Showing 444001 words to 447000 words out of 479911 words

Chapter 149 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6188

bi, gefin magariba suka sauka.

Da ya ɗan matsa kusa da ita, sai ta maze ta matsa tana haɗe rai, dan haka ya rabu da ita.

Da daddare da kyar ta yadda ta ci abinci, shi ma ba da yawa ba.

Ya riƙo hannunta zata ƙwace, ya riƙe gam, ya ce "Haba hafsatuna, ni ne fa, ki yi haƙuri dan Allah, ki bani dama na gyara kuskuren da nayi miki a baya, Please" tayi shiru, ba ta ce masa komai ba, saboda ta kasa manta mummunan halin da ta faɗa a wancan karon a dalilin aurensa.

Da kyar ya lallaɓata, kamar budurwar da ba ta san komai ba, sai dai a wannan karon ita kanta ta san da banbanci, dan a wacan karon, banda tsabar kayan tsubbu, da abubuwan da ba ta san ko na menene ba, da su aka yi mata gyaran jikinta.

A wannan karon kuwa, ta san da banbanci, domin kuwa maman dr. Ta kankarota ta kankaro martabarta a idon mijinta, dan a wancan karon ko maganin sanyi ba ta yi amfani da shi ba, sai kayan tsubbu da abubuwan da ƙawaye suka din ga ba ta shawara a kai.

Shi kansa yadda ya yi appreciating ɗin ta a wannan karon, ya sha bamban da lokacin da tana budurwa.

(07069711327 ga masu buƙatar kayanta, su na iya tuntuɓarta kai tsaye, she's always available for you)

*****

Viper kuwa kimanin sati biyu kenan, tun da Allah ya sa aka ɗaura aurensa da Nabil, babu wanda ya nemi wani daga shi har ita, kuma hakan ya ɓatawa kowannensu rai.

Abba ya sanar mata, da babu ita babu yawo, idan ba wurin aiki ba, dole sai da izinin Al'amin.

Rashin kiranta da bai yi a waya ba, ya tabbatar mata da sam ba ya ƙaunarta, auren dolen ne dai kawai, shi ma ya nemi ya aureta ne kawai saboda mafitarsa.

Kasancewar hidimar bikinsa, tare da na Walid za a haɗa, ya sanya yayi delay na komawa aiki, domin sanin shirye-shirye da yakamata yayi.

Yana son ya tambayeta, abin da take buƙata na harkar biki, amma ya shareta.

Ta koma wurin aikinta, ana ta yi mata Allah ya sanya alkhairi, aka din ga tambayarta meyasa ba ta tafi hutu ba, ta ce ɗaurin aure aka yi, ba ayi biki ba.

Aka din ga bata gudunmuwar biki, ta in da ta zata, da in da ba ta ma zata ba.

Kawai tana zaune a office taga alert ɗin dubu ɗari biyar, da sunan Al'amin da komai.

Sai a lokacin ta kira wayarsa, ya ɗaga amma yayi shiru.

"Naga ka turo mini kuɗi"

"Ki fara sayen abin da ki ke buƙata na lefe, zan sake turo wasu, na san wannan ba za su isa ba".

"Ni bana so" ta faɗa a daƙile.

"Menene ba kya son?"

"Kuɗin, ni ka bani account number na dawo maka da su"

Wani malolon takaici ya ƙule masa zuciya ya ce "Bani da lokacinki, ki same ni a gidan su rahama, sai ki dawo mini da kuɗin" ya kashe wayarsa.

Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe ta fara harhaɗa kayanta.

Da ta isa gidan su ramam, Maman ramma ta ce "Amarya ke da kanki, ina ta cewa Aminun ya zo ya kai ni gidanku, amma haryanzu shiru"

Nabila ta ce "Dama baya nan? cewa fa yayi na zo na same shi a nan"

"A'a ya dai ce zai zo, amma bai ƙaraso ba tukuna" yanayin fuskar Nabila da ta gani babu fara'a, ya sanya ta din ga yi mata nasiha, tayi haƙuri ta rungumi mijinta su zauna lafiya kamar yadda yar uwatta tayi.

Ita kuwa Nabila gani take, ba zasu gane ba, ba su san waye Al'amin bane.

Ita a tata wautar, da gaske zuwa ta yi ta mayar masa da kuɗinsa, sam bai iya rarrashi ba, ba ta san tarko ya yi mata ba.

Awanta guda a gidan, ya zo, kuma yaƙi shigowa cikin falon, ya ce ta je ta same shi a sitting room ɗin harabar gidan.

Ta tashi ta ce "Mama ina zuwa" ta fita ta ƙarasa ɗakin.

Sai dai tana arba da shi, duk wannan fitsarar da take ji da ita, ta nemeta ta rasa, sai tsoro da fargaba da suka mamayeta. Lallai miji yafi gaban wasa.

Ya ɗago ya kalleta, doguwar riga ce a jikinta, sai mayafin rigar. Gaba ɗaya Nabila ba ta da wayo, ko kaɗan, abin da ba ta sani ba, ba wai dawo masa da kuɗi ne ya kawota ba, son ganinsa ne ya kawo ta, ba tare da ta yi lissafin hakan ba.

Ya kawar da kansa ya ci gaba da danna wayarsa.

"Ka bani account number ɗinka, na mayar maka da kuɗinka, ni bana buƙatar komai daga wurnka, ba zaka taɓa iya bani abin da nake so ba".

Ramma ta yi sallama da ƙaton faranti, shaƙe da kayan abinci, ta gaida Al'amin ya amsa, ta kalli Nabila da ke tsaye ta haɗe rai, ba ta ce komai ba ta fita.

Ta fara ƙosawa da tsayuwar da take yi, ya miƙa mata hannunsa, ba tare da ya Kalle ta ba ya ce, "Bani wayarki na saka miki account number ki dawo mini da kuɗina" babu musu ta ƙarasa ta miƙa wayar, ya yi amfani da hakan, ya janyota jikinsa.

Wata ƙaramar ƙara ta saki, jikinta ya hau tsuma, ta kalli fuskarsa, babu alamar wasa a tattare da shi, wani irin kallo yake yi mata da ba ta san a yaya zata fassara shi ba.

Ayshercool
08081012143

Sake ƙasa yayi da muryarsa, ya ce "Ina sake roƙonki, ki bani dama, kin yi mini kuskuren fahimta ne kawai, ban san yaya zan yi miki bayani ba, amma za ki ga komai a aikace"

Bakinta ta motsa za ta yi magana, amma a dole ta haɗiye maganar, biyo bayan dogon harshensa da ya saka a kan laɓɓanta.

Bayan su Walid sun fita, ya kalli liti ya ce "Ina jinka, me zaka ce mini?"

"Wai wannan farar yarinyar yar uwar Nabilan ce ne?"

"Eh"

"To kuma har muka fito ba ka yi mata magana ba, ka san dai ka fini faraa'a da kalar masu kirki"

"In yi mata magana in ce mata me? Ko dai sonta ka ke yi ne?"

"To wa ya san mini ma, amma ɗan yi mata magana, gata can sai waya take yi "

Walid ya ce "In yi mata magana in ce mata uban me? Kai ka yi mata mana, tun da sonta ka ke yi. Babanta dai tsohon soja ne, wallahi kayi masa shirme sanyawa zai yi kuratan nan, su yi maka dukan jaraba na gaya maka"

Liti ya ce "Ta Allah ba taka ba, kuma a yanzu zan nuna maka banbancina da kai" kawai ya nufi in da Walida take waya, tana ta surutu da wata ƙawarta mai kwaliya, tana son tayi booking na bikin Nabila.

Ta kammala ta juyo, ta ga Liti a tsaye.

"Sannu dai"

Ta ce "Yauwwa, ya gida ya shirye-shirye na ganku tare da wanda Arfa zata aura, ina kyautata zaton abokansa ne"

Ya girgiza mata kai ya ce "'yan uwansa ne mu"

Tayi murmushi ta ce "Masha Allah, Ubangiji Allah ya sa zamu gani"

"Amin, ashe tana da ƙanwa babba kamar ke, ai mu ita kawai muka sani"

"Ai muna da yawa ma, ba a fiye ganinmu bane, daga makaranta sai gida".

Liti ya ce "Masha Allah, ai haka ake so, ki ce tare zamu yi hada-hadar biki, to Allah ya sa a gama lafiya, sunana Abdallah"

Ta jinjina kai ta ce "To yaya Abdallah, sunana maryam ana ce mini Walida"

Walid kuwa satar kallonsu yake yi, yadda liti ya nutsu yake baza capacity a gaban budurwa, kai ba zaka ce shi ne yake wani iya shegen ba, sai gashi yana ta hira da shi da walida, abin da haryanzu Walid ba ya iya sakin jiki yayi sosai da Shahida.

Duk da Nabila ba ta saki jiki gaba ɗaya da Viper ba, amma ta ɗan ji sauƙin damuwar da take ciki, amma har a lokacin faragaba ba ta bar zuciyarta ba.

Sai da ta kwana biyu aka sallameta, ta ɗauki hutu a wurin aiki, ta ma daina fita gaba ɗaya, sosai Nabila ta zama so silent, dan ma Sumayya na tare da ita, tana ƙarfafa mata gwiwa.

Abbu suna ta shirye-shirye, suna zaune da shi da Viper da daddare, Shahida ma an gama gyara gidan da zata zauna, Abbu ya yi mata sababbin furnitures. A weekend za a kawo kayan lefe.

Viper ya dubi Abbu, yadda yake ta kashe kuɗi babu ƙaƙƙautawa, dan haka yake cewa auren yara uku zai yi.
Ga Viper, ga Walid ga kuma Shahida.

"Abbu muna ta godiya Allah ya saka da alkhairi"

Abbu ya ce "Da aka yi me?"

"Kuɗin da ka ke ta kashewa a kanmu"

"Amfanin neman kenan ai Al'amin, kuma a baya ai ban yi muku ba, Allah dai ya sanya alkhairi"

Viper ya amsa da Amin, sannan ya ce "Abbu wata alfarma nake son sake nema a wurinka dan Allah"

Abbu har so yake Viper ya nuna yana son yayi masa wani abu, hakan na sanya mishi nustuwa, ya ji cewa lallai ya yafe masa.

"Ka ga ramma yar uwata ce, kusan ita da mahaifiyarta sukaɗai suka rage a ɓangaren mahaifiyata, da nake kallo ina jin daɗi. To naga ba tsufa tayi ba, kuma zamanta haka is not safe, na ce dan Allah idan da dama, ban takura maka ba, dan Allah ka aureta.
Hakan zai fi sama mata nutsuwa, tun da shi aure garkuwa ne ga mace, duk tsufanta kuwa.

Abbu ya shafi gemunsa yayi murmushi ya ce "Yanzu dai ka bari na fara kawar da ku tukuna, ayi wannan maganar"

"Eh ai dama ba yanzu ba, na san da hidindimu a gabanka, idan Allah ya sa komai ya daidaita nake nufi"

"To ɗan gidan Abbu, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

Al'amin ya ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya ƙara arziki"

Saura sati ɗaya biki, Viper ya aiko su Walid wurin Nabila, suka yi sa'a Walida ta dawo daga aike.

Suka gaisa da su Walid, Liti ya ce "Walida, wurin sisternki muka zo an aiko mu, ko zaki yi magana da ita"

"Me zai hana" mintuna goma, sai ga Nabila ta fito, amma yanayin da suka ga Nabila, duk sai jikinsu ya sake yin sanyi, babu wannan karsashin nata, jikinta duk a sanyaye.

Haka suka gaisa sama-sama, suka ce Viper ne ya aiko su da kaya su kawo mata.
Ruwa da lemo ne carton hamsin, ga buhun fulawa har da kuɗi, wai ta ƙara a abin da za ta yi hidimar biki da shi.

Tun da yaje dubata a asibiti, bai sake nemanta ba, ita ma kuma ba ta neme shi ba, ta so kiransa a waya, amma ta fasa ta jira Abba ya dawo ta nuna masa.

Faɗa ya hau yi, a kan yadda yake ta ɗawainiya da ɗorawa kansa nauyi, ya kira Abbu yana mita Abbu ya ce "Haba ranka ya daɗe, ni ban ma san an yi ba, kuma abu ne da yakamata ya yi, dan haka ai babu laifi, amma ayi haƙuri idan mun yi laifi"

Major ya ce "Ai an riga an zama ɗaya, a din ga sauƙaƙawa juna, wallahi mun tanadi komai na shirin bikin nan, bayan uban kuɗi da ya din ga turo mata na haɗa kayan lefe"

Abbu ya ce "Kar ka damu fa, auren fari sadaka aka bashi ai, sisinsa ba ta yi ciwon kai ba, wannan kuwa ya daki jikinsa yayi, sai ya fi riƙewa da kyau"

Major ya ce "Aishikenan, Ubangiji Allah ya sanya musu albarka baki ɗaya"

Saura sati biyu biki, Abbu ya kai Major da Baba gidan Nabila, flat ne mai kyawun gaske, a cikin unguwar jambulon da ke Kano.

Tun duniya na kwance, lokacin da baban su Viper ya fara tashen kuɗi, mahaifiyar su ta sanya ya saya wa Al'amin da Sadik gidaje, ta ce saboda maza ne, idan ya sai musu ya taimake su.

A haka kuma da ɗan abin da take samu a hannunsa, da yan sana'oin ta, ta din ga sayen filaye tana ɗan ajiyewa.
Aka zo ita ta rasu, Sadik ma ya rasu, dan haka Al'amin bayan gidan da yake da shi, da babu yadda ba ayi da Abbu ya sayar ba yaƙi, Rahila ma tayi ƙulafucin gidan ta gaji.

Miliyoyi aka din ga ambatawa gidan ya sayar yaƙi, yanzu gashi ya yi rana, aƙalla Viper yana da gidaje huɗu, da manyan filaye biyu, dan ma ya bi gonar da yake da ita a ƙauye, ya saka an sayar tun Jauhar na raye.

A auren nan Viper ba ƙaramin jin jiki yayi ba, duk da Abbu yana taimaka masa, amma kuɗaɗen hannunsa duk sun ƙare, a haka sai da aka sayar da filinsa ɗaya, saboda shi yake taimakawa Walid ma.

A duk lokacin da ya tuna a yadda ya auri Jauhar, da a al'adance zai iya cewa auren sadaka, sai ya ji tausayinta, ko da wasa ba ta taɓa nuna masa, ta ji zafin irin auren da aka yi mata da shi ba.

Liti duk da yana supporting ɗin Walid shi ma a kan shirin bikinsa, gefe guda yana ta karɓar kuɗi a hannun babansa, ya ƙara ƙawata wurin shayinsu aka mayar da shi joint.

Kasancewar Viper ya kwana biyu bai je wurin ba, ranar da Liti ya addabe shi ya je, sai da ya zubar da ƙwalla.

JAUHAR MEMORIAL JOINT. Haka aka rubuta a wurin, sannan ga kan famfo ɗaya da aka janyo, liti ya ce "Ga sadaƙatul jariya, mun yi wa ƙanwarmu da ni da Walid, alkhairin Allah ya isketa har cikin kabarinta, ƙoƙarin inganta rayuwarka da tayi, ba kai kaɗai ta yi wa ba, har da mu".

Cikin wurin duk an rubuta, dan Allah ku karanta wa marigayiyya Jauhar ƙulhuwallahu ƙafa uku, Allah ya jiƙanta da sauran musulmi baki ɗaya.

Idan Viper ya ce yana da kalamai, ko wani abu da zai yi, domin nu na godiyarsa ga bayin Allan nan da suka kasance da shi, a halin tsanani da na jin daɗi, to ya yi ƙarya.

Su Abba sun yaba gidan Nabila ba kaɗan ba, manyan ɗakunta uku, da falo biyu, ga komai a wadace dai-dai misali.

Duk da ba a rasa 'yan tsegumi ba, da aka je jere, da suka din ga gulmar, a iyayi irin na Nabila, da yadda ta din ga dating manyan mutane masu kuɗi, ba su yi zaton zata ƙare a wannan gidan ba, duk da shi kansa yadda ake cewa ɗan daba ne, sun zata mara galihu ne da abin yi, dan sun raina kansu da suka ga gidan da ɗan daba zai saka amarya a ciki.

Nabila dai ta kama wuridin ya haiyyu ya ƙaiyyum bi rahmatika astagis, aslih lii sha'ani kullahu, wala takilni ila nafsi, ɗarfatu ainin.
Domin samun mafita a kan maganar aurenta da Viper.

*****

Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, aka fara gudanar da biki, shi kansa Viper yayi rama saboda rashin hutu. Dinner da kamu, duk amare ne suka je ba angwaye, Nabila ta yi kyau sosai, farar fatarta tayi kyau da kaya da kuma kwalliyar da aka yi mata, haka ma Shahida ta sha kyau.

Sumayya ma sai kai wa da komowa take yi, tayi kyau sosai da sosai.

A hada-hadar kai komon biki, liti suka ƙara sabawa da walida, har da karɓar lambarta.
Walid ya ce "Zaka gane kurenka, ka gama yi wa Nabila rashin mutunci, ka zo kana bin ƙanwarta, Allah ya kawo mata lokacin ramawa"

"Kai dai ɗan baƙin ciki ne, saboda Allah ya kawo maka lokacin aure, duk sai ku tafi ku bar ni, to baka isa ba".

An ci an sha, an yi biki lafiya aka kammala lafiya, da yamma aka fara shirin kai amare.

Nabila na ta kuka, ba kuma wai dan zata bar gidan nan ba, kawai ji take auren Vipern tsoro yake bata ba na wasa ba.

Abbu ya yi wa Viper da walid nasiha sosai da sosai, haka Shahida ya gargaɗeta a kan kar ta biye wa mahaifiyarta, ta ɗorata a kan keken ɓera, ta kashe mata aure.

Ranar da aka ɗaura auren su Walid, a ranar Viper ya yi walimarsa, tare da abokansa, wanda dama su Walid ne, sai kuma sojoji.
Amma ba a manta baya a harkar, dan hatta tsofaffin yaransa 'yan cau-cau, da marasa ji sai da suka halatta, sai dai a wannan karon, ba rashin hankali aka yi ba, kamar yadda na auren jauhar ya gudana ba, kowa taitayinsa ya shiga, mussaman da sojoji suka cika wurin.

Nabila ta rirriƙe sumayya tana kuka, ita ta zauna da Nabila, har bayan isha'i, kowa ya watse, ta kira wands zata aura, Faruk wanda ɗan uwa ne ga Alhaji mu'azzam.

Amma fafur Nabila ta hanata tafiya, sai da Viper ya shigo.

Kamar yadda ya saba komai nasa daban, shikaɗai ya shiga gidan, sai da Sumayya ta tafi ya rufe gidan, ya tsaya yana ƙarewa gidan kallo, ko ina hasken fitilar solar.

Ya tuna lokacin da ya je wa jauhar, butsu butsu, Walid ne ma ya takura masa, ya haɗo shi da kayan dauɗarsa ya rako shi. Ɗan guntun murmushi ya yi, ya shiga ya iske Nabila a bedroom, ta ƙunshe kanta da mayafi.

Ya ce "Ki taso ki yi alwala mu yi salla" a hankali ta motsa, ta saukko daga kan gadon, idanunta duk a kumbure, rabon da ya ganta tun a asibiti, ko ta waya ba su sake magana ba.

Ta je ta fara yin alwala, shi ma yayi ya fito, amma ya ga ta ja ta tsaya a gefe.

Sai da ya raɓata ya tayar da sallar sannan ta bi bayansa, bayan sun idar yayi addu'a gwargwadon abin da ya iya.

Ya janyo mata ledojin da ya shigo da su, ya ce "Bismillah ga abinci, me zaki ci a nan?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba komai"

"Saboda me?" "Na ci abinci a gida"

Kawai ya ce "Ok"

Da ya motsa sai ta zabura, gaba ɗaya ta takura kanta, ta hana kanta sukuni.

Ya tashi ya bar mata ɗakin, sai bayan awa guda, sannan ya koma, ta kwanta a ƙasa ta lulluɓe jikinta da lafayarta, sai dai tana jin motsinsa ta sake zabura ta tashi zaune.

"Ki je ki kwanta, tun da bacci ki ke ji" sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta tashi taje ta kwanta.

Ya ɗaukko sabon bargonta ya ƙara mata, tana kallonshi yana rage kayan jikinsa, zuciyarta na tsananta bugawa tana rarraba ido, yana juyowa suka haɗa ido, tayi wuf ta shige cikin bargo.

Yana kashe fitila, ta tashi zaune, yana kallonta, ya zo ya samu wuri a farkon gadon ya kwanta, amma taƙi kwanciya.

A ransa ya jinjina hali irin na Nabila, ya san dai ba ta isa hana shi abin da yayi niyya ba, amma tabbas zai sha fama da taurin kai. A yanayi irin na Nabila, da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login