Showing 321001 words to 324000 words out of 479911 words

Chapter 108 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6135

just like that, she's very young and innocent, ina jin babu daɗi, na san yadda zan ɓullowa lamarin"

Tare da Salim suka cigaba da shige da fice, suka samo wani wan baban ramma, Abdul ya danƙara masa kuɗi, babar ramma bata sani ba, aka ɗaura musu aure, sai bayan an ɗaura ya je ya din ga yi wa babar ramma masifa, wai Allah zai rufa wa ramma asiri, amma tana ƙoƙarin tonewa, da ta samu ma mai kuɗi da kyau kamar wannan ya saurari yar ta ta, a wurin ɗan birni kamar Abdul ai ramma a bar ƙyama ce.

Cikin kuka ta ce "Wallahi balarabe ba zai yiwu ba, ban san wani zancen aurar da ramma ba, lokacin da nake wahala ta da ya ta da me ka taimake ni, ina har gonar su ta gado ka cinye".

"Oho miki, koma menene rashin iya takaucinki, da son abun duniya ya sanya ki ka kaita aikatau" da kansa ya shiga ya kwaso wa Abdul kayan ramma, ya sake ba wa babar ramma kuɗi, ya ɗauki kaya suka tafi.

Suna tafe Salim ya ce "Ranar da asirinka ya tonu ban sanka ba wallahi, ko kuma ka gama abun da zaka yi, salin alin ka sakar musu 'ya"

Abdul ya ce "Ban aureta dan na saketa ba, sai dai ayi wadda za ayi"

Ya je ya samu ramma, ya kai mata kayanta, da goro da alawa ya ce "Gashi nan, hankalinki ya kwanta an ɗaura mana aure yau" cikin mamaki ta kalleshi ta ce "Aure kuma kamar yaya?"

"Ba damuwarki kenan ba? Ke ba zaki auru ba? To an ɗaura yau, yayan babanki wai malam bala, shi ne ya ɗaura mana aure"

"Wane irin aure ne babu istibura'i? Cewa nayi ina sonka ne ma?"

Ya ce "Meye istibura'i?"

"Sai nayi jini uku a addinance, dan tsaftace mahaifata kan ka aureni, tun da zina kayi da ni, kuma ni bana sonka".

Abdul ya kalleta ya ce "Allah ya nuna mana wata ukun, kuma ni ina sonki ai, Shikenan an wuce wurin".

Ramma tayi kuka a kan wannan wulaƙanci da Abdul yayi mata, da nuna mata tsantsar isa da gadara, ta fara yi masa misbehaving ta daina tsoronsa, amma ko a jikinsa, sai dai zamansu tare ta gane yana da wasu ɗabi'u na tausayi da sauƙin kai, rashin tarbiyya da ilimin addini ne kawai yake ɗawainiya da shi, bai sake nemanta ba, sai da ta cika watanni uku, kamar yadda ta buƙata.

Idan tana yi masa masifar ba dan Allah ya aure ta ba, ya kan ce mata "Ba dan ina sonki ba, babu dalilin da zai sanya na zauna da ke watanni uku ina kallonki, kina gindaya mini sharuɗa ina ƙyale ki".

****
Mahaifiyar Abdul ta ce "Aure ka yi bamu sani ba Abdul, rashin muhimmancin namu har ya kai haka?"

Ya kalleta ya ce "Ko zan mutu ba zaku yadda ku aura mini rahama ba, zaku yi iƙirarin yar talakawa ce, ba tare da la'akari da ɓarnar da na akata mata ba. Kuma sakawa zaka yi a kasheta, sannan mutumin nan da ka saka aka kashe, ba ruwana babu saka hannuna a ciki. Zan ɗauki matata mu bar garin nan, dan Allah kar ka neme ni, takara kuma ka bawa wani, ba zan iya ba" ya ɗauke wayarsa, mahaifiyarsa ta bishi tana ƙwala masa kira, amma yayi waje.

***
Viper ne ya shigo ɗakin da Nabila take, tana zaune ya shigo da waya a kunnensa ya ce "Eh na je wani wuri ne, ɗan mama ya dawo gidan nan ne, ya gudu na neme shi na rasa, ya kuma kashe wayarsa"

Walid ya ce "A'a bai dawo ba, ko laifi yayi maka ka ce zaka hukunta shi?"

Yayi murmushi ya ce "Laifi yayi, kuma duk in da ya shiga zan nemo shi, zamu gauraya da ni da shi"ya katse wayar ya ƙarasa gefen Nabilaya zauna.

"Vi"

"Mmm"

"Wai dan Allah ina ne nan? Ina son na tafi gida ne"

"Ai ba zaki koma gida ba, kin zo kenan"

Dariya tayi, dan ta zata da wasa yake yi.

"Daga fitarka ka sha sigari ko?"

"Eh"

Nabila ta ce "Au eh, baka jin kunya wai ka amsa ka tsaye, sai ƙauri ka ke yi, ba na son ƙaurin abar nan ko kaɗan wallahi"

Ya tsura mata ido, ya girgiza kai ya ce "You can't be her"

"Who?"

Ya lanƙwasa ƙafarsa ɗaya a kan gadon ya ce "Jauhar, ba ta taɓa nuna warin sigarina da wiwi yana damunta ba, sai dai ta ce ; Master kar a sha da yawa, dan Allah a sha kaɗan, idan nayi shaye-shaye na dawo, ta bani ruwan wanka, ta bani wankakkun kaya, ta fesa mini turare, sai daga baya na fahimci, warin wiwi ne ba ta so, amma bata taɓa yi mini complain ba. Yanzu bana iya shan komai, na yadda ƙwaƙwalwata da lafiyata suna da amfani, ko dan ganin bayan wanda suka cutar da mu. Ke kuwa masifaffiya ce, always angry, ki ka gaya mini ina ƙaurin taba"

"Sai na zama irin ta zaka so ni? Gaskiya ba zan iya shiru ba, ni kawai ka daina gaba ɗaya"

Viper ya ce "Ai babu wannan maganar tsakanina da ke, na gaya miki ki daina wahalar da kanki" ya yi maganar yana miƙa mata wayarta.

Karɓa ta yi tana hararsa ta ga sunan sumayya ta ce "Ba zan ɗaga ba"

"No, ki ɗaga baki san me za ta ce miki ba"

Ta ɗaga ta saka a kunnenta ta ce "Ina jinki"

"Nabila kina ina ne?"

"Menene?"

"Kawai malama kina ina?"

"Ki gaya mini meyafaru? Nayi nisa ne"

Sumayya ta ce "Mahaifin Viper, ya zo gidan radionmu, ya ce yana son zai yi magana da ke, na ce masa zan haɗaku, zan yi miki magana"

Nabila ta ce "Are you serious dan Allah da gaske?"

"Wallahi da gaske nake yi miki"

"Shikenan, in sha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan zo zamu haɗu, kin karɓi lambarsa?"

"Eh na karɓa"

"Shikenan in sha Allah zan zo" ta katse wayar, ta ga wani irin kallo da yake yi mata.

"Vi snake, menene? Abunka ne ya zo yana nemana, wataƙila.....

"Silent. Kar ki kuskura ki fara, ke gaba ɗaya baki da lissafi, idan wani trap ɗin ne fa?" Yayi maganar cikin hargowa.

"Bari na zama kamar jauhar, ba zan biye maka ba ai yanzu, hukuma sai da rarrashi, hadari malafar duniya. Tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah. Nifa duk da ina da labarin abun da babanna yayi wa mahaifiyata, fata nake yi na ganshi, haka zaka cigaba da rayuwa ba dangi, kaikaɗai sai su oga Walid, sai kuma Ni" ta yi maganar tana murmushi.

"Ka bari mu haɗu da Abbu dan Allah, na san maybe nemanka yake yi, so yake ya ganka, haba sweetheart, namijin duniya, kar ka saka muyi babu, kai ba uba nima haka, kayi haƙuri dan Allah, ka manta da komai My Vi. Magana fa nake yi an yi mini shiru, talk mana, ko sarautar ce ta motsa? Master magana nake" tsigar jikinsa ta mimmiƙe ya juya yana kallonta.

"Ban taɓa kallon wani abu na ji ina son shi ba, sai kai Vi, duk a dalilinka na rasa ajina da jin kai na 'ya mace. Gashi ka yi ta hantarata, baka tausayina ko kaɗan.
Ɗan nuna mini hoton 'yar madara mana, ko sau ɗaya ne"

"Hotonta mai tsada ne, yarinya mai haƙuri da aji"

"Ni kuma masifaffiya mara aji, daga nan kuma sai me?" Ya fuskanci kawai kunna shi take yi.

Ya ajiye mata wata leda, ya ce "Gashi nan, abinci ne, za a kawo miki kaya"

"A'a nifa ban gane ba, gida fa?"

Ya miƙe tsaye ya ce "Ba sa buƙatar ki, na fi su buƙatar ki a yanzu, muddin wani abu ya sameki, ni aka jiƙawa aiki"

Nabila ta ce "Ban gane ba, garkuwa zaka yi da ni?"

"Na ma yi" yayi maganar tare da ficewa.

****
Hanklin can gidan su Nabila ya tashi, bayan an shafe kwana na biyu, ba a san in da take ba, Abba ya maze kamar ko a jikinsa, amma hankalinsa a matuƙar tashe yake. Nasir ma ya din ga up and down, haka ma sumayya dan sai da ta gaya wa Kankarofi an nemi Nabila an rasa.

Ta gaya wa Nasir cewa, ranar da ta ɓata sun yi waya, bayan la'asar kuma da alama tana cikin ƙoshin lafiya.

Nasir ya ce "Abu ne mawuyaci ace barin gidan nan tayi, wataƙila mutanen da take addabawa ne suka sace ta"

Aka din ga kiran wayarta, amma a kashe.

Kwana na uku, Nasir ya kira wayarta, ta shiga, amma ba a ɗagawa.

Dan haka ya saka layin a tracker, ya fara tracking in da wayar take, sai dai ga mamakinsa, wayar tana cikin garin kano.

****
Abdul tamkar zai haukace, duk wani lungu da saƙo na gidan ya duba, amma bai ga ramma ba, ya dudduba ko ina da ina, amma bai ganta ba. Ya kira wayarta amma a kashe.

Taka jikinsa ya hau tsuma, ya tabattar da cewa Indabo ne ya saka aka ɗauke ta, jikinsa na rawa ya ɗaukko mota ya fito, tare da sakawa a ransa komai zai faru sai dai ya faru, amma sai indabo ya fito masa da matarsa, ko kuma shi da kansa ya tona musu asiri kowa ya huta.

****
Nasir yayi mamakin surƙuƙin wurin da yake indicating in da wayar Nabila take, da shi da abokan aikinsa, ƙarshe ajiye motar suka yi, suka din ga shiga wurin da ƙafa, suna cigaba da dubawa.

A tsaye suka tarar da shi ya juya baya, hayaƙi yana tashi.

Nasir ya ce "Malam waye kai?"

Sai da ya ja sakanni, sannan ya juyo a hankali, hannunsa ɗaya da wayar Nabila, ɗaya kuma riƙe da sigarinsa, gaban rigarsa ɗauke da sunansa Viper da hoton maciji a jiki.

"Al'amin Viper, ko ka ce mai zamani"

Ayshercool
08081012143

77
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa


https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA




Cikin matsanancin mamaki, Nasir ya cigaba da takawa zuwa gaban Viper, ya ɗan bayar da tazara tsakaninsa da shi.

Nasir ya ce "Dama kai ne Vipern?"

Ya ɗan kaɗa kai ya ce "Ni ne Viper, abun mamaki ko? Haɗuwar mu biyu, amma baka san ni ne ba, haryanzu ina mamakin wane irin aiki jami'an tsaron ƙasarmu su ke yi, kodayeke ƙulafucin cin hanci ne yake rufewa galibinku idanu, ku danne masu gaskiyar cikinku, ko ku sauya musu ra'ayi domin neman mafitarku kawai"

Nasir ya ƙare masa kallo ya ce "Ina 'yar uwata take? Ina Nabila?"

Viper ya jujjya wayar Nabila sannan ya ɗagawa Nasir ita ya ce "Baka buƙatar yi mini wannan tambayar, tun da ka samu wayarta a hannuna"

"Tana ina?"

"Tana wurina ƙarƙashin kulawata, na fiku buƙatar ta, ina buƙatar ganinta a raye domin nayi surviving, dan haka za ta cigaba da zama a ƙarƙashin kulawata, har zuwa lokacin da ya dace"

A fusace Nasir ya ce "A matsayinka nawa, am arresting you, ba zan bar wurin nan ba, sai na kama ka"

Viper ya kalle su gaba ɗaya 'yan sandan su biyar ɗin ya ce "Bisa wace dokar? Ko bisa umarnin indabo da ka karɓar wa kuɗi, zaka kama ni?. Viper ya zaro takarda a aljihunsa ya ce "Na sami wannan takardar yau da safe, kai ma kuma ka je ka bincika, kotu ta hana hukumar 'yan sanda da kowace hukuma kama ni, har sai an kammala bincike, dan haka ba ka da wannan ikon, hannunka bashi da ƙwarin ɗaukar ƙarfen cikin wannan wutar, ba zaka jure ba, muddin ka taɓa kuwa, zaka yi ƙunar da zata yi dalilin rabaka da hannun"

Nasir ya fizgi takardar hannun Viper, jikinsa na rawa, ya hau karantawa, tabbas Viper da gaske yake, kotu ta bayar da umarnin hana kama shi.

Nasir ya riƙe takardar, ya zaro bindiga a jikinsa, ya ce "Idan kuma na kashe ka a wurin nan fa, waye ya sani?"
Viper ya nuna masa mutanen bayansa ya ce "Ku 'yan sanda ai ba dukkanku ne masu amana ba, wane tabbaci ka ke da shi cewa mutane huɗun nan na bayanka, ba zasu tona maka asiri cewa ka kashe ni ba? Beside kana sakin bullet ɗin bindigar ka, kaima za a kashe ka, tunaninka a banza na zo nan na jiraka? na san kana tracking ɗin wayar, shiyasa na jira ka zo ka iskeni"

Ya ciro ID card ya ɗaga wa Nasir ya ce "I am an NIA officer, and also a former thug, ni ba da bindiga zan yi maka illa ba, ƙarfe zan saka maka, a ɗan daba na zan yi maka illa, ba jami'i ba.

Sauke bindiga Nasir yayi, ya ce "NIA officer how?"

"Kamar yadda ka gani. Maganar Nabila kuma, bari na gaya maka wani abu, na san kana sonta amma ta haramta a gareka, muddin ina ganin fuskar matata a ta Nabila, aurenta ya haramta a gareka, ba kai ba kowa ma. Nabila tana wurina, kuma zan mayar da ita wurin mahaifinta, wannan shi ne tukuicin da zan yi mata, bisa ga jajircewarta da ceto rayuwata"

"Mahaifinta like how? Me ka ke nufi da hakan?"

"Hoton da na bata, ta kai muku ku yi mata bayani, amsar da ku ka bata, ta sanya na yanke shawarar yin abun da ya dace" Nasir zai kuma magana, wani ya ƙaraso wurin da babur, sanye da riga mai tambarin NIA (National Intelligence Agency) Viper ya hau babur ɗin, suka bar wurin.

Dafe kai Nasir yayi, yana tunanin wannan wane irin rikitaccen al'amari ne, tayaya riƙaƙƙen daba ya zama jami'in cibiyar samar da bayanan sirri da leƙen asiri? Ya aka yi kuma ya san mahaifin Nabila, anya wannan duk ba wata shiryayyiya ba ce ba?.

"DSP yakamata fa mu bar wurin nan, ni gaba ɗaya ban yadda da mutumin nan ba, i don't think we are safe here" bai ce uffan ba, ya yinƙura ya tashi suka bar wurin.

****

Gida Nasir ya nufa, a wahale, cike da damuwa da tashin hankali, yama rasa ta ina yakamata ya fara, meyakamata yayi.

Ya za ayi hukuma kamar wannan, ta bar jami'inta yana tafka rashin mutunci son ransa. Yayi shiru yana tunanin yadda wasu abubuwan suka din ga faruwa, ya aikata laifi, amma a bi a goge duk wani trace da zai nuna shi yayi, ko kuma a gano shi.

Babban abun da ya ƙara baƙanta masa rai, shi ne umarnin kotu, na hana kama Viper, ana tuhumar mutum da laifi, har na kisan kai, amma ace kotu tayi umarnin dakatar da kama shi a kan me?.

A ƙofar gidan su, ya tarar da manya-manyan motoci har da na 'yan sanda, cikin sauri ya yi parking, ya shiga cikin gidan domin ya ga mai yake faruwa, baba magajiya ta sanar masa major ne yayi baƙi.

Hankalinsa bai kwanta ba, ya nufi ɗakin Abba, dan tabattar da abun da yake faruwa.

Ya tarar da Alhaji mu'zzam kankarofi, tare da wasu jami'an tsaro, da kuma Abba a falonsa.

Abba ya ce "Yauwwa, ƙaraso Nasir" ya ƙarasa ya shiga, ya zauna suka gaisa.

Abba ya ce "Ka gane wannan ai ko?" Yayi maganar yana nuna masa Alhaji mu'azzam.

Nasir ya ce "Eh ya je asibiti duba Arfat"

"Ashe babban mutum ne ni ban sani ba, ya ce Nabila tana ƙarƙashin kulawar hukuma, saboda rayuwarta na cikin hatsari, wanda take karewa ya rasu, ba a san me zai iya faruwa da ita ba"

Kamar shashasha Nasir ya tsaya yana bin su da kallo, shi kuma meya kawo shi cikin wannan lamarin? Tare da Viper suke harƙalla kenan? Amma da kamar wuya ace kamilin mutum da ya san doka, kamar sa ace yana hulɗa da mutumin banza kamar Viper.

"Mu'azzam wada kankarofi, mai bawa shugaban ƙasa shawara na musamman a kan harkar tsaro" ya faɗa yana kallon Nasir da ya ga yana yi masa wani irin kallo mai cike da tuhuma".

Major ya ce "Haryanzu ina mamaki, da ka ce kai ne dai wada kankarofi, ni na zata suna ne kawai ya zo ɗaya"

Alhaji mu'azzam ya ce "A'a, ni ne dai, a rayuwata ina son 'yanci da walwala, dan haka ban fiye son takura ba, ko yawo da gayyar jami'an tsaro ba duk in da zani.
Na san ka ɗauki zafi a kan abubuwan da Nabila take aikatawa, na kasada, amma ni burgeni tayi, kuma daga ranar farko da na ganta a law firm ɗin su, nake bibiyarta, nake taimakonta, akwai ire-iren ta, brave citizens, da cin hanci da ƙarfin iko, ya sanya ake tauye su su kasa kataɓus, a kanta na ce bari mu jarraba ayi supporting ɗin ta, mu ga wace irin baiwa da gudunmawa zata bai wa ƙasa, and Alhamdilillah ko iya haka tayi rawar gani "

Major ya jinjina kai ya ce "Haka ne sir, amma abun da aka yi ya isa haka, ina son a dawo mini da 'ya ta, abun da tayi Allah ya amfana, ni aikin ma a haƙura da shi, tayi aure. Ba zan lamunci zuba mata ido, tana kare rayuwar ɗan ta'adda ba. Aikinta na neman kawo mini rabuwar kai a cikin iyali. Ga ɗan uwanta yana fafutukar neman mai laifi, ita kuma tana kare shi ba. Sunanta ya ɓaci a idon duniya ba, ina buƙatar ta dawo a haƙura kawai"

Alhaji mu'azzam ya ce "Am sorry to say sir, Nabila ta ɗaukko aikin da kammala shi ne kawai mafita, da ceto dubban al'umma, za ta aikata abun da da yawa sun yi yunkurin yi, amma ba su yi nasara ba. Bani da ikon dawo maka da ita, umarni ne na musamman kareta da lafiyar ta"

Abba ya numfasa ya ce "Na ji, amma Allah ya amfana haka nan, a dawo mini da 'ya ta, ban ga dalilin da zai sanya, a ɗaukar mini yarinya ba da iznina ba a ɗaga mini hakali har haka ba"

Alhaji mu'azzam ya ce "Na san an yi maka laifi, shiyasa muka zo har gida baka haƙuri, kuma ta ɗan samu mini attack ne mun kaita Asibiti, daga baya kuma muka lura da matsanancin haɗarin da rayuwarta take ciki, ka ɗan bamu lokaci"

Nasir kamar yayi maganar Viper, amma yayi shiru, kenan da gaske Viper yake shi jami'in sirri ne, ko kuma wata kitumurmurar ce?.

Abba suka yi ta jayya da Alhaji mu'zzam, haka ya haƙura, sai dai bai ji zai yi shiru da maganar nan ba, dole a dawo masa da 'yar sa.

Bayan tafiyar su, mutanen gidan suja din ga tambayar meyafaru, Abba ya gaya musu ba wani abu, a kan Nabila ne, tana wurin hukuma saboda tsaron lafiyarta.

Masu jiran su ji baƙin labari, duk ba haka suka so ba, baba magajiya kuwa addu'a ta cigaba da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login