Showing 420001 words to 423000 words out of 479911 words

Chapter 141 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6126

iya da ƙaddara".

Viper ya yi shiru bai sake cewa komai ba.

Abbu ya sake numfasawa ya ce "Yakamata na gaya maka abin da nake son na gaya maka, kar lokaci ya ƙure mini"

Al'amin ya tattara hankalinsa a kan Abbu.

"Zuwa yanzu Al'amin babu wani wanda ya san kan kasuwancina sosai, duk wanda na janyo sai yayi ƙoƙarin cutar da ni. Sannan akwai gadonka na mahaifiyarka da kuma ɗan uwanka, sun zama manyan kadarori, kar karɓi abinka ka tallafi rayuwarka, kuma ina son ko bayan babu raina, ka cigaba da jujjuya harkar kasuwancin nan, kar abun da zan bar maka ya ƙare ba tare da ka tsaya da ƙafarka ba"

Viper ya gyara zamansa ya ce "Babu in da zaka mutu ka je"

Abbu ya yi murmushi ya ce "Faɗa kawai ka ke kaima"

Ya rausayar da kai ya ce "Abbu already ina aiki, ni ba zan iya kasuwanci ba"

"Aikin me?"

"Sojoji nake yi wa aiki, ba zan iya haɗawa ba, ko zan haɗa ma, sai dai wani ya riƙe mini, wasu alfarma nake nema ka yi mini"

Cikin sauri Abbu ya ce "Na menene?"

"Na farko, ina so ka taimaka ka jagoranci Abdallah, liti ka mayar da shi wurin mahaifinsa, a nema masa afuwa, dan na san nine silar barinsa gida baki daya, ko ba ni bane, na taka muhimmiyar rawa a hakan.
Abu na gaba kuma, a yanzu Walid ba shi da kowa sai Allah sai ni, maraya ne, yan uwansa ba sa ta tashi, duk masu ƙaramin ƙarfi ne. Ina roƙonka ka sanya mini shi a harkar kasuwancinka, ka bashi babban gurbi, sannan ka aura masa Shahida" shiru Abbu yayi yana kallon Viper.

Ya cigaba da cewa "Na san zaka ga abin wani iri, amma bana zaɓen tumun dare, daga ni har su muna ta ƙoƙarin gyara kura-kuranmu, mu sake sabuwar rayuwa ne. Kuma Walid mutum ne mai amana, ba zai taɓa ci maka amana ba, duk rintsi duk wahala, Walid ba ya cin amana, ni na yarda idan ma ba zaka saka shi a kan naka kasuwancin ba, ka bashi gidana ɗaya, a sayar da sauran kayana, a koya masa harkar kasuwancin katakon, sannan ka aura masa Shahida. Ba kuma dan na cutar da ita ko rayuwarta ba, zan iya yi maka rantsuwa da Allah, ko Walid ba shi da komai, Shahida ba zata wahala ba, ina ƙara tabattar maka da mai amana ne. Shi liti shagon shayinmu yake so, ya ce ko na mutu shi zai gajeta tun da shi ne ya rayata ba ni ba, ya je ya ƙarata da ita, Walid ko duk wani abu da na gada za a ƙarar, dan Allah a bashi ba zan iya biyan bawan Allah nan ba".

Abba ya jinjina kai ya ce "Na ga alama, shikenan babu damuwa idan ma ya fi hakan za ayi masa, sai dai ita Shahidan ka yi magana da ita idan ta amince, ka san halin mata kar ayi abu, azo a ji kunya"

Viper ya ce "In sha Allah ba za a ji kunya ba, Walid mutum ne mai haƙuri da kawaici, kuma mai amana"

"To shikenan, ba zan taɓa maka kayan gadonka ba, amma zan ɗauke shi a kasuwa, zan bashi auren Shahida muddin ta amince, ni ma na shaida ɗawainiyar da yake yi da kai, Allah ya tabattar mana da alkhairi".

Likita ne ya shigo yayi musu bayanin jikin Abbu da sauƙi, jininsa ne ya hau sosai, kuma an samu ya sauka, zuwa washegari za a iya sallamarsa.

Maƙwabta da abokanan kasuwancin Abbu suna ta zuwa duba Abbu, suna ta so su magantu da ganinsa tare da Viper, ya ƙara girma, da kwarjini sannan akwai alamun ƙarin nutsuwa a tattare da shi.


*****
Bunkure ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda rashin sanin abin yi, dan tun bayan da Nabila ta damƙa mata kundin ƙorafe-ƙorafen da zata kai ma'aikatar Shari'a a kanta, ta rasa yadda zata yi. Gashi ma'aikatar shari'ar duk waɗanda ta sani yanzu ba sa nan, an yi musu canjin wurin aiki, tana ta kasa kunne ta ji ta ina za a nemeta.
Tsananin damuwa ya sanya ko baccin kirki ba ta iya yi, sai ta sha tayi mankas tukuna.
Duk da abokan aikinta, na ta ƙarfafa mata gwiwa, da nuna mata cewa za ta iya fuskantar ƙalubalen da yake gabanta. Ga mutane duk sun dawo daga rakiyar Foundation ɗin ta, kuɗaɗen da suke tallafawa ƙungiyar domin taimakon mutane, duk sun daina saboda sun gano cewa cuta ce.
A dalilin Nabila, mutane da yawa suka samu 'yancin yin magana, tare da sanarwa duniya tallafin da aka nema da sunansu, ko aka basu, ana dawowa a karɓa, wasu kuma ma ba a basu.
Sosai social media da gidajen rediyo, maganar bunkure ta yamutsa hazo, ko ina zancen ake yi.

****
Washegari aka sallami Abbu daga asibiti, suka koma gida.
Shahida na ɗakinta, tana kwance tana karatun Alqur'ani, Viper ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ta yi masa iznin shiga, ya shiga ya zauna, ya dube ta ya ce "Kin gama idda ko?"

Ta jinjina masa kai, ba tare da ta ɗago ba.

"Magana nake son mu yi, shawara ce, ba dole zan yi miki ba, zaki iya cewa a'a idan abin bai yi miki ba"

Ta jinjina masa kai.

"Na san zaki ji abin wani banbarakwai, amma ba zan yi miki zaɓen tumun dare ba, kuma ba dole zan yi miki ba, ina son Abbu ya haɗa aurenki da Muhsin ne, abokina Walid. Na san zaki yi mamaki, ko ki ji babu daɗi, saboda duba da yanayin mummunar rayuwar da muka yi a baya. Dama kowane mutum tara yake bai cika goma ba, duk wani halin kirki na mutum, sai an tarar da shi da wani hali da ba a so, kuma yanzu muna ta ƙoƙarin gyara ɓarnar da muka yi ne a baya. Ina baki tabbacin Muhsin mutumin kirki ne, kuma zaki ji daɗin zama da shi, ya fi ni nagarta da halacci, da zunzurutun haƙuri. Kema kuma na san mutuniyar kirki ce, a dalilinki ina fatan ya ƙara shiryuwa, amma ina baki tabbacin zaki iya dukan ƙirji a gaba, ki ce kin yi dacen mijin aure. Amma ba dole nake yi miki ba, na tuntuɓe ki ne dai da maganar, kafin nayi masa, idan kuma ba kya son sa babu wani abu shikenan shawara ce".

Sai da Shahida ta ji dummm, tabbas Walid ma tsohon ɗan sara suka ne, kuma bata san shi da wata sana'a ba, amma kwana biyun nan da take zuwa asibiti, suka ɗan zauna tare, akwai nutsuwa da dattaku a tattare da shi, kuma karo na farko kenan, da Al'amin ya yi ƙoƙarin yin wani abu a kan rayuwarta, ta san ba zai cutar da ita ba, dan haka ta numfasa ta ce "To yaya duk yadda ka yi dai-dai ne, in dai ka amince, nima na yarda".

"A'a kar ki yi mini haka, ki gaya mini abin da yake zuciyarki, ko kuma dai na fara turo shi ya nemi yardar ki da kansa, amma magana ta domin Allah bamu iya soyayya irin wadda ku ke so ba, sai dai ki koya masa, kin san mazaje we are always serious" yayi maganar yana ɗan murmushi.

Ita ma murmushin ta yi tana sunkuyar da kai.

Nan ya cigaba da koɗa mata nagartar Walid, da ƙoƙarin da ya din ga yi wa rayuwarsa.

Za ta iya cewa, ba ta taɓa zama sun yi hirar kirki mai tsawo da yayan nata ba sai yau.

Da daddare ya bar gidan, ya tafi can gidan da suke zama, Walid suna ta faɗa da liti, a kan liti yayi musu wanki, ya ce ba zai yi ba, ya saka Viper ya dawo da ɗan mama yayi, tun da ya fi jin maganar sa, dama ɗan mama ne yake yi musu.

Viper ya ce "Rabu da shi mai laya, kai ka kusa shiga daga ciki, a din ga haɗa kayan ka masu datti a bayar wanki, ka bar Liti"

"Wace zata aure shi, bai iya komai ba sai saka aiki, daga kai har shi?"

Viper ya ce "Seriously, Walid Abbu zai baka auren Shahida, abin da ya rage maka kawai ka nemi yardarta" waro ido Walid yayi ya ce "Wane Walid ɗin?"

Liti ya yi shewa ya ce "Sai dai kai maigida, Allah ya ja zamaninka ka daɗe ka yi ƙarko irin na dabino, Allah dai ya saka da alkhairi"

Walid ya ce "Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, uban waye zai bamu aure a haka? Mai zamani ka daina wannan wasan"

Viper ya kwanta ya ce "Ba wasa nake yi ba, da gaske nake, ka nemi soyayyarta kawai, aure zan yi muku, Abbu ma ya san zancen. Kai kuma liti sai dai ka nemo da kanka, tun da na san kai ba gwaninta ake yi maka ba"

Walid ya ce "Dan Allah a daina wannan wasan, wai waye ma zai bani wani aure? Dan Allah ka bari ta samu mutumin kirki ta aura"

Viper ya tashi zaune, ya dafa kafaɗar Walid ya ce "Kai ma mutumin kirki ne, shiyasa ba zan so wata ta samu ba, alhalin ga ƙanwata, ku daidaita kawai sai da safe" yana gama maganar ya kwanta.

Walid ya zauna kamar soko yana rarraba ido, Liti kuwa dariya ya din ga tuntsirawa, saboda har gara Viper ma da Walid, dan shi kamar ma tsoron mata yake ji, shi ko da wasa bai taɓa tare budurwa ba.

Liti ya din ga tsokanarsa, yayi masa banza ya kwanta, hango Shahida yake yi, yarinya nutsatsiya yar gayu, wai kuma ta aure shi shi dai abin bai yi masa tsari ba.

Washegari za su je duba Abbu da yamma, kamar ya fasa zuwa, saboda gaba ɗaya kunya ce ta kama shi.


Kasancewar Viper ya riga su tafiya, ya sanar wa Shahida, su Walid za su zo duba Abbu, dan haka ta shirya, za su yi magana ita da Walid ɗin.

Duk abin nan, rahila ba ta san me ake shiryawa ba.

Sai bayan la'asar, su Walid suka zo, duk yadda yake ɗan sakin jiki da Abbu su yi hira kasa yayi, ya din ga mutsu-mutsu, kamar ya nutse a ƙasa, liti yana ankare da shi, kamar ya yi dariya.
Liti ya ce zai je ya dawo, ya fita ya yi nasa wuri, bayan sun yi wa Abbu sallama, a ƙofar gida Viper ya ce "Na yi mata magana, za ta fito ku yi magana, mu haɗe a jungle"

"Dan Allah Viper ka ce da wasa ka ke yi, ni wallahi ban san me zan ce mata ba, wallahi kunya nake ji"

"Malam yakamata ka girma, ka yi mata tatsuniya if you like" zai sake magana, suka yi ido huɗu da Shahida, ta fito cikin doguwar rigar abaya maroon.

Viper ya yi gaba yana murmushi, Walid ya ɗan diririce.

Ta ƙaraso tayi masa sallama ya amsa, ta saci kallonsa, dogo ne shi ma, sai dai bai kai Viper jiki da tsawo ba, kuma yana da haske sosai, sai dai laɓɓansa baƙi ƙirin, idanunsa kuma jajaye, yana da dogon hanci da gemu kaɗan ba mai yawa ba.

"Sannu ya jikin Abbu?"

"Da sauƙi Alhamdilillah"

"Amm na san wataƙila mai zamani ne ya takura miki, idan ba kya so na, ki rabu da shi kawai, Allah ya zaɓa miki miji nagari, rigimarsa ce kawai ta saka ya ce wai zai aura mini ke" yadda duk yake a rikice ne ya sanyata murmushi ta ce "Yaya Muhsin, mu yi addu'a mana, bamu san me Allah ya ɓoye ba, mu nemi zaɓin Allah, in dai nima zaka kula da ni, ka din ga lallaɓa ni kamar yadda ka ke yi masa ai ba wani abu" sunkuyar da kai ya yi yana murmushi, sai dai kamar ya zuba da gudu dan kunya. Bai fi mintuna goma ba, yayi mata sallama.

Da ya koma can gidan da suke, kamar wanda ya aikata zunubi, liti ya saka shi a gaba, ko murmushi yayi, sai ya ce tunanin Shahida yake yi, ya hana shi sakat.

Da daddare Shahida ta kira Viper, ta tambaye shi ya suka je gida. Maimakon ya bata amsa, sai ya miƙa wa Walid wayar.

Tayi masa ya yaje gida, sannan ya ce zai ɗauki lambarta a wurin Viper.

Washegari da sassafe, Viper ya shirya ya fice ya bar su, dan yai zai koma wurin likitan ƙwaƙwalwa, kuma yana son ya ga Nabila.


***
Ƙarfe tara na safe, Nabila ta fito falon madam Halima, hannunta riƙe da jakarta, da court ɗin ta, kawai ta ga Viper a falo, suna magana da Madam.

"Mummy good morning"

"Morning sweetheart, kin fito?"

"Eh, Good morning" tayi maganar tana kallon in da Viper yake, bai amsa ba, ya ci gaba da magana da Madam.

Kitchen ta nufa, kusan mintuna biyar, madam ta tashi ta shiga ɗakinta, Viper ya bi bayan Nabila.

Sai da ta tsorata da ganinsa unexpected.

Wuri-wuri ta yi da ido tana kallonsa.

Ya sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce "Abin da ki ka yi mana kina ganin kin kyauta ko? Nayi tafiya mai hatsari, ya na je ya na dawo, bai dame ki ba? Kin yi mini laifi amma ba ki iya bani haƙuri ba, yau zamu koma asibiti you don't even care to call me. And a gabana ki ka bi kankarofi, duk dan ki tura mini takaici".

Tayi shiru ta ɗan kalle shi ta ce "Ba faɗa ka ke yi mini ba, komai ka yi ta hantarata"

Ya ce "Ke ki ke yin abin da zan hantarekin ai. Akwai muhimman batutuwa da yakamata muyi discussing, kawai kina wani fushi mara dalili.
Ana ta matsa mini lamba, za ayi posting ɗina wurin aiki, da zarar na kammala aikin da nake yi a kan Indabo, ina son ayi aurenmu dai-dai lokacin da zan tafi aiki"

"Kai da wa?"

"Ni da waye a nan wurin?" Yayi maganar yana tsareta da idanunsa.

"Allah ya baka madadin matarka da ka rasa, ba zan iya aurenka ba Vi, i fulfill my work on you, amma mu bar wannan maganar Please"

Sai da ya nazarceta sannan ya ce "Ƙarya ki ke yi mini da ki ka ce ki na so na kenan?"

Ta ɗan ja da baya, saboda tsoron yadda idanunsa suka fara sauyawa ta ce "Ko ma ya ne, kai ka fara discouraging ɗina, a lokacin da ka yi fatali da tayina, ka ce mini ba wannan maganar, bayan jauhar baka kallon kowace mace. Nima kuma na gamsu da hakan ba zan iya auren mijin 'yar uwata ba. Amma Alhamdilillah na cimma burina a kanka, tun da ka dawo yadda take fata kafin ta mutu".

"Ba kya so na kenan? Ba zaki aure ni ba?" Ta jinjina masa kai, tana kawar da kanta gefe alamar eh.

Juyawa ya yi, ya fara takawa, wayarsa ta fara ringing, ya cirota ya saka a kunnensa ya ce "Na'am"

A razane ya ce "What Walid ɗin? How?"


Ayshercool
08081012143

100
Cike da gigicewa ya ce "Gani nan, kar ka sanar da kowa"

Saboda rikicewa, sai ma ya rasa ina ne hanyar fita, sai daga baya.

Nabila ta ce "Vi menene? Meyafaru?" Bai kulata ba, yana ƙoƙarin fita, Madam Halima ta ce "Au nan ka biyota, na zata tafiya ka yi ai" sai dai yanayin fuskarsa ya nuna mata akwai damuwa.

"Viper menene? Meyake faruwa ne?"

"Walid, gayen nan da muke zuwa da shi, na baro su a gida, ya fita yin refiiling, shi ne bai koma ba, Abdallah ya bi hanya ya tarar da cylinder gas ɗin a gefen hanya, da takalmansa da agogonsa, that means ɗauke shi aka yi" tuni kamanin Viper suka canza, saboda tashin hankali.

Yana ƙoƙarin fita, madam ya ce "Wait Viper, tattara hankalinka ka nutsu, tunani al'amarin nan yake buƙata da nutsuwa, ba gaggawa ba.
Yanzu na san Joseph ya ƙaraso, zai fita da Nabila, ya kai ka ku je a tabattar da abin da yake faruwa, sannan ka kira Oga ka sanar masa da halin da ake ciki" ya jinjina kai ya wuce cikin hanzari ƙirjinsa na bugawa da sauri.

Da sauri Nabila ta ce "Bari na bi shi Mummy, kar ya je yayi wani abun, kin san shi da zuciya da wutar ciki"

"Kya ma gama gulmarki ne daughter, Allah ya bayyana shi cikin aminci" ta amsa da Amin.

Kafin ta ƙarasa har ya riga ya shiga mota, sai da ta haɗa da sauri, sannan ta ƙarasa ta shiga baya, kasancewar gaban motar ya shiga.

Tana shiga ta ji Viper yana waya "Liti kar ka matsa daga wurin, gani nan zuwa, kuma kar ka gaya wa kowa, ka kira wayarsa ne?"

"A gida fa ya manta ta a kan window ya fita"

"Shikenan gani nan zuwa"

"Nabila na ta son tayi masa magana, amma ta san a ƙule yake da ita, dan haka ta ja bakinta ta tsuke"

A haka suka isa dai-dai wurin da liti yake, yana ta buge-bugen waya.

Yana zuwa ya tarar da Liti a hanyar shiga rukunin kamfanunnukan da a bayan su gidan nasu yake, bai taɓa komai ba, yadda ya tarar da takalman walid, da cylinder gas da agogonsa a yashe.

Viper ya yi shiru, yana nazartar wurin, Joseph ma fitowa ya yi, suna dudduba wurin, ya kalli Viper cikin broken English ya ce "Oga, da alama sai da aka yi kokowa da shi kafin a tafi da shi"

Su na nan tsaye Viper yana duba wayarsa, sai ga motar Civil defense sun zo wurin, su ka yi wa Liti tambayoyin da yakamata, suka yi investigation a wurin. Su ka yi ta bawa Viper haƙuri, da ƙoƙarin kwantar masa da hankali.

Jiki a sanyaye Nabila ta ce "Ka yi haƙuri, in sha Allah yana cikin ƙoshin lafiya, bari na tafi"

"Ki shiga mota, mu ajiye ki, zan bi bayan civil defense ɗin nan, na ji me ake ciki"

Ta jinjina masa kai, ta shiga mota suka tafi suka ajiyeta a wurin aiki.

"Idan kin kammala, ko za ki je wani wurin, ki kira ni kar ki fita, i don't think you are safe".

Nabila ta ce "Ok shikenan na gode"

Abu kamar wasa, aka shafe kwana biyu, babu Walid babu ɗuriyarsa, hakan ya ƙara ɗaga hankalin Viper fiye da tunani, tun yana ɓoye-ɓoye, har maganar ta fita, sai da ya sanar da Abbu. Duk da ba wata shaƙuwa tsakanin ta da Walid, amma ta san shi da yayanta, kuma yana nuna damuwa da abin da ya shafe su. Sosai hankalinta ya tashi, Abbu kansa da shi ake ta zarya.
Alhaji mu'azzam ma sai kwantarwa da Viper hankali yake yi, liti ya fi kowa shiga damuwa, dan kuwa har wata irin muguwar rama yayi, a ƙa'ida shi ne yakamata yaje yayi refiiling ɗin, ya tsaya jan jiki, Walid ya zuciya ya tafi ya yo, tsautsayin ya faɗa masa. Duk in da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login