Showing 369001 words to 372000 words out of 479911 words

Chapter 124 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6166

d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327  Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327  sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊



Abin da Nabila ta faɗa ya sanya Viper jin ƙirjinsa ya tsananta bugawa.

Ta sake cewa "mu yi zumunci kawai, zumuncinmu ya ɗore, amma yanzu na fahimce ka, da ka yi ta jaddada mini, ba zan taɓa zamo wa jauhar ba" zai yi magana.
Hafsa ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama, hannunta riƙe da leda cike da kayan marmari, ta ƙarasa tana murmushi.
Bayanta saifu ne yake biye da ita, tana zuwa ta dungurar da ledar ta zauna a kusa da Nabila ta ce "Waliyiyya kin warke ya jikin?"

Nabila ta yi murmushi, ta fuskanci Hafsa 'yar uwatta ce, dan tana kama da ita kaɗan, ta ce "Jiki Alhamdilillah".

Ta kalli Viper ta risuna ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau yaya hafsa" ya kirata da yadda jauhar take kiranta.

Sai ta yi murmushi ta sake kallon Nabila ta ɗora hannunta a goshin Nabila ta ce "Ba kya zazzaɓi ma, kin warke sai mu tafi da ke gida ko? Ko gidanku zaki koma ke da shi? Har gidan naku nake zuwa ba a sani ba, baba ya ce idan na kuma zuwa Yaya tijjani ya zane ni"

Saifu ya kalli Nabila ya ce "Yaya jikin naki?"

Nabila ta ce "Na ji sauƙi Alhamdilillah"

"Allah ya sauwwaƙe, ga hafsa nan ita ma yar uwammu ce, yakamata ace duk an gabatar miki da yan uwanki, amma sai Allah ya sa kin warware, zan je duba wani abokina, idan na dawo zan zo na ɗauke ta. Ina amfani da wannan damar wurin baki haƙuri, da nema wa mahaifinmu afuwarki ki yi haƙuri dan Allah. Sannan ku yi haƙuri da abubuwan da za ta yi, tana misbehaving wasu lokutan, tana fama da matsalar ƙwaƙwalwa ne, ta damu a kawota wurin ki ne"

"Baba ya ce kar ka sake ce mini mahaukaciya, ni da hankalina dan Allah jauhar na yi kama da mahaukaciya?" Hafsa tayi maganar kamar zata yi kuka.

Nabila ta girgiza kai ta ce "Ko kaɗan" Saifu ya juya ya tafi, ba tare da wani ya kula wani tsakanin sa da Viper ba.

Bayan ya fita Hafsa ta ce "Jauhar ina jaririnki ne?"

Viper ya ce "Ba jauhar ba ce ba" ta kalli Nabila ta kalle shi ta ce "Ita ce mana"

Ya ce "Kalle ta da kyau dai" ta sake ƙurawa Nabila ido, ta kalleshi ta ce "Jauhar ce mana, ina ɗan naku to?"

Ya ce "Tambayeta"

Nabila ta ce "Ta tambaye ka dai"

Viper a hankali ya ce "Ya rasu"

Ta ɗan yi shiru ta ce "Shi ba zai dawo ba kenan kamar yadda ita ta dawo, to yaushe zata samu wani cikin, ina son na ga ta haihu wallahi, ka san baba cewa yake yi, idan ku yi aure ku haihu da ƙuruciyarku, sai su zama kamar ƙannenku" gum Nabila tayi jin katoɓarar da Hafsan tayi.

Gaba ɗaya suka yi mata shiru, ta kalli Nabila ta kalli Viper ta ce "Baku gaya mini ba"

Viper ya kalli Nabila ya ce "Abla tana magana, yaushe zaki sake samun wani cikin ki haihu?"

Nabila ta ce "Na shiga uku"ta yi maganar tana sunkuyar da kai, sai ya faɗi magana ya wani maze kamar ba shi baz wannan nannauyar maganar tayi masa sauƙin faɗa haka yana kallonta.

Ya basar ya ce "Ina mijinki ne?"

"Ni bani da aure, rabuwa muka yi, uwargidansa ta hana shi kula ni, sai dai ya ɗauketa su tafi yawo su bar ni a gida. Nayi ta kuka na gaya wa Anty, amma wai na yi haƙuri, na zo na daina bacci, na je asibiti aka bani wani magani na kwana biyu, tun daga ranar da nayi bacci na ji daɗi, na din ga kai wa wani mai chemist yana bani ina sha, har ya fara ƙara mini da wasu ina sha.
Gaba ɗaya baya yi mini irin yadda ka ke yi wa jauhar, idan na zo gidanku naga yadda ku ke yi, in yi ta kuka, kuma fa anty ce ta din ga bani magani dan ya aure ni, amma wallahi ina son shi, na din ga shaye-shaye da ban san shi nake yi ba sai daga baya. Zama yaƙi daɗi ya sake ni. Bayan ya sake ni fa sai da ya auri wata kuma ta zauna ita ba ayi mata irin yadda aka yi mini ba. Na cigaba da shaye-shaye damuwa ta yi mini yawa, mai chemist yayi mini haɗin wata ƙwaya ya ce zan manta da damuwata ashe ƙwaƙwalwa ta ya taɓa mini sai aka ce wai na zama mahaukaciya. Amma nima na san alhakin ki ne ya kama ni, ki yafe mini dan Allah ƙanwata"

Nabila da tausayin Hafsa ya sanya ta fara hawaye, ta kalle ta ta ce Jauhar zuciyarta daban ce, ta musamman ce. Ita ai kusan kun gama yi mata komai da ku ka aura mata sanyin idaniyarta.

Turo ƙofar ɗakin aka yi hafsa ba ta waiwaya ba, amma ta tsorata gabanta ya faɗi, jin ƙamshin turaren Alhaji mu'azzam ya cika ɗakin.

Sallama ya yi suka amsa masa, ta ɗaga kai a hankali, suka yi ido huɗu da shi, gabanta ya sake faɗuwa, zai iya cewa tun da ya saketa bai sake ganinta ba sai yanzu.

Jan jikinta tayi, ta haye gadon da Nabila take.

Ya miƙa wa Viper hannu, amma Viper ya tsaya yana kallon sa, Nabila ce ta ɗan gyaɗa masa kai, a hankali ya miƙa masa hannu, suka yi musabaha. Ya ja wata kujerar ya zauna.

Ya ce "Barrister ya jikin?"

"Alhamdilillah" ta amsa a hankali.

Ya kalli Viper ya ce "Ashe ka kawo ƙarshen labarin da kanka?"

Viper fuskarsa babu yabo ba fallasa ya ce "Eh na kawo"

"Na san kan labarin ya ƙarƙare da sauran rina a kaba, ina yi muku fatan alkhairi. Nabila zuwa yanzu kin san wanene ni, da dalilin da ya sanya na din ga bibiyarki, ta tabbata jauhar Sister ɗinki ce ko? Duk na san mahaifinki, ban yi garajen sanar da shi komai ba, saboda binciken da nayi a kanki, babu ta in da ya nuna jauhar da ke akwai alaƙa, ashe akwai ɗin dai. Na tayaki murna"

Nabila ta jinjina kai ta ce "Na gode sosai, Jauhar da ni twins ne, abubuwan ne da tsayi sosai amma bani da bakin yi maka godiya Allah ya saka da alkhairi. Ga wannan ita ma tana cikin 'yan uwana, sunanta hafsa"

Ya kalli hafsa da tayi tsuru, yayi murmushi ya ce "Na santa ai, hafsa mun san juna ko?" Hafsa ta kalleshi, kawai ta dira ta ɗaya side ɗin, ta zari takalmanta za ta fita, Nabila ta ce "Ina zaki je?"

Ba ta juyo ba ta ce "Waje zafi nake ji, kar ki da mu ina da hankali ba wani wurin zan je ba" ta kai bakin ƙofa walid ya turo ƙofa ya buge mata goshi.

A rikice ya ce "Ya salam, yi haƙuri dan Allah, ban dan kin taho ba" ta yi murmushi ya ce "Bakomai ai babu zafi tayi waje.

Suka shigo ɗakin, suka gaisa da Alhaji mu'zzam, ya tashi da hanzari ya ce "Bari na je waje na amsa waya, daga nan zan wuce, amma ina son zama da ku, a kan shari'ar nan amma ina zuwa dai" Alhaji mu'azzam ya fice daga ɗakin.

Kawai suka ga Viper ya saka dariya, gaba ɗaya suka zuba masa ido, Nabila tunani take yi, anya ta taɓa ganin dariyar Viper haka.

Walid ya ce "Mutumina meyafaru ne ka ke dariya, dariyar da rabonka da ita tun 'yar madara na raye"

Ya ce "Muhsin, wani abu ne ya bani dariya"

"Akhbirni mutumina, meyafaru ne?"

Ya tsagaita ya mayar da dariyar murmushi ya ce "So mugun wasa ne, mai saka ma'abocinsa yi masa biyayyar dole ko bai shirya ba, babu wata waya fa da zai amsa, ya bi matarsa ne kawai, maybe yana kewarta"

Nabila ta ce "Ita ce Hafsan da oga walid ya bani labari, dama zancen Alhaji mu'azzam take yi?" Viper ya jinjina mata kai alamar eh.

"Ikon Allah, yanzu duk tsawon wannan lokacin kun san komai, ku ka rufe ni"

Viper ya ce "Yanzu ai gashi kin sani".

Can bayan ɗakin Nabila ta zagaya, hawaye na zubowa daga idanunta, ta tsaya tana ta share hawayenta, ta jima a tsaye tana share hawayen, sannan ta juyo da niyyar komawa, kawai ta ga Alhaji mu'azzam a bayanta a tsaye.

Tsuru-tsuru ta yi kamar mara gaskiya.

"Haba hafsa, ko gaisuwa babu, tamkar dodo daga ganina sai ki hau gudu? Ya goshin naki?"

Cikin inda inda ta ce "Lafiya ƙalau, babu zafi"

Alhaji mu'azzam ya ce "Ya kumbura fa, kuma ki ce babu zafi?" Ta ɗaga kai alamar eh.

Ya taka a hankali zuwa gabanta, ya mamaye ta da ƙamshin turaren sa, ta kalleshi, yana sanye da yadi ash mai tsada riga da wando, Alhaji mu'azzam akwai kwalliya da ado.

"Kin ga wata sabuwa daban mai kama da jauhar ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a jauhar ce".

"Ba jauhar ba ce, wannan sunanta Nabila. Hafsat" ya kira sunanta a hankali.

Tsigar jikinta ta tashi, taƙi kallonsa.

"Meyake damunki ne? Kin rame kin yi duhu, ba gayunki kamar da, meyafaru haka?"

Kawai kuka ya ƙwace mata, har da sheshsheƙa. Jauhar yake so ba hafsa ba, amma yana tausayin ta mussaman da ya ganta yanzu. Daga baya ya fuskanci ba wai kuɗinsa kawai take yi wa ba, tana matuƙar son sa.
Amma shi kansa bai san ya aka yi ya din ga misbehaving ba, kuma a lokacin ƙanwar indabo tsohuwar budurwarsa jidda tana ta bibiyarsa ya aureta.

Handkerchief ɗin sa ya ɗaukko, ya fara share mata hawayen. Ƙoƙarin rasa nutsuwar sa ya fara yi, ita ma ganin idan ta cigaba da tsayuwa, za su iya ɓarna, dan har wani tsuma take yi, soyayyar sa ƙamshin turaren sa, da maganganun da ya fara yi mata, narka mata zuciya yake yi, hakan ya sanya ta buge hannunsa daga fuskarta, ta raɓa shi ta bar wurin.

***
Abdul yana kwance a gadon asibiti, hannunsa ɗaya da ankwa, mahaifiyarsa na gefe tana ta uban kuka, tamkar an ce mata gawar Abdul ce a gabanta. Ga Indabo can yana fuskantar hukunci. Jami'an tsaro na son ɗaukar statement dan a shiga kotu, amma ko magana ba ya iya yi, idan ya yinƙura sai aman jini.

Bunkure ma kamar zata haukace, dan ko ta wani ɓangare tana samun suka, kuma babu sassauci. Mutane sun fara juya mata baya, tare da gazgata zancen Nabila da tayi a kanta a kwankin baya aka din ga attacking ɗin ta.

Nabila ta bar Asibiti, ta koma gidan madam Halima.
Viper ya dage da yi wa Nabila nasiha, tare da tausarta, a kan ta karɓi mahaifinta, tayi haƙuri sannan ta nemi gafarar major shi ma, dan bai cancanci abin da tayi masa ba.

"Ni ka ƙyale ni dan Allah, in ji da raɗaɗin rashin 'yar uwata da hake addabar ruhi da gangangar jikina, koma menene ya faru laifinsu ne na kasa samun nutsuwar karɓar dukkaninsu".

A fausace ya hau ta da faɗa "Are you out of your sense, rayuwata ba ta zama darasi a gare ki ba? Duk abin da ya faru a tsakaninsu, ke ina ruwanki ne a ciki? Could you imagine mahaifinki na yi mini kuka a kan na shawo masa kanki ko sau ɗaya ki yi masa kallon uba, ya riƙe ko da hannunki ne, ya ji daɗi? Ya rasa jauhar, babu tsammani kin bayyana a gare shi, ba tare da ya san ki na raye ba, amma kin ƙi saurarsa ina ruwanki da abin da ya riga ya wuce? Wallahi ko kaffara ba zan yi ba da yar uwakki ce ba zata yi haka ba, jauhar ta daban ce, mai tausayi da jin ƙai ce. Na san da ke aka yi wa abin da aka yi mata a kaina bijirewa zaki yi. Da haƙuri da siyasa ake cin ribar zaman duniya ba fushi da shirme ba. Kin nuna rashin jin dadin ki abin da aka yi miki da farko daga baya kuma sai ki saukko ki haƙura ai"

Sumayya da tana wurin, ita kanta sai da ta tsorata da faɗan da Viper yake yi.

Nabila kuwa kuka take yi wiwi, wasu lokutan gara faɗan Abba da na Viper, gaba ɗaya sai ya razanata ya saka ta rasa abin da yake yi mata daɗi.

"Ki tashi ki shirya, zamu je ki nemi afuwarsa, sannan mu je mu ga ɗan mama, da su Rahama"

Haka Nabila ta shirya, sumayya tana ta mamakin samun abin da zai iya tsorata Nabila ya sakata kuka, bayan Abba.

Yau ma a ƙofar gidan su jauhar, aka yi parking, tare da sumayya suka zo, da sallama suka shiga.

Baba yana gareji, yana ba wa saifu sallahun wanke masa mota, Nabila suka shiga.

Cak ya tsaya yana kallon su, da sumayya da Nabila.

Kallo ɗaya Sumayya ta yi wa Baba ta gane baban Nabila ne.

Rikicewa yayi ya nufota duk da jikinsa a sanyaye ya nufeta, idanunsa cike da hawaye.

Yana ƙarasowa ta faɗa jikinsa tana sakin wani irin kuka mai karya zuciya.

A hankali ta ce "Baba" tana kuka yana kuka, kamar wani zai ƙwace masa ita, haka ya ƙanƙame Nabila, yana kuka har da majina.

Sumayya da take tsaye ita ma fashewa ta yi da kukan, cikin matsanancin tausayin su, ta san irin artabu da ƙalubalen da Nabila ta din ga fuskanta a kan rashin uba, a gidan major yadda suke kiranta da tsintacciyar mage wai babu wanda ya san babanta, Nabila ba ta da wata magana da ta wuce fatan ganin mahaifinta, ta ji ina ma ita ma tana da rabon sake ganin mahaifinta a rayuwa.

Viper yana hango su daga waje, ya sunkuyar da kansa hawaye na cika masa ido, cike da fatan ina ma shi ne ya sake ganin Jauhar ta bayyana a rayuwarsa ba tare da ya yi tsammanin hakan ba.

Nabila ta ce "Sumayya ga babana, kin ga babana"

"Na gan shi Nabilata, Ina tayamu murnar ganin Baba, burin da muka daɗe muna fatan Allah ya cika mana"

"Ki yafe mini 'ya ta, abin da ya faru ba da son raina ba ne ba, wani abu ne da ba zan ce ga a yadda ya faru ba, na san mai laifi ne a gareku da mahaifiyarku, ke kaɗai ki ka rage mini a cikin su, dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini" yayi maganar cikin matsanancin kuka.

Ya rungumi Nabila zuwa cikin gidan, sumayya na biye da su, yaran gidan duk su ka kewaye su, wasu na taya su kuka wasu na kallon su.

Ya ce aje a ce wa Al'amin ya shiga.

Nabila ta kwantar da kanta a kan cinyar baba, tana cigaba da kuka.
Bayan Viper ya shigo su ka gaisa da Baba, ya kalli sumayya ya kalli Viper ya ce "Anya Aminullahi wannan ma ba tawa ba ce?"

Viper ya yi murmushi ya ce "Duk naka ne Baba, an baka"

"Na san fuskarta ne, ta na kama da wani wanda na sani, amma ba zan iya tuna waye ba? Ya sunan mahaifinki?"

Sumayya ta share hawayenta ta ce ba ni da wayon sanin mahaifina, amma dai sunansa Tahir ladan.

A take ya yi sak, ya ce "Wane Tahir ladan ɗin? Coustom ne?"

Sumayya ta jinjina masa kai ta ce "Ka san shi?"

Yayi shiru ya ce "Tare mu ka je ɗaurin aurena a jalingo, abokin aikina ne, lokacin da aka yi mini transfer daga in da na bar mairamu shi ne ya koma, ya je yayi reporting a wurin aiki, ya koma yayi hatsarin mota ya rasu.

Viper ya ce "Kenan dai duk 'ya'yan naka na kawo maka"

Kamar ƙaramin yaro ya kalli Sumayya ya ce "Ni babanki ne, ke ma 'ya ta ce ai, na gode Aminullahi, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"

Viper ya ce "Baba da ka yi haƙuri da kukan nan haka, saboda su ma su samu ƙwarin gwiwar yin haƙuri, mu gode wa Allah kawai"

Ya jinjina kai yana maimaita Alhamdilillah.

Baba ya din ga shafa kan Nabila, amma hawayensa suka kasa tsayawa.

Zakiyya tare da maman hafsa su ka shigo ɗakin da sallama, su na kallon yadda ya saka su Nabila a gaba yana kuka.

Viper ya na ganin Zakiyya ya haɗe rai, tamkar ya ga abin ƙyama.

Su ka zauna su ka din ga surutai marasa ma'ana, marasa tushe balle makama. Tare da taya su kukan cike da makirci.

"Baba ina hafsa?" Nabila ta tambaya da kyar.

"Ta je gidan kakaninta da su ka haifi mahaifiyarta".

"Baba shikenan ban san jauhar ba, ba kuma zan ganta ba, ban san mama ba, ita ma kuma ban santa ba, mun rayu a wurare daban-daban, ba mu san juna ba" tayi maganar tana sake fashewa da kuka.

Cikin sigar rarrashi ya ce "Hakan hukuncin Allah ne, ki yi haƙuri, mu masu tarin laifi ne a wurinki, mussaman ni, na san ni ne baban mai laifi, duk da major ma mai laifi ne, bai kamata ƙiyayyar da yake yi mini ya sanya, ya nesanta ni da ke ba, ya kawo mini yarinya amma bai kuma waiwaiyarta ba, amma Alhamdilillah na ji dadin yadda ya kula mini da ke"

Viper ya numfasa ya ce "Baba yakamata mu koma haka, da su"

Baba ya ce "Aminullahi, dan girman Allah ka bar mini ita"

"Ka yi haƙuri, ai aikin gama ya riga ya gama, tun da har komai ya riga ya bayyana, sai da na saka hannu na ɗauki excuse sannan na fito da ita, shi ma bisa uzurin aiki za ta yi, kuma ka ga a hannun Abba aka yi yarjejeniya a ka ɗauketa, da niyyar ba ta kariya, har a kammala shari'ata, addu'ar ka muke fata".

"Yanzu ka na nufin mijin 'yar uwatta take karewa, Allah al-hakimu, Allah ya bayar da nasara, yayi muku jagora dukkaninku"

Su ka amsa da Amin gaba ɗaya.

Baba ya ce ya bari su ci abinci, Viper ya ce "Lokacinsu a ƙididdige yake, idan su ka saɓa akwai matsala"

Har gaban mota ya rako su, yana rungume da Nabila kamar zai mayar da ita cikin sa.

Su ka je bakin motar, ya riƙe hannun sumayya, ya riƙe na Nabila, ya kasa tsayar da hawayensa, ya kalle su ya sake fashewa da kuka ya ce "Ku yafe mini dan Allah, ku ci gaba da haɗa kanku, Allah ya yi muku albarka, Allah ya jiƙan mahaifinki ke kuma Allah ya jiƙan mahaifiyarki da jauhar"

Su na kuka su ka shiga motar, su ka ja, su na tafe a hanya, Viper bai rarrashe su ba, dan ba wani ƙwarewa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login