Showing 183001 words to 186000 words out of 479911 words

Chapter 62 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6159

babyna?" Yayi maganar yana shafa bayanta.

Ta ce "Ni babyn ko wa?"

"Ƙatuwa da ke ke ce babyn, unborn dai"

Boti ya hawo saman kujera, ya hawo jikin Jauhar, Al'amin ya kai hannu zai cillar da shi, ta riƙe shi tana dariya ta ce "Master dan Allah ka bari magen nan ya huta, duk ya tsaneka saboda cin zalinsa da ka ke yi, akwai buƙatar na yi muku sulhu"

"Babu sulhu tsakanina da wannan abun"

Ta ɗauki boti tana shafawa ta ce "Boti ku daina faɗa da master dan Allah" muzurun ya kawar da kansa gefe, Al'amin ya ƙwace shi ya ajiye shi a ƙasa, ya koma da baya yana kartar carfet ɗin yana yi masa kuka.

Jauhar ta din ga dariya, ta ce "Wallahi daga kai har shi dariya ku ke bani"

Al'amin ya lumshe ido ya buɗe, yana shafa cikinta ya ce "Duk kin zama ƙazama, kalli kin daina kitso, ga wata uwar riga kin saka, wadda sai an saka irinki goma a ciki, ni ɗaga rigar na din ga kallon jaririna"

"Master kenan, ba zaka gane ba, ni kaina ba na son zama da kan nan a haka, amma da an fara yi mini kitso zafi yake yi mini, kayana kuma duk sun yi mini kaɗan, amma idan na saka rigar nan taka, balance nake yi a ciki"

Ya kashingiɗa a jikin kujera, yana cigaba da kallonta, yana jin wani irin kusanci da shauƙin kasancewar sa da ita wuri ɗaya. Kullum yana ƙara girmama lamarin Ubangiji yadda ya ƙaddara kasancewar su tare, wanda idan ba ƙarfin ikon Allah ba, babu abun da zai haɗa shi da ita, har ya nemi aurenta. To wa ma zai bashi auren yarinya irin jauhar a yadda yake.

"Master ka san menene?"

Ya girgiza mata kai.

"Na ji an ce akwai lokacin da ma'aurata kan gaji da juna, ko miji ya ji matarsa ta gundure shi, dan Allah idan Allah ya raya mu ka fara jin irin haka a kaina, dan Allah ka yi haƙuri kar ka canza mini, na saba da kai sosai da sosai. Ina jin daɗin yadda na samu mai tausayina wanda ya mayar da ni mutum, yake zama ya saurari damuwata. Dan Allah ko nan gaba ka samu wadda ta fini, ko na fara gundurarka kar ka yi mini wulaƙanci ko ka manta da ni dan Allah" tayi maganar very serious.

Ya ƙura mata ido, yana mamakin maganganunta.

"To ai ni ko yanzu kin gundureni, duk kin hana ni rashin ji na, na saba da rayuwata ta ɓalla ƙarafa da hawa network duk kin hanani, zaman haƙuri kawai nake yi da ke, kin isheni"

Wasa yake yi mata, kawai ya ga tana kuka.

A ɗan rikice ya ce "Haba Madarata, ke yanzu idan aka ce miki zan yi miki abu makamancin haka zaki yadda? Ina sake maimaita miki ni ɗan halak ne bana manta alkhairi. A lokacin da kowa ya yasar da ni, yake yi mini kallon mara amfani a lokacin ki ka rungumeni a yadda nake, ki ka yi ya ɗawainiya da ni, ba tare da kin gaza kin ƙosa ba, bana fatan Allah ya nuna mini ranar da zance kin gundureni"

Ta share hawayenta ta ce "Ka san wani abu, kai diamond ne da mutane ba su farga da shi ba, suke maka kallon mara amfani. Sai yanzu da ƙyallinka da haskenka ya fito"

Ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana murmushi ya ce "Ke dai ki ke kallon hakan, ga al'umma na zama mara amfani, saboda ɗan daba ne ni"

"To ni dai kana da amfani a wurina"

Yayi murmushi ya ce "A ɓoye fa rigima kawai ki ke so ki yi na rarrasheki, to na ji sannu yi haƙuri"

"Yauwwa mata da yawa ba ayi mus irin yadda ka ke yi mini ɗin nan, zuciyar zinare ce da kai master, kana da tausayi sosai da sosai" ta kara kunnenta a ƙirjinsa ta ce "Zuciyarka sai kiran sunana take"

Al'amin ya ce "Ni dai yi magana a hankali, na ji babyna yana motsi, kar kwanciyar da ki ka yi ce kika takura masa, tashi zaune"

Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Master, zaka dawo ka tarar da ni, ina 'yar gala-gala da cikin nan, duk sai nuna banbanci ka ke yi"

Shi ma kallon fararen idanunta yake yi yana dariya, ya ce "To breakfast fa, me zamu ci?" Ta tashi zaune ta ce "zan dafa maka wani abun, amma ni anty wasila nake jira, za ta kawo mini wainar gero"

Ya tsuke fuska ya ce "Roƙo ko?" Ta ce "A'a geron da ka kawo na ɗiba na bata tayi mini, idan ni na yi ba zan iya ci ba"

Ya ce "Ok"

Har azahar yana gida, jauhar ta hana shi fita, sai azahar yayi shiri ya fita, saboda sallar azahar, yanzu jauhar ta daina fama da shi a kan yin salla a kan lokaci.
Sai ga anty lubabatu, ta zo maƙwabciyar su mai ba ta aikin bead a gida.

"Oyoyo anty lubabatu, yau ke ce a gidan".

"Yau gani na lallaɓo, an ce mini kin kusa juyewa, na ce bari na zo ga ya kike"

Jauhar ta ce "Ohh ni zahra'au in ji wa? Ba a gaya miki daidai ba"

"Eh ba a gaya mini ba, ni na gani yanzu ai"

Da sauri jauhar ta kalli cikinta ta ce "Haba dai dan Allah a na gani" Anty lubabatu ta kwashe da dariya ta ce "Lallai yarinya, wannan uwar ƙibar da ki ka yi ma da haka ki ke? Kin zama uwar mata"

Juahar ta yamutsa fuska ta ce "Na yi muni ko?"

"A'a babu wani muni, wallahi kin yi kyau, kallo ɗaya mutum zai yi miki ya san a kwanciyar hankali ki ke. Jauhar gyaran gida aka yi miki haka, lokacin da na zo gidan nan kina amarya tsurar bulo ne fa, ikon Allah har da sola, wato a duniya idan Allah yana yinka ko wa ma yaƙi ka. Ga Alhaji mu'azzam can Allah ya bar su da shi, matarsa na ta gana wa hafsa azaba, abu har da 'yan sanda, ya ce idan ba zata zauna da matarsa lafiya ba tayi mata biyayya ta tafi gida. Gidanku kuma ana ta tashin hankali, Anty zakiyya ta ce mama ke yi mata asiri"

Cikin damuwa jauhar ta girgiza kai ta ce "Bari kawai Anty lubabatu, lamarin gidan nan namu sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma wasu lokutan har da laifin baba, kodayeke shi ma sun mayar da shi sai yadda suka yi da shi, ai da ni aka ce ina yi wa hafsan asiri. Ko gidan ya hanani zuwa, sai idan da daddare ya kaini na gaida baba na dawo gida"

"Allah ya taimake ki, ke da suka so su tozarta rayuwarki Allah ya rufa miki asiri, ɗan daban da suka aura miki dan ki wulaƙanta, hakan ba ta faru ba"

"Tababs babu abun da zan ce wa Allah sai godiya, Anty lubabatu mijina a maza ɗari irnsa ɗaya ne tak. Daba da shaye-shaye su ne ƙaddararsa amma, ya ci sunansa amintacce rauninsa mutane suke kallo, basa kallon nagartarsa" sun daɗe suna hira sosai kafin ta tafi.

Kusan duk bayan kwana biyu zuwa uku, sai hajiya kakar Al'amin ta kira Jauhar ta yi mata ya jiki, dan tun wani zuwa da tayi ta fuskanci hakan.

Tun da ya fita da azahar har bayan magariba bai dawo ba, sai da ta kira shi a waya, ya ce mata gashi nan.

Hnakali a tashe ya dawo mata, dan sai da gabanta ya faɗi ya ce "Master lafiya?"

"Nura aka kawo daga Abuja, wai ba shi da lafiya, tun lokacin nan da ya ce mini ba shi da lafiya, yake kwance"

Ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka?"

Ya ce "Ban sani ba, an dai kai shi asibiti, na je na ganshi a galabaice, yayi magana ya faɗi meyake damunsa ya ƙi, na ga a galabaice yake sosai, an saka masa ruwa da sauran abun da yakamata gobe in Allah ya kaimu dai zan koma".

Jiki a sanyaye ta ce "Allah sarki Nura, sai da ka ce idan ba zai iya ba ya dawo, wataƙila dan kar ka yi masa faɗa ne ya zauna bai dawo ba. Allah ya bashi lafiya"

Ya amsa da Amin.

Ya ciro mata envelope ya ajiye mata.

Ta ce "Menene wannan?"

Ya ce "Duba ki gani mana"

Hotunasu ne shi da ita, wanda galibi a wayarta suka yi, ya kai aka ciro su, sai kuma ƙatuwar viva, da aka yi frame ɗin hoton da suka yi na sallar eid ɗaya an rubuta musu happy marriage life, ɗaya kuma an rubuta first eid with habibi.

Tayi murmushi ta ce "Kamat yayi a rubuta Master weds madara" duk da a cikin damuwa yake sai da yayi murmushi, ya ce da safe zai kafe a falo.

Ta kalleshi tana murmushi, bai taɓa ce mata yana son ta ba, sai dai actions ɗin sa, yana tabattar mata da hakan. Da fari kai ba ka ce ya iya duk wani abu da yake da alaƙa da kulawa ba, saboda he's always serious, sai dai a hankali ainihin halayensa suke fitowa.

Jikin Nura yayi tsananta, kullum Al'amin cikin sintiri yake, jauhar ce mai lallaɓawa tayi musu girki, mahaifiyarsa ce take zaune da shi a asibiti tana kula da shi, gashi an rasa gane abun da yake damunsa, Al'amin har gona ya saka aka sayar masa a ƙauye, saboda kula da Nura, dan asibitin kuɗi ya saka aka mayar da shi.

Da daddare babar Nura ta fita, Al'amin ya zo, cikin ƙarfin hali ya ce wa Al'amin "Yau ina Antyna ba ta zo ba?"

Ya ce "Eh, ni na hanata zuwa, tayi nauyi. Nura yakamata zuwa yanzu ka gaya mini menene yake damunka, ana ta kashe kuɗi an rasa gane abun da yake damunkaa yayi maganar cikin damuwa"

Nura ya ce "Idan na gaya maka ba zaka yi fushi da ni ba?"

"Ya za ayi na yi fushi da kai? Ka gaya mini in san ta in da zan kamo bakin zaren".

Ya riƙe hannun Al'amin ya ce "Na san ba lallai na rayu, amma ba ka da laifi ka taimaki rayuwata ne. Na gayawa mama na ce kar ta gaya maka. Lokacin da na ce maka na fasa tafiyar nan, Honorable ne ya ce sai ya yi ɗabi'ar mutanen annabi luɗ da ni, na ƙi yarda, ni kuma na kasa gaya maka, dan ya ce idan na gaya maka, kashe mai unguwa zai yi, amma idan na amince shikenan, ba wanda zai san an yi kuma zai bani aikin.
Na ɗauka daga haka shikenan, sai dai tun da ya tafi da mu, a wani gida aka ajiye mu, abun da suke yi mana kenan, yana da masu kula da mu, babu ta in da mutum zai gudu, kuma ba shikaɗai ne yake yi mana hakan ba, akwai wasu manyan mutane a ƙasar nan, da duk zan gaya maka sunayensu.
Kuma kamar tsafi suke yi ta hanyar amfani da mu, bana iya riƙe bayan gida, mama ce take gyara mini kafin mutane su zo dubiya, Indabo ya lalata mini rayuwa amma ka rufa mini asiri dan Allah, kuma kar ka zargi kanka! Ina da hujja mai ƙarfi da zan baka a kan haka!

Ayshercool.
08081012143

45
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724




Gaba ɗaya fuskar Al'amin ta sauya takmar ta horo, ta koma Al'amin ɗin sa na ainihi, tamkar bai taɓa sanin wani abu wai shi dariya ba. Wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa, jijiyoyin goshinsa zuwa kansa suka miƙe suka kukkumbura, idonsa yayi wani irin ja mai ban tsoro, bugun zuciyarsa ya ƙaru da saurin gaske, jikinsa ya fara ɗaukar wani irin zafi saboda tashin hankali da tsananin ɓacin rai.

Ba tare da tunanin halin da Nura yake ciki ba, yayi wa hannun guduma wani irin mugun riƙo, da sai da ƙasusuwansa suka yi ƙara.

Nura ya ɗora ɗaya hannun a kan na Al'amin ya ce "Yaya, kai ɗan uwa ne da Allah ya bani rana tsaka a titi, duk wannan abun ka yi ne dan inganta rayuwata, ba ka taɓa yin wani abu da zaka cuceni ba, na san da ka san abun da zai faru da ni kenan, ba zaka bari na je ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka, ni na san ba zan rayu ba, abun da suka yi mini ya fi na kowa muni da tashin hankali, ban san yaya zan misalta maka ba, amma dan Allah kar ka yi yinƙurin yin wani abu, idan ba haka ba za su yi maka illa. Na bar su da Allah ka tayani Addu'a Allah ya yafe mini laifukana, idan na mutu dan Allah ka yi mini wanka kar asiri na ya tonu, ba na son a zargeka da abun da mutane ba su san menene ainihin abun da ya faru ba.
Wurin bayan gidana ya riga ya ɓaci, kowa ya gani zai gane meyafaru dan Allah kar wani ya je kan gawata idan ba kai ko mama ba"

Al'amin ya riƙe hannun Nura gam, amma ya kasa magana sai wani irin numfashi mai haɗe da huci, ya sunkuyar da kai yana sauke numfashi.

Yanayin yadda mahaifiyar Nura ta tarar da Al'amin, ya sanya ta gane ya gaya masa.

Ta ƙarasa gaban gadon, jiki a sanyaye ta ce "Al'amin, ka kwantar da hankalinka dan Allah, zan iya dafa Alqur'ani na rantse, ba zaka kai mini nura in da za a cutar da shi ba, na san da ka san me zai faru kenan ba zaka yadda ya je ba, a irin yadda yake bani labarin zamanka da shi. Iya ɗawainiyar da ku ka din ga yi da mu kai da matarka ya ƙara tabattar mini da haka. Cuta ce an riga an cuce mu, amma mun bar wa Allah, ni ba zan zargeka ba"

Ya saki hannun Nura a hankali, ya tashi ya juya ya fice.

Nura yayi ajiyar zuciya ya ce "Allah ya sa kar ya ce zai ɗauki wani mataki, dan mutanen nan sun wuce duk yadda yake tunani, ni dai ku cigaba da yi mini addu'a da fatan cikawa da imani"

Duk da juriya da mahaifiyar Nura take yi, sai da ta kasa ta zubar da hawaye, cike da karaya, dan magana kawai Nura yake yi, amma komai sai an yi masa, gashi buni-buni jininsa ya ƙone, sai an saka masa wani, dan bayan bayan gidan, har da jini ne yake zuba daga wurin, jini sosai ba kaɗan ba, a tunaninsa da na mahaifiyarsa ɓoye wa likitocin ainihin abun da ya faru shi ne rufin asirin su, dan babu wanda zai fahimce su, cewa za a yi shi ya kai kansa, saboda kwaɗayi da son abun duniya, dan Nura ya yi girman da ya fi ƙarfin ace dole aka yi masa.

Ikon Allah ne kawai ya kai Al'amin gida, dan ko me za ayi masa bai san ya aka yi ya isa gidan ba.

Jauhar har ta yi bacci, dan 'yan kwanakin nan bacci take yi sosai da sosai, duk in da ta ji kwanciya ta yi mata daɗi sai bacci.

Ba ta farka ba, sai bayan sha biyun dare, shi ma dan taji ta gaji da kwanciyar ne, a hankali ta tashi jikinta duk yayi tsami, ta kalli ƙofar ɗakin Al'amin, ta tashi ta nufi ɗakin, ta ɗaga labule ta shiga.

Yanayin kwanciyar da ya yi, ya tabattar mata da yayi shaye-shaye ya bugu, dan wata irin kwanciya yayi.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban katifarsa ta zauna a hankali ta ce "Haba master yau kuma?" Dan bai fiye shan abun da zai gusar masa da hankali gaba ɗaya har haka ba, yana yi amma ba sosai ba, ya fi ganewa busa hayaƙi. Kuma kwanakin nan da Allah ya taimaketa tayi galaba a kansa, bai fiye shan abun buguwa ba sai shan sigari, wiwin ma ya rage shan ta sosai, amma ta zo ta tarar da shi a wannan yanayin.

Da ƙyar tana haki, haka ta gyara masa ƙafarsa da hannunsa, ta shafi sumar kansa, sai wani irin gumi yake yi, naman fuskarsa yana ɗan yi rawa lokaci zuwa lokaci ga ajiyar zuciya da yake ta yi a kai kai.

Ganin ba ya hayyacinsa, balle su yi magana, ya sanya ta tashi ta tafi ɗakinta, cikin zullumi da tunanin me aka yi masa?.

Kiran sallar farko ya farka, sai dai zuciyarsa cike da tsananin baƙin ciki da ɓacin rai, ya san ko ya je gida ba zai samu indabo ba yana Abuja, kuma ba zai iya tafiya Abuja ba, cikin fargaba zai tafi kar yana matsawa wani abun ya samu Nura.

Alwala yayi ya fice, a hanya yayi sallar asuba, ya ƙarasa Asibitin, maman nura na ta kokowar yadda zata ɗaga shi, ta saka masa pampers, yayi mata girma.

Al'amin ya bubbuga ƙofar, ta ce "Waye?"

Da ƙyar ya iya magana ya ce "Al'amin ne"

Nura ya ce "Mama buɗe masa"

Ta buɗe masa ya shigo, Nura ya gaida Al'amin, jinjina kai kawai yayi, suka gaisa da maman Nura, da ƙyar yake iya magana, saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali.

Ya taimaka mata, suka canzawa Nura pampers, jinin da Al'amin ya gani a pampers ɗin ya ɗaga masa hankali, gaba ɗaya halittar duburar Nura ta fito waje, babu ƙyanƙyami babu komai, ya taimaka mata suka gyara shi, suka saka masa pampers uku, kamar yadda take saka masa, sai kuma ta kawo zannuwa ta tuttura masa ta toshe ko ina, ta fesa masa turare, ta kunna turaren wuta, ta shiga banɗaki ta wanke kayan da aka cire mas.

Al'amin ya rasa me ma zai cewa Nura, abun duniya ya ishe shi, ya ji ya tsani kansa, komai baya yi masa daɗi.

A hankali ya kalli Nura ya ce "Zan gaya wa likitoci, su duba idan da abun da za a iya yi, ayi maka babu dabara a ɓoyewa likitoci wannan lamarin"

Da sauri Nura ya ce "Dan Allah kar ka yi mini haka, ka rufa mini asiri, wallahi babu wanda zai yadda dole aka yi mini, na san ba zan rayu ba, lokaci kawai nake jira, dan Allah yayana wannan ce alfarmar ƙarshe da zan nema a wurinka, dan Allah kar ka gaya wa kowa"

Cikin matsananciyar damuwa Al'amin ya ce "Nura ka yafe mini, wallahi ban san abun da zai faru ba kenan, na zata hakan zai taimaki rayuwarka ne... Sai ya kasa ƙarasawa muryarsa ta fara rawa.

Guduma ya ce "Wallahi na sani, kai mutumin kirki ne yayana, dan Allah idan na mutu ku din ga yi mini addu'a, na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login