sai ya sanya ta fasa.

Gashi yanzu sam ba ta iya bujirewa buƙatar sa, rayuwa suke yi tamkar ma'aurata, ta yi kuka tayi istigfari amma da ya zo ya kalallameta da zance, sai ta bayar da kai bori ya hau, wasu lokutan idan ta kalli hidimar da take yi masa, ta gyaran gida, kula da abincin sa, yin wani abu da zai saka shi farinciki sai ta yi sai ta ji haushin kanta ya isheta.

Abdul kuwa Asibitin su doctor AK ya wuce, ofishin sa ya je suka gaisa ya ce "Kai ne zaka yi morning kenan?"

Ak ya ce "Eh ni ne your excellency kai fa zuwa yanzu ya ci ace ka ajiye Lab coat, tun da ana ta ƙishin-ƙishin kai ne zaka zama lamba biyun garin nan, zaka koma field ɗin dadynka"

Abdul ya ce  "Nifa Ak ko lamba ɗayan ƙasar nan na zama, ba zan iya daina aikin likita ba, ina gudanar da office ina consultation" suka tafa tare da kwashewa da dariya tare.

Ak ya ce "Sannu doctor excellency, ina ƙanwar ka da kuka zo tare kuwa? Baka wani tsaya mun gaisa da ita ba, ko dan kar na ƙyasa ka bani ita, ai ban taɓa sanin kana da ƙanwa ba, na zata kai ne ƙarami"

Abdul ya tsuke fuska ya ce "A wane room patient ɗin take ne?"

"Ai ta uzzura sai da aka sallameta, amma Alhamdilillah jikinta yayi kyau sosai, sai dai ka yi mana ward round idan da abun da za a taimaka mana ayi mana" ya jinjina kai ya juya ya fice daga office ɗin.

***
Tun bayan da ɗan mama ya tabattarwa Viper an sallami Nabila daga asibiti, yake kallon wayarsa yake jiran kiran wayarta, amma shiru ba ta kira shi ba, har ya fara tunanin ko ƙarya ɗan maman ya yi masa da ya ce ta warke an sallame ta.

Shigowar Walid ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya ɗaga kai ya kalle shi, Walid ya ciro wuƙarsa ya zareta daga cikin gidanta, ya kalli Viper ya ce "Lakwari da gaske yake, na iske madaki, ƙafarsa ba ta takuwa, raunin da ka yi masa ya zama gyambo a ƙafarsa, ga shaida harafin sunanka na zana masa a gadon bayansa, yadda shi ma ba za a kammala na sa labarin ba, dole sai an ambaceka"

Viper yayi kamar zai yi murmushi ya ce "Mai laya"

Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, Allah ya kiyaye mini kai ɗan amanata"

Viper ya ce "Ina kewar wancan kwanakin, kwanakin da aka yi rashin ji da gaske, yanzu girma ya fara zuwa duk an daina wasu abubuwan"

Walid ya yi murmushi ya ce "Rashin jin ai duk ba na daɗi bane ɗan uwa, duk da kai ƴar madara ta fara saita mana kai, Allah ya karɓi kayarsa, amma duk da haka ba zan gushe ba ina jinjinawa Nabila, dan ita tayi abun da muka kasa, albarkacinta mun sake ganin walwala a tare da kai, duk da ba ta kai ta wancan lokacin ba"

"That angry bird, masifaffiya" ya furta yana kallon liti ya ji me zai ce.

Aikuwa kamar mai jiran ƙiris hya e "Ba wata tsiya da ta tsinana masa, sai shegen naci da taurin kan tsiya, mara kunya da ita sai kayan ƙaton kai kamar injin markaɗe da ƙwala-ƙwalan idanuwa kamar an soya aya, ai wallahi 'yar madara duniya ce, ga kunya da girmama mutane, wannan tsagerar kuwa, tana zazzarewa mutane ido, ni har mamakin mai zamani nake yi wallahi".

Walid ya ce "Ai ita ce daidai da ku, daga kai har mai zamanin, mu da muka kasa iya masa, ita ai gata nan yana saurarenta"

"Ba wani nan, ni haryanzu ba gama yarda nayi da ita ba, yar leƙen asiri ce"

Walid ya ce "To tayi leƙen asirin, ai ba asirinka ta leƙa ba ko?"

"Ware, ban da naga kuna ta tata, da sai na saka tsumagiya na jiƙa mata jikinta, sai na yi mata mazinacin dukan da ba zata iya tashi ba, na rama muguntar da yayanta yayi mini a station"

Viper yana gefe yana jin su, wasu lokutan faɗan Walid da liti nishaɗi yake saka shi, kamar sako da sako.

Nabila wuni tayi da waya a hannu, amma shiru babu kiran Viper, shi ma haka ne, wuni yayi yana kallon wayar ta sa yana sauraren kiran wayarta, amma ba ta kira ba.

***

Nasir ne zaune a ɗakinsa, yayi zurfi sosai a cikin tunani, yana ta tuna wasu abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin nan sosai yake jin yana zargin Arfa tana aikata wani rashin gaskiya, da take ɓoyewa, mussman da ya ji ta ambaci viper lokacin da ta farfaɗo, ba zai yiwu a ce magagi ne kawai ba, kuma a yan kwanakin nan tayi watsi da lamarin cewa zata taimaka masa a kan nemansa balle ya ce tsananin saka abun a ranta ne ya sanya ta farko da sunansa, amma haryanzu yana son sanin dalilin da ya sanya Indabo ya ce zai yi tarko da Nabila ya kama Viper, menene haɗinta da shi?.

Nabila tana zaune a kan gado, tana waya da Alhaji Wada, sai kashe murya take yi, wai ita haryanzu ba ta warke ba, ya biye mata sai sangarta take yi, kamar ba babban mutum ba yana lallaɓata, tun da ya ce zai kuma zuwa gida dubiya ta ce masa ai ta warke ba sai ya zo ba.

Sallamar baba magajiya ce ta sanya tayi masa sallama, ta ɗago ta kalleta da murmushi.

"Yauwwa yar gari, ai dama zuwa nayi na tashe ki, ki samu ki karya ki sanya wani abun a cikinki, ashe ma kin tashi "

"Eh hajjaju, ina kwana"

"Lafiya lau, ya ƙarfin jiki kuma?"

Nabila ta ce "Alhamdilillah da sauƙi"

"To Allah ya ƙara kiyayewa, ki cigaba da addu'a Allah ya ƙara tsarewa, dama mu ma addu'a cikin yin ta muke babu dare babu rana, Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ki yawata faɗarta babu adadi, da yardar Allah ba dai mutum ba sai dai Allah"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Kin faɗa kin nanata mini, na daɗe da haddacewa ai"

"Kya ci ƙaniyarki da kin daɗe da haddacewa, zamanin nan na yanzu waya ce miki ana zama haka? Kana da ido ba na ganin gari ba, Addu'a kake tuƙuru iya yinka, baka san waye maƙiyin fili da na ɓoye ba"

Sosai Nabila take dariya ta ce "Aikuwa maƙiyina yana ruwa, dan ni kaina ba wani cikakken saiti ne da ni ba in ji Abba"

"Ke ki yi addu'a kawai yar nan, tashi ki je ki samu abun da zaki ci" ta saukko daga kan gadon, ta fice falo tana miƙa, wayarta take kallo lokaci lokaci, duk kiran Viper take jira, amma shiru.

Sauda ta kalleta ta ce "'yar asara an fito"

Nabila ta ce "Wallahi kuwa, Allah ya nufa barka da safiya, bazawara uwar son banza ga gadonki ga na asara"

"Arfa, me ki ka ce?"

"Sauda kin sani sarai bana shiru idan aka gaya mini babu daɗi, ni yanzu a kan tsini nake, magana ɗaya mara daɗi ki ka yaɓa mini, sai na yi miki goma mai zafi, ba girmata ba Allah ya sa haifata ki ka yi" Sauda za ta yi magana, ta jiyo takun Abba yana saukkowa daga kan bene, dan haka ta haɗiye maganar ta, tana kallon Nabila.

***
Abbu ne zaune a gefen gadonsa, fuskarsa sanye da farin glashi, ya zubawa hoton hannunsa ido. Shi da Zahra'u ne, da sadik, shi kuma hannunsa riƙe da Al'amin, bai fi shekaru biyu ba a lokacin, sai dai fuskar nan ta sa tamau, babu alamar fara'a.
Murmushi Abbu yayi, tun Al'amin yana yaro baya son wargi, ba shi da faa'a, ya tuna yanzu a jikin hoton ba kowa sai Al'amin, shi ma ga yadda ya zama, rabon da ya saka shi a idonsa, tun fitowarsa daga prsion da ya zo masa nan, kusan shekara guda kenan.

"Wai meyafaru ne kamar kuka fa kake yi?"

Ya ɗaga kai ya kalli rahila ya ce "Kuka kuma?"

Ta leƙa ta kalli hannunsa, ta kwaɓe baki ta ce "Kai ta wani abu kamar ƙaramin yaro, ka ɗauki hoto ka saka a gaba kana kuka, haba kai kuwa?" Yayi mata shiru bai ce komai ba.

"Abbu, dan Allah magana nake so mu yi da kai"

"Ina jinki"

"Dan Allah ka yi haƙuri ka yafewa Abba, ya koma kasuwa, sai raragefe yake yi a gari da shi da Nazifi, ina tsoron kar su faɗa wani mummunan halin, rashin sana'a ga matashi babbar matsala ce".

Ya ƙare mata kallo ya ce "Rahila, nawa ɗan ma da ya kangare, sallama shi nayi, ba zai yiwu in cigaba da jan ɓarayi a jikina suna zalunta ta ba, su yi ta yawo babu sana'ar, ai uban su yana raye, ya nemi abun yi ya ba su"

"Ni kake kallon idona ka ke cewa yarana ɓarayi?"

"Na faɗa rahila, ba ɓarayin bane ba? Wane irin gata ne ban yi musu ba, ƙarshe rashin lafiya na kwanta aka rasa wanda zai zauna da ni a cikin su a asibiti, ƙarshe cewa ki ka yi kar na ga laifin su, ba hakkinsu bane ba, amma ni na riƙe su na ciyar da su, na kula da su, ni nawa hakkin ne? Yanzu nake ƙara danasanin biye miki, na wofantar da nawa ɗan, kuma ki tattatara su gaba ɗaya su bar mini gida, dan ba hakkina bane ba riƙon su"

Cikin takaici ta ce "Wallahi ba zan rabu da 'ya'yana ba, sai dai na tattara da ni da su mu bar maka gidan"

"Allah ya raka taki gona, ya tsare hanya"

Cikin fargaba ta kalleshi ta ce "Au babu ruwanka kenan in tafi baka damu ba?" Tashi yayi, ya ja tsaki ya mayar da takardun gabansa ya bar ɗakin.

***
Nabila ta kasa jurewa, hankalinta ya fara tashi, ko wani abun ne ya samu Viper, duk da bai fiye kiranta ba, sai da ƙwaƙwƙwaran dalili, amma shirun yayi yawa. Yau take shirye-shiryen komawa wurin aiki, Barrister Habib ya tabattar mata da an gyara office ɗin ta, an canza mata wani.

Har ta shirya ta tsaya, ta kira lambar Viper.

Yana kwance idanunsa a lumshe, yana ɗan kaɗa ƙafa, ya ji ringing ɗin wayarsa.

Ganin lambarta sai da ya yi ajiyar zuciya, amma ya zubawa wayar ido, sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga kuma yayi shiru.

"Hello Viper"

"Salamu alaikum" ya faɗa a nutse.

"Wa'alaikum Salam, kana lafiya?"

"Ƙalau"

Cikin marairaicewa ta ce "Wai baka san abun ya same ni bane ba? Kwana nawa baka ga kiran wayata ba baka neme ni ba, wrong connection na wearing aka yi a office ɗina, wuta ta shi, aka rufe ni ta waje fa"

"Na sani"

"Ka sani?"

Ya ce "Eh"

Cike da takaici ta ce "Kuma ka kasa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login