Showing 426001 words to 429000 words out of 479911 words
sha ɗawainiya, dan Allah tun da ka farfaɗo ka saka shi ya ci abinci Please, haryanzu baya mayar da hankali, duk ya rame. Ya fi yi mini kyau lokacin da kumarinsa"
Walid ya ce "Vi an ce ka din ga cin abinci ka rame"
"Zan zageka da kai da Vi ɗin"
"Allah ya baka haƙuri, an hanamu faɗar master, Vi ɗin ma an hanamu, to ai shikenan"
Nabila ta rausayar da kai ta je bayan Viper ta yi ƙasa da murya ta ce "Zamu je ganin likita kar mu makara fa" ɗagowa yayi ya kalleta, kamar ba zai tashi ba, sai kuma ya tashi ya nufi hanyar fita.
Fitarsu ke da wuya ya tsaya cak, ya waiwayo ya kalleta ya ce "Kar ki sake ƙoƙarin yi mini yawo da hankali, ko kuma nuna kin damu da ni, bana son yaudara" yayi maganar yana nunata da yatsansa.
"I don't fake it, kai baka san halin da ka saka ni ba, lokacin da na nuna maka so saboda Allah. Na ji da farko i fake it, daga baya kuma da gaske na ƙaunace ka Vi, yakamata ƙwaƙwalwarka ta tunatar da kai, abubuwan da ka yi mini, kuma ka gaya mini. A gabanka abokinka har ce mini yayi bani da class, ina yawo a cikin maza, duk dan ina sonka, ina fatan daga kaina, zaka din ga kiyaye abin da zaka gaya wa mace, mata bama mantuwa.
Duk motsin da nayi ban taɓa burgeka ba, kullum cikin kyarata ka ke yi, amma haryanzu ina yi maka kallon abu mai muhimmanci a gareni, mussaman kulawar da Jauhar ta samu a wurinka, ka yi mini afuwa Vi, bana fatan ƙuntata zuciyarka".
Cikin tsananin dakiya da jarumta, ya jinjina kai, ya ce "Na fahimta"
Duk yadda ya so cire Nabila daga zuciyarsa abu ya gagara, sai a lokutan nan, da ta fara yi masa wulaƙanci ya ga ashe ya shaƙu da ita, shaƙuwa ba ta wasa ba.
Cikin ikon Allah Walid ya samu kulawa sosai da sosai, gashi ba shi da ƙan jiki, nan da nan jikinsa ya fara warkewa, sai dai ya kan manta da ba shi da lafiya, idan yana riƙe da wayarsa, Shahida tana turo masa saƙonnin, babban abin da ya ƙara yi wa Shahida daɗi, ita kanta kunyarta Walid yake ji, balle yayi kule-kulen mata, saɓanin mijin da ta rabu da shi, saboda yana da kuɗi, yan mata kowa ma kulawa yake yi, kishi kamar ya kasheta, gashi ba abin da yake iya amfana mata.
***
Sallamar da ake ta dokawa a tsakar gida ne, ya sanya dattijon mutumin, sauke farin tabarau ɗin fuskarsa ya ce "Waye ne?"
Ya bankaɗo cikin ɗakin ya ce "Nine, ko har an manta da ni ne, nake ta sallama aka yi shiru?"
Dattijon ya ce "Ina fa, waye ya isa ya manta da sarkin gida? Maraba lale da Abdallah"
Liti ya ƙarasa ya na faɗin "Likkafa ta ci gaba, gida ya sha gyara"
"Yau kai ne a gidan ka tuna da mu kenan?"
"Ai kullum kuna raina, na san ina zuwa dattijuwarka za ta tayar mini da hankali, ta saka ka kore ni"
"Hmm sannu, na samu labarin ɗaya uban naka yayi free, kotu ta wanke shi ko?"
"Aiba shikaɗai ta wanke ba, har mu, ai bamu da wata nutsuwa idan yana cikin damuwa. Ban ga tsohuwar nan ba, ko ta rasu"
"A'a ni uwata ba ta mutu ba, tana nan ƙalau, sun fita da gyatumarka"
Liti ya ce "Lallai ta sha miya, amm Alhaji, dama na zo baƙi ne, wata bazawara ce take so na, shi ne ta turo iyayenta, suka zo nema mata aurena wurinka, tana fatan zaka bata ni"
"Ikon Allah, ita bazawarar"
"Eh, amma dan Allah kar ka yarfa ni, ko ka tona mini asiri ka ce wai ba na ji, abu ne da aka yi shi ya wuce, yanzu na shiryu na daina, dan Allah kar ka ce musu wai bana ji, kaga sirikaina ne"
Alhaji ya yi dariya, ko bayan shekara dubu, Abdallah ba zai canza hali ba,duk da Ya lalace yana son abin sa, amma gwaggo mahaifiyarsa ke nema tayi masa baki, saboda soyayyar da yake yi masa, kuma hakan yana da alaƙa da tsanar da ta yi wa babar litin ya ce "To Baba, ba zan yarfaka ba"
Liti ya fita waje, yayi musu iso, Abbu ne tare da Baba, mahaifin jauhar, da kuma Viper.
Alhaji ganin Liti da manyan mutane, ya tashi ya karɓe su cikin girmamawa. Bai fi sau biyu ya taɓa ganin Viper, yanzu da kyar ya gane shi, saboda lokacin da ya san shi yana da ƙuruciya sosai.
Nan Abbu ya gabatar masa da kansu, tare da gaya musu abin da ya kawo su, a kan yayi haƙuri, ya yafewa Liti, tun da yanzu duk sun watsar da shirirtar da suka yi a baya, dama har da ƙuruciya.
Nan Alhaji yake sanar da su, yadda ya kai liti ƙasar waje karatu, amma ya dawo an koro shi, sai ma shaye-shaye da ya koyo, ga rashin kunya da yake yi wa kakarsa, wanda hakan ya ƙara tunzura shi a kan litin.
Viper ya ce "In sha Allah Alhaji, Abdallah ya shiryu ba zai sake ba, dan Allah ayi mana afuwa, ayi haƙuri"
Alhaji ya ce "Dama baku muke ƙi ba, halayenku ne ba ma so marasa kyau, Ubangiji Allah ya ƙara rufa mana asiri"
Nan kuma hira ta ɓarke a tsakanin su Abbu, tare da tattauna manyan matsalolin da ya jefa yaran nasu ga halaka.
Bayan sun gama da gidan su liti, suna tafe, tausayin Walid ya mamaye zuciyar Viper, su duk sun daidaita da iyayensu, shikuwa ba shi da kowa, sai Allah sai barbaɗaɗɗun danginsa marsa amfani. Yayi Addu'ar Allah ya sa Shahida ta rayu da abokin nasa cikin aminci da mutuntawa, mussaman da ya ga ya fara sakewa da Shahidan.
Maganar Baba ce ta dawo da shi hayyacinsa da ya ce "In sha Allah, gobe zan je gidan Major, mu yi wadda za mu yi, ya bani 'ya ta, na ƙarasa riƙonta na aurar da ita, na fuskanci bai san zuru ba".
Ayshercool
08081012143
101
Abbu ya ce "A'a Alhaji Bashir, abi komai a hankali, zamu je mu same shi sai a tattauna".
"Alhaji Ibrahim, na san na yi wa maitama laifi, amma yadda yayi reacting ban ji daɗin hakan ba. Gaba ɗaya ya tsaya mu fuskanci juna yaƙi, ya mayar da ni kamar maƙiyinsa nima fa a ƙa'ida yayi mini ba dai-dai ba".
Sai a lokacin Viper ya ce "Baba dan Allah ka yi haƙuri ku sasanta, wannan rashin jituwar taku, yana taɓa Nabila sosai da sosai.
Kuma haryanzu tana cikin barrack a zaune, ta rasa yadda ma zata yi dan Allah ku yi haƙuri ku sasanta".
Baba ya ce "Ba ƙi na yi ba Aminullahi, na bashi duk wata dama, a matsayin sa na wanda yake uba a gareta, kuma ya raineta, idan ya gaji ni ya bani abata, nima na rayu da ita ko yaya"
Viper ya ce "Haka ne, kana da gaskiya. Amma ka yi haƙuri dai, a bi komai a sannu, aje a same shi, ayi masa bayani, na san zai fahimta in sha Allah" haka Viper ya ci gaba da rarrashin sa.
Alhaji kuwa hira suka ɗora da Liti, kamar ba barin gida yayi, kusan shekara guda bai ganshi ba. Ya din ga bashi labarin gwagwarmayar da suka sha, da halacci da kirkin matar Viper, tare da ba shi labarin yadda Nabila ta shigo rayuwarsu, ashe 'yar uwar marigayiyya ce.
Sallama aka yi a tsakar gida, Alhaji ya amsa, Liti kuwa ya tsuke fuska.
Sai da mahaifiyarsa tayi turus da ta ganshi, ta ce "Abdallah yau kuma kai ne a gidan"
"Saboda ba sunan babanki bane ba, kuma ba sunan mijinki bane ba, shiyasa ki ke faɗar sunan yadda ki ka ga dama kamar ke ki ka raɗa masa, to sunan mijinki usmanu ki ka faɗa" tsohuwar da suke tare ta yi maganar a hasale.
Ta mayar da idonta kan liti ta ce "Sannu ɗan nema, kai kuma sai yau Allah ya dawo da kai, shanshani mai ƙafar gantali"
"An saka mini sunan kirki, saboda wani sunan mijinki, kin ɓata mini suna wani liti. Kuma nan fa ke ki ka saka aka koreni, ba dole na tafi ba, ni wallahi na zata ma kin mutu"
"Salamatu ce zata mutu ba ni ba, babarka ba"
"Kowa ma dai sai ya mutun nan, duk ƙulafucin mutum da duniyar kuwa"
Alhaji ya yi gyaran murya ya ce "Baba gwaggo ce fa, mahaifiyata ce" liti yayi shiru yana hararta.
Mahifiyrsa kuwa kallonsa take yi, ta zata tafiyar da yayi, zai sake lalacewa ne, dan abin yana damunta, amma sai ta ga kamar ya ɗan nutsu, babu askin banza, gashi normal shiga yayi, kuma babu alamar buguwa a tattare da shi.
Har yamma yan tare da mahaifinsa, saboda ya fi shaƙuwa da shi, yan uwansa duk mata ne suna gidan aure, shi ne kawai namiji.
Da yamma aka gama abincin dare, aka zuba masa, ya saka fulasan a leda ya ce tafiya zai yi.
Alhaji ya ce "Ina kuma zaka je?"
"Can in da nake mana Aljaji"
"Au sake barin gidan zaka yi?"
Liti ya ce "A'a, dama zuwa nayi ai na gani, idan zaku haƙura ku yafe mini to, idan kuma naga za a sake tozarta ni, idan na cika wandona da iska nayi gaba, in tafi ikko. Amma Alhamdilillah na ji daɗi da naga ba a hantare ni an koreni ba, wurin yan uwana zan koma, Walid ba shi da lafiya yana Asibiti, ni nake kwana da shi, amma zan dawo ai. Na gode sosai da ku ka yafe mini"
"Dama ba tsanarka muka yi ba babana, halayen da ka ke yi ne bama so, amm Alhamdilillah daga kai har uban ɗakin naka, naga nutsuwa a tattare da ku, Allah ya ƙara shirya mana ku"
"Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, na gode sosai da sosai Alhaji"
Alhaji ya ce "Jeka Allah ya bayar da sa'a" ya amsa da Amin.
Gwaggo ta fara masifa ta ce "Au barinsa zaka yi ya tafi? Kana kallonsa?"
"Gwaggo ki yi haƙuri dan Allah, ba kowane lokaci ƙarfi da fushi yake amfani a wurin tarbiyya ba, wasu lokutan rarrashi da addu'a suke buƙata.
Yanzu barin gidan da yayi, ba wai hakan ne ya saka ya ɗan nutsu ba, addu'a ce kawai, kina ji da tasirin wata yarinya a rayuwar abokinsu"
"To shi ma ayi masa auren mana, tun da ya fara tsufa yana shashanci"
Ficewa Liti yayi, dan idan ya biye mata, lokuta da dama a baya lokacin yana kan ganiyar shaye-shaye, ya sha yinƙurin ɗura mata ashariya, ko kuma ya sureta ya buga da ƙasa, saboda a cewarsa tana yi masa shishishigi da munafunci.
*****
Saƙo ne ya riski Naja'atu Bunkure, a kan cewar ma'aikatar Shari'a ta soke lasisinta, har sai an kammala bincike a kanta.
Hankalinta yayi mummunan tashi, ta kira Indabo a waya cikin tashin hankali, yana ɗagawa ya ce "Ya kuma aka yi?"
"An soke lasisina daga ma'aikatar shari'a, wai sai an kammala bincike a kaina, dama ba ta janye ɗin ba?"
"Kuma dai? Ta janye ƙarar fa, sai da na tabattar da hakan, kuma yanzu nima nake samun labarin wannan shegen yaron da na saka a kashe, dan ya ƙara zama jan kunne ga Vipern, bai mutu ba, wai yana raye a asibiti"
"To ni ina ruwana, licensed ɗi na fa aka yi siezing, wane irin abu ne wannan, duk wahalar da na sha kafin na zo wannan gaɓar, sai da na kai ƙololuwa sannan zan yi faɗuwar baƙar tasa, wannan mummunan ƙarshen, wallahi ba zai yiwu ba"
"Ki yi haƙuri ki daidaita nutsuwar ki, zan san abin yi, ki yi haƙuri ai hakan ba zai yiwu ba sam" kashe wayar tayi, tana jin yadda kanta yayi mata wani irin mugun nauyi, ta ma rasa me za ta yi ko ta ce gaba ɗaya.
***
Walid jiki yayi kyau sosai, Viper yana gefensa yana yi masa magana, amma hankalinsa yana kan wayarsa da yake dannawa da hannu ɗaya.
"Ɗan marayan zakina, ya jiki, ina son na zo na ƙara dubaka, amma ina jin kunyar yaya, kuma ga mama babu lafiya ita ma"
"Kar ki damu, ina samun saƙon gaisuwarki ai, jiki Alhamdilillah da sauƙi"
"Allah ya ƙara tsare mini kai"
"Amin ke ma haka"
"Amma Yaya ya gaya maka na taɓa aure, har shekara uku?"
Walid yayi mata reply da"Har ɗaurin aurenki mun je ni da Walid a madadinsa a lokacin yana tsare a gidan yari"
"Lallai kun cika abokan amana, ina son abotarku. Amma kana ganin babu ƙwara a ciki, kaga kai ba ka taɓa aure ba, ni kuma na taɓa"
Walid ya ce "Ko kaɗan, Viper ba zai haɗani da abin da ya san akwai cutuwa ba, kuma ni ba wannan nake dubawa ba, nima kin san irin rayuwar da muka yi a baya, kuma ni ba wani mai ƙarfi bane ba, buga-buga ce dai muke yin ta, amma kin ga ke kuma 'yar gayu ce, matar manya ce, ina fatan hakan ba zai zama da shiga hakkinki ba"
Voice message ta yi masa, ya rage volume yana saurara ta ce "Babu wannan maganar, ni kawai sonake nima ka so ni kamar yadda ka ke son Yaya Al'amin, ka ji my, Allah ya sa kai nawa ne nikaɗai, kuma ka daina ce mini Shahida gaskiya, sunan soyayya zaka samo mini nima" ta ƙarasa maganar tana dariya, dan ta san ƙarshenta, sauka zai yi daga online ɗin.
Aikuwa haka yi, ya rufe data yana murmushi, sai suka yi ido huɗu da Viper, da ya gaji da magana ya zuba masa ido, sai yayi sauri ya ajiye wayar yana ɓoyeta kamar yayi rashin gaskiya.
Viper ya ce "Wai me ka ke yi a cikin wayar ne?"
"Tilawa" yayi maganar yana mazewa.
"A'a karatun kalaman da tayi maka kake yi wa tilawa kenan, ai fa Walid an fara soyayya babu sarki sai Allah, muna zaman zamanmu Viper ka saita masa hanya, yake ta zaƙewa"
Viper ya ce "Ai naga alama, me take gaya maka ne har haka?"
Liti yayi farat ya ce "Wai ɗan marayan zaki, wani gursumemen gardi, kwana yake yana murmushi"
Viper ya yi murmushi ya ce "Na ji daɗin hakan sosai, ɗan uwana na cikin farinciki, Allah ya tabattar mana da alkhairi. Kai kuma goga wa zaka samo mana ne mu aura maka?"
Liti ya ce "Mhmm, wani zance mara amfani tsohuwar nan ta gidanmu take yi, da na lalace cewa tayi a koreni, Alhajinmu yana sangarta ni, saboda ba ta son uwata. Amma akwai jikarta da take son uwatta, ta gama lalacewa yarinyar nan na girmeta, amma saboda tsabar yawo da gantalin bin maza, duk ta fara tsufa wai a haɗamu aure"
Viper ya ce "A'uzubilalimatillahi"
Walid ya ce "To meye a ciki, ku rufa wa juna asiri shikenan"
"Wa za a rufa wa asirin? Wallahi da budurcina ba zan auri lalattaciya ba, ta gama bayar da free services a kwararo ba, Allah ya kiyaye"
"Walid ya ce "A gidan uwar wa ka ke da wani budurci, mace ne kai? Kai ma fa a lalacen nan kake, shaida ɗaya zan yi maka bama kula 'yar kowa"
Ya ce "Yauwwa to barka, a bar ni da ɓalla ƙarafa da caji, amma banda shashanci, dama aure ta taɓa yi da sauƙi, amma ta gama gantali wai a bani, kai tsohuwar nan ba ta ƙaunata"
Viper sai da yayi dariya, jin yadda liti yake ta ɓaro zance.
Tashi ya yi ya fita, yana son ganin Nabila sosai da sosai, amma ya fara tsorata da abubuwan da take yi masa, ya kasa gane da gaske take yi ba ta son shi, ko kuwa dai kawai rigima ce irin ta ta.
Wayarta ya kira, sai dai sai da ya fara harzuƙa sannan ta ɗaga, murya ƙasa-ƙasa ta yi masa sallama.
"Kina ina?"
"Na je gidanmu ne"
"Meyasa ki ka fita? Ban gaya miki kina cikin barazanar rashin tsaro ba?"
A hankali ta ce "Joseph ne fa ya kai ni" tayi maganar kamar a shagwaɓe.
"Meyafaru muryarki tayi ƙasa?"
Nabila ta ce "Bana jin daɗi ne, bani da lafiya"
"Meyafaru?" Ya faɗa kamar an yi masa dole.
"Ka san an yi ƙura ne jiya, ina ta fama da tari, ban yi bacci ba sosai, sai kuma na tashi da ciwon kai"
Ya ɗan lumshe idanunsa ya ce "Asibiti fa?"
"Na sha magani a gida, zan kai rahama awo gobe in Allah ya kaimu zan ga likita daga nan"
Ya ce "Ok take care, idan da wani abu let me know"
Ta ce "Ok na gode sosai, a gaida Oga walid"
Ta ajiye wayar tana jin wani iri a jikinta, tunani take yi, ko ya daina sonta ne, ya ajiye maganarta a gefe kamar yadda ta nema?.
Shi ma sauke wayar ya yi, yana jin yayi kewar rigima da shagwaɓarta, kenan da gaske dai ba ta son sa kenan? Bai taɓa tunanin idan yayi mata maganar aurensu, za ta ce ba zata aure shi ba.
****
Ramma ciki ya tsufa sosai, kullum cikin lissafi take, yaushe Abdul zai fito, gashi sati huɗu ake bata a wurin awo, wani abun tana ji tana gani, tana so, amma babu yadda ta iya, sai dai ta haƙura tayi shiru. Saboda tana tsoron tayi wani abun mama ta hantareta, dan sam ba ta ƙaunar cikin nan.
Ramma ta san da Abdul ba a tsare yake ba, da zata ga gata da kulawa, amma tana matuƙar jin daɗin yadda Nabila take nuna mata kulawa da damuwa da ita da sumayya.
Yau bayan ta kai ta awo, suka biya aka yi sayyayar kayan haihuwa.
Daga nan ta kaita wurin Abdul, yau ma kamar kar su rabu, sauransa wata ɗaya ne ya fito daga prison, bakin ramma har kunne saboda murna.
Washegari da yamma, Alhaji mu'azzam ya zo gidan, mama ta karɓe shi, kamar yadda ta saba har take tambayarsa yaushe za su koma ƙauye, sun zo sun zaune masa a gida.
Ya ce "Haba Hajiya, ai kin girmi rayuwar ƙauye yanzu, ko dan asirin rahama, ba zaku koma ƙauye ba, kema kuma ina fatan Allah ya baki mijin aure, kema ki yi aurenki a nan birni ki huta".
Maman ramma ta ce "Ashha, ga 'ya har da tsohon ciki nayi aure, ai aure kuma yanzu sai dai naga ana yi wanda nayi Allah ya sanya albarka"
Alhaji mu'azzam ya ce "Saboda me, shekarunki nawa ne?"
"Na kusa arba'in idan ma ban yi ba, tun ina shekara sha uku aka yi mini aure"
"Kuma ki ce kin wuce aure, a'a ai aure garkuwa ne"
Yayi waya aka shigo masa da wata shirgegiyar akwati, ya saka aka kirawo masa ramma.
Ya ce "Sannu rahama, kin kusa shiga watan haihuwa ko?" Ta bashi amsa tana sunkuyar da kai ƙasa.
"Babu wata matsala dai ko? Nabila na kai ki awo,