Showing 246001 words to 249000 words out of 479911 words

Chapter 83 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6062

ki yi haƙuri ki daina kuka" a haka ya ɓuge da rarrashin ta, ta nuna masa komai ya wuce, yana fita tayi masa gwalo, tare da ajiyar zuciya.

Ta ɗaukko wayarta ta ce "Bari na kira na ji ya jikin ɗan marayan zakina" sai dai wayarsa a kashe, haka ta haƙura.

***
Gaba ɗaya ramma ta fita daga harkar Abdul, abun duniya ya addabe shi, gashi ya kasa gano in da mahaifiyar ta take, babban tashin hankalinsa kar ta gano cewar mahafiyarta ta ɓata. Dan bai san wane irin kalar bori zata yi masa ba.
Ga Indabo ya uzzura masa, dan har an kai masa kuɗin aure, ga shirye shiryen takararsa na ta ƙara yin nisa, amma gaba ɗaya hankalinsa baya kan takarar. Abokansa sai mita suke yi masa a kan duk ya canza, ga aurensa an saka su fara shiri, amma ya kasa mayar da hankali a kai, sun kasa gane kansa gaba ɗaya.
Babu wanda ya tsaya saurara da bashi amsa a kan surutun da yake yi.

Yana zaune yana kallo, amma hankalinsa ba a kan kallon yake ba, tunani kawai yake yi.

Ramma ta ƙaraso kansa ta tsaya, ya ɗaga kai ya kalleta, ya tashi zaune sosai ya ce "Rahama, ya aka yi ne?"

Ta ƙaraso ta durƙusa a kan gwiwoyinta, hawaye na bin fuskarta ta ce "Abdul yasar, dan son da kake yi wa Allah da annabinsa, ka mayar da ni gaban mahaifiyata, naga message a notification ɗin ka, wai aure zaka yi, dan girman Allah ka mayar da ni wurin uwata da ɗan uwana, na yadda zan ƙarasa rayuwata, a rushen zan tattara ta na rayu, ba ma na saka ran zan zan yi aure, na yarda na rayu a haka"

Ya kalli ramma ya ce "Daga ganin message sai ki ce aure zan yi? Bincike ki ke yi mini kenan? To ni ba wani aure da zan yi ".

Cikin kuka ta ce "Ka daina yaudarata Abdul, ka rabu da ni, idan kana son iyayenka, na gaji, na gaji na gaji da haƙuri, da fatan zaka mayar da ni gida, ka ƙyaleni dan girman Allah, ai ka gama morar abun da kake so zuwa yanzu, kowace irin ƙishirwa ce ka kasheta zuwa yanzu ka rabu da ni dan Allah " tayi maganar cikin ɗaga murya.

Abdul ya kalleta a tsanake ya ce "Kin manta alƙawarin da ki ka yi mini ne?"

"Babu wani alƙawari da nayi maka, ni ban san wani alƙawari ba, ka mayar da ni gida"

"Wallahi ƙarya ki ke yi ki rusa maganar da muka yi da ke, da alƙawarin da ki ka yi mini"

"Ka yi mini duk abun da ka ga dama, amma ni dai ka sakeni na koma gida, idan duk matan duniya ne ka je ka aura, ban damu ba, amma a yanzu tun da dai ka gama da rayuwata dan Allah ka rabu da ni"

Abdul ya tsura mata ido, yadda take kuka wiwi har da majina.

Ya saukko daga kan kujerar, ya zauna a gabanta ya ce "Rahama kishina fa ki ke yi"

Kamar zata kai masa mari ta ce "Ƙarya ne, Allah ya kiyayeni ya tsare ni da kishin ƙazamar halitta mara tsoron Allah kamar ka, ni kishin rayuwata nake yi"

Ya sauke numfashi ya ce "Zan mayar da ke, amma sai kin cika mini alƙawarina, sannan kin haifa mini ɗa sannan zaki koma gida, kin ga idan kika haihu duk duniya babu wanda ya isa ya raba ni da ke" yayi maganar yana share mata hawaye.

"Abdul ba zan taɓa yafe maka ba, na bar ka da Allah"

"Duk cikin kishina ne, matsayin matar da zan aura daban, naki ma daban, you are like my guest house, wurin hutawa ta da nishaɗina"

Jiki a sanyaye ta ce "Ka cuce ni Abdul, duk saboda ina 'yar talakan ƙauye, mara gata mara galihu"

Ya girgiza mata kai, ya haɗe bakinsa sa nata, wata irin ajiyar zuciya take yi, a hankali ya cire bakinsa daga nata, ya kalli idanunta ya ce "Iya wuya rahama, ina tare da ke, ban ga wanda ya isa ya raba ni da ke ba. A lokacin da maza da yawa suke gudun matan da suka lalata, ni a dai-dai lokacin soyayyar yarinyar da na lalatawa rayuwa ta yi mini kamun kazar kuku".

Jiki babu ƙwari ta cw "A hakan? Wace irin soyyaya ce zaka yanke mini farincikina ba tare da wani dalili ba, bana sonka Abdul ko kaɗan"

"Ki saurari zuciyarki, kina jin zafin abun da nayi miki ne kawai, amma kina so na rahama, nima kuma ina matuƙar sonki"

"Da ban yi wa kaina, da mahaifiyata adalci ba, idan na fara sonka Abdul yasar"

"Zuciyar ki, cike da ƙuruciya, kina ƙoƙarin sakawa kanki ƙiyayyata ne ta ƙarfin tsiya ne".

"Wallahi wannan ba so bane, ka gama lalata ni, ka samu abun da kake so, kuma ka ce sona kake, me yayi saura?"

"Kin san abun da na ɗauko ki ki yi mini, kuma na daina kamar yadda ki ka buƙata. Wuri ɗaya nake kwana da ke nake tashi, amma na daure, ban sake yi miki ba, kuma na lazumci istigfari kamar yadda ki ka gaya mini. Kar ki saɓa alƙawarinmu mana. Wa ki ka taɓa ganin ya lalata yarinya ya bita kuma yana so? Ke kin san waye ni a garin nan da ƙasar nan. Na fiki shekaru, da ilimi da tarin dukiya, amma gaba ɗaya na bar abun da yake gabana na tattara hankalina a kanki, ki yafe mini mana sweetheart, ki yarda ki so ni, zan goge laifukana zan kuma mayar da ke wurin mama in sha Allah"

"To yaushe?"

"Very soon, da zarar kin yafe mini, kuma kin cika mini alƙawari"

Ramma ta share hawayenta ta ce "Abdul ta yaya zan haihu da kai, in kalli duniya in ce musu me? Baga mata nan zaka aura ba, ba sai ku haihu ba?"

"Naki nake so please" yayi maganar yana sumbatar goshinta, cikin tsananin so da shauƙinta.

***

Yau ma uban sammako Nabila ta yi, ta tafi asibitin da Viper yake, sai dai ba ta ɗauki motarta ba.

Yanzu ma ɗan mama ta tarar, yana ta sharar uban bacci, babu liti babu Walid.

Viper kuma yana zaune, ya jingina da bango idanunsa a lumshe.

Murmushi tayi, tare da farin cikin ganinsa a zaune.

Ta ƙarasa ta zauna ta ce "Yallaɓai, good morning, ya jiki? Alhamdilillah na ji daɗin ganinka a zaune" sai dai kamar mai bacci, bai buɗe idonsa ba.

Hannunsa ta kalla, ɗaya da drip, ɗaya kuma kamar lazumi yake yi. Wani irin farinciki ya kama Nabila.

Wani baƙin abu ta hanga, a gefen pillown sa, ta saka hannu ta janyo, ta ce "Menene wannan, ko kayan da zaka canza ne?" Tayi maganar tana buɗewa.

"Wannan rigarka ce?" Buɗe idonsa yayi ya kalleta, cikin wani irin zafin nama ya fizge rigar daga hannunta, ya hau waige-waige.

Ta ce "Menene? Meyafaru?"

Ya kalli in da ɗan mama ya saki baki yana bacci, ya kalli taga babu hanyar shiga ko fita ta tagar, ya sake ɗaga rigar.

Baƙar riga ce shirt, mai ɗauke da hoton tambarin dragon a gefen rigar, bayanta kuma an rubuta wasu alphabets, da bai bar Nabila ta karanta ba. Duk da jikinsa babu ƙwari haka ya saka ƙarfin sa, ya yayyaga rigar, yana cigaba da waige-waige.

Cikin rashin fahimta ta ce "Wai me yake faruwa ne?" Ya girgiza mata kai, ya sake jingina.

Nabila ta kalle shi ta ce "Akwai damuwa fa, jiya an yi settling bills ɗin ka, sai dai bamu san waye ba, an ƙi gaya mana ko wanene" ya ƙura mata ido, ta jinjina masa kai, alamar da gaske take.

"Dan Allah ka gaya mini, menene yake faruwa ne, bai kamata ka ɓoye mini komai ba, tare fa zamu yi gwagwarmayar nan" Sai ya lumshe idanunsa ma, yaƙi kulata.

"Haba master, yar suganka ce fa, talk mana" a hankali ya fara kaɗa ƙafa, amma bai yi magana ba.

"Sweetheart" ta faɗa tana dariya ƙasa-ƙasa.

"Sweetheart magana nake fa" sai ya kwanta ya juya mata baya baki ɗaya.

"Am sorry wasa fa nake yi maka, ya ƙarfin jikinka to, ina fatan akwai progress, kana samun sauƙi?"

Ya girgiza kansa alamar "A'a"

Ta ce "Ohh ni Nabila ina ganin mulki yau, Allah dai ya jaddada rahama da Fatima jauhar, ta yi ƙoƙari sosai"

Ya ce "Amin" tausayin sa ne ya sake kama ta, ta ce "To tashi ka karya, na san yanzu za a zo yi maka allurai, kuma na san kana jin yunwa"

Bai yi magana ba liti ya shigo da leda a hannunsa, ya kalli ɗan mama da yake ta bacci, ya dake shi da ƙafarsa ya ce "Tashi, ɗan asara, idan ma sace shi za ayi, kana kwance ka shanya baki kamar fatarin mata kana bacci" ɗan mama ya tashi yana mutsutsuka ido.

Jauhar ta kalleshi ta ce "Ina kwana?"

Ciki ciki ya amsa, ya dafa Viper ya ce "Maza ya ne, ya jikin?"

"Alhamdilillah"

"To masha Allah, ga brush ɗin da toothpaste, ka wanke bakin, yanzu Walid zai kawo abinci, sai ka yi wanka ka canza kaya"

Ya yinƙura ya tashi zaune, ya ƙurawa ɗan mama ido, sannan ya ce "Kai waye ya shigo ɗakin nan jiya da daddare?"

"Likita ne, sai mai bada magani Nurse, sukenan"

"Ƙarya kake yi"

Ɗan mama ya ce "Wallahi sukaɗai na gani"

Liti ya ce "Dama ya kwanta yana ta uban bacci, ya za ayi ya san me ake yi? Ina fatan ba wani abun ne ya faru ba?"

"Babu komai"

Da Al'amin ya shiga banɗaki, sai Nabila ta fita tana waya da barrister Habib, ya ce lallai yana son ganinta, Sumayya T ladan ta turo wasu mata, kuma zasu taimakawa aikinta a kan bunkure.

Nabila ta yamutsa fuska ta ce "Ka sallame su kawai, babu buƙatar na gansu"

"Kamar yaya, abu mai muhimmanci da ki ke nema, ki ce a sallame su"

"To ai nayi nisa ne, yaushe na bar abun da nake yi na zo"

"Ki bari koma menene ki taho yanzun nan" to kawai ta ce masa, ta ajiye wayar.

Ta cikin niƙabinta, take ƙarewa asibitin kallo, wurin cashier ta sake zuwa, sai dai yau wata mace ce. Suka gaisa Nabila tayi mata bayanin abun da ya faru jiya, ta buƙaci ta dubo receipt ɗin da aka turo musu na biyan kuɗin, ta ciro ta bata.

Ta shiga computer ta duba, ta kalli Nabila ta ce "Ban ga receipt ba, kawai an saka bill settled"

"Ina ne ofishin MD, ko admin na asibitin nan, dole fa a nemo wanda ya biya kuɗin nan"

Ta ce "Ba sa shigowa da wuri, amma maybe zuwa anjima"

Nabila ta juya ta koma ɗakin Viper.

Ya canza kaya ya zauna a kan gadonsa.

Har walid ma ya zo, ya buɗe masa wainar shinkafa ta sha ƙuli-ƙuli, yana lallaɓa shi ya ci.

"Barrister har kin zo ashe?"

Ta ce "Eh oga Walid, na zo tun ɗazu, naje likita ya duba ni, allurar da master ya caka mini jiya, hannuna ya sage" da sauri Viper ya kalleta.

Walid ya ce "Subhanallah, Allah ya sauwwaƙe ya ƙara afuwa"

Ta kalli wainar gaban Viper, ta ce "Oga walid ɗauke wainarka, na dafo masa abinci.

Ta janyo ledar viva daga ƙarƙashin gadonsa, ta buɗe food plask, ta ɗaukko mini tea flask ɗin ta, ta haɗa masa tea.

Faten dankalin turawa ne, ya sha ganye sosai da nama, sai ƙamshi yake yi duk ya cika ɗakin da ƙamshi.

Ta miƙa masa shayin ta ce "Bisimillah ranka ya daɗe, kaga tea ne, da ɗuminsa sai ka samu cikinka ya warware, kaga tun jiya baka ci komai ba, ina fatan Allah ya baka lafiya da wuri, mu cigaba da aiki muna addu'a, in sha Allah sai mun dangana da nasara"

Ya ɗaga kai yayi mata wani irin kallo, ta ce "Ba danni ba, dan Allah idan baka ci ba ba zan ji daɗi ba, dan kai na girko na kawo maka. Lafiyarka na da matuƙar muhimmanci a wurina please mana, ka karɓa" ya miƙo mata hannu, ta saka masa kofin tana kallonsa tana murmushi.

"To yi bisimillah ka fara sha".

Ɗan mama ne yake ta ƙoƙarin yin dariya, amma yana jin tsoro, ganin yadda aka bar Walid da busashshiyar wainarsa. Liti kuwa ƙyaƙyatawa ya din ga yi ya ce "Walid, miƙo mana wainar nan, mu ƙaddamar mata"

"Sannu maye, aikuwa ba zaku ci ba, ku ci kanku"

Nabila murmushi ta yi, ta cigaba da yi wa Viper hira, cike da tausayawa, da bashi ƙwarin gwiwa a kan haƙuri da ƙaddara.

Sannu a hankali yake cin abincin, har ya cinye tas, ya shanye shayinsa.

Wani murmushin ta sake yi masa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin. Allah ya ƙara maka sutura da ingantacciyar lafiya, ya baka tsawon rai ya bamu nasarar ɗaukar fansar abun da aka yi mana. Har cikin raina nake jin zafin abun da ya faru da kai, but before then. Please promise me ka daina z1y ³y2ubar da hawayenka, wanda ka yi ya isa. Kuma kayi mini alƙawarin ba zaka sake shan ƙwayoyin da za su illata mini kai ba"

Liti ya tashi ya ce "Nikam nayi waje, wannan wace irin fitsara ce?"

"Ka kalleni mana dan Allah" ya ɗaga kansa ya kalleta.

Duk da idanunsa sun yi mata nauyi, amma ta ce "Ka ce Nabila, nayi miki alƙawari ba zan sake shan miyagun ƙwayoyi ba, ba zan sake yi wa kaina allura ba, zan baki cikakken goyon baya in ɗauki fansata ta hanyar da ta dace"

"Tashi zan kwanta" ya faɗa a taƙaice.

Duk wannan zubar da ta gama yi, ba su ne a gabansa ba, kawai ta tashi zai kwanta.

Ta fuskanci aiki ne jawur a gabanta, ba ta sare ba taƙi tashi, ta kuma ƙi magana.

Ya ture ta, ya raɓa ya kwanta ya juya mata baya.

"Allah ya baka lafiya ya jaddada rahamarsa ga marigayyiya jauhar".

"Amin ya Allah, na gode" yayi maganar idanunsa a lumshe.

Tayi murmushi jin ya amsa, ba ya wasa da duk abun da ya shafi Jauhar.

Walid ne ya rakota, take ce masa "Ku yi haƙuri da wasu abubuwan da zaku ga ina yi, ina yi ne saboda sama wa ƙwaƙwalwarsa nutsuwa, idan ba haka ba zai iya rasa hankalinsa baki ɗaya"

Walid ya ce "Karki damu na fahimce ki, ki rabu da liti, ba kan gado ya cika ba dama".

***
Ramma na kwance a jikin Abdul, yana waya da mahaifiyarsa, tana yi masa magana a kan haɗa lefensa, ya ce su yi duk abun da yakamata, yau zai je asibiti ne, zai yi tiyata cikin dare, dan haka yayi busy. Ya kashe wayar, ramma ta motsa tana ƙoƙarin tashi ya riƙe ta ya ce "Beb, ina zaki kuma?"

Rai a haɗe ta ce "Na gaji da kwanciyar tashi zan yi"

Ya tashi zaune ya ce "Haba rahama, nifa duk wani motsinki ina gane me kike nufi, ai na baki haƙuri, kin san dalilin auren nan.....

"Ni cewa nayi na damu da aurenka? Ina ruwana ne ni damuwata na koma gaban iyayena"

Abdul ya ce "Zaki koma, amma sai Allah ya sa kin samu ciki kin haihu, am doing this for your own benefits, saboda ke duk nake haka".

"To bana so, ka daina"

"Haba sayyada, ba fa zina zan yi ba aure zan yi, kin ce in yawaita istigfari Allah zai yafe mini, to ke kuma kin ƙi ki yafe mini, ki yi amfani da iliminki mana haba sayyada rahama"

"Ba wata sayyada, sayaddar da ka kafawa ƙahon zuƙa sai ta haifi ɗan shege ko?"

Kawai ya kama dariya, ya ce "Ke dai ba a iya miki, idan an yi nan sai ki yi can, anjima zan kai ki shan ice cream mu ɗan fita mu zagaya".

"Ba zan je ba"

Ya ce "Shikenan huta roro, na ɗauki amaryata mu je"
Tayi tsaki, ta sauka daga kan gadon, ta nufi toilet.

***Bunkure ta fito daga shari'a kenan, ta nufi motarta, ta tarar da Nabila a tsaye tana jiran isowarta.

Ta tsaya ta kalli Nabila, Nabila ta kalleta ta ce "Na je office ɗin ki sau biyu, an ce ba kya nan, kin yi balaguro, da ki ka dawo kuma, bani da isashshen lokaci.
Ina son sanin in da ramma take, ita wadda aka yi wa fyaɗen, da shi kansa likitan da yayi documenting ya tabattar da an yi mata rape, ba wai takarda kawai ba.

"Ke, kin fara wuce gona da iri fa, kar ki bari na waiwayeki, nayi yinƙurin ɗaukar mataki a kanki"

"Wane matakin kenan? Harka ce ta aiki fa, idan kina da gaskiya menene na ɓoye-ɓoye. Nayi mamakin yadda kina mace, once a rape victim, amma ki zama tsanin kare masu laifi. Na san kin ga shaidar da na gabatar a kotu, ta sautin muryar mahaifiyar ramma, kuma ko sama ko ƙasa an nemeta an rasata yanzu. Shikenan idan kina taƙama da kun saye lawyoyi da alƙalai, ki shirya motsi na gaba da zan yi.
Sai na bankaɗo duk wani shu'umanci, da zalunci da ki ke yi, kuma ko a ina kuka ɓoye ramma, sai na tona muku asiri, na tonawa wanda yayi mata fyaɗe asiri. Kar ki manta ɗan hakin da ka raina....... Bata sake cewa komai ba ta tafi ta bata wuri.

Wayarta ta ɗaukko ta tura wa Indabo message. "Yakamata ka motsa a kan yarinyar nan, ta fara wuce gona da iri"

Kasancewar ta sha zirga-zirga, a gajiye ta ƙarasa office ɗin su.

Wurin Barrister Habib ta fara nufa, tana zuwa ta tarar da Sumayya da wasu mata su biyu, a Office ɗin Barrister Habib suna jiranta.

Suka gaisa da Habib, ta juya ta fice, zai yi magana, Sumayya ta ce "Bari na je na same ta.

Ta iske Nabila a office ɗin ta, ta ce "Arfa, tun safe fa bayin Allah nan suna jiranki, har na zo nima, baki zo ba ina ki ka je ne haka?".

"Sumayya wai baki da zuciya ne, alaƙa da ke ce bana so, na menene zaki din ga bibiyata kuma?"

"Nabila, dan Allah ki tsaya mu yi magana, mu fuskanci juna dan Allah"

"Babu wani abu da zan fuskanta, ni kin riga kin sire mini, ki fita ki bani wuri, ko ni baki wuri" Sumayya ta tsaya tana kallon Nabila.

Nabila ta zo zata fice, Sumayya ta riƙe ta, ta ce "Ni yakamata na fice na baki wuri, na san nayi kuskure amma yakamata ace ko sau ɗaya kin saurare ni.
Tabbas ina bayar da duk wasu bayanai, da aka nema a kanki, amma ni baki san a wani hatsarin rayuwata take ciki ba, domin kare taki. Ni 'yar halak ce, zan daina binki dan ki saurare ni, amma zan cigaba da aikin da aka bani a kanki. Idan kin ga dama, ki saurari matan can, idan kuma kin ga dama, ki kore su, matsalarki ce ba tawa ba" ta ja da baya, ta buɗe ƙofa ta fita.

Ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login