Showing 252001 words to 255000 words out of 479911 words
dai ba ma yi maka gwaninta ko?"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ka san wani abu?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
"Ni fa na gaya wa Sumayya, na san tana bibiyata, duk da jiya ta kawo mini wasu mata, da suka yi mini complain a kan Bunkure, amma mun yi faɗa da sumayya.
Sannan an sake ajiye mini file a office ɗina, na ƙarashen labarin Naja'atu Bunkure.
"Ku ka yi faɗa ba ƙawarki ba ce ba?"
"Eh, amma meyasa zata ci amanata?"
Ya kalleta ya ce "Ya aka yi ki ka tabattar da cin amana ne ya sanya take bibiyarki?"
"Saboda kai ka gaya mini"
"Ban ce tana bibiyarki dan ta ci amanarki ba, kuma baki da tabbacin da gaske nake ko akasin haka"
Ta gyara zamanta ta ce "A labarinka da na ji, baka ƙarya dan ka ci amana, kuma bana tunanin zaka fara a kaina"
Ya jinjina kai ya ce "Bani wayarki" ta ɗaukko wayarta ta bashi, ya nutsu sosai yana ta daddanawa.
"Yayanki ma na ƙoƙarin yi wa layinki kutse, sai dai na rufe damar hakan. Yana zarginki a kan da shi kansa bai san menene ba. Yayanki ya ga Indabo yana yi masa aiki a kaina, yana kuma gargaɗin sa a kan abun da ki ke yi a kan bunkure, na san zuwa yanzu ya matsa miki lamba a kan ki rabu da ita"
Ta waro ido ta ce "Ya aka yi ka sani? Anya yayan kuwa?"
Ina bibiyar kiran wayarsa ta hanyar amfani da wayarki, hakazalika duk wasu maganganu da yake yi, recording ɗin suna kan computer ki. Wayarsa da Indabo kawai nake bibiya, ba ruwana da sauran harkokin sa.
Ta ce "Subhanallah, amma yaya ya bani kunya, shiyasa yake ta uzzura mini? Amma nima ka yi hacking ɗin wayata kenan? Kana jin duk wayar da nake yi da samarina?"
Tsaki yayi, ya jefa mata wayarta. Ya ce "Ina magana serious kina yi mini shirme?"
Ta ce "To ai kar ka ji ina kalamai ne, ka zo kana kishi, nifa duk ba son su nake yi ba, kai kawai nake so" tayi maganar da niyyar sake kunna shi.
Ƙoƙarin tashi yayi, tana dariya ta ce "Yi haƙuri, dan Allah ka duba mini ƙarashen labarin nan, na Najar bunkure ka gaya mini menene opinion ɗinka".
"Mu yi aiki kawai, ki daina yi mini wannan shirmen"
"Ba shirme bane ba fa, ni da gaske nake" ya karɓi file ɗin, ya cigaba da duddubawa.
Ya ɗaga kai ya kalli walid ya ce "Mai laya"
"Mai zamani".
"Yakamata ku je ku daba mini mahaifiyar Nura, tun da na fito yakamata ace na je na ganta, amma ba zan iya ba, ban san wace irin karɓa zata yi mini ba, maybe ita ma irin kallon da ake yi mini, take min"
Liti ya ce "Haba maza, babu lallai gaskiya"
Nabila ta ce "Ina kakarka to? Wadda oga walid ya bani labarinta?"
"Ta mutu ina prison"
Walid ya ce "Har tare da ita mun je prison, sau biyu ba a bari mu ganshi. Baiwar Allah nan tashin hankali da damuwa ne, suka haɗu suka kasheta"
Jiki a sanyaye ta ce "Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, ya sanya sun huta baki ɗaya, da yar madara, da Hajiya, da mamana da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya" suka amsa da Amin.
Walid ya ce "Mamanki ta rasu?"
Ta jinjina masa kai ta ce "Eh, ban ma santa ba, sai dai hotunanta na gani a wurin Abba"
"Allah sarki, Allah ya jiƙanta"
Liti ya ce "Shiyasa ba kya ji, ina tausayawa mariƙanki, sun sha wahala da ma ba kowane maraya ne yake ji ba"
"Oganku shi ne na farko a marasa jin, in dai maraya baya ji" ta yi maganar tana satar kallon Viper.
"Amma Viper, ka sake komawa wurin Abbanka kuwa? Na san zuwa yanzu ya huce, zai kuma fuskance ka, ka yi masa bayani, shi fa tsakanin ɗa da iyaye sai Allah" yayi mata shiru.
"Ni ka bani dama naje na same shi, na san zai fahimce ni"
Ya ajiye file ɗin ya ce"Kar ki kuskura ki fara wannan gangancin, kar ki kusanci unguwarmu, ko ki ce zaki je unguwar da gidana yake, idan ki ka yi ɗaya daga ciki, zan yanke aikin da zan yi da ke, kuma hakan zai iya sanya wa na kashe ki"
"Au ba zaka daina zancen kisan kan nan ba ko? To maza nima ka kashe ni, na ga wanda zai din ga rarrashinka.
Ta tashi ta ɗauki jakarta, ta tattara kwanukanta, ta ce "Bari na tafi, kar nayi yamma da yawa, zamu yi magana" tashi ya yi ya ce "Muje"
"Rakani zaka yi? To muje" suka fita kamar gaske. "Ina sake gargaɗinki, kar ki sake ki ce zaki nemi gidanmu ki je, ko gidan su 'yar madara, zaki ɓata mini aiki, duk da na samu labarin sun bar unguwar, idan kuma ki ka ɓata mini aiki, ba na jin zan iya yafe miki"
Ta ce "Subhanallah, in sha Allah ba zan je ba, amma yakamata ku daidaita da mahaifinka.
"Ba wannan ne a gabana ba"
"To menene a gabanka? Iyaye fa ba a fushi da su"
"Ki rabu da ni"
Ta ce "To, Allah ya baka haƙuri"
"Ki cigaba da kula sosai da sosai a kan zuwanki wurin nan, za a iya biyoki har nan, bana tunanin iya wayarki ake bibiya"
Ta kalleshi ta ce "Akwai wata mota da na lura da tana bina kwanakin baya, amma ba wannan ba. Na faa tunanin anya a cikin yaranka babu wanda suke sanar da wasu abubuwan da muke yi? Ko kuma wani yana binka ko kuma ni da ake bi, an san ina zuwa wurinka ba? Suwaye suka ɗaukeka kwana biyu? Sannan ya aka yi aka san kana asibitin nan, har aka biya maka kuɗin asibiti"
Ya sauke numfashi ya ce "Kar ki shagala da tunani da yawa, ki manta da abubuwa masu muhimmanci, ki je zamu yi magana"
Ta kalleshi ta ce "To, amma dan Allah ka ɗaga wayata da daddare in ji muryarka, ka ji Oga" wani irin mugun kallo yayi mata, ya nausa ya bi wata hanyar, ita kuma tayi gaba tana murmushi.
***
Ramma na zaune a kusa da Abdul, yana kallon ball, ita kuma ta kunna radio a wayarta, tana ji.
Ya kalleta ya ce "Dan Allah ki rage radion nan"
"Ina ruwanka da ni ne, ka yi kallonka mana"
"Kin cika mini kunne da radio ne"
"To ita ball ɗin magana ake yi? Ba ihu bane ba kawai?"
Abdul ya ƙure volume, ita ma ta ƙure volume, ta kara masa radion a kunnensa.
Yayi mata shiru ya ce "Kya yi kya gama"
Sumayya ce tare da murtala a studio, suka gabatar da program, kasancewar an samu akasi masu gabatar da program a dai-dai lokacin ba su samu zuwa ba.
Program suke yi akan abubuwan da suka shafi rayuwa, suna yi suna karanto saƙonnin masu sauraro.
Murtala ya ce "T ladan, ga wata tambaya daga masu sauraro, wai an ce a tambayeki, wace irin alaƙa ce tsakanin ki da Nabila Yusuf maitama, da kullum ba kya taɓa aiki ki tashi, baki ambace ta ba, baki tsokane ta, ko saka waƙoƙi domin jin daɗinta ba?"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Barrister Nabila, voice of voiceless a lady of her words, a hardworking, strong minded young barrister, she's exceptional, lovely and simple sister of me" tayi maganar tana jin zafin saɓanin da suka samu a tsakanin su.
Murtala ya ce "Tirƙashi, duk wannan kirarin itakaɗai?"
"Sosai, Nabila mutum ce ta mussaman a rayuwata, ina yi mata son fisabilillahi"
"To yanzu da saurayinki, da Nabila wa ki ka fi so?" Ta kwashe da dariya ta ce "Uncle murtala wannan ai haɗa faɗa ne"
"To yanzu kafin muyi sallama da masu sauraro, gaya mana kalma ɗaya tak a kan Barrister Nabila"
"Mai gaskiya ce, ina yi mata fatan nasara, ya ɗaukaka mini ita, ya kuma kare mini ita a duk in da take, ya dauwwamar da ita a kan gaskiya"
Murtala ya ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, Allah ya bar wannan ƙauna, kafin mu ƙarƙare shirin, mun karɓi takardar wata baiwar Allah da za a yi wa ɗanta aikin ƙaba, amma ba ta da hali, tana neman taimakon bayin Allah. Akwai kuma wadda take neman kuɗin sayawa mahaifiyarsu magani mai fama da hawan jini, muna fatan zaku taimaka"
Nabila kuwa tana driving, ba ma'abociyar jin radiyo bace ba, amma saboda sumayya take sauraren radio. Hawaye ta din ga sharewa, tare da tuna abun da ta yi wa sumayyan.
Ramma kuwa cewa ta yi "Allah ya ƙarfafi wannan baiwar Allah, ya tabattar da ita a gaskiya, kar ya kauce hanya, kamar waccan munafukar mara imani" Abdul yana jin ta, yayi mata shiru. Ganin bai kulata ba ya sa ta ce "Ba zaka ce amin ba"
"Ni fa ball nake kallo"
"Allah ya sa a cinye club ɗin da kake yi"
"Ba amin ba" ya ɗauki wayarsa, ya kira admin ɗin asibitin sa, ya ce a je gidan radion su sumayya, a kai yaron nan ayi masa aiki kyauta, mai hawan jinin ma a kai ta a bata magani.
Ramma ta ce "Kalle shi kamar na Allah" duk yaƙi kulata, ta tashi ta nufi ɗaki, ta saka hannu ta kashe tv ta riga ɗaki da gudu, kawai yayi dariya.
***
Kwanaki biyu, Nabila ta daina samun Viper a waya, sai dai da ta kira walid, ya tabattar mata da lafiyarsa ƙalau.
Nabila ta fara gazgata zancen Viper, duba da yadda Nasir yake kashe-kashen kuɗi, ya canza mota ya cigaba da gininsa, kuma salarynsa gaba ɗaya ba wani shahararre bane ba.
Nabila tana kwance tana waya da Alhaji Wada M karofi, yadda yake lallaɓata yake yi mata magana, har kunya yake bata.
Fuskar viper kawai take hangowa, yanzu da shi take yi wa kalaman nan, da tuni ya haɗe rai yana hararta. Bayan sun yi sallama ta ajiye wayar, Walid ta shigo ɗakin ta ce "Arfa, isa ne ya shigo yanzu, wai ana sallama da ke a waje"
"Kai, wane ɗan baƙin cikin ne zai hana mini jin daɗi a magaribar nan? Ni fa ban yi da kowa za a zo wurina ba"
Walida ta ce "Ace ya tafi kenan?"
"A'a gani nan zuwa"
Ta yafa mayafin abayarta, ta fita, a ƙa'idar Abba a cikin gida suke zance, ganin bai shigo ba, ya sanya ta gane lallai wanda ya zo ɗin baƙo ne.
Ta zira kai ta leƙa ƙofar gida, dan duba waye.
A opposite ɗin gidan ta ga Viper a tsaye yana kallon ta.
Ayshercool
08081012143
61
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Gaban Nabila ya faɗi, cikin matsanancin tsoro da tashin hankali, ta din ga waige-waige tare da dubawa, idan akwai wanda ya ganshi, amma layin babu kowa, sai manyan security light da suka haska ko ina.
Ta sake kallonshi, ta tabattar shi ne, ta ƙarasa in da yake da sauri ta ce "Viper, waye ya nuna maka gidanmu? Yau kuma ba office ba har gida?"
"Akwai matsala ne?" Yayi maganar yana ƙara ƙureta da ido.
"Au tambayata ma ka ke yi? Amma dai ka san yayana nemanka yake yi ko meyasa zaka zo gidanmu, lallai sai ka tona mini asiri ne? Waye ma ya nuna maka gidanmu?"
"Shi yayan naki, ki shiga ki gaya masa gani ya zo ya kamani mana, shikenan ki daina wahalar da kanki da fargaba mana. Kina tunanin zan yi aiki da wadda ban san wacece ba?"
Ta ce "Yanzu dai duk ba wannan ba, dan Allah mu je daga wancan lungun, mu yi magana"
Ya sha kunu ya ce "Ban gane muje lungu ba"
"Eh mana, mu je can mu yi magana kar a ganka"
"A'a ni ba zan shiga lungu a daren nan ba"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, to ai ba wani abun na ce ayi a lungun ba, magana kawai zamu yi kar a ganka nake tsoro"
"Kuma sai ki ce in shiga lungu"
"Na shiga uku, sai ka ce wata 'yar iska, kar ka yi mini wata mummunar fassara mana"
Viper ya ce "Ke da duk baki yi wannan tunanin ba, ki ka amince da aiki tare da ni, ki ke iƙrarin zaki taimake ni? Ki tsaya ki saurare ni" ya yi maganar fuskarsa ɗauke da matsananciyar damuwa. Duk da bai kasance mai fara'a ba, amma yau akwai damuwa sosai a tare da shi.
"Amma dan Allah waye ya nuna maka gidanmu"
"Ba wannan ne ya kawo ni ba"
"To Allah ya baka haƙuri sir, me yake tafe da kai?"
"Nura" ya faɗa a taƙaice.
"Waye hakan?"
"Ƙanina Nura guduma, bayan mutuwarsa ina duba mahaifiyarsa, sai dai bayan an tsare ni ban samu damar yin haka ba, amma su Walid sukan je amma ba ko yaushe ba, bayan fitowa ta kuma, bani da cikakkiyar nutsuwa, kuma ina matuƙar jin nauyinta ban je ba, ban kuma saka su walid sun je ba"
Nabila ta nutsu tana sauraronsa, duk a tsorace take, kar wani ya ganshi, duk da akwai facemask a fuskar sa.
"Mijin da ta aura bayan baban Nura ya rasu, shekaru biyu da suka wuce, tana ta fama da rayuwa, ga yaranta guda biyu, a taƙaice dai jiya da su Walid suka dawo daga garin, sun tabbatar mini da 'yar ta aka yi wa fyaɗe ita kuma ba a san in da take ba" Nabila ta zabura ta ce "Kuma?"
"Yarinyar da ki ke bincike a kan case ɗin ta, Naja bunkure ta shiga case ɗin"
Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kalmar nan ko daɗin ji ba ta da shi, dama ita ce? To ba su gano in da maman take ba?"
"Ina gaya miki kina tambayata, na baki nan da sati biyu rak, tun da kin ce wanda ake zargi ba shi bane ba, ki fito da mai laifin, ko kuma ni na fito da shi ta ƙarfin tsiya".
Cikin rashin fahimta ta ce "In fito da mai laifi kuma ta ina? Nima bulayin nemansa nake ai saboda in wanke client ɗina"
"Sai fa kin nemo shi, ko kuma ki tabattar an yankewa mutumin nan hukunci dai-dai da abun da ya aikata"
"Amma dai ka san ni lawyer ce ba 'yar sanda ba ko? Jami'an tsaro sune za su yi maka wannan aikin, ni kuma na tsaya na tabattar kotu ta yi adalci"
Ya tsare ta da idanunsa ya nuna ta da yatsansa ya ce "Ke zaki yi, ba wanda zai yi sai ke, ki nemo ainihin mai laifin, ko kuma ki bari a hukunta wannan mutumin"
"But he's not guilty, he's innocent, ka bari na bi komai a hankali"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "No matter what it takes, ki binciko ainihin mai laifin nan, an cutar da matar nan fiye da yadda ki ke tunani"
Nan ya warware mata ɓangaren labarin sa na Nura, da ba ta sani ba.
Rawa ƙafafuwanta suka fara yi, jikinta yayi wani irin sanyi, ta kasa magana.
"Ki din ga yi mini uzuri wasu lokutan, ni mutum ne mai tarin laifuka ga mutane, bana son in ga wani a cikin damuwa, ina tsoron ace matar nan guduwa tayi saboda baƙin ciki, ba haka ba ma, voice message ɗin da ki ka kunna mini, sai a yanzu na sake tabattar da muryarta ce, ta tabattar da har gida wanda yayi rape ɗin yaje ya ɗauke 'yar, dan haka ramma tana tare da wanda ya yi mata fyaɗe, kuma Naja'atu Bunkure ta sanshi, ba dan ta tsayawa yarinyar ta shiga case ɗin ba, dan ta bawa mai laifin kariya ne".
"Yanzu ka yadda wanda nake karewa ba shi da laifi?"
"Na sani, amma dole ki yi wani abu, a nemo yarinyar nan da mahaifiyarta"
Nabila zata yi magana, aka haske su da fitilar mota, ta saka hannu ta kare saboda hasken fitilar, shi kuwa yayi ƙuri yana kallon fitilar.
Viper ya ce "Ko dai ki gaya masa ya kashe fitilar nan, ko na haɗa idonsa da na motar na ɗauke musu wuta gaba ɗaya"
Fitowa yayi daga motar ya ƙaraso in da suke, ya kalli Viper, sai dai a wannan karon ma ya ji wannan faɗuwar gaban. Kallo ɗaya ya yi wa Viper, ya tuna a in da ya ganshi.
Ya kalli Nabila ya ce "Arfa waye wannan? Irin wannan samarin kuma ki ka koma kulawa?"
Ta kalli Viper sannan ta kalli Nasir ta ce "Yaya me yayi maka ne? Na gaya maka tun waccan ranar he's my client"
"Client like how? Shi ne zai din ga biyoki har gida? Get inside kafin na kwaɗeki a wurin nan" Addu'a take Allah ya sa kar Viper ya hasala.
Viper ya ciro wata fitila daga aljihunsa, ya haske idon Nasir, ya matsa daf da shi, Viper ya fishi tsawo sosai ya ce "Talk to me, like a man, baka din ga yi mata shouting ba"
Ya ja da baya ya kalli Nabila ya yi mata alama da hannunsa na i will call you.
Ta jinjina masa kai, shi kuma ya juya zai tafi.
"Waye kai?" Nasir yayi maganar cikin dakewa, dan muryar Viper kawai a bar tsoro ce.
Viper ya juyo, ya kalli Nabila, da ta bashi tausayi, ban da tana wurin, kuma bai san me abun da zai aikata ka iya haifarwa ba, da sai ya sakawa Nasir iraƙi sannan ya gaya masa waye shi, kamar yadda ya yi wa tijjani yayan yar madara.
Ya kalli Nasir ya ce "A man" ya faɗa a taƙaice.
Nasir ya waiwaya, ya kalli Nabila zai fara masifa, amma ta zura da gudu ta shige gida.
Rufa mata baya yayi, yana masifa har ɗakinta ya bita, yana yi mata bala'i, ganin yana neman ya tozarta ta a gabam mutanen gidan ya sanya ta fara kiran sunam Abba da ƙarfi.
Aikuwa Abba ya saukko daga kam benensa yana faɗin "Wai waye yake taɓa mini yarinyar nan, kai Nasir menene haka? Dukanta zaka yi? Shekara Ashirin da biyar sai ka kamata kana duka dan rashin mutunci?"
"Abba ba dukanta zan yi ba"
"To me ka yi mata take wannan kururwar haka?"
"Abba gaba ɗaya Arfa ta canza, ta tsiri wasu irin ɗabi'u na rashin gaskiya, rannan na je ofishin ta, na tarar da ita da wani mutum, gaba ɗaya bai yi kama da mutanen kirki ba, yauma still ta tsaya da wani a waje, maimakon cikin gida tana zance, kamar dai wancan mutumin ne, gaba ɗaya bai yi kama da mutanen ƙwarai ba"
Abba ya kalli Nabila ya ce "Arfa, yayanki a kan gaskiya yake, ni kaina shige da ficen samarin nan naki, ya fara isata".
"Abba, wallahi ba mutumin banza bane ba, kuma ko mutumin banza ne, ba wata muguwar alaƙa ya gani tsakani na da shi ba, na gaya masa client ɗina ne kawai, amma yaƙi yadda kwanan nan komai nayi sai ya din ga zargina