Showing 234001 words to 237000 words out of 479911 words

Chapter 79 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6101

Ki ke kiranta da wasu layukan daban, shi ne ki ka yi disconnecting ɗin bibiyar kiranki da ita da muke yi ko?"

"Ni kuma, ban gane nayi disconnecting ba? Wallahi ban yi disconnecting ba"

"Ƙarya ki ke yi, some hours back, aka yi disconnecting, zaki ga matakin da zamu ɗauka a kanki da ita, sannan zuwan da tayi me kuka tattauna?"

Sumayya ta dafe kanta ta zauna, sannan ta ce "Mota aka saya mata, sai labarin sabon saurayinta da tayi, Alhaji Wada M karofi, sai ƙorafin rashin nasara da take hangowa a kan shari'ar da suke yi".

P.A ya maimaita "Ki ka ce Alhaji wada M karofi?"

"Eh, shi"

"Ki cigaba da sanya ido a kanta, kina kawo mana rahoto, akasin haka zaki ga abun da ba kya so " ta kashe wayar ta dafe kanta.

***
"Indabo ya ga yarinyar nan"

Gaba ɗaya suka kalli Al'amin, liti ya ce "Shikenan, ai na san a rina"

Walid ya ce "Ya aka yi ka gane haka?"

"Mun yi magana da ita sosai yau, ana bibiyar ta, ana bibiyar kiranta da wata ƙawarta, na yi disconnecting duk wata hanya da za a cigaba da bibiyar kiranta. Amma rayuwarta na cikin hatsari, kuma idan ta cigaba da zuwa za a gane inda muke".

Liti ya ce "Shiyasa tuntuni na ce, a sallameta ta daina zuwar mana nan, amma walid ya nace".

"I think i will sealed a deal with her"

Suka haɗa baki suka ce "Kamar yaya?" Yayi shiru yana lissafa yatsun hannunsa.

Liti ya ce "Ka yarda da ita ne? Ni haryanzu tantama nake yi a kanta ne"

Walid ya jinjina kai ya ce "Lallai a tafawa mata" Viper bai sake ce musu komai ba daga haka, ya tashi ya fita.

***
M karofi yana zaune yana shan shayi, wani jami'in tsaro, ya shigo da Indabo cikin falon.

Karofi ya kalli Jami'in tsaron ya ce "Zaka iya tafiya" ya mayar da idonsa kan Indabo ya ce "Barka da zuwa sirikina, kwana da yawa, muna haɗuwa a Abuja, amma da ni da kai, babu wanda yake ziyarar wani. Duk ni yakamata ace ina kawo gaisuwa. Bisimillah zauna mana.

Indabo ya zauna, ya kalli M karofi ya ce "M karofi"

"Ma'aruf Indabo"

"Sabo da kaza fa, baya taɓa hana a yanka ta"

Karofi ya ce "Wannan haka yake, ko a siyasance, ko ma a normal life"

"Auren 'yar uwata maijidda da kake yi, ba zai hana idan kayi mini kan kara nayi maka na itace ba, hawainiyarka ta kiyayi ramata"

Yayi murmushi ya ce "Yakamata kayi mini fashin baƙi, akan wannan kurman baƙin da kake ta karanta mini"

Indabo ya yi wata ƙwafa ya ce "Soyayya da ka je ka fara da 'yar cikinka, saboda abun kunya, kuma yarinyar da take ta gwagwarmayar sai ta tona mana asiri, wadda ka tsayawa, wallahi muddin asirin Abdul ya tonu kaine ba wani ba, kuma sai nayi maganinka a siyasance da duniyance"

M karofi ya ce "Iko sai Allah, kana nufin Nabila wai? Taɓ ai ni ban taɓa sani ba, banda yanzu da kake gaya mini. Ina da lawyer a law firm ɗin su, shi naje gani, na ganta naji ina sonta, kai idan nayi niyyar tonawa ɗanka asiri, da wani zancen ake yi ba wannan ba.
Kuma ni ban yi abun kunya ba, sonta nake yi da aure. Tun da ƙanwarka ba yar gwal bace, da zata hanani zama da mata ba.
Naji daɗin wannan gargaɗi da kayi mini sosai da sosai, amma ka kwantar da hankalinka, babu ruwana da shari'arku, nima aikina nake yi. Zaka iya tafiya idan baka da abun cewa".

Indabo ya tashi, ya kalli idon kankarofi ya ce "Kifi yana ganinka mai jar koma"

Karofi ya ce "A juri zuwa rafi dai " Indabo ya fice yana baza babbar riga.

***
Nabila ta sake komawa gidan abokiyar aikin ramma, amma still bata same ta ba, aka sake gaya mata ta koma garinsu, sai dai samun sunan garin ma ya gagareta, ta kasa samu.

Tana kwance a kan gadonta, ta buɗe videos da hotunan da ta yi wa Viper, ta zuba masa ido, tana jin daɗin tsokanarsa da take yi, na cewa tana son shi, tana son zama kishiyar 'yar madara, mugun kallon da yake yi mata, ba ƙaramin dariya yake bata ba.

Mussaman da ta samu ya kulata, a haɗuwar su ta ƙarshe, duk da a ƙarshe, korarta yayi.

Tana kallon hotunan tana murmushi, ta ɗauki ƙaramar wayarta, ta saka lambarsa ta kira.

Sai da ta kira da ainihin lambarta, sannan ya ɗaga.

"Ohh Allah, kayi saving lambata ne?, Ina ta kiranka da ɗaya layin amma baka ɗaga ba. Ina ta kallon hotunanka, ina son in yi bacci .
Ka san ranar da nayi maka hotunan nan, har murmushi fa kayi, ka din ga fara'a murmushi yana yi maka kyau sosai dear. Yaushe zaka ƙarasa bani labarinka ne? Yakamata ka gabatarwa jauhar ni, a matsayin amarya, zan yi mata biyayya sosai da sosai, in tayata sonka. Ba zan yi kishi da ita ba, ina sonta sosai da sosai, dan Allah ko sau ɗaya ka haɗani da ita mana" kamar da iska take, haka yayi shiru ya ƙi magana.

Ba ta gaji ba, ta sake cewa "Ina ƙaunar yar madara saboda Allah, dan Allah ka ƙarasa mini labarin ta".

"Meyasa ki ka shigo rayuwata?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Labarin dogo ne, ba zan ɓoye maka ba, da dai ina taya Yayana nemanka ne, saboda nayi suna, na rama abun da Bunkure ta yi mini, na wulaƙanta ni a gaban jama'a. Shi ne na din ga up and down, har na haɗu da wannan litin, mara kirki".

"Saboda ki yi suna ki ke son taimakona?"

Nabila ta ce "Eh, a da ba, amma jin labarinka gaba ɗaya ya canza mini tunani, nake jin zan iya yin komai, dan na ga na ƙwato maka hakkinka, da kai da yar madara, duk da ban san ƙarashen labarin ba. Amma gwiwata ta fara sanyi, na fuskanci Naja'atu Bunkure nan, tana da goyon baya daga sama, kuma indabo babban mutum ne shahararre sosai, ina buƙatar support sosai, kai kuma sai korata kake yi kana hantarata".

"Idan na ƙarasa miki labarin, that means duk tsanani babu gudu babu ja da baya, zaki tsaya a shari'ata komai wahala da sarƙaƙiyarta?"

"In sha Allah, i promise it"

Ya sake cewa "Kin tabattar zuciyarki zata iya ɗauka komai muni, komai daɗin abun da zaki ji?"

Cikin ƙwarin gwiwa ta sake cewa "Eh zan iya"

Viper ya ce "Take your time to think, ki yi comparing da ƙalubalen da ka iya biyo bayan hakan"

Ta lumshe idonta, hatta muryarsa, mai daɗi ce, duk a buɗe take saboda bayan naturally yadda take, wiwi da shaye-shaye sun ƙara making ɗin ta deep.

Ba ta bashi amsa ba, ya kashe wayar.

Walid ya ce "Mai zamani, ka yadda da maganarta kenan? Zaka ɗauki fansa ta hanyar shari'a"

Mai zamani ya girgiza kai ya ce "Ta riga ta shiga tarkonsu, kuma na fuskanci ba ta ji ko kaɗan, zata iya salwantar da rayuwarta". Walid ya yi murmushi mai cike da jin daɗi ya ce "To ɗaya maganar fa? Zaka gaya mata?"

Al'amin ya kalli walid, yayi shiru bai ce komai ba.

***
Jikin ramma da sauƙi sosai, tana zaune a gefen gado, Abdul yana bata abinci, gefe ga magungunan ta. Wayarsa da take ringing ya ɗaga ya saka a hansfree ya ajiye  ya ce " 'yar mutanen bunkure, ya ake ciki ne?"

"Abdul"

"Na'am"

"Ya ka yi da yarinyar nan ne da ka yi wa fyaɗe? Wata yarinya ta tsaya kai da fata, sai ta wanke dattijon nan, mun yi duk abun da yakamata, ta koma tana amfani da social media against me, hankali na ƙoƙarin dawowa kaina, sai sintiri take yi wai lallai sai an kai yarinyar gaban shari'a, ga wani voice message da yake yawo na uwar yarinyar...... Abdul ya cire wayar daga hansfree, ya saka a kunnensa, yana kallon ramma.

"Ka gaya mini yaya ka yi da ita? Tana raye ko ta mutu? Mu san abun da zamu shirya a kan shari'ar, an je gidansu babarta bata nan an nemeta an rasa"

"Kina ji? Zan zo in anjima yanzu ina wani uzurin ne" ya kashe wayar, ya kalli Ramma zai yi magana, amma ya kasa saboda mugun kallon da tayi masa.

"Rahama ki tsaya ki saurare ni ki ji"

"Kayi mini shiru tun ba shaƙeka ka mutu na huta ba, azzalumin banza da na wofi, in sha Allah sai Allah ya tarwatsa ka da kak kai da duk masu goya maka baya kuna cutar mutane"

Fafur ta ƙi saurarsa, tayi watsi da kayan karin kumallon, ta tashi ta bar masa ɗakin.

***
Nabila ta daina shiga harkar Nasir, dan sosai ya sakata a gaba, da masifar lallai sai ta daina case ɗin bunkure, saboda lafiyar ta da rayuwarta, ita kuma ta ce babu wanda ya isa.

Sumayya ce ta kirata da wata lamba, ta ɗaga ta ce "Waye?".

"Ke ni ce"

Nabila ta ce "Yar 419, yau kuma da lambar wa ki ka kirani, ko aiki ki ke yi a kaina ne?"

"Nabila, bar wannan maganar kin san menene?"

"No"

"Maganarki da muka saka a radio, a kan bunkure, wata mata ta zo mini, ta ce lallai ke take son gani, akwai information da zata baki a kan bunkure, ta ce macuciya ce, abun babu daɗin ji, bama itakaɗai ba, akwai gwarama, mutane sun fara magantuwa fa"

Nabila ta ce "Abubuwa sun fara yi wa kaina yawa, zan zo har gida na same ki"

Ta ajiye wayar ta dafe kai tana tura baki. Duk da tayi farinciki da haka, dan kuwa gagarumin cigaba ne, amma gaba ɗaya ba ta yadda da sumayya ba yanzu, dole tana buƙatar ganin Viper kafin tayi wani yinƙuri.

Babu tsammani ta ga Nasir ya shigo office ɗin ta, ta tashi tsaye ta ce "Yaya lafiya?"

"Nabila wai ke meyasa a duniya ba kya nemawa kanki zaman lafiya ne? Gaba ɗaya na kasa gane kanki a 'yan kwanakin nan, menene yake damunki ne?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Me kuma nayi?"

"Comment ɗin da ki ka yi da safe nake magana a kai" yayi maganar yana ciro wayarsa ya daddana, ya buɗe facebook ɗin sa, ya tura mata wayar.

Ta kalli wayar, posting ne da hukumar yan sanda tayi, na cigaba da neman Aminu Viper ruwa a jallo, saboda ayyukan ɓarna da yake cigaba da yi.

Tayi comment da "Wannan abun kunya ne ga rundunar tsaron Nigeriya, ace kuna tsare da mutum a prison, a sake shi kuma a dawo ana nemansa, ba shi ne abun bincike ba, hukumar 'yan sanda, da prison, da ta shari'a su ne abun tuhuma da zargi" aikuwa mutane suka yi caa a kan comment ɗin ta, suna reply.

"Yanzu yaya fisabilillahi menene laifina a cikin wannan comment ɗin nawa, ita hukumar 'yan sandan, dan ayi comment ai suka yi posting ɗin, kuma gaskiya na faɗa. Akwai ayar tambaya a kan ma'aikatar Shari'a, hukumar yan sanda da ta gidan yari a kan case ɗin nan, kar ka yi wani tunani daban, ina goyon bayan gaskiya ne kawai"

"Nabila ba kowane lokaci gaskiya take tasiri a ƙasar nan ba, yanzu ki ka shigo cikin system ɗin nan, ƙasar nan ta wuce duk yadda kike tunani".

"Na sani, amma rashin yin wani yunƙuri na kawo gyara, shi ne ke kawo mana koma baya yaya, ba wai ina goyon bayan Aminu Viper ba ne ba, menene gaskiyar abun da yake faruwa nake son sani"

Cikin takaici ya girgiza kai ya ce "Idan kin ƙi ji, ba zaki ƙi gani ba arfa".

Ya ɗauki wayarsa ya juya ya nufi hanyar fita, ya kama handle ɗin ƙofar office ɗin ya murɗa ya buɗe. Sai dai wanda suka yi ido huɗu da shi a tsaye ya sanya gabansa wani irin mummunar faɗuwa. Ya raɓa jikin Nasir ya shiga cikin office ɗin, Nabila ta waro ido tana kallonsa tana kallon Nasir.

Ayshercool
08081012143

57
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Kallonta yake yi ta cikin baƙin glass ɗin idonsa, duk da ya saka facemask, babu yadda za ayi Nabila ta kasa gane shi.

Nasir ya tsaya ya waiwayo, yana son sake ganin waye, duk da fuskarsa a rufe take da face mask, amma ya tsaya ƙyam a tsakiya, ya juya wa Nasira baya, yana fuskantar Nabila.

A hankali ya ƙarasa takawa, yaje ya samu wuri ya zauna a kan kujera, ba tare da yayi magana ba.

Nabila kuma ta kalleshi ta kalli Nasir.

Nasir ya juya ya tafi, yana fita da saurin gaske ta ƙarasa, ta rufe ƙofar office ɗin ta saka mata key.

Ta dawo ta kalleshi, ya cire facemask ɗin sa da glass ya ajiye a kan teburinta.

"Su maciji an fito daga rami, kuma kai tsaye aka yo wurina,  dan Allah meyasa ka ke son lallai sai ka haɗu da yaya Nasir ne? Da ya gano ka da ni da kai zai haɗa duk ya kama, dan ban san me zan ce masa ba"

Ta dafe ƙirjinta ta ce "Wayyo Allana, haryanzu zuciyata racing take yi, ranka ya daɗe irin haka sai ka kirani a waya, ka ce in zo kana son ganina, amma wannan dirar mikiyar da ka yi mini ohh my God me ma zan ce ne? Allah ya sa babu wanda ya sanka" ta zagaya ta buɗe fridge ɗin office ɗin ta, ta ɗauki plate ta ɗoro masa apple, ayaba da lemo ta zo ta ajiye masa.

Ta tsiyayo ruwan zafi a dispenser ta haɗa masa tea mai zafi, ta buɗe jakarta ta ɗaukko ɗan ƙara min flask, ta juye masa dankali a kan plate da ƙwai, ta ce "Bisimillah, fara cin abincin sai mu yi magana naga yanzu safiya ce" yayi shiru yana danna wayarsa.

"Ka ci abinci, wanne zaka fara ci?"

Still bai yi magana ba, har ta fara jin haushi.

"Sweetheart, magana nake fa, 'yar suga na magana" ya ɗago ya kalleta.

Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ajiye, ta ɗauki kofin shayin ta miƙa masa ta ce "Ba dan ni ba, dan Allah ka sha, a gabanka na haɗa, ban kuma son da zuwanka ba, balle ka ce na zuba wani abu a ciki dan Allah" tayi maganar cikin kwantar da murya.

Ya saka hannu ya karɓa, sai dai kamar ƙaramin yaro, ya zubawa kofin ido.

Ta ɗaukko plate ɗin dankalin, ta riƙe a hannunta, ta kalle shi ta ce "Sha mana" ya tsareta da idanunsa masu ban tsoro.

Ta sauke nata idanun, saboda yadda nasa suka yi mata nauyi.

Ta saka hannu ta kai kofin bakinsa, ya buɗe bakinsa a hankali, ya fara sha.

Tayi ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, ya sauke kofin, ta miƙa masa dankalin, kamar mai koyon cin abinci, haka yake ɗauka yana ci.

"Yauwwa My dear" yana ci, Adam apple ɗin maƙogwaronsa, na kaiwa na komowa, sai yayi kamar zai yi magana, sai ya fasa ya haɗiye maganar tare da abincin, da ƙyar yake haɗiye abincin, a duk lokacin da ya saka abinci a gaba zai ci, haka yake ji, sai ya cakala ya bar shi, tun su liti suna lallaɓa shi ya ci abinci, har sun haƙura sun ƙyale shi, sun zuba masa ido.

"Master, ciwonka ya gama warkewa, Alhamdilillah Allah ya ƙara tsarewa, ka daina zuwa in da za a cutar mana da kai dan Allah"

Yayi mata shiru, yana cigaba da cin abinci.

"Ko in ƙara gudun AC naga kana gumi" ya girgiza mata kai alamar a'a.

Tana tayi masa hira, har ya cinye abincin tas.

Ta ce "Alhamdilillah" ta miƙa masa tissue ya goge hannu.

"Wai dan Allah meyasa kake ta kallona ne? Ko wani abun nayi?" Nan ma ya girgiza mata kai.

"Kamar bacci ka ke ji fa, ko an sha ne?"

"Me fa?" Yayi maganar yana kallon ta.

Ta ce "Bakomai"

"Aiki na zo yi" ya faɗa a taƙaice.

Ta ce "Aikin me?"

"Computer zaki bani"

Ta ce "Ok, desktop ta aiki ce, bari na baka laptop ɗina" ta ɗaukki laptop ɗin ta ta bashi, ya buɗe ya fara dannawa.

Ta zauna a kusa da shi, tana kallon mai zai yi, sai dai ta kasa gane me yake yi ɗin, wasu irin lambobi da alphabets kawai take gani a screen ɗin system ɗin.

Sunan Yaya Nasir ne ya fito a kan wayarta, ta ɗaga ta kai kunnneta, tayi shiru.

"Arfa"

"Na'am"

"Waye mutumin da ya zo office ɗin ki?"

Ta kalli Viper sannan ta ce "Baƙona ne"

"Wane irin baƙo?"

Nabila ta ce "Client ɗina ne, ya zo muyi magana ne a kan wata shari'a meyafaru?"

Nasir ya ce "Gaba ɗaya ban yadda da shi ba"

"Daga fara ganin mutum yau ka ce baka yadda da shi ba yaya? Ka san shi ne?".

"A'a kawai jikina ya bani wani abu ne, amma akan case ɗin menene?"

"Is confidential, and against my professional ethics, ba zai yiwu na gaya maka ba, idan na dawo mayi magana" ta katse wayar.

"Meyasa ki ke tsoron gaya masa ne? Shi ne DSP Nasir ɗin? Shi a yadda yaken nan matsoraci yake son kama ni, ai karo da karo sai rago, na raina jarumtarsa"

Ta tsuke fuska ta ce "Ya haka? Yayana ne fa, banda cin fuska"

Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Da lokacin da nake mai zamanina ne, aka bashi aikin kama ni, sai na yi masa karayar da zai shafe shekara yana zaune yana jinya. A yanzun nan da muka haɗu, ba zamu rabu lafiya ba.
Tarbiyyar Jauhar ce da girma ya sanya wasu abubuwan nake kawar musu da kai".

Ta ce "A hakan? Yanzun ma fa kana zuwa ka sari mutane, ka yi faɗa da neman magana"

Ya matso da fuskarsa saitin ta ta, ta ja da baya. "Lokacin da nake mai zamanina, bana bin ƙofa komai girmanta, sai dai na kama katanga kamar ɓarawo, bana biyo hanya ayi gaba da gaba da ni. Bana tsoron kowane irin nau'i na fitina ko tashin hankali, idan aka kwana biyu ban ji ni cikin rigima ba, sai na ji ni kamar mara lafiya.
Aiki tuƙuru da jajircewa tayi a kaina, ba dan ƙaddara ta rusa tanadi da burikan rayuwata ba, ta ci kaso mafi yawa na tarbiyantar da rayuwata a kan tafarki madaidaici. Ki daina haɗa kanki da ita"

Ta lumshe idonta ta buɗe ta ce "Shiyasa na ce tun da ita 'yar madara ce, ni kuma sai na zama 'yar suganka, amma ka ƙarasa mini labarin ta dan Allah" ya zauna sosai ya cigaba da danna system sannan ya ce "Idan na ƙarasa miki labarin ta, hakan na nufin we sealed a deal, da babu gudu babu ja da baya kenan, komai rintsi komai wahalarsa?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"A'a ki sake tunani, mussman ranar da zata fasu kina ɓoye shahararren ɗan ta'adda kamata"

"Kai ba ɗan ta'adda bane ba, ta'addancin da aka yi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login