Showing 279001 words to 282000 words out of 479911 words

Chapter 94 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6119

da bakina, ba wasa nake yi maka ba, da fari wasa nake yi, amma yanzu ya zame mini gaske, ban taɓa tunanin zan iya cewa wani namiji ina son shi ba, amma kai naga kamar nutsuwar ka ta kai na gaya maka"

Ya ce "A'a karki yaudari kanki, wace nutsuwa nake da ita?"

"Rauninka mutane kawai ke iya gani, ni kuma nagartarka nake gani, kamar kai ne zaka zama dai-dai da ƙaddarata"

Wani abu ya ji yana nema ya rinjayi zuciyarsa, mussman da ya fara ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila tana kuka.

Cikin ƙarfin hali, yayi ta'awizi ya kaurara muryarsa cikin tsare gida ya ce "Jauhar ɗaya ce, kuma na sameta ta suɓuce mini, babu wata mace da zata iya maye mini gurbinta, sanya wata macen a zuciyata tamkar cin amanar 'yar madara ne, a kanta na gama soyyaya, kuma na gama aure, dan haka kar ki ƙara yi mini wannan maganar, ki nemi wani ki aura, wanda iyayenki za su yi alfahari da ke da shi, jauhar ma ƙaddara ce ta saka aka bani ita"

Ta share hawayenta ta ce "Nabila mace ce mai aji, aji ma na gaske, ban taɓa mafarkin fara furtawa wani namiji ina son shi ba, raunin macen kenan, daga tausayi na faɗa sonka ban shirya ba, kai banda ƙaddara da haɗin Allah, me zai kai mace kamata yin kasada da rayuwata kamar wata wawuya ina nemanka ina zaman zamana?.
Sannan ka sani idan akwai macen da nagartarta zai hana a auri wata mace bayan wafatinta, to Sayyada Khadijah ce Allah ya ƙara mata yadda, kuma idan akwai macen da soyyayar da ake yi mata, zai hana ayi mata abokiyar zama, to sayyada Aisha ce radiyallahu anha.
Baka san wace damuwar ce a raina ba, ka zaɓi ka yi mini haka, ko baka so na, ba haka yakamata ka yi mini ba, bani mukullin motata na tafi" tayi maganar tana kuka tare da miƙa masa hannu.

Kallonta kawai yake yi, babu in da ta bar 'yar madara a kamanni, hatta kukan nan da take yi, jauhar kawai yake gani, sai dai Nabila ta fi jauhar murya, da kilewa kuma ita mafaɗaciya ce.

Loosing control ɗin sa ya kusa yi, da zuciyar sa take raya masa, ya rungumeta ya rarrasheta, sannan ya ji menene damuwarta, fizge mukullin motar tayi, ta ƙara gaba tana kuka.



Ayshercool
08081012143

67
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Cikin zafin nama ta juya tana kuka, ta nufi hanyar barin wurin, har ya ɗaga ƙafa da niyyar ya bi ta, sai kuma ya fasa, dan idan ya bita bai san me zai ce mata ba, yana kallonta ta hau motarta ta bar wurin.

Bashi da zaɓin da ya wuce shi ma ya bar wurin, sai dai ya tafi zuciyarsa cike da wasi-wasi, ko cikin duhu aka tara mata dubu, zai cire 'yar madararsa, amma haryanzu ya kasa gane dalilin da ya sanya Nabila take kama da jauhar, ba kuma wai kama sama-sama baz kamannin ne tamkar an raba kara biyu.

Ya cigaba da takawa a hankali ya bar wurin.

***
"Indabo ina fatan ka saurari program ɗin da wannan sheɗanun yaran suka gabatar, ka shirya ɗaukar mataki ne, ko kuma ni na ɗauka da kaina? Na gaya maka ba zan bari wahalata ta shekaru ta tafi a banza ba, in ƙare a lalace, ƙaramar yarinya ta rusa ni ba, ko dai ka saka a dakatar da program ɗin nan, ayi abun da ya dace a kanta, ko kuma ni zan ɗauki matakin abun da ya dace"

Indabo ya kalleta ya ce "Naja, wai yaushe ki ka zama haka ne? Duk wata matsala tare muke magance ta, amma wannan sai nema ki ke yi ki zame, ba fa wata babbar matsala bace ba"

"A wurinka ne ba babbar matsala ba, kuma ƙaramar matsala ita ce take zama babba. Kana jin manyan lauyoyin nan da basu samu dama a kaina ba da, yanzu sun samu suna ta bata goyon baya, mutane sun fara farga da abun da take yi, ni na rasa wai waye uban ɗakinta ne waye ya tsaya mata?"

Ya numfasa ya ce "Kankarofi ne"

"What? Kankarofi kuma? Meya kawo shi cikin wannan maganar?"

"So yake lallai sai ya ga bayana, ya rama abun da ya faru a baya, maimakon ya rama a siyasance, ba ta haka yake son yi ba, so yake lallai sai na tozarta"

Naja ta ce "Ikon Allah, to menene ribarsa, alhalin kuna sirikai?"

"Aurenma da ya auri jidda, duk cikin plan ne na siyasa, kin san ita siyasa babu maƙiyi na dindindin, kuma babu masoyi na dindindin, mun zauna jam'iyya ɗaya da shi a baya kamar yadda na taɓa gaya miki. A lokacin nan mutane suna matuƙar sonsa, duk da ba wani babba bane ba, kuma naga take-taken ana kiransa ya fito takarar kujerar da nake hari. Na shiga na fita da wasu mutane, sai da suka fita suka bar mana jam'iyyar, duk da a lokacin ba wani mayar da hankali yake a kan siyasar sosai ba, gidansu yan kasuwa ne, shi ne yake taɓa siyasa.
Bayan sun bar jam'iyyar, aka bani takara, shi ma jam'iyyar da ya koma, suka bashi takara, nayi ta bita da ƙullin siyasa, da yi masa yarfe kala-kala.
Ni da yan jam'iyyar mu, kasancewar muke da mulki a sama, muka shiga muka fita, aka murɗe zaɓen, ya ce shi ba zai kai ƙara ba, jam'iyyarsa suka kai ƙara, amma duk aka kori ƙarar, duk da haka mutane suka so yi mini bore, shi suke so. Na haɗa kai da shugabannin jam'iyyarmu, muka kunno masa wuta ta sama, EFCC suka zo har gida suka kama shi, aka yi seazing ɗin wasu kadarorinsa, da zimmar ya mallake su ba bisa ƙa'ida ba.
Kasancewar ba shi da manyan iyayen gida, bai iya shige-shige da neman wurin zama da biyayya a wurin manya na wannan lokacin ba, ya sanya sai da aka tsare shi a prison, ana binciken sa, bayan an sake shi duk da haka aka ƙwace masa kadarori.
A lokacin mahaifinsa ya ce, baya son sa da harkar siyasa, ko zai yi ya bari sai bayan ransa, sai ya cigaba da kasuwancinsa, kuma bai taɓa ce mini uffan ba, sai bayan rasuwar mahaifinsa ya dawo yake taɓa harkar siyasa, har aka yi masa muƙamin nan, ashe ya ƙwafe wannan abun a ransa, so yake sai ya ɗauki fansa ta ƙarfin tsiya yanzu"

Naja ta ce "Taɓ, gaskiya kana ruwa indabo"

"Ban gane ina ruwa ba?"

"Au muna ruwa zan ce? Wannan rigimar ai ban san lokacin da aka yi ta ba, balle ace da ni aka ƙulla a nemi mafita, a kanka yake neman fansarsa, dan haka ni kar a saka ni a ciki ba zai yiwu ba, haka kurum ana nema ayi mini tsirara a idon duniya"

"Naja"

"Na'am"

"Haka ki ka ce? Kin san bana tafiya da butulu?"

"Babu in da nayi maka butulci, na bauta maka da ƙarfina da gangar jikina, abun da nake yi ba butulci bane, iya ruwa ne fidda kai"

Ya jinjina kai ya ce, "Haka ne, na fahimta"

***

Abdul ne a zaune, ya zubawa ramma ido, tamkar mahaukaciya, gaba ɗaya ta burkice masa, idanunta sun yi jawur saboda kuka, yana kallonta rabonta da abinci tun jiya, muryarta duk ta dashe saboda kuka, ya ma rasa ya zai yi mata, yayi tsawar ya zare idon, amma duk a banza.

Ya kaɗa ya raya taƙi cin abinci.

"Rahama" ta ɗago ta kalleshi kamar wata dodanniya.

"Me ki ke so?"

"Ka duba ni, wallahi ba zan zauna da cikin shege ba, idan shi ne ka cire mini, ka mayar da ni gaban uwata, na gaji da yi maka biyayya baka da niyyar cika alƙawarin da kayi mini, ban sani ba ko sai ka cika alƙawarin ka na kasheni sannan hankalinka zai kwanta".

"Yanzu da kanki ki ke cewa a zubar da ciki? Alhalin lokacin da tsautsayin nan ya faru, mun nemi a zubar a rufe maganar amma ku ka ƙi"

Kamar ta ɗura masa ashar ta ce "Wancan idan tsautsayi ne wannan fa? Wallahi Abdul zan kashe kaina in huta, na gaji"

Ya ce "Is ok, shikenan yanzu ko cikin ne babu lallai na gani, ki bari zan tafi da ke asibiti na yi miki gwaje-gwaje sosai, amma sai kin yadda kin yi wanka kin ci abinci"

Cikin rashin wayo ta jinjina kai, ya lallaɓata da kyar, ta yi wanka, ya dafa tea da indomie ya bata, sai dai tana gama ci, ta hau amai.

Ya ce "Kin gani, ulcer ta kama ki, daga jiya zuwa yau da baki ci abinci ba, shiyasa kina cin abincin ki ka yi amai"

Cikin kuka ramma ta ce "Wallahi ciki ne da ni, ni bani da wata ulcer "

"In ji wa? Ulcer ai tana saka amai, baki ga nima yadda take yi mini ba ne? Ai rashin cin abincin ne ya janyo haka, kuma idan ki ka cigaba da ƙin cin abincin tumbinki ne zai ta rarakewa, komai ki ka ci sai kin yi amai".

"Dan Allah da gaske kake, ulcer ba ciki ba?"

"Zan yi miki ƙarya ne?" Yayi maganar yana tsuke fuska.

"To ka rantse da Allah"

"Ba zan rantse ba, ina likita zan yi miki ƙarya ne? Kuma kan nayi miki allura ban gaya miki allurar tsarin iyali na iya ɗauke miki al'ada ba, tun da artificial homones ne aka saka a jikinki ba?"

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh ka gaya mini"

"Amma shi ne ki ke ta yi mini wannan borin ko rahama, ni ko?"

"Da ka san me nake ji a zuciyata da baka ce ina yi maka bori ba, na gaya maka mamana mu biyu ne da ita, yayanmu ma ya mutu, ya za ayi hankalinta ya kwanta ina nan? Kalli tsawon lokacin da na ɗauka ban ganta ba, ka tausaya mini mana"

Ya saka hannu yana share mata hawaye ya ce "Zan mayar da ke rahama, sonake sai na sanar da mahaifina komai tukuna, bana son sunanki ya ɓaci kamar yadda ki ke ta iƙrari"

"Ɓacin suna na nawa kuma? Ai ya riga ya ɓaci"

"Zan gyara shi da yardar Allah babyna"

Sai da yayi ajiyar zuciya da yaga ta ɗan nutsu har ta ɗan saduda, sai da ta samu bacci, sannan ya tashi ya fita, ya kira saif a waya ya ce masa su haɗu.

***
A harabar gida Nabila ta tarar da Nasir, tana gama parking ya fito daga cikin tasa motar ya tareta ya ce "Daga ina ki ke?"

Kamar ta wanka masa mari, a hasale ta kalleshi ta yi shiru.

"Ina magana kin tsare ni da ido"

"Iska na fita sha"

"Wa ki ka gaya wa, sai Abba ya dawo yayi ta faɗa ko? Kuma wace irin shan iska ne zaki fita ki yi nisa da gida, kukan me ki ke yi ma?"

"Dan girman Allah ka ƙyale ni" tayi maganar cikin sauti mai ƙarfi, ta nufi cikin gida da sauri, kamar mahaukaciya sabon kamu.

Ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofa ta wulwula jakar hannunta tayi jifa da ita, ta samu wuri ta zauna ta dafe kanta, da take jin tamkar zai rabe biyu.

"Ya haiyyu ya ƙaiyyum, ya zuljalalu wal ikram" take ta maimaitawa, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi.

Viper ya ƙular da ita, amma tafi jin haushin kanta, da ta iya buɗe baki, ta furta tana son shi, a da ko me za ayi mata, ko da wasa ba ta taɓa sakawa a ranta zata iya furtawa wani tana son shi ba. To saurayi ya ce yana sonta ma, wahalar da shi take yi, ko da tana sonsa, saboda ta ja ajinta, amma wai yau ita ta furtawa wani so, kuma yayi rejecting ɗin ta kai tsaye.
Viper yana da qualities ɗin da ya cancanci a so shi,  ba ta taɓa zaton wasan da take yi zai zama gaskiya ba, dan ita da fari tsokanarsa kawai take yi, sai kuma matsanancin tausayin sa sa take ji, gashi tausayi ya juye ya koma mata soyayya shi kuma baya ta tata, ga wannan tsohon ciwon nata da ta fama. Zuwa yaushe Abba zai fuskanci gurbin ido ba ido bane ba, duk wani abu da ya faru a baya, bata san an yi shi ba, ba ta san maman nata ba dama wannan an tabattar mata da bata raye, to mahaifinta fa, komai lalacewarsa zata so ta ga abun ta, kuma komai ya yi wa mahaifiyarta, wani abu ne da ya wuce a baya, da ba ta nan ma aka yi shi, to na menene za a gadar mata da wani abu da ba shi da tushe balle cikakkiyar makama.

Ta zabura ta tashi, ta watso drower littatafanta, ta ɗaukko hotunan mahaifiyarta, cikakkiyar bafulatanar yarinya ce ba wata babba ba, fara sol da ita mai dogon hanci, tayi ɗauri irin na mutanen da, ta zubo da dogon gashinta ta ƙarƙashin ɗan kwalinta, har ka kafaɗarta, dukkanin hotunan uku, fuskarta ɗauke da murmushi daga yanayin hotunan zaka fahimci ba ta da hayaniya, kuma mai yawan murmushi ce.
Ta daɗe tana kallon hotunan tana kuka, ta gaji ta kwanta a kan gado, sai ajiyar zuciya take yi.

Washegari da safe, ta shirya zata tafi wurin aiki, ta shiga wurin Abba ta gaishe shi, amma ya shareta yaƙi amsawa, sai gajiya tayi, ta tashi ta fita.

Ko da taje wurin aikin ma, kanta ta kifa a kan teburin office ɗin ta.

Barrister Habib har yayi knocking ya shigo, ba ta sani ba, sai da ya daki teburin, sannan ta ɗago.

"Nabila ya dai? Na ji program ɗin ki ya ɗau hankalin mutane, ki zo a mayar da hankali wurin neman shaidu, kin shigo kuma kin zo nan kina bacci"

Tayi shiru ba ta ce Komai ba.

"Wai meyafaru ne?"

"Ba na jin daɗi ne"

"Yasalam, sannu kuma kika fito? Kina da tiral ne yau?"

"A'a, na zo ne dama mu cigaba da aikin shari'ar nan, ai na sha magani, bari na biyoka office ɗin"

Tare suke aikin, amma sam hankalinta baya kan aikin, ƙarshe ya ce, su bari sai ta samu sauƙi tukuna.

***

A wani wurin cin abinci saifu suka haɗu da Abdul, suka zaune saifu ya ce "Mutumina harkar siyasar nan duk ta ɓoye mana kai, wurin chilling ɗin ma duk ka daina zuwa. Hafsa ta ce tana son ta zo ta ganka, na ce ko ta je asibiti baka zama, ayyuka sun yi maka yawa, asibitin ma ba wani zama kake yi ba"

Yayi murmushin ƙarfin hali ya ce "Ya jikin nata?"

"Da sauƙi sosai Alhamdilillah, likitanta ma sun sallameta, sun ce ta warke, ina ga wani abun ne yake damunta, ta ce kafi dubata sosai, na rasa wani siddabarun kake yi wa patient suke liƙe maka"

"Saif, mu bar wannan maganar, akwai damuwa fa"

"Ta me?"

"Haryanzu babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi kuma ta matsa mini, kullum cikin kuka take"

Saifu ya ce "Ai fa Abdul ka yi mugun ganganci abun da ka aikata, ka mayar da ita wurin iyayenta, tun kafin asirinka ya tonu, sunanka ya ɓaci"

"Saif, ni fa ba ta sunana ya ɓaci nake yi ko akasin haka ba, ni wallahi burina kawai na cigaba da ratuwata da ita, wani irin abu nake ji a kanta, da rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne"

"Kai Abdul, ba ka gama ɗibar abun da kake so ba, ko haryanzu bai isheka ba?"

"Ba wannan nake yi wa ba, ita nake so, tun bayan da na ɗaukota take bani tausayi, ka san ban taɓa raping ba, sai a kanta, wallahi son rahama nake yi, so mai tsanani".

Cikin mamaki Abdul ya ce "Taɓɗijan, aurenka ne fa yake gabatowa, yanzu yaya kenan, gashi ana ta fitina a kan ainihin wanda ya yi mata fyaɗen, wata lauya ta kafe, sai an fito da ita ta bayar da shaida a kotu. Ina ga fa dolenka ka gaya wa mahaifinka gaskiya, ya ɗauki matakin da yakamata a rufe abun nan".

"Ina son gaya masa, amma ina tsoron abun da zai iya yi, ba zai ɗauki maganar da sauƙi ba"

"To ai kuwa ko da yaya zai ɗauki maganar, haka ne kawai mafitar"

Abdul ya yi shiru yana zancen zuci.

***
Viper yana zaune, ya tsurawa hoton jauhar ido, yana hararo kamannin Nabila a cikin kansa.

Walid ya dafa shi, ya ɗaga kai ya kalle shi.

"Ya ake ciki ne? Mutuniyar kwana biyu, yakamata ace fa shirye-shirye sun yi nisa a kan shari'ar ka, ta ina za a fara?"

Viper ya ce "Fushi take yi "

Walid ya ce "Fushin me? Wani abun ya faru ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Akwai magana a bakinta da yakamata na saurara, wataƙila zai haska mini abun da kake gaya mini, sai dai ta bijiro da abun da dole na taka mata burki"

"Wane abu ne?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Bakomai"

"Mai zamani, yakamata ka din ga bin komai a sannu, mata fa dukkansu ba irin jauhar bane, jauhar one in million ce, ba kowace mace ce zata iya juriyar da ta yi ba, kar ka yi treating ɗin Nabila yadda kake treating ɗin Jauhar, suna da banbanci"

Yayi shiru, ya cigaba da kallon hoton hannunsa.

"Allah ya jaddada rahama a gareki, ya kyautata makwancinki my wife " yayi maganar yana shafa haƙoranta na jikin hoton da yake da shi da ita ne, fuskarsa da ƙuruciya sosai lokacin.

Walid ya ce "Amin" ya karɓe hoton, ya ajiye shi a wani wurin.

Yayi shiru yana tunanin ko me Nabila take son ta gaya masa? Ko yanzu tana wani hali? Da gaske son shi take yi, ko kuwa dai still da wasa take yi? Kukan da tayi ya tabattar mata ba wasa take yi ba.
To su mata babu wuya sun fara son mutum kenan? Ya ga damuwa sosai da sosai a cikin idanunta da suka haɗu, ya so ya ji menene damuwarta, amma ta zo da lamari mai girman gaske, son da take yi masa wahalar da kanta kawai zata yi, yana cikin wannan halin na ɓoye-ɓoye, idan ta fara son shi yaya zata yi, tun da ba aurenta zai yi ba, kuma shi ba ma wannan ne a gabansa ba gaba ɗaya.

***

Kusan kwanaki huɗu, amma Abba baya saurar Nabila, fushi yake yi da ita sosai, gajiya tayi da fushin da yake yi da ita, ga habaici da yar da magana da ake yi mata a gidan.

Ta shirya tafiya aiki, ta shiga ɗakinsa, ya na karyawa.

"Abba ina kwana" yayi mata shiru ya cigaba da karyawa.

Ta tashi ta je gabansa ta zauna cikin kuka ta ce "Dan Allah Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, dan Allah ka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login