Showing 258001 words to 261000 words out of 479911 words

Chapter 87 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

7035

ta iske shi da shi da Nasir, hankalinsa a tashe.

"Arfa, me ki ka je ki ka aikata? Yayanki ya ce kin yi posting a social media kin tayar da tarzoma jami'an tsaro suna nemanki"

Nabila ta ce "Wallahi Abba ban tayar da tarzoma ba, gaskiya kawai na faɗa, kuma haryanzu a hukumance ni ban ga cewar DSS su kama ni ba"

"Ƙaniyarki da ke da hukumar, amma dai kin san ni yanzu ba da bane ba da zaki je ki tsokano mutane ko, tsokanar taki ma, ki ka kasa yin dai-dai da ke, sai in da zaki sha wahala, haka kurum ki tayar mana da zaune tsaye, muna zaman lafiya a ga DSs sun yi mana dirar mikiya a gida, kamar wasu yan ta'adda".

"Abba ba su da hurumin kama ni, ban ɓata wa kowa suna ba, gaskiya kawai na faɗa"

"Rufe mini baki, ko na saka ki tsallen kwaɗo yanzun nan, mara kunya fitsararirriya".

Wayarta ce take ringing, ta ce "Bari na ɗaga waya"

"Hello yaya Habib"

"Nabila kina ina ne?"

"Ina gida, yanzu zan fito wurin aiki"

"Maza ki hanzarta ki ƙaraso, na ga wani rumors yana yawo, a kan posting ɗin da ki ka yi jiya, wai Dss suna nemanki, duk da ba officially na ga sanarwar ba, magoya bayanta ne suke ta zuzuta maganar, maza ki ƙaraso mu riga su ɗaukar mataki"

"To Barrister, gani nan in sha Allah" ta sauke wayar ta ce "Abba daga law firm ɗinmu ne, bari na tafi"

"Ki tafi ina, an ce ana nemanki?"

"Eh zan je in ji me za su ce ne"

Abba ya kalli Nasir ya ce "Ka kai ta law firm ɗin na su, duk yadda ake ciki, ka kirani, zan je na ga likita sai na biyo"

Sam Nasir ba haka ya so Abba ya yi wa Nabila ba, ya so ya ja mata kunne sosai, ya taka mata burki a kan abun da take yi, amma bai yi hakan ba.

Suna tafe a mota, ba ta kula shi ba, sai waya take yi da sumayya da murtala, sumayya ta ce zata ƙarasa law firm ɗin su Nabila.

Tana sauke wayar sumayya, kira ya shigo, an rubuta Confidential a kan lambar.

Ya kalli Nabila, ya kalli wayar, kasancewar Bluetooth ne a kunnenta, ya sanya ta amsa dan kaucewa zargin sa.

"Hello boss"

Viper ya ce "Ya ake ciki? Sun kama kin ne?"

"So ka ke su kamanin kenan?"

"Am asking? Ya ake ciki?"

"Eh, ba su da hurumin kama ni, yanzu ina hanyar law firm ɗin mu ne, Oga na a wurin aiki ya ce maza naje, a riga su ɗaukar mataki".

"Ok, amma you over react, na so ace a sannu ki ka bi abun, amma yanzu zamu raba hankalinsu biyu, zan yi wa Indabo aike, hakan zai sanya su kasa tsayar da hankalinsu wuri guda"

Ta kashingiɗa da jikin seat ɗin mota ta ce "Aiken me?"

"Ke da waye a motar nan?"

"Meyasa ka tambaya?"

"Akwai rashin sukuni da tsoro a cikin maganarki, ke da wayar"

Nabila ta waro ido ta ce "Kai ya aka yi ka gane, vi.... Saurin katse maganar tayi, da tuna katoɓarar da kusa tafkawa.

Tayi gyaran murya ta ce "Zamu yi magana anjima, yanzu ina cikin zullumi jami'an tsaro za su kama ni, ka bari na yi salati na nemi agajin Allah"

Viper ya ce "Ok" ya kaste kiran.

"Da wa ki ka yi waya?"

Ba tare da ta kalli Nasir ba, ta bashi amsa da abokin aikina ne.

***

Ramma ta takure kanta sosai da sosai,  tun da Abdul ya dake ta, ya fice daga gidan ba ta sake ganinsa ba, itakaɗai take kwana take tashi, kuma ya ɗauke wayar da ya bata, da take kiransa a ita, hatta system ɗin sa guda ɗaya da yake ajiye mata, yana koya mata computer ko tayi kallo, dan har fina-finai na hausa, yake yi mata downloading dan su din ga ɗebe mata kewa, gaba ɗaya ya haɗa ya kwashe, ƙofar da zata fito da ita, ta sauka daga kan bene ma zuwa falon ƙasa, duk ya haɗa ya rufe.

Sam ba ta ko iya cin abinci, damuwa ta dawo mata sabuwa fil, ta rasa abun da yake yi mata daɗi baki ɗaya.

Tana zaune bayan sallar isha'i a bedroom, ta ji ya buɗe ƙofa ya shigo, a razane ta waiwaya ta ɗan ja da baya.

Ya ɗan tsura mata ido, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, ya nufi in da take hannunsa da leda.

Ya ajiye ledar, sannan ya zauna a kusa da ita, amma ta sake ja da baya.

"Guduna kuma ki ke yi yau?" Da ya motsa sai ta zabura, dan gani take dukanta zai kuma yi.

Shammatarta yayi, ya janyota jikinsa, ya rungumeta a ƙirjinsa ya ce "Am sorry please, ki yi haƙuri dan Allah" ta yi shiru ba ta ce masa komai ba.

"Ki yi haƙuri, tsantsar tashin hankali da na shiga ne, ya sanya na aikata miki abun da nayi, bana son gardama da taurin kai, tun da ki ka ga na ajiyeki, duk da irin son da nake yi miki, da magiyar da ki ke yi mini, ban mayar da ke gida ba, akwai matsala ne, mamanki ina zuwa wurinta, na tabattar mata da kina cikin ƙoshin lafiya, abin da ki ka yi shirin yi, barazana ne ga rayuwarki. Wallahi regret ne ya hanani dawowa tun da na fita na nutsu, gaba ɗaya nake cikin damuwa, amma ki yi haƙuri dan Allah"

Tayi lamo a jikinsa, amma taƙi magana.

"Rahama talk dan Allah, ki yi mini magana mana ko na ji daɗi dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, son da nake yi miki ne ya sanya na ga abun da ki ka aikata barazana ne ga cigaba da kasancewarmu tare, ki yafe mini" ai kamar gunki, taƙi cewa uffan.

Ya ɗago fuskarta, yana kallonta, amma ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Ya janyo ledar gabansa, ya buɗe tsire ne fal a ciki, ya ce "Ki ci abinci, duk kin faɗa kwana biyu, dan Allah ki yafewa Abdul ɗinki, ba zan ƙara dukanki ba"

Ta saka hannu ta share hawayenta ya ce "Yauwwa babyna, ai na zaki yafe mini, kina da yafiya shiyasa nake ƙara ƙaunarki Rahama, Allah ya yi miki albarka ya shirya miki ni" da ƙyar ya din ga bata abincin a baki, ta ci kaɗan ta tashi, sam taƙi sakar masa fuska.

***
Nabila suna zuwa law firm ɗin su, Barrister Kabir ya balbaleta da faɗa, Nasir ma ya taya shi, akan kasadar da ta yi.
Duk da Nabila ba ta son faɗa a rayuwarta, amma ko a jikinta, ta maze tana cunkusa baki.

Barrister Habib ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri haka, aikin gama fa ya riga ya gama, ta riga ta aikata, sai a san abun yi, kuma wannan duk ba abu ne na tayar da hankali ba, in dai mutum yana da gaskiya, ai faɗa ba nasa bane ba.
Nabila shigo office mu yi magana.

Barrister Kabir ya ce "Naga kamar goya mata baya kake yi Habib, idan kuka janyo abun da ba zaku iya ba, to ku tsaya can, kar ku raɓa ni a ciki"

"To barrister idan ba a goya mata baya ba, kware mata baya zamu yi, ma'aikaciyarmu ce, tayi abun da wani bai yi yinƙurin yi ba, ai kamata yayi a duba, idan akan gaskiya take, a ƙarfafeta, shigo mu yi magana"

Nabila ta shiga cikin office ɗin sa, ya ce "Good girl, i like your confident, a lady of her words, kin dage sai kin cimma burinki a kan matar nan"

Ta ce "Yanzu dai ba wannan ba, meye abun yi, kafin a zo a kamani, nima su saka a kaini prison a ajiyeni babu Shari'a kamar yadda suka yi wa Viper"

"Suka yi wa Viper ita da wa?"

Nabila ta ce "Oho mata, shi ma wannan case ɗin ina nan zuwa kansa, zata gane bata da wayo ai"

Yayi murmushi ya ce "Ba wannan ba, na yi wa Bashir ma magana, yana hanya, zamu yi maza mu shigar da ƙara, a kan lallai kotu ta dakatar da kamun da aka ce Dss su yi miki idan ma da gaske zasu kamakin, ba su da wannan hurumin, sannan su daina yi miki barazana dan kin faɗi albarkacin bakinki"

"To ayi sauri ayi, dan wani update ɗin zan saki, da ni take zancen"

Duk da hantarar da Barrister Kabir ya yi wa Nabila, tare da shi, da sauran lawyoyin law firm ɗin, suka haɗu suka tattara bayanai, da hujjoji da za su kai kotu, dan hana kama Nabila.

Suna can suna ta ƙoƙari, Nabila suka keɓe da Sumayya, ta tura mata videon yaron da ya ketawa zulaiha haddi, a cikin abokansa a ƙasar amurka.

*Wannan shi ne Najib, wanda ya keta wa yarinya zulaiha haddi, har ta kaita ga rasa ranta, a shekarun baya, shin ina shari'ar ta tsaya? Ko ya fi ƙarfin doka ne, dokar a kan talaka kawai take aiki?
Kwana kwanan nan, mun ga yadda labarin wani matashi ya cika dandalin sada zumunta, a kan yadda aka tsare wani matashi shekara goma sha biyu, a gidan gyaran hali, bisa zargin sa da aikata fyaɗe, sai bayan shekaru goman nan, a ziyarar da wani bawan Allah ya kai gidan, ya tausaya masa, ya tsaya masa aka cigaba da yi masa shari'a har aka gano ba shi da laifi, saboda shi talaka ne ya sanya Bunkure foundation ba ta shiga ire-iren cases ɗin nan, sai dai na mata kawai? Me zai saka ace mata kawai foundation ɗin take tsayawa ban da maza? Anya babu wata maganar a ƙasa?.
Wannan ra'ayina ne a matsayina na ƴar ƙasa, wanda yake da ja, a gaban Alƙali zai ƙalubalance ni, ba wai a din ga yi mini barazana ba* tayi posting ɗin tana murmushi, ta ce "Sumy na zama celeb fa"

"Zaki ci ƙaniyarki ke da celeb ɗin, kina kan sirɗin duniya kina rashin mutunci, akwai buƙatar mu nutsa sosai, mu cigaba da samo hujjoji, dan mutane su yadda da abubuwan da ki ke tonawa, dan na san haryanzu akwai masu tantama a kai"

"Haka ne, wannan kuma sai idan muka sake tsayawa a gaban kotu a kan case ɗin ramma"

"Allah ya ƙarfafeki, ya baki sa'a"

"Amin godiya nake masoyiyya"

Sumayya ta ce "Amma Nabila ya za ayi da Indabo ne? Ina tsoron mutumin nan, kin ga kuma shi babba ne, tun a lokacin na so na kai report, amma yayi mini kashedi a kan haka, babu ma wanda zai yadda da ni, saboda muƙaminsa"

Nabila ta ce "Rabani da zancen wannan mutumin, ni yanzu wannan matar ce a gabana, shi kuma akwai dai-dai shi"

"Wa kenan?"

Nabila ta basar da zancen ta shiga wani.

***
"Indabo ka yi wani abu a kan lamarin nan, lallai a kama yarinyar nan a koya mata hankali, ban san da me take taƙama ba, ba a taɓa samun tsageran da yayi mini abun da take yi mini ba, idan fa asirina ya tonu, kuma naku ya tonu wallahi"

"Kar ki damu, muke da ƙasar fa, babu abun da ta isa tayi, na riga na bayar da order da ta kamata"

Ta kashe wayar, cikin fushi, tana mamakin ƙarfin halin Nabila, manyanta ma sun gaji sun ƙyaleta, ba a iya ja da ita, amma yanzu yar ƙaramar alhaki ta sakota a gaba.

Indabo ya daddana wayarsa, ya saka a kunnensa, "Barka da wannan lokaci distinguish senator"

"Barka dai, ya ake ciki ne maganar yarinyar? Na ji kun ce Dss su kamata ya ake ciki, dole fa a toshe duk wata hanya da za a tonawa bunkure asiri dole a tosheta".

"Sir yarinyar nan fa tana da wayo, kuma tana da wanda suka tsaya mata, ta tafi kotu, ta ce lallai a hana kamata kuma ba wanda ta ɓatawa suna, sai dai bunkure ta ƙalubalanceta a gaban shari'a"

Ya numfasa ya ce "Haka ta ce? Wane alƙalin ne? Wace kotun ce zan bayar da umarni a bi umarninta a ƙi bin nawa"

"Honorable ka gane wani abu, abun nan fa ya haɗa da social media, ba zai yiwu mu yi abu gabagaɗi ba, su kansu ƙungiyar lawyoyin ba zasu bari ba, kuma madam tana da magauta a cikin su kansu lawyoyin, za su iya taimaka mata, idan aka yi over reacting, to asirin da ake gudun tonuwarsa zai tonu"

Indabo ya ce "Shikenan, na fahimta".

***
Madaki ya kalli ƙafarsa, ya kurma wani irin uban ihu, tamkar mahaukaciya, Lakwari ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri ka daina wannan ihun, hakan ba mafita bane ba".

"Ka rabu da ni nayi ihun nan, sai na kashe yaron nan, abun kunya ne ace kamar ni, ƙasƙantaccen maƙiyina, ya ga bayana ya sabauta rayuwata, sai na kashe mai zamani na ƙarar da zuriyar su*.

Lakwari ya kalli ƙafar madaki, ta kumbura kamar mai dundumi, sai wani irin koren ruwa ne yake fita daga cikin ciwon ga wari da yake yi, ga maganin da aka bashi, aka ce ya din ga sakawa, ya sanya raunin ƙara jagwalgwalewa, ko iya taka ƙafar baya yi.

"Madaki, ka yi haƙuri mu je asibiti a duba ƙafar nan, ni fa ban ga alamar ciwon nan yana warkewa ko zai warke da haka ba, ƙara jagwalewa yake yi".

"Idan na je asibiti asirina tonuwa zai yi, idan lakwayen nan suka san alkadarina ya karye na shiga uku, kai ka san ta'adin da na yi ai"

"Haka ne, amma duk da haka yakamata muje asibiti a duba ƙafar nan, tun da babu sauƙi a ciki" ya din ga lallaɓa madaki har ya samu ya amince.

Viper yana tsaye tare da su liti, ɗan mama ya shigo, Viper ya ce masa ya ake ciki?

"Komai normal, saƙonka ya isa cikin aminci da kwanciyar hankali. Na shiga area na yi bincike sosai, babu wanda ya san in da madaki yake, amma an tabbatar mini da yana jinya, kuma lakwari ne a tare da shi, sai dai ba a san in da yake ba"

Viper ya zaro russia, ya jujjuyata a hannunsa, ya kalli ɗan mama ya ce "Ka nemo duk in da suke, ina son ka samo target mai kyau, in da zan ritsa lakwari, na san ƙafarsa ɗaya ta mutu zuwa yanzu, zan hari wani wurin na daban kuma"

"Sai da kai ubangidana, abun da ka ce shi za ayi"

"Bari mu ga respond ɗin da Indabo zai yi, idan ya ga saƙona"

***
"Hello, barka da wannan lokaci"

"Yauwwa barka sir"

"Ina magana da justice maijidda ɗan rimi ne"

"Eh nice"

"Good, ina fatan kin gane mai magana?"

Tayi murmushi ta ce "Ya za ayi na ce ban gane ba sir, na gane"

"Masha Allah, akwai ƙara da wata yarinya da sauran lawyoyi suka shigar gabanki, barrister Nabila Yusuf maitama, a kan ki hana Dss kamata, da kuma hana yi mata barazana, ki bi tsarin doka ki yi abun da ya dace, na san dole za a nemi ki yi wani abu ba dai-dai ba, idan ki ka yi akasin abun da doka ta tanada, zai iya janyo wa ayi seizing license ɗinki, nima umarni aka bani daga sama"

"In sha Allah sir, zan yi abun da ya dace ba tare da son rai ba, na gode sosai da sosai"

Ya ce "Yauwwa"

A media kuwa aka cigaba da samun musayar ra'ayi, kowa da abun da yake faɗa, waɗanda bunkure foundation ta cutar, suma suka samu damar bayyana ra'ayoyin su, duk da mutanen da suke ganin hassada ta sanya ake yi wa bunkure hakan sun fi yawa.

Bayan Bunkure ta gama sakankancewa, ta gama da babin Nabila, sanarwa ta fita, kotu ta haramtawa Dss kama Nabila, ko yi mata barazana a kan abun da take aikatawa, a matsayin ta na ƴar ƙasa, tana da ƴancin faɗar albarkacin bakinta.

Indabo kuwa yana cikin majalisa, ya zauna, ya fara ƙoƙarin buɗe envelope ɗin da aka bashi, aka ce an aiko masa da ita.

Ya buɗe ta ya ƙara ciro wata ƙarama a ciki.

Hoton ciki ya kalla, Simon ne tare da Viper a cikin hoton. Simon yana daga cikin yaran da Indabo ya lalatawa rayuwa, kuma ya zama ɗaya daga cikin masu yi masa hidima, a wannan gidan da suke sheƙe aya da shi da ire-iren sa, da suka sanya neman duniya a gaba.
Wanda shi ne ya kuɓutar da Nura guduma daga gidan, ya saka shi a mota, ya haɗa shi da wani ya kai shi kano. Shi kuma ya gudu daga gidan, indabo ya bayar da cigiyar a nemo simon, ya bayar da kwangilar a kashe shi, aka tabattar masa da an kashe shi, amma hoton ya nuna masa kwanan nan aka ɗauka.

Cikin tashin hankali yake sake kallon hoton, tabbas na kwanan ne hoton, saboda Viper ya ƙara girma, fuskar nan babu annuri a tattare da ita ko kaɗan.

"Simon yana raye kenan?" Ya tambayi kansa, ya juya bayan hoton ya ga an rubuta Viper da jan abu.

Bai san ya tashi tsaye ba, sai da na kusa da shi ya ce "Honorable, ya aka yi ne? Me kake gani?"

"A'a ba komai, ulcer ta ce ta tashi" ko izini bai nema ba, yayi waje daga cikin majalisar kamar babbar rigarsa zata harɗe shi ya faɗi.

***

"Assalamu alaikum, Assalamu alaikum ba kowa a gidan ne?"

Walid ya ce "Wa'alaikum Salam, barrister yau ke ce?"

"Ina wuni Yaya walid"

Yayi murmushi ya ce "Lafiya ƙalau, yau kin tuna mini da ƙanwata jauhar"

Ta ce "Allah sarki, Allah ya sa tana aljanna"

Ya amsa da "Amin"

"Ina ogan yake?"

"Ya tafi caji"

Ta ɗan yi turus ta ce "Caji kuma, kamar wani power bank?"

Yayi dariya ya ce "Ya ce, ya fita shan iska yana wurin wancan dutsen"

Ta ce "Ok, bari na je"

"To Allah ya sa yana ƙasa, ba saman ya hau ba"

Nabila ta ce "Idan ma saman ya hau, zan bi shi"

Da tazara daga gidan zuwa dutsen, duk da daga gidan sai ka zata taku kaɗan zaka yi ka ƙarasa.

Daga nesa ta hango shi, a zaune a ƙasa-ƙasa, ta hango tashin hayaƙi a wurin.

Ta ƙarasa da ƙyar, dan duk ta gaji, kwali guda ne a gabansa, ta ƙarasa ta kai hannu ta ɗauke, caraf ya riƙe hannunta. Tsorata tayi, dan cikin sanɗa ta ƙarasa wurin, amma har ya ankare da ita ya hanata ɗauka.

Ta haɗe rai ta ce "Sakar mini hannu, nan ka gama cewa zan saka a lungu, shi ne zaka wani riƙe mini hannu?"

"Ni na kawo ki? Ban ce ki daina zuwa ba ma?"

"To ko kirana ba ka sake yi a waya ba, idan ma an kama ni, ko ma menene ya same ni, ba ruwanka ko?" Tari ta fara yi, saboda hayaƙi, sakar mata hannu ya yi, tayi sauri ta ɗauke kwalin sigarin da ashanar, ta tura a jakarta.

Satchet ɗin maganin da ya leƙo a gefen aljihunsa, shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login