Showing 255001 words to 258000 words out of 479911 words

Chapter 86 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6070

na rasa me nayi masa gaba ɗaya"

"A'a Arfa, Nasir yana cikin masu goyon bayanki a gidan nan, tun da har ya magantu, to ya fiki gaskiya, ki san irin mutanen da zaki din ga tsayawa, kuma ki din ga mu'amala da su, yanzu a cikin samarin nan naki, lallai ki duba mai nutsuwa ya zo in ganshi, nima zan fi samun kwanciyar hankali ace kina ɗakinki" Nabila ta yi shiru, Abba yayi ta yi mata nasiha, bayan ya gama ya fita, Nasir ya bi bayansa.

Nasir ne ya bi bayan Abba, suka shiga ɗakinsa ya ce "Abba, yakamata ka ja wa arfa kunne, wasu abubuwan take yi kwanan nan, shishishigi a kan wasu abubuwa. Ta sako wannan barrister Naja'atu Bunkure a gaba, kar ta je ta janyo wa kanta wata matsalar"

Abba ya ce "To ai ni kaga ban sani ba, ban san me take aikatawa ba wasu lokutan, amma babu komai, zan yi mata nasiha, ka san ba kowane lokaci faɗa yake tasiri ba".

Nasir ya ce "Haka na, sannan kuma Abba"

"Sannan kuma me, ina jinka"

Ya ɗan muskuta ya ce "Abba dan Allah ka bani auren Arfa"

Take annurin fuskar Abba ya ɗauke, ya ce "Auren arfa kuma?"

Ya ɗan yi shiru yana wasa da yatsunsa.

Abba ya numfasa ya ce "Kenan kishi ne ya saka ka shigo kana yi mata faɗa?" Ya girgiza kai ya ce "A'a Abba, ba haka bane ba"

"To, Nasir kai ɗa na ne, hakazalia arfa, babu wani banbanci a tsakaninku, dan haka ba zan so abun da zai cutar da ɗayanku ba. Ba zan manta abun da mahaifiyarka tayi mini a kan yarinyar nan ba, kuma haryanzu ina kallon irin ƙiyayyar da take nuna mata, na daɗe da gane kana sonta, amma ina fatan ta samu wanda hankalinta zai kwanta da shi. Muddin ka aureta mahaifiyarka ba zata taɓa barinta ta zauna lafiya ba.
Ni bani da matsala da son da kake yi mata, amma ka nemi yardarta, da ta mahaifiyarka tukuna"

Nasir ya ce "To Abba, na gode sosai" ya tashi ya bar ɗakin.

Nabila banɗaki ta shige, ta rufe ƙofa ta kira Viper.

"Yanzu fisabilillahi ka kyauta mini kenan? Ka saka an yi mini faɗa, Allah ne ya rufa mini asiri, dan Allah ka daina zuwa in da nake, gara ka kirani na zo da kaina"

"Ki je ki yi tunani a kan abun da na saka ki, ki san abun yi sati biyu kawai ki ke da shi"

"Ya kake bani umarni ne a haka, ka din ga lallaɓani mana, why are you always bossy ne? Sai da safe zan duba na ƙara effort, ina iya ƙoƙarina a kai, tauye ni ake yi, ka san ba ni da kowa sai Allah ni, amma ka yi mini addu'a in sha Allah ni zan kawo ƙarshen bunkure"

"Allah ya sa" ya kashe wayar.



***
Ramma ce ta ƙurawa wayar Abdul ido, ta kalli ƙofar banɗaki, yana ciki yana wanka, ta miƙa hannu ta ɗauka ta bar ɗakin.

Bai jima ba ya fito daga banɗakin, sai dai ya nemeta ya rasa a ɗakin, ya fita nemanta, ya tafi kitchen, ya tarar da ita a tsaye a kitchen, da wayarsa a kunnenta cike da rashin gaskiya.

Babu tsammanni ta ji ya fizgota, ya kwaɗa mata mari, har sai da ta faɗi ƙasa.

Ya duba call logs ɗin sa, ya ga ba a ɗaga kiran da ta yi ba, ya kalleta a matuƙar fusace ya ce "Saboda kin ga ina ɗaga miki ƙafa shi ne zaki tsallake gona da iri, zaki wuce makaɗi da rawa? Bari na koma miki ainihin Abdul ɗina, kuma wannan huakan da ki ka yi, dai-dai yake da sake nesanta kanki da iskar 'yanci. Kuma bari na sake gaya miki, babu wani mahaluki da ya isa ya rabani da ke a duniyar nan ko waye shi, idan kin ga dama ki cigaba da ƙoƙarin lallai sai kin bar gidan nan, zaki ga yadda zan yi da ke"ya fice daga kitchen ɗin ya bar a zaune, hannunta riƙe da kuncinta, hancinta har ya fara zubar da jini, saboda azaba.

Ta rasa me ma yakamata tayi, saboda zuwa yanzu zuciyarta ta ƙeƙashe, kukan ma ba iya yin sa take yi ba.

Ta ja wuri ta zauna sosai saboda jirin da take ji.

***

Sallama take yi a tsakar gida, ta ce "Na shigo ko na koma?"

Umma da take ƙofar kitchen ta ce "Idonki kenan arfa? Yaushe rabonki da gidan nan?"

"Tuba nake umma, ayyuka ne sun yi mini yawa sosai, amma ayi mini afuwa dan Allah"

Umma ta ce "To Allah ya yi jagora"

"Amin umma, ina sumayya?"

"Tana ɗakinta"

Nabila ta nufi ɗakin sumayya, ta sameta tana ta aiki a cikin computer, sallamarta kawai ta amsa, ta mayar da hankali ta cigaba da abun da take yi.

"Sumy, dan Allah ki kalleni mana"

Sumayya ta ɗago ta kalleta ta ce "Idan na kalleki mai zai amfana miki, ni da nake munafuka?"

Jiki a sanyaye ta ce "Dan Allah ki yi haƙuri, nayi kuskure abun ne ya bani mamaki ya ɗaure mini kai"

Tuni hawaye ya cika idon sumayya ta ce "A yadda muke da ke, ban taɓa tunanin wani zai kawo miki aibuna ki yadda ba, ba tare da kin yi bincike ba, amma kai tsaye ki ka danganta ni da kalmar munafunci, baki san wahalar da nake ta yi dan kare rayuwarki ba"

Nabila ma sai ta saka kuka ta ce "Dan Allah masoyiyya kiyi haƙuri ki yafe mini, ɓacin rai ne, kin ga sam baki yi mini bayanin komai ba, na samu labarin an saka ki kina bibiyata, dole na shiga damuwa kuma ke baki gaya mini ba"

Sumayya ta dubeta ta ce "Waye ya gaya miki ana bibiyarki ta hanyata?"

"Ba shi da amfani faɗar, amma dan Allah waye ya saka ki bibiyeni, ki din ga kai masa rahotona?"

Sumayya ta kalli Nabila da take ta share mata hawaye, Nabila cikin jin kunya da sanyin jiki, take ta ƙara bawa Sumayya haƙuri.

Sumayya ta numfasa ta ce "Honorable indabo ne"

Nabila ta waro ido ta ce "Indabo kuma? Meye alaƙata da shi? Me na yi masa?"

Nan Sumayya ta warware wa Nabila yadda suka yi da Indabo, lokacin da ya ce taje gidansa su yi program.

Hankali a tashe Nabila ta ce "Amma meyasa baki gaya mini ba Sumayya?"

"Ya za ayi na gaya miki? Ya ce muddin ki ka sani, zaki iya rasa ranki, kuma na san dole zaki iya aikata wani abu, da zai sanya su yi miki illa, babban abun da ya bani mamaki bai wuce lokacin da muka yi waya da ke ba, ki ka ce kin haɗu da Viper, ya ƙara rikicewa gaba ɗaya, amma na tabattar masa da ƙarya ki ke yi, baki haɗu da shi ba, ina tunanin akwai wani abu a tsakanin sa da Viper, dan cewa yayi, zai yi wa Viper tarko da ke, ya kama shi"

Gaban Nabila ya faɗi, gaba ɗaya sai kanta ya kulle.

"To tayaya zan zama tarkon da za a kama Viper? Meye alaƙata da shi?"

Sumayya ta ce "Ban sani ba, amma dan Allah ki nutsu, kar ki aikata wani abu da zai saka ya cutar da ke, wallahi rashin imanin mutumin nan ya wuce tunaninki, ke hatta a wurin aikina akwai masu saka mana ido, da kin zo sai su kirani, su ce me muka tattauna, har wayar da nake yi da ke suke bibiya shiyasa nake kiranki da wasu lambobin"

"Na shiga uku, to ni uban me na yi masa? Sumayya da wace lambar suke kiranki?"

"Private number ce, ba sa kirana da lamba" zumbur Nabila ta tashi.

Sumayya ta ce "Ina zaki je?"

Tayi waje da sauri ta ce "Zamu yi qaya kawai" a tsakar gida ta yi wa Umman Sumayya sallama ta fice.

Ƙaramar wayarta ta ɗauko, ta kira Viper, ya ɗaga a rikice ta ce "Kana nan ne, gani nan zuwa"

"Ke tsaya mana, ki zo ina?"

"In zo wurinka mana ina cikin ruɗani da rashin fahimta"

"Koma menene ki nutsu, ki yi mini bayani ina jinki"

"Ni ba wani bayani da zan yi maka, kawai zan zo gani nan".

Ya ce "Hanya babu kyau, na gaya miki kar ki zo fa"

"To a ina zamu haɗu? Rayuwata tana cikin hatsari, ni kawai kana ina, na shga uku"

Viper da yake zaune ya tashi tsaye ya ce "Malama ki nutusu ki yi mini magana, kina cikin hatsari kamar yaya?"

A fusace ya ce "Na gaya miki hanya babu kyau, ana bibiyarki ko kin manta? Za a fara tracking wuraren da ki ke zuwa yanzu haka. Ki tsaya ki saurare ni.

"To ina jinka"

"Zan tura miki adress ɗin da zaki same ni, idan kuma ni in zo shikenan"

Ta ce "A'a kar ka zo"

"Ki samu wuri ki ajiye motarki, zan turo miki adress ɗin in da zaki same ni".

"To ka yi sauri" ta cigaba da tafiya a motar, tana waige-waige ko zata ga wani yana bin ta.

Ya turo mata adress ɗin da zata same shi, ta ajiye motarta, ta bi adress ɗin.

Wurin kamar garden haka yake, ba kowa a wurin, sai manyan bishiyu, ga wurin sanyi mai daɗi.

Tana tsaye tana waige-waige, ta ciro wayarta, tana ƙoƙarin kiransa, kawai ta ganshi unexpected a bayanta, sakin wayar tayi ta hau ihu.

"Menene?"

"Ba tsorata ni ka yi ba, sai ka zo kana wani sanɗa da na zura da gudu fa, ka daina wannan sanɗar".

Ya kalleta ya ce "Idan ban yi sanɗa ba, ban amsa sunan Viper ba, sai da aji hucina, ko bayan nayi ɓarna a ankare da na zo wuri, gani menene?"

Ta ƙare masa kallo ta ce "Ɗan beauty"

Ya tsuke fuska ya ce "Neman me ki ke yi mini?"

Cikin damuwa ta ce "Mu zauna, na gaji da tsayuwa"

Suka samu wuri suka zauna, ta ce "Dan Allah Viper meye haɗina da Indabo? Shi ya saka sumayya take bibiyata. Ta gaya masa yadda suka yi da sumayya.

Ya numfasa ya ce "To me zan yi miki?"

"Ban gane ba, ka gaya mini meyasa Indabo yake bibiyata, me nayi masa?"

Cikin ko in kula ya ce "Ya za ayi in sani?"

"Dan Allah ka gaya mini, kai ma fa ka tambayeni ko na haɗu da shi, me kake ɓoye mini ne? Dan Allah ka gaya mini mana"

"Meyasa liti ya rikice ranar farko da ya ganki, ya amince ya kawo ki maɓoyata?"

Ta ce "To ya za ayi in sani, ina tambayarka kana tambayata? Ka gaya mini mana"

Ya ɗago ya tsura mata ido.

"Ka yi magana mana, dan Allah meyasa yake bibiyata, ta ce ya rikice lokacin da ya ji na ce na haɗu da kai" still bai yi magana ba.

"Talk please"

Zuciyarsa ya ji tana harbawa da sauri, ya girgiza kai ya ce "Kamar na ji kin ce mamanki ta rasu ko?"

Turɓune fuska ta yi ta ce "wai ina ta rayuwata, kana tambayata wani abun daban".

"Nan gaba zaki so jin dalilin da ya sa na tambaye ki, bana surutun banza ni"

Kamar za ta yi kuka ta ce "To ni yanzu ya zan yi da wannan indabon?"

Viper ya ce "Ba ruwanki da shi, ni ne dai-dai shi, ki ji da bunkure karki manta, sati biyu kawai na baki ki yi mini aikina"

Ta narke murya ta ce "Nawa zaka bani ne da ka sakani aikin, ka san dai ba lawyer gwamanti ce ni ba"

"Nawa ki ke so?"

"Kai nake so" gabansa ya faɗi, da ya tuna Jauhar sararta ce faɗar haka.

"Kina wuce gona da iri" yayi maganar yana kallon in da yake facing.

"Daga zuwanka, ka saka DSP ya haɗa ni da Abba, an ce sai na duba samarina na fito da miji, sai ka aureni, tun da duk kai ka janyo koma menene"

"Are you serious? Ɗan ta'addan zaki aura kina gidan masu kaki?"

Ta ce "Eh mana, ka bani dama na zama yar suganka"

Ya ɗora hannunsa a kan ƙirjinsa, ya ce "Ki daina wannan wasan ba na son sa ko kaɗan, haryanzu ina jin motsin jauhar a cikin zuciyata. Idan ki na irin wannan maganganun ji nake tamkar na aikata zunubi mai girman gaske, babu wani abu da zan iya haɗawa da soyayyar jauhar a zuciyata, ki kiyaye wannan ki daina wannan wasan, kar ya zama gaske".

"Ba ka son yar sugar kenan sai madara ko?"

"Ke ki ka san sugan, ni ba na ta'amalli da shi ma"

"To zuma fa ko mazarƙwaila" ya yi mata shiru.

Ta tashi ta ce "Kar ka so ni ɗin, amma to ni ya zan yi da wannan indabon bashi da imani, kar ya kashe maka ni"

Viper ya ce 'Idan ya kashe ki ya hutar da ni"

Murguɗa masa baki tayi, ta kama hanyar tafiya. Sai da tai nisa sannan ya waiwaya yana kallonta.

Ita kanta murmushi ta yi, saboda yau ya sake, babu wannan alamar ƙuncin da damuwa a tare da shi.

***
Da daddare Nabila tana kan social media, taga wani dogon rubutu, da aka yi, na jinjinawa Naja bunkure, a kan ayyukan ta na jin ƙai. Sumayya na ganin posting ɗin, tayi tagging ɗin Nabila.
A take Nabila tayi reposting ɗin post ɗin, tare da caption kamar haka *Lokaci yayi da yakamata mu san haƙiƙanin ayyukan da Bunkure foundation ke gabatarwa, shin da gaske dan talaka take yi, ko kuwa dan rufe ɓarnar masu ido da kwalli kawai take yi?.
Mu duba case ɗin yarinya zulaiha, da ya faru shekarun baya, wadda ta fuskanci cin zarafi, daga wani ɗan mai kuɗi, bunkure foundation sun shiga case ɗin domin su tsaya mata, a hukunta shi, amma ƙarshe sai labarin mutuwar zulaiha muka ji, ta kashe kanta ta hanyar shan fiya-fiya, shi kuma wanda ya aikata, yana shekarar ƙarshe na kammala karatun degree a ƙasar Amurika.
Bana ƙwaina sai da zakara, akwai tarin hujjoji da nake da su a kan maganata.

Jikinta na tsuma, ta yi posting ɗin, ta rufe data.

Tayi addu'oin kwanciya bacci, ta kashe wayarta, har ta rufe ido maganganun ta da Viper suka faɗo mata.
Lumshe idanunta ta yi, amma maganar sa ta din ga kai komo a zuciyarta.

*Ba zan iya haɗa soyayyar jauhar da komai ba, dan haka ki ma daina wannan wasan*

Dafe ƙirjinta ta yi, ta ce "Na shiga uku,  tausayin sa kawai nake ji, da wasa nake yi, me nake ji a raina ne?' ta tambayi kanta.

Wasi-wasi ne kawai, ta bawa kanta amsa tare da kwanciya.

Washegari da safe bayan sallar asuba, ta kwanta ta sha bacci, kasancewar lahadi ce, babu aiki.

Sai wajen ƙarfe goma ta tashi, ta yi wanka ta fito ta shirya ta ɗauki wayarta ta kunna.

Jerin saƙonni ne suka din ga rige-rigen shigowa wayarta, bayan ta kunna data.

Messages kuwa, ga na barrister Habib, ga na summaya.

Ƙarƙashin post ɗin ta kuwa, comment ya kusa dubu, da masu kare Bunkure da masu zagin Nabila, kasancewar alherin bunkure galibi mutane suka sani.

Ta ɗaga kiran wayar sumayya da yake shigowa, ta ce "Ya ne?"

"Nabila daga tagging ɗin ki a post, kin rikita media"

Nabila ta ce "Ai makaho ba ya sanin ana kallonshi sai an taɓa shi, bar su su gama haukan da kare ta, ina nan zan saki maganar ramma bayan an kuma zaman kotu".

"Amma Arfa kar fa ta yi miki wani abu"

"Ba abun da ta isa ta yi, ai ina da hujjoji "

"Allah ya ƙara tsare ki, zan cigaba da nemo miki sahihan bayanai a kan ta"

Naja ta kalli posting ɗin ta yi murmushi ta ce "Bari na nuna wa yarinyar nan ainihin kalata da take son gani.

Kira Nabila ta gani da private number, babu tsoro ko fargaba ta ɗaga.

"Wane irin move ne haka, kin san mutanen nan ba za su barki ba ko?"

Nabila ta ce "Kai ka bani aiki ka ce nan da sati biyu, aka yi sara a kan gaɓa, sumayya ta yi tagging ɗina a kan post ɗin, na ga ya dace na tofa wani abu".

Viper ya ce "Shikenan, amma ki shirya matakin da za su ɗauka a kanki"

Nabila ta ce "Ina da kai ai, idan na je aiki zan kiraka"

Nasir ne ya faɗo ɗakin ta ya ce "Nabila, wai meyasa baki da hankali ne"

Ta kalleshi ta ce "Me nayi kuma?"

"Ban ja miki kunne a kan Naja'atu Bunkure ba? Kin je kin tsokanota, gashi an fitar da sanarwa hukumar DSS suna nemanki, an shigar da ƙararki for defomation of character".

Ayshercool
08081012143

62
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Ta ce "Ban gane ba, su DSS ɗin uban me na yi musu suke nema na, kamar wata 'yar ta'adda".

"Shut up, ina magana kina yi mini gatsali, abun da nake ta ankarar da ke kenan ai, matar nan tafi ƙarfin ki, ba sa'ar yinki ba ce ba, amma saboda zunzurutun taurin kai, da zigar da ki ke ɗauka, kin cigaba da abun da ki ka ga dama, da yake ba kya son zaman lafiya"

"Ina son zaman lafiya DSP, kuma duk abun da nake yi da hujja nake yin sa, dan haka a gaban kotu yakamata ta ƙalubalance ni, ba wurin DSS ba, uban me nayi mata?"

"Look arfa, matar nan ba zata bi abun da doka ta tanada ba, dan tana tsoronki, koma menene za ta yi shi ne, dan kawai ta tozarta ki, ta nuna miki ke ɗin ba kowa ba ce ba, kuma babu abun da wani ya isa yayi. Ko hurumin DSS ne su kama ki, ko ba hurumin su ba ne, za su yi abun da ta ce ne, kuma babu mai ƙwatarki"

Kawai Nabila ta saki murmushi ta ce "Ai DSP duk wanda ya ce ayi wasan jifa, ya san me ya taka ne? Dss ai ba lahira bane ba, a yadda nake ji na yanzu, hukuncin Allah shi ne abu mai razanarwa da firgitarwa a gare ni. Ban fara wasan ba, sai da na tabattar da ingancin ƴan wasa na. Ita taƙamarta tana da manya a sama, da zasu tsaya mata, abun da ta manta da ita da manyan banzan nata shi ne, ƙanan na ƙasa su suka zama tsaninsu wurin zuwa ƙololuwar in da suke tafka tsiyar, daga zarar na ƙasan sun yi bore, na saman dolennsu su shiga hankalinsu, ita ta iya Black market ni ta hanyar shari'a zan nuna mata kuskurenta legally"

"Shut up a beg, uban me ki ka taka, mara hankali kawai, zaki tayar wa da mutane zaune tsaye" tayi masa shiru ya fice yana sababi.

Nan fa yan gidan, suka samu topic of discussion, ko a jikinta, ta gama shirinta tsaf, Baba magajiya ta iske a falo, ta ce "Yauwwa arfa, dama ke zan zo na kira, babanki na nemanki yanzu da gaggawa".

Duk da sauri take yi, amma ta nufi ɗakin Abba,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login