Showing 273001 words to 276000 words out of 479911 words

Chapter 92 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6142

nemana a waya, da mutuwa na yi fa"

"Allah ya jiƙanki, zahra ma da mutu haƙuri nayi, balle ke. Sai ki ƙara taka tsantsan da abubuwan da ki ke yi"

Wani ƙululun takaici, ya tokare mata wuya, sosai ta ji zafin abun da ya ce mata, kawai ta katse wayar.

Walid ya ce "Viper, kamar baka kyauta ba fa" yayi masa shiru, hakan ya sa shi ma yayi shirun bai kuma cewa komai ba.

Baƙin ciki da ɓacin rai ya sanya, babu wanda ta yi wa sallama a gidan ma, tayi tafiyarta.

Tana tafe a hanya ta din ga jin wani abu mai kama da kishi, da ɓacin rai yana taso mata, har ga Allah ba ta san jauhar ba, amma tana son ta saboda Allah, amma abun da yayi mata yau, ya sanya ta ji ranta ya sosu.

"Meyake damuna ne? Wai son bawan Allah nan nake yi? Na shiga uku me yake shirin faruwa da ni ne? Idan ta tabatta son shi nake yi, na yi wauta, to yaya ma za ayi hakan ya yiwu abu daga wasa?" Har ta ƙarasa wurin aiki, tunani take a zuciyarta. Tayi shiru tana sauraren zuciyarta dan ta tabattar da abun da take tunani gaskiya ne ko akasin haka, amma bata kai ga hakan ba, aka ƙwanƙwasa glashin motarta, masu gadi ne suke yi mata barka da dawowa, tare da yi mata sannu da jiki".

Ta saukko daga motar, suka gaggaisa, sannan ta shiga ciki, a cikin ma murnar ganinta suka din ga yi suna yi mata sannu.

Ko mintuna talatin ba ta yi a sabon office ɗin ba, barrister Habib ya ƙaraso.

"Autar lauyoyi, ƙaramar su babbar su, aminiyar sumy, ƙaramar sauro ka da ƙatuwar giwa, ba giwar ba hatta toron ma kayarwa ki ke yi"

Nabila ta yi murmushin yaƙe ta ce "Ni har ka bani kunya ma"

"To yaya jikin naki?"

"Alhamdilillah yayi sauƙi sosai"

Ya ce "Masha Allah, yanzu ya ake ciki da batun shari'ar nan? Zamu je prison ɗin ne wurin mutumin?"

"Za a bari mu ganshi kuwa?"

Habib ya ce "Za'a bari mana ba dole ba, ai na je lokacin kina gadon asibiti, ba na son abun da zai kawo tsaiko a harkar shari'ar gaba ɗaya" 

"Kai amma na gode sosai yaya habib "

"Kar ki damu Nabila, ba ke ba, hatta ni na ji haushin yadda shari'ar nan ta gudana, kuma cin mutuncin harkar shari'a ne, a wannan karon zamu yi nasara in sha Allah "

"Allah ya sa yaya Habib" suka fito suka hau motar barrister Habib suka fita.

Nasir da yake bin Nabila a wata motar, ya ga fitar Barrister Habib da Nabila, ya sake rufa musu baya, sannu a hankali ba tare da sun san yana bin su ba, sai dai azabar kishi ya sanya ya ji har wani dishi-dishi yake gani.

A wannan karon Nabila tayi mamakin yadda aka basu damar ganin baba maigadi, ba tare da an raina mata hankali kamar yadda aka saba ba.

Suka gaisa cikin mutuntawa, duk ya rame yayi wani iri.
"Baba, ina mai sake baka haƙuri, amma ban karaya ba, in sha Allah zamu ɗaukaka ƙara ne"

Jiki a sanyaye Baban ya ce "Kina ta ɗawainiya, ni idan babu hali, kawai a bar maganar nan, na bar wa Allah"

Barrister Habib ya ce "No ba zai yiwu ba, ka manta yadda muka yi da kai wancan zuwan da nayi muka haɗu?"

Yayi shiru ya sunkuyar da kai.

"Ka yi magana mana, mun yi magana da kai fa sosai baba, ka bata haɗin kai dan Allah, a wannan karon muna fatan ayi nasara, ka yi mata bayani, saboda ƙoƙarin kamanta gaskiya har nema aka yi a sabauta rayuwarta, ka yi magana baba, ka yi mata bayanin komai.
Nabila let's record it Incase"

Ta jinjina kai ta ɗaukko wayarta, ta danna recording ta ajiye.

Cikin tsoro ya ce "Dan Allah to kar ku gaya wa kowa, kun ga yarana duka mata ne, na aurar da wasu, ina da biyu ƴan mata, an ce muddin na yi magana abun da ya samu ramma zai same su, koma su rasa rayukansu gaba ɗaya tsoro nake ji" mamaki ya cika Nabila, dan ita duk bai yi mata wannan maganar ba.

"Baba, ni na baka tabbacin nan, babu abun da zai samu iyalanka, ka ba ta cikakken haɗin kai, idan ka bari ta sake faɗuwa a shari'ar nan, kaga magauta sun yi galaba a kanta, kuma yayan da ka ke yi wa, ka ɓata musu suna"

Ya jinjina kai ya ce "Ana saura kwana biyu uwar ɗakin hajiya jidda, tayi waya ta ce aje garin su ramma, ta dawo su haɗu da ɗaya mai aikin, ayi mata gyaran gida, saboda tana ji da Ramma sosai, tana da biyayya, kuma bata yi mata sata.
Ranar an ɗaukko ramma, suna ta aiki, zulai ta tafi kasuwa, ɗan yayar matar gidan ya zo, sunansa Abdul, ban daɗe da fara aiki a gidan ba, dan babban mutum ne sosai mutumin, in da suka baro, jami'an tsaro ne suke yi masa gadi. Unguwar nan da suke ne, jami'an tsaro layuka suke gadi, ni kuma aka samo mini buɗe ƙofa da rufewa a gidan.
Bayan yayi mata, ya tafi zulai ta fito tana kururuwa, bayan ta dawo daga wurin sayen kayan miya. Bayan mun kai ta Asibiti, magana ta bazu, aka ce an sallame ni daga aiki, amma za a neme ni, daga baya yan sanda suka je gidana suka tafi da ni, wai zan ba da bayanin abun da na sani, muna zuwa aka rufe ni aka ce ni ake zargi, kuma aka yi mini barazana da muddin na ce bani bane ba yarana na cikin haɗari"

Nabila ta ƙulu ta ce "Amma meyasa baka yi mini wannan bayanin ba ni, na san ta ina zamu ɓullowa lamarin? Nayi ta wahalar neman shaida ka kuma ƙi bayani a kotu"

Barrister Habib ya ce "Kwantar da hankalinki, ki yi haƙuri kin san uba da 'ya'ya"

"Ki yi haƙuri na san nayi kuskure amma a tsorace nake ne nima"

Ta kalleshi ta ce "Ya sunan mai gidan?"

Ya girgiza kai ya ce "Ban sani ba"

"Ya za ayi ka yi aiki a gidan wanda ba ka san sunansa ba?" Yayi shiru ya sunkuyar da kai.

Barrister Habib ya ce "Tashi muje, ma ƙarasa sauran aikin" haka suka fito Nabila tana mita, barrister Habib yana bata haƙuri.

Law firm ɗin suka koma, suka fara arranging ɗin yadda zasu yi appeal, sun gama ta fito suka haɗu da barrister Kabir, yayi mata sannu, tare da yi mata kashedi, a kan ta raba kanta da aikata duk wani abu da zai sanya ta shiga matsala, ta bishi da to, ta fita ta shiga motarta ta nufi gida.

Nasir bai ga wani abu ba a bibiyar Nabila da ya yi yau ba, amma bai ji zuciyarsa ta gamsu ba, ya sakawa ransa zai yi assigning wani wanda zai din ga bibiyar masa ita lokaci zuwa lokaci.

***
Su liti suna karyawa, Viper kuwa yana zaune yana yanke farcensa da nail cutter.

Wayar liti aka kira, ya karɓa ya ɗaga ya ce "Ya ne?"

"Normal, kwana biyu ba ku shigo gada ba fa"

"Eh ka san yanayin ne, sai muna bayyana muna ɓacewa, meye labari?"

"Baban Viper ne ya zo rumfa, ya na neman ka, ko kai ko walid" liti ya kalli walid ya kalli Viper.

"Meyafaru yake nemanmu?"

Ya ce "Ban sani ba, ya dai tambaye mu, ko Viper yana zuwa wurin, muka sanar masa rabonmu da shi, tun kafin a kama shi, shekara shida kenan"

Liti ya ce "Normal ne, zan faso fatan rumfa komai lafiya?"

"Lafiya ƙalau tana ta garawa"

Ya jinjina kai ya ajjye wayar.

Liti ya cigaba da kallon Viper, Viper bai kalle shi ba ya ce "Ko dai ka yi magana, ko kuma ka daina kallona"

"Allah ya baka haƙuri, na daina kallonka" kamar ya gaya wa Viper, zuwan mahaifinsa rumfar shayinsu, sai kuma ya fasa ya haɗiye maganar.

***

Abdul ne yayi sallama a falon, ya shigo a gajiye, ta amsa sallamar tana tashi zaune daga kwancen da take.

Ya ajiye jakarsa, ya kwanta a jikinta ya ce "Wash"

Ta ce "Sannu"

"Yauwwa sweetheart" ta kama hannunsa, ta cire masa agogon hannunsa.

"Tashi a cire safar"

"Ki bari na huta na gaji"

Ramma ta ce "Ƙato da kai kana shagwaɓa, wataƙila ma ba wani aiki ka yi ba kake wani wash"

Ya ce "Kaii, baby kin san mutum nawa na yi wa tiyata kuwa? Ga kusan asibiti uku naje na ga marasa lafiya"

"To tashi ka yi wanka, ka ci abinci" ya kalleta ya yi murmushi ya tashi zaune, ya shafa kanta ya ce "Allah ya yi miki albarka babyna, i so much love you" yayi maganar yana sumbatar goshinta.

Kallonsa take yi, tana son jin matsananciyar tsanarsa a zuciyarta, amma abu ya gagara, sai wani ma kyau da ta ga yayi mata.

Ya tashi ya tafi bedroom, yayi wanka, Ramma ta goge hawayenta tana fatan Allah kar ya jarrabeta da son Abdul.

Yayi salla ya fito, ta bashi abinci.

"Beb, in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe, zan bayyanawa duniya ke, ina daf da gayawa babana maganarki, a san yadda za a gyara lamarin mu cigaba da rayuwarmu, am ready na ɗauki kowane risk mu zauna tare in sha Allah my rahama"

Tayi ajiyar zuciya tare da murmushi.

"Dan Allah ko sau ɗaya ki ce kina so na mana"

"A'a ni ban iya ƙarya ba"

Ya ce "Zaki yi bayani ne"

***
"Hello masoyiyyata"

Nabila ta ce "Na'am sumy kalar kyau"

"Albishirinki?"

"Kuɗi dubu goma"

Sumayya ta ce "Mayyar kuɗi, ba za a bayar ba"

Tayi dariya ta ce "Fesa mini"

"Arfa ranar monday in Allah ya kaimu, zan fara aiki, ni da yaya murtala zamu buɗe gidan radion"

Nabila ta miƙe ta ce "Dan Allah masoyiyya"

"Wallahi da gaske, ke Allah ne ya kawo mana mafita, an bani damar ƙirƙirar programs, har na sami program ɗin da zamu din ga yi tare, mu ci karenmu babu babbaka, babu mai yi mana barazana da daka tsawa".

"Ke gani nan zuwa gidan naku ma, tare da ni za a buɗe gidan rediyon nan in sha Allah"

Duk wannan abubuwan da Nabila take yi, ƙarfin hali ne kawai, zuciyarta na tare da Viper, tunaninsa kawai take yi, tama rasa wane irin tunani take yi a kansa, ga zuciyarta da take ta azalzalarta da son ganinsa.

Tare da Nabila aka yi bikin buɗe sabon gidan radio, mutane suka din ga kiran wayar suna yi wa Sumayya fatan alkhairi, tare da tabattar mata da duk in da ta tafi suna tare da ita.

A program ɗin farko da suka fara yi da sumayya, suka sanya masa suna ƙeƙe da ƙeƙe.

Tun da sumayya ta gabatar da Nabila, kasancewar masu saurare sun santa a bakin sumayya, suke ta tura saƙonnin gaisuwa, wasu kuma suna tambayarta dalilinta na ƙalubalantar bunkure foundation, duk da irin gudunmawar da take bawa al'umma.

Sumayya ta ce "Masoyiyya, kin ji tambayoyin masu sauraro mai zaki ce?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Babu abun da zan ce, sai su kasance da mu a sabon shirinmu, na ƙeƙe da ƙeƙe. Ba wai bunkure foundation ba, duk wani abu da ake kitimurmura a cikin sa, ko rashin adalci zamu yi bajekolinsa a wannan shiri, kuma program zai iya bi ta kan kowa, duk wanda ya ga kuma an yi masa ba dai-dai ba ya ƙalubalance ni a gaban shari'a.
Manyan shari'oi da aka yi bita da ƙulli a ciki, yadda ake danne hakkin mara galihu ake tsayawa yaran masu kuɗi, yadda ake wasa da hankalin talaka, da tauye masa hakki, shi fa wannan program ɗin, kai har da shari'ar wani gawurtaccen matashi da ya shahara, jami'an tsaro suna nemansa, sai dai abun mamaki shi ne sai da ya shafe shekaru biyar ba ayi masa shari'a, a shekara ta shida aka sake shi, kuma yanzu an ce ba bisa ƙa'ida aka sake shi ba wai nemansa ake yi.
Akwai tarin kwamacla a harkar shari'a a ƙasar nan, a shirin ƙeƙe da ƙeƙe zamu fayyace abubuwa da dama, na ban mamamki" suka ƙarƙare program ɗin cikin wasa da barkwanci.

***
Alhaji wada hankali kwance yake zaune yana shan lemo a kofi, yana kallon indabo da yake ta haƙilo yana magana.

"Karofi, ka shiga gonata da yawa, ka kiyayeni, muddin kana son yarinyar nan ta rayu, ya zama dole ka takawa shirin nan da zasu fara gabatarwa burki"

Karofi ya ce "Sabod me? Kai da kake ɗaukar nauyin gidan radion ka ake abun da ka ke so waye ya hana ka? Ni na ɗauki nauyin program ɗin dan haka babu ruwanka da abun da ake yi"

"Karofi, ka san na fi ƙarfin kafi ga bayana ko?"

"Ai ka san shi ƙarfen cikin wuta sai da ɗan uwansa ƙarfe, babban mutum mai kima a ƙasar nan, bai kyautu ace ka na ɓata lokacinka a kan wata ƙaramar alhaki kamar wannan yarinyar ba.
Auuu ashe fa ta sako wani zance a maganarta, mai kama da maganar Al'amin Viper, wato mai zamani. Kana tsoron ta tona maka asiri cewa kai ne ka saka aka kashe matar Viper ko? Ka kwantar da hankalinka ba ta san wannan labarin ba, idan har ba tana haɗuwa da Viper ba ya gaya mata da kansa"

Wani irin shock indabo yayi, ya sandare a tsaye, jin yadda Alhaji mu'azzam wada kankarofi yake farke sirrin da bai taɓa tunanin wani mahaluki ya sani ba.

Ayshercool
08081012143

66
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724




Indabo da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce "Kankarofi"

"Indabo"

"Wace irin magana kake faɗa ne?"

"Irin wadda ka ji da kunnenka, ka zata daga kai sai waɗanda kuka aikata laifin ne ku ka sani? Kamar na so na fika iya playing cards ɗina ko?"
Indabo zai yi magana, Jidda ta shigo wadda ita ce matar kankarofi, kuma ƙanwar indabo.

"Yaya yana ganka a tsaye ne? Ba dai har tafiya zaka yi ba?"

Kankarofi ya ce "Eh, ya ce tafiya zai yi, dama ziyarar ta bazata ce, mu je na taka maka" kamar wawa haka indabo ya bi kankarofi suka fito.

Ya sake kallon indabo da yake ta rarraba ido, kamar shege a rabon gado ya ce "Ka fa kwantar da hankalinka, kar ka yi zaton zan gaya wa wani wannan sirrin tsawon shekaru  kenan, ina dakonsa ba wanda ya sani, ko ma na faɗa bani da wata ƙwaƙƙwarar hujja a kai, ina gargadinka ne kawai ka kiyayi yarinyar nan".

"Kankarofi"

"Indabo"

"Hawainiyarka ta kiyayi ramata, sanin wannan sirrin ba shi yake nufin kana da lago na ba"

Kankarofi ya ce "Na sani, na ankarar da kai ne kawai, na san abun da kake yi, dan haka kar ka tsallake gona da iri".

Indabo kawai ya jinjina kai zai juya ya tafi, Kankarofi ya ce "Na san zaka yi mamakin yadda aka yi na sani ko? Ba abun mamaki bane ba, kar ka je ka sakawa kanka damuwa da dogon tunani" bai ce masa komai ba, ya yi gaba.

***
Abdul yana kwance yana bacci, saboda daren jiya bai yi bacci ba, ramma tayi bacci, aka kira shi asibiti, sai bayan sallar asuba ya dawo.

Ramma ce ta shiga ɗakin a gigice, tana dukansa a kafaɗarsa.

Ya buɗe idonsa ya ce "Meye haka kuma?"

"Ka tashi"

"In tashi in yi miki me? Rahama ban yi bacci ba fa jiya, ina asibiti".

A gigice ta ce "Ina ruwana? Abdul ban ga al'ada wancan watan ba, wannan ma lokaci ya wuce"

"Kuma shi ne zaki tashe ni ina bacci?"

"Dole na tashe ka, me hakan yake nufi ka tashi ka duba ni, ba zan sake ɗaukar ciki ba, ni ka tashi ka duba ni"

Tashi yayi daga kan gadon, bai ce mata komai ba, ta bi bayansa tana kiran sunansa, amma ya rigata fita ya kulleta a ɗakin, ya tafi wani ɗakin ya yi kwanciyarsa.

***
Sosai sumayya take jan jama'a a sabon gidan radion da kama aiki, da ita da murtala.
Saboda bayan kasancewar ta sananniya, tayi ƙoƙari wurin samar da sabbin shirye shirye masu ƙayatarwa, wanda za su tafi dai-dai da matasa da ma dattijai baki ɗaya. Wasu daga cikin abokan aikinta da ta baro a can, suka din ga yi mata magiyar suma ta samar musu gurbi a in da ta koma, suma su koma. Yanzu sumayya ba ta da fargabar ta samo rahoto, a kushe ace mata ba irinsa ake buƙata ba, saboda kawai bai yi dai-dai da abun da wasu suke son ji ba.

Ranar farko da suka gabatar da program ɗin ƙeƙe da ƙeƙe ita da Nabila, program ɗin ya yamutsa hazo,  dan tayi sukuwa tayi zamiya, ta ƙarewa bunkure foundation ta tas da hukumar shari'a, tayi bayanin yadda shari'ar baba mai gadi ta kasance a kotu, tare da jaddada idan har da gaske dan al'umma suke ayyukansu, ya zama dole a bayyana ina ramma take, idan kuma da gaske tana asibiti, a bawa lauyoyi da ƴan jarida damar zuwa su ganota, kuma a kawo bayanin likita a kan abun da yake damunta zuwa lokacin da aka gaza ganinta a gaban kotu.
Hatta lauyan gwamanti ta din ga challenging ɗin sa, a yadda suka din ga taka doka yadda suke so.

Nan fa mutane suka din ga tururuwar kiran waya, wasu suna sharhi, ciki har da wani lauya mai zaman kansa, da ya kira waya, ya tofa albarkacin bakinsa tare da tabattar da akwai jabun lauyoyi da suke yi wa doka hawan ƙawara, a yi cuwa-cuwa a danne hakkin mai ƙaramin ƙarfi, a wanke yaran masu ido da kwalli, ire-iren foundations ɗin bunkure suna da yawa. Ya ƙara faɗaɗa bayanan da Nabila tayi, tare da fito da wasu abubuwa ma da ita hankalinta be kai, kai ba.

Nabila ta ji daɗin program ɗin sosai da sosai, dan kuwa ji tayi, zuciyarta ta rage raɗaɗi da baƙin cikin abun da aka yi musu a kotu.

Bayan kammala program ɗin, still cigaba da kiran wayar a aka yi, ƙarshe sai kashewa suka yi.

Sumayya ta ce "Mutuniyata kin yi bala'i fa"

Nabila ta ce "Ke ni ɗin ta wasa ce? Ai sai Najar bunkure ta zubar da hawaye, yanzu ta ƙarƙashin ƙasa zan yi analysis nawa ƙungiyar take samu na tallafi a wata, da kuma abun da ake spending wurin tallafwa mutanen da ake iƙirari. Ni ɗin fa ba ta wasa ce ba"

Sumayya ta ce "Ba wani ta wasa ko ba ta wasa ba, dole mu daga da Addu'a fa, Allah ya tsaremu Masoyiyya"

"Amin dai, amma yanzu meye abun yi?"

Sumayya ta ce "Eh to, kamar yadda ki ke tunanin kawo ƙarshen bunkure, ni kuma sonake na ci uban indabo, duk da ya fi ƙarfina, amma zai ga abun da 'yar matsiyata zata iya yi, dan wallahi sai na kusa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login