Showing 330001 words to 333000 words out of 479911 words
munafunci ka ke yi, amma kuwa ka yi asara dan wannan ba aikin yi bane ba, kuma saboda tsabar ƙwarewa, ko da wasa baka taɓa gaya mana ba. Ni dama na daɗe ina zargin baka da gaskiya"
****
Miƙa tayi sosai tana addu'a, ta ji kamar gadon da take kai, ya sha bamban da wanda ta kwanta a kai, ta tashi zaune a hankali, ta ganta a cikin wani katafaren bedroom, bisa wani ƙaton gado.
Tayi tsuru da ido, tana tunanin ko mutuwa tayi.
Wata mata ce tayi sallama, ta ce "Kin tashi? Ga banɗaki nan idan zaki yi alwala ki yi wanka ki rama sallolin da ake binki".
Nabila ta ce "Ina ne nan baiwar Allah? Ko mutuwa nayi ne?"
Matar ta ce "A'a, wanda suka kawo ki, zasu zo su yi miki bayani, ga kaya nan ko zaki canza".
Ta tashi a hankali tana addu'a, ta shiga banɗakin, ta yi wanka, ta yi alwala, ta fito ta din ga salloli, daga iya abin da ta iya tunawa, ga wata irin yunwa tana ji, gaba ɗaya ta kasa tantance meyake faruwa gaba ɗaya.
Matar ta dawo, ta kawo mata abinci, amma Nabila ba ta taɓa ba, ta takure a gefe.
Viper ne ya shigo, ta ɗago kai ta ƙura masa ido, har ya ƙarasa gabanta, ya zauna ya ce "Sannu, ya jikin?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Kamar nayi kuskuren yinƙurin taimaka wa rayuwarka, kana ƙoƙarin rusa tawa, ta hanyar ganin ka haukata ni, me nayi maka haka? Kuma ina ka kawo ni nan?"
"Ba ki yi kuskure ba, domin kuwa kin yi sara ne a kan gaɓa, kuma zaki alfahari da ƙaddarar da ta haɗa ni da ke"
"In yi alfahari bayan na haukace ko?"
Viper ya girgiza kai ya ce "Ba zaki haukace ba, tambayoyin da nayi miki, haryanzu nima ina buƙatar samun amsarki, sai dai bani da tabbacin samun amsarsu duka.
Amma bari mu gani, ko a cikin abin da zan gaya miki zamu gano bakin zaren, rayuwata kamar ƙwallon ƙafa take, daga wannan ƙafa zuwa wancan, daga wannan tudu zuwa wancan rami.
A haƙiƙanin gaskiya, ban yi shekaru biyar a gidan yari ba". Nabila ta waro ido tana kallonsa.
"Nayi zaman gidan yari, cikin tsananin razani, cikin matsananciyar damuwa da ƙuncin zuciya, tare da fatan Allah ya sa da an mayar da ni kotu, a yanke mini hukuncin kisa, na huta, amma ranar da aka saka a cigaba da shari'ar ta wuce ba a cigaba ba.
Azaba da wahalar da nake sha a gidan, bai ɗaga mini hankali ba, kamar yadda halin da nake ciki, bai hana wasu din ga ƙoƙarin nemana da mummunar ɗabi'a ta neman maza ba, ciki har da ma'aikatan wurin.
Abin da su madaki suka yi amfani da shi suka shaƙa mini, ya cigaba da affecting ɗina.
Azaba da takura, ya sa na zame musu mahaukaci, na danne wanda suke cewa sarkin gida, na kusa janyo maƙogwaronsa waje, nayi masa dukan mutuwa, saboda sun zata dolo ne ni, duk da sun san labarin waye ni, prsion ɗin ta sha banban da wadda ake kaini.
Suka ajiyeni a wani wuri, suka din ga gana mini azaba, wai nayi yinƙurin yin kisan kai, ba wanda ya duba abin da ya neme ni da shi. Aka ajiyeni, babu wanka, babu wanki, babu ci babu sha, sai azabar duka. Wurin ga ƙazanta da rashin tsabta, a haka kuma a kan fito da ni, ace za a saka ni aikin wahala.
A halin da nake ciki, na tsinci wani ɗan ƙarfe, da zai iya zama makami, na farwa wani, dan fuskar madaki na gani, sai da aka ƙwace shi da kyar, na huda masa wuya, sannan naga ashe ba shi bane ba, ƙwaƙwalwa ta ce ta fara samun matsala, banda kururuwar da nake yi wasu lokutan, ina kiran matata da ɗa na, tare da alwashin kashe madaki. Aka rabani da sauran fursunoni, aka ce na haukace.
Watarana, cikin dare ina kwance, na san idona biyu, amma bakomai nake ganewa ba, fatana na farka daga baccin da nake yi, na ganni tare da matata.
Kawai wani mutum ya saka mukulli ya buɗe in da nake, ya fara lalubena, duk a galabaice nake, kwana uku ba abin da aka bani na ci, sai na tsaya naga me zai yi mini, kar nayi masa wani abun, na je ƙwaƙwalwata ce take gaya mini shirme, kamar yadda ta saba. Sai na ji bai nufi yi mini lalata ba, kawai ya soka mini wani abu, kamar allura a cinyata, ya fara zuba mini wani abu mai tsananin zafi a jikina, ruwan allurar na shiga, ina jin kamar ana fizgar naman jikina, a take na kurma ihu, na tashi na shaƙe shi, ina dukansa, ina cewa shi ya kashe jauhar, sai na kashe shi. Ina dukansa jikina yana ƙara sanyi, kamar ana zare mini laka.
Aka zo aka raba ni da shi, nayi masa jina-jina, ni kuma na faɗi a wurin, basu bi ta kaina ba, suka fice da wancan. Ina kwance na ji wani abu mai sanyi na bin hancina, a taƙaice dai, kasheni yayi yinƙurin yi mutumin.
Washegari ina kwance kamar gawa, ina jin duk abin da ake yi, amma ba zan iya motsi ko magana ba, aka ɗauke ni, aka ce za a kai ni Asibiti, ayi mini magani, ashe wasa farin girki, maimakon a kaini asibiti, sai aka yi wani wurin da ni.......
Ayshercool
08081012143
79
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
"Bana iya gane ina ake, saboda a matuƙar galabaice nake, amma naji a jikina, yakamata ace idan asibiti ne ya ci ace an je, duk da bana sanya ran zan rayu, a maganar da mutanen motar suke yi, jini nake ta fitarwa ta hancinca, ga azabar yunwa da datti, na gidan yari, tufafina tamkar mahaukaci, dan a mazaunin da aka ajiyeni kenan.
Aka yi parking ɗin motar, aka canza mini wata, wadda nake kyautata zaton ambulance ce, dan a ciki aka toshe hancina da bandeji, saboda jinin da nake zubarwa, aka saka mini ruwa, muka cigaba da tafiya. Tun ina jin maganganun da ake yi a motar, tafiya taƙi ci taƙi cinyewa, har na daina gane komai, na buɗe ido na ganni a wani wuri, a kan gadon asibiti, an tuɓe kayan jikina, sai gajeren wando, na tashi a gigice cikin matsananciyar kiɗima, ina ihu saboda ban san meyafaru da ni ba, na farka ina zaton zan ga madaki da jauhar, ina hana shi cutar da ita, wani ɓangaren ina tunanin ko ina prison ne, wani yayi galaba a kaina. Sai dai na ji ni a ɗaure da ankwa dukka hannayena, na din ga ihu saboda yadda naman jikina yake yi mini wani irin azababben zugi, kamar ba zan rayu ba.
Wasu mutane da ban san suwaye ba, suka zo kaina, da allurai suka yi mini, ɗaya daga cikin su ya ce "A cigaba da kula da shi mu gani, will he survive the poison, duk yadda zaku yi, ku yi ƙoƙarin ceton rayuwar sa" haka na sake fita hayyacina na farka, sai dai a wannan karon, ban ji wannan raɗaɗin ba.
Aka cire mini ankwa, aka tashe ni zaune, aka kawo mini abinci, kamar mayunwacin kare, haka na dirarwa abincin nan, kamar zan haɗa da kwanon saboda yunwa, ina ci ina jin kamar ana yayyanaka kayan cikina da wuƙa, amma azabar yunwar da nake ji, ya sanya naƙi daina ci, sai dai ban gama ci ba na din ga amai, haɗe da jini, wai duk cikin side effect ɗin allura da aka yi mini ne, kashe ni aka so ayi.
Ba a sake bani abinci ba, sai ƙarin ruwa da allurai, mutanen wurin ba kowa ke jin hausa ba, ni kuma bana magana, suna bani damar yin salla, aka fara koya mini cin abinci.
Ba wanda na tambaya dalilin kai ni wurin nan, kuma babu wanda yayi mini bayani, a haka har na shafe wata guda cif.
Duk yadda suka so nayi magana, bana yi, sai dai wasu lokutan ina rasa tunanina, na din ga ganin madaki da jauhar a zahiri, na din ga yinƙurin shaƙe duk wanda yake kusa da ni. Sai da na ɗan samu nutsuwa, aka aske mini gemuna da sumar kaina gaba ɗaya, aka kuma saka mini ankwa, aka rufe mini ido, aka sakani a mota, aka bar wurin da ni.
Wani wurin aka sake kai ni, mu huɗu ne a wurin, kowa da wurin da ake ajiye shi tamkar ceil. Na fauskanci nikaɗai ne musulmi babu bahaushe, sai ƙabilu, kullum bayan nayi sallar asuba, da sassafe haka za a kaimu wani wuri, ana bamu training na azabatarwa, wanda ka iya zama ajalin mutum.
Idan muka gama, zamu saka wasu riguna, masu tambarin dragon, za a kaimu wani wuri, in da ake bamu darasi, malamanmu turawa ne, class ɗin mu huɗun nan ne, kowa da computer sa, ayi mana darasi ta online. Waɗanda suke kula da mu, wasu irin zaratan ƙartin sojoji ne, sun kai su goma sha biyu, a kan mu huɗu kawai.
Azaba ta ishe ni, ban ga alamar za a mayar da ni gida ba, na gaji, gaba ɗaya na rasa ina rayuwata ta dosa, bani da wani burin da ya wuce na mutu na huta. Za a bamu abinci mai kyau, a bamu abin sha mai kyau, amma azabar da ake mana ta ishe ni. Wataran ana tsaka da bamu training, na fizgi bindigar wani, nayi yinƙurin kashe kaina, suka riƙe ni, aka ɗauke ni aka kai ni wani ɗaki, da ban zaci zan fito da rai ba. Sai da na kwana bakwai a ɗakin, ko class bana zuwa. Ranar na takwas, ogansu ya zo ya same ni, yake tambayata meye matsalata na yi yinƙurin kashe kaina.
Na ce masa su mayar da ni garinmu, ina son ganin matata.
Ya ce mini muddin ina son komawa gida, sai na basu haɗin kai, na yi wa ƙasata aiki, sun san ni yaron dodo ne, kuma akwai amfanin da zan yi musu, dan haka dole na mayar da hankali a kan training da kuma karatun da nake yi, kuɗi aka ware masu nauyi, saboda mu yi wannan karatun.
Na ce ni ba zan yi ba, su kasheni kawai su daina wahalar da rayuwata.
Ya ce ba zasu kashe ni ba, in yi abin da suka umarceni, idan ina son na ga matata. Sai na tambaye shi, matata na raye? Ya ce tana raye, zan ganta idan na daina taurin kai, nayi abin da ake so. Kuma ko ina so ko bana so, ubangidana ne ya nema mini wannan aikin, tun kan ya mutu, dan haka sai dai na mutu a process ɗin, tun da na san sirruka masu muhimmanci da zasu taimaki ƙasa. Na din ga tunanin, wane irin laifi na yi wa dodo, zai zaɓa mini wannan azabar, sai dai tsananin ɗoki, da daɗin bakin zan ga matata, ya sanya na saduda, gashi suka saka mini ido sosai da sosai, saboda suna iƙirarin bani da lafiyar ƙwaƙwalwa, kuma bana ji.
Wata makaranta muke yi a russia, ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa kawai ake bamu, duk da na san abubuwa da yawa ni, ta online muke makarantar, a training ɗin nan aka koya mana duk wani nau'i na haɗawa da wargaza bindiga, ilimin makamai, leƙen asiri, da duk wani nau'i na abin da ya shafi harkar tsaro.
Suka ce mini ƙwazona, shi zai bayar da damar komawata garinmu, har naga matata, na roƙe su ko a waya, a haɗani da matata tun da sun ce tana raye, suka ce ba zasu haɗamu ba, zan ɓata musu aiki.
Na zage damtse, lokutan jarrabawa, ina cikin overollers, ina tashi da points masu kyau, na fara sabawa da wahalar training, jikina duk ya murɗe, sai dai babbar matsalata bana cikakken bacci, bana iya bacci, da na rufe idona, zan ganni a falo, tare da jauhar madaki zai kasheta, gaba ɗaya sai na tubure musu, na hau ihu. Ko abincin da nake ci, bana cin sa ta daɗin rai, saboda damuwa da tunani. Abokan karatuna a kan basu damar shan giya, har mata a kan kawo musu, amma ni duk ba wannan a gabana.
Tun ina lissafi da sanya ran ƙarewar wannan wahala, naga babu rana babu wata, na zauna nayi tunani, babu yadda za ayi, jauhar na raye a gurfanar da ni a gaban kotu, a tuhume ni da laifin kisan kai, naga kawai raina mini hankali suke yi, sai kuma wata zuciyar ta ce mini ai mafarki nake yi, sai dai na rasa wanne ne mafarkin wanne ne zahirin?.
A haka na shafe shekaru a wurin nan, ban taɓa barin kewayen in da muke ba, na rayu da matsanancin ƙunci da damuwa a zuciyata, wasu lokutan sai an yi mini allurar bacci nake iyawa.
A haka muka kammala karatu, sauran ukun aka ce, za ayi posting ɗin su, in da ake son su gabatar da ayyukansu, ni kuma sai an yi settling issue ɗina. Mun zama sojojin leƙen asiri.
Ni dai jinsu kawai na din ga yi, sauran suka din ga murna, aka shirya mana walima, sauran duk sun saba da su, ni duk yadda aka so ja na a jiki, a yi raha da ni, a saba ban yadda ba, dan ni kaina na san rabi mai hankali rabi mahaukaci nake. Abokan karatuna kuwa, basa shiga harkata, dan duk lokacin da ƙwaƙwalwa ta ta haska mini fuskar madaki, a jikin ɗaya, sai na kusa kashe shi, dan duk da training ɗin da aka bamu, na fi su ƙarfi nesa ba kusa ba, kuma ba addinmu ɗaya ba, ba ƙabilarmu ɗaya ba.
Sai da na ji haushin dodo, duk da baya raye, na ji ya sakani a masifa, duk da ina fatan sanya indabo, biyan bashin abin da ya aikata ciki har da kisan dodo.
Ana gobe za a mayar da ni kano, ina ta murna zan koma naga jauhar, naga ɗana, dan na san a lokacin ya yi wayo, ban san meyafaru ba, ko me suka yi mini ba, sai farkawa nayi, na ganni a prison. Hakan ya ƙara burkita ƙwaƙwalwa ta, na fara tunanin wani mafarkin na kuma yi, na din ga kiran sunayen shugabbaninmu da suka bamu training, ina cewa su zo su cika mini alƙawarin da suka yi mini, su haɗa ni da jauhar ɗina da ɗana kamar yadda suka yi mini alƙawari, gashi ko za a kashe ni, ban san sunan garin da aka kaini ba.
Gandirobobi, suka yi mini dukan tsiya, wai na cika musu kunne da hauka, matar da na kashe da hannuna, bayan na sha na bugu, na amsa hakan a kotu, yanzu kuma na zo na ishe su da shirme. Suka yi mini dukan tsiya, amma na kasa daina kururuwar kiran sunaye da magiyar su haɗani da jauhar, gaba ɗaya na zama mahaukaci, ni kaina a lokacin na yadda ni mahaukaci ne. Wasu lokutan idan na buɗe jikina, ina ganin tabon raunuka da wahalar da na sha a wancan garin, amma fafur aka nuna hauka nake yi, da sambatun ƙarya.
Tun da suka tabattar mini ni na kashe jauhar, na ƙara rasa tunanina, damuwa da tashin hankali suka koma sabbi fil.
Kusan watanni uku, cikin dare ina kwance, dama ɗakina daban, aka tashe ni aka ce na fito, na fita na bi bayan wanda suka kira ni, aka fitar da ni wajen gate, wai an karɓi court order na tafi.
Na tsaya ina kallonsu, ina mamakin wane mafarkin kuma na sake shigowa, suka rufe gate ɗin prsion ɗin, suka bar ni a tsaye.
Zuciyata ta raya mini maza kafin na farka daga baccin, na je na ga jauhar, ko zan farka dai na ganta.
Na fara tafiya a duhun nan, har garin Allah ya waye. rana ta ɗaga, na isa unguwar mu, ban manta hanya ba. Sai dai Abbu ya tabattar mini da jauhar ta mutu, ni na kasheta, na tafi na bar masa gida.
Mutanen unguwa suka din ga kallona, har da masu gudu.
Babu tunanin komai ko tsoro, bayan na je dabarmu, su Walid suka karɓe ni, suka kuma tabattar mini da cewar na rasa Jauhar.
Na burkice musu, amma suka riƙe ni suna kula da ni, kawai sai ga sanarwa daga hukumar 'yan sanda, wai a kamo ni, a raye ko a mace, da fari suka ce na gudu daga prsion, daga baya kuma wai an sake ni ba bisa ƙa'ida ba.
Walid ya ce "Kome za ayi, ba zasu yadda a sake mayar da ni a kulle ba, sun san ba zan taɓa kashe 'yar madara ba.
Na tarar da su da ɗan mama, na san shi tun da na taɓa yi masa rauni, shi ne ya bayar da gidan da muke zaune muke ɓoye.
Idan nayi kamar na gaya musu, rayuwar da nayi ana bani training, sai na tuna aikin sirri ne, an gargaɗemu a kan haka, kuma bani da evidence ni kaina bani da tabbacin cewa a gaske nayi wannan rayuwar.
Bana iya bacci, bana iya cin abinci, ga azababben ciwon kai, ga nauyin ƙirji, kawai na koma shaye-shaye fiye da da, duk da a wurin training ina shan sigari da wiwi, sai dai bana shan miyagun ƙwayoyi, ko giya.
Amma bayan tabattar da mutuwar jauhar, na cigaba da shaye-shaye ina fatan ko haukacewa nayi, na manta da duk wata rayuwa, wadda nake tunanin gaske ce ko mafarki, amma kayan cajin basa ɗaukata.
Ganin ɗan mama na din ga yi tamkar Nura, dan ba zai fi sa'ansa ba, ya din ga yi mini biyayya, hakan ya sanya nake son sa sosai, saboda su Walid kullum cikin faɗa muke, suna hana ni shaye-shaye.
Shi kuwa samowa yake yi ya kawo mini, a hakan idan na bushi iska, sai na tafi gidana na dura ta katanga, na kan yi iya ƙoƙarina nayi kuka, amma bana iyawa, sai dai na yi ta jin ƙunar rai da bugun zuciya.
Na kan yi yinƙurin zuwa na ɗauki fansar abin da madaki yayi mini, amma su Walid su hana ni, suka samo mini waya keypad suka bani incase ina buƙatar wani abu, basa nan, ɗan mama shi yake yi mini duk wata hidima, kawai wannan mutumin ya fara kirana, yana ƙara dagula mini lissafi. Kayan shaye-shayen ya zama basa ɗaukata, sai dai nayi ta tamɓele, suna iya ƙoƙarin su a