Showing 282001 words to 285000 words out of 479911 words
yi haƙuri ka yafe mini, in sha Allah ba zan sake maganar babana ba, idan raina ne ya ɓaci aka yi mini gori, duk sai na ji babu daɗi amma dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini ba zan sake ba" da fari yayi mata shiru, amma daga baya ya numfasa ya shafa kanta ya ce "Kukan ya isa haka, na ji na yafe miki, duk da kin sha yi mini wannan alƙawarin amma ba kya cikawa, yau da mahaifinki wani abun kirki ya tsinanawa mahaifiyarki, rabuwar arziki aka yi, babu yadda za ayi na nesanta ki da shi har haka, na yanke duk wata alaƙa tsakaninki da shi. Ki yi haƙuri na san kina haƙuri da abun da ake yi miki, da zarar kin yi aure shikenan kin wuce wurin, ki yi haƙuri ki cire maganar mahaifinki a zuciyarki"
Nabila ta jinjina kai, amma ƙasan zuciyarta ba ta ji zata iya daina maganar mahaifinta ba.
Ta tashi ta fita ta tafi aiki, ita ma ta fita daga harkar Nasir gaba ɗaya.
Yau ba ta da shari'ar da zata halatta, dan haka tana office tana ta nazarin shaidunta, da za su yi appeal.
Wayarta ce tayi vibrating, ta ɗaga ta duba "Mu haɗu a restaurant ɗin da ki ka je, zamu yi magana mai muhimmanci" ta zubawa wayar ido tana kallonta, ta ajiye wayar. Har mamakin kanta take yi, yadda take abu babu tsoro take wannan kasadar haka.
Ta ajiye wayar ta kifa kanta, can ta miƙe, ta tattara system ɗin ta da kayanta, ta tashi ta fito, suka yi karo da barrister Habib.
Ya ce "Yauwwa wurinki zan zo dama, ina son mu je unguwar da abun nan ya faru ne, ko da wani abu da zamu kuma samu, da bamu haske a kan shari'ar"
Ta ce "Amm ganin likita zan je ne, ko mu bari sai gobe in Allah ya kaimu?"
Ya ce "Subhanallah, jikin ne dai?"
"A'a ba wani abun damuwa ne sosai ba, zan dai je na ga likita ne, yau yakamata na koma dama"
"Ok, to Allah ya ƙara afuwa"
Ta amsa da Amin.
Ta je wurin cin abincin, ta kira wayarsa ya ɗaga.
"Gani na zo ina wurin"
"Ki miƙe sosai ciki, ki tambayi Vip 2" ta ƙarasa ta tambaya, aka nuna mata, ta buɗe ta shiga.
Yana zaune, ya ɗora ƙafafuwansa a kan tebur, yana sanye da facemask da facing cap ya rufe fuskarsa.
Fuskarta babu annuri, ta ƙarasa ta ja kujera ta zauna, ta ajiye jakarta da wayarta, da mukullin motarta, amma ba ta ce komai ba.
A yanayin yadda ta tafi wancan karon, bai zaci da ya ce ta zo zata kuma zuwa ba.
Tayi masa shiru, tana danna ƙaramar wayarta.
Ya ɗan daki teburin ya ce "Attention, magana zamu yi"
Ta ajiye wayar ta ce "Ina ji"
Ya ja babbar wayarta, ya buɗe ya ɗaukko tab ɗin sa, ya fara daddanawa.
Mai kawo abinci yayi knocking, ya kawo ruwa da lemo.
Ya sauke facemask ɗin sa ya ce "Yaya ake ciki da maganar wancan case ɗin, zuwa yaushe zaku yi appeal ɗin? Sonake ki kammala da wancan shari'ar, sannan ki mayar da hankali a kan tawa, already ina da shaidu guda biyu a ƙasa" har yayi maganar ya gama, bata ɗago ta kalleshi ba, wasa kawai take yi da zobunan hannunta.
"Magana fa nake yi"
"Ina ji ai"
"Ba jin nake buƙata ba, hankalinki zaki bani" iya idanunta ta ɗaga ta kalleshi tana yi masa wani irin kallo.
"Ina magana a kan yaushe zaki yi appeal, ki zo ki fara processing tawa, ina da shaidu biyu a ƙasa" still ba ta ce komai ba ta cigaba da kallonsa.
Zubawa sarautar Allah ido yayi, ya saka mata nasa idon shi ma, ta gyara zamanta, ta kwantar da hannunta a kan teburin, ta ɗora kanta ta kwanta ta yi masa shiru.
Ƙasa yayi da muryarsa ya ɗan matsa ya ce "Meyake damunki ne?"
Kawai ta fashe da kuka, yayi mata shiru, tayi iya yin ta, ta ɗago ta share hawayenta ta ɗauki jakarta, ta ɗauke wayarta daga gabansa, ta juya za ta fita.
"Ina miki magana zaki tafi? Ina zaki je ina yi miki magana?" Yayi maganar cikin tsawa da sai da ta firgita, ta ja da baya tana kuka.
"Talk" yana mata tsawa tana ƙara sautin kukan nata.
"Meyake damunki? Kin san haka zaki yi mini, ki ka yi mini tayin dawowa normal rayuwata? Ki ka ce zaki taimaka mini"
"Ina amfanin tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani kuma yake so? Ba cewa kai baka so na ba? Rashin amsa tayina bai yi mini ciwo ba, irin halin ko in kula da ka nu na wa rayuwata, hakan na nufin duk da risk ɗin da na saka rayuwata baka damu ba ko da zan rasa rayuwata. Saboda kana ganina a haka do you know what am going through ne? To an fasa taimakon naka, i destroy the deal and i am out of it, ka je kayi duk abun da ka ga dama"
Murmushi ya yi, sai da haƙoransa suka fito, abun da ba ta taɓa gani ba.
"Angry bird, always angry for no reason, duk saboda na ce bana sonki, ki ke wannan abun? Ba zan taɓa sonki ba, zuciyata ta jauhar ce itakaɗai"
"Ai baka burgeni ba, da aka zauna baka bi ta lahira ba"
Viper ya ce "Ai nayi niyyar bin nata, ki ka hanani, wannan deal ɗin sai an kai ƙarshensa da ke"
"Komai zaka yi, ba zan sake zuwa in da kake in dai ni yar halak ce, babu amfani tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani" ta raɓa shi ta wuce ta bar wurin.
Ajiyar zuciya yayi, ya koma ciki ya zauna.
Gida ta tafi, abun duniya duk ya dameta, tana ganin kiran sumayya, amma ta share ba ta ɗagawa, gaba ɗaya ta zama so silent.
***
Abdul ne yake kallon ramma, yadda take ya shiri, ya ce wai shirin me ki ke yi haka ne?
"Asibitin ka zaka tafi da ni, ni dai mu je ka duba ni na tabattar"
"Rahama haryanzu tunaniki ƙarya nake yi kenan?"
"To wa ya sani, tun da haryanzu ban ji na warke ba, amai yaƙi tsayawa, muje idan ma shi ne kawai ka zubar da shi"
Ya girgiza kai ya ce "A'a ni ba na zubar da ciki gaskiya"
Ta kalleshi sheƙeƙe ta ce "Yaushe ka fara tsoron Allah, har ka ke cewa ba ka zubar da ciki?"
"Ai lokacin da zan kama aiki, rantsuwa nayi, ba zan ci amanar aikina ba"
"Kai har wata darajar rantsuwa ka sani? Ni ka daina yi mini wasan kwaikwayon nan, kawai mu tafi"
"Rahama mutuwa fa aka yi a wurin zubar da cikin nan"
"Na ji, bakomai, Allah ya yi mini rahama".
Ya sauke numfashi ya ce "Na ji, zamu je, amma wallahi ki ka takura mini ba zamu je ba, kuma kar ki dame ni"
Ta haɗe rai ta ce "Zan baka nan da sati ɗaya, idan na ji shiru zan kuma magana" ta cire mayafinta, ta bar ɗakin.
***
Unguwar gidan aikin ramma take son sake zuwa, kamar yadda barrister Habib ya buƙata, take ta yi masa yawo da hankali.
Tana daf da shiga mota, ta tsaya tana amsa kiran waya.
"Salamu alaikum, Barrister, walid ne"
Ta ce "Oga walid, ya kake?"
"Lafiya ƙalau, mutumin ne babu lafiya fa, ko zamu haɗu a wani wurin mu kai shi asibiti a motarki, saboda yanayin tsaro"
Gabanta ya faɗi ta ce "Subhanallah, wani abun ya je ya sha?"
"A'a, ai rabon da ya sha wani abu, an kwana biyu, ciwon ciki yake yi, tun yana yi sama-sama, tsakanin jiya da yau har suma yake yi"
A rikice ta ce "Ya salam, a ina zamu haɗu to? Ina wurin aiki gani nan"
Da gudu gudu, ta ƙarasa ta hau motar, ta ja, tana tafe tana waya da su, har suka haɗu, sun ɗaukko shi a adaidaita sahu.
A sume suka saka shi a motarta, hankalinta yayi mummunan tashi ta ce "Oga walid yana numfashi?"
"Eh yana yi, Suma dai yake ta yi"
"Yanzu wane asibitin zamu nufa? Ka ga wancan ga matsalar da aka samu"
Suka tattauna suka yanke shawarar kai shi wani asibitin daban.
Asibitin shi ma a wajen gari yake, amma yayi kyau ya tsaru, ko ina tsab da shi.
Nan da nan aka shiga da shi emergency, aka fara yi musu tambayoyi a kan meyasame shi.
Su walid suka yi musu bayani, aka tafi da shi wurin yin scanic.
Nabila ta fita da sauri, dan ta je ta ji ya tsarin Asibitin yake, da biyan kuɗin, taga ɗan mama yana ƙoƙarin komawa in da ya baro su.
Ta ce "Sannu ɗan mama"
Ya ce "Yauwwa, an gano meyake damun nasa?"
Tayi murmushi ta ce "Suna ƙoƙarin yin hakan dai, wannan karon ma ka je ka sanar da su ne su zo su biya bills ɗin asibitin nasa?"
Yayi turus yana kallonta, ya ce "Kamar yaya?"
"Kamar yadda wancan karon kayi, kai ka yi waya aka biya bill ɗin Viper, dan babu wanda ya san mun je asibiti, yanke muka din ga yi, mu ƙaddara ma wani ya sani yana bibiyarmu, ana tsaka da treating ɗin sa hankalinmu yana kansa, ka zame ka fice. Kana kawo masa miyagun ƙwayoyi a duk lokacin da ya buƙata, abubuwa da yawa idan ba na kusa da shi ba babu yadda za ayi a san su, wa ka ke yi wa aiki?"
Ayshercool
08081012143
68
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Ɗan mama yayi murmushi, ya ƙara taku biyu gabanta, ya kalleta ya ce "You better count yourself out of this. Ba ni da niyyar cutar da Viper, da cutar da shi zan yi, da tuni na yi so bakinki ƙanin ƙafarki" daga haka ya miƙe ya nufi in da suka baro su walid.
Aka fito da Viper a kan gado, aka ce za a ba su ɗaki, za a turawa likita result ɗin.
Kamar yadda Nabila ta yi tsammani, an biya bills ɗin, ta din ga yi wa ɗan mama kallon tuhuma, shi kuwa da sun haɗa ido, sai yayi mata murmushi, hakan ya ƙara jefata cikin tunani.
Likita ya shigo da file a hannunsa, suka sake gaisawa, ya tattaɓa cikin Viper, sai dai duk da an yi masa allurai ya samu bacci, da ya taɓa cikinsa ɓangaren dama, sai da ya zabura ya motsa.
Ya duba scanic ɗin hannunsa, ya ce "Hantarsa ce ta kumbura gaskiya, amma ƙodojinsa da sauran abubuwa lafiya ƙalau, amma duk da haka zaku yi x-ray na cikin, mu sake tabattarwa ko da wani abun"
A tsorace Nabila ta ce "Likita hantarsa ta kumbura kuma?"
"Eh, amma karki damu babu wani abu in sha Allah, idan aka yi x-ray ɗin, akwai likitanmu da zai zo ya duba shi, ba wani abun tayar hankali bane ba, zai samu sauƙi in sha Allah"
Walid ya ce "Allah ya sa"
Ɗan mama ya ƙurawa wayarsa ido, sannan ya kalli Nabila, yayi mata alama da su haɗu a waje.
Ya tashi ya fara fita sannan ta bi bayansa.
Ya ce "Ana bibiyarki, yanzu aka turo mini saƙo, zaki bani mukullin motarki, zan kawo miki ita gida a matsayin bakanike"
"Nifa ban fahimci duk wannan abun ba"
"Tsayawa dogon bayani, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ki ga gaggauta muje na raka ki, na ɓulla da ke wata hanyar ki hau napep ki tafi gida, zan kawo miki motar gida".
"Kamar wani abun kake shiryawa a kaina" ya miƙa mata wayarsa, ta karɓa ta duba, message aka turo masa aka yi masa bayanin kar ta tafi a motarta, akwai yiwuwar a kamata, ko kuma ayi mata wani abu.
Bai bari ta yi wa su liti sallama ba, ya fitar da ita daga asibitin, ya tare mata abun hawa ta hau ta tafi tana mamaki.
Ta koma gida, duk a gajiye, abubuwa duk sun dame ta, tana ta tunanin ciwon Viper, tayi ta addu'a Allah ya bashi lafiya, sai ta ji ba ta kyauta ba maganganun da ta gaya masa, haɗuwarsu ta ƙarshe.
"Allah ka bashi lafiya, ka bani ikon cika masa alƙawarin da nayi masa"
"Arfa"
"Na'am" ta amsa tana daga zaune.
"Ina motarki?" Nasir yayi maganar yana shigowa cikin ɗakinta.
"Lalacewa ta yi, na bawa bakanike"
"Wane bakaniken?"
"Bakanike dai mai gyara mota"
"An ce an ganki da wasu maza a motar, a can ring road, sai dai ba a san in da ku ka yi ba, na saka jami'ai a arear in da ake tunanin kin bi, aka kama wani da motar yanzu haka yana tsare a wurina"
Ta miƙe tsaye ta ce "Wai dan Allah yaya me kake nufi da ni ne? Motata ta lalace zan yi gammo na ɗauketa a kaina ne, na kira masu gyara su tafi da ita sai ya zama laifi, na menene zaka saka a din ga bibiyata ma?"
"Saboda baki da gaskiya arfa, gaba ɗaya kin canza, kuma ba kya tsoron salwantar da rayuwarki"
"Kalli, kamar da gaske ka damu da rayuwar tawa, ba ta rayuwata kake yi ba, mafitar ka kawai kake nema Yaya Nasir, amma ai ramin ƙarya ƙurarre ne ka cigaba da bibiyata. Na roƙe ka ka saki bawan Allah, gyaran mota kawai na bashi, abun arziki bai kamata ya zama na tsiya ba" ta fita daga ɗakin gaba ɗaya ta bar shi.
Da daddare ta kira walid, ta ji ya jikinsa, ya tabattar mata jiki da sauƙi sosai, ya farka ma.
Nabila ta ce "Oga walid, shaye-shayen nan ne fa ya fara taɓa shi, ya janyo masa wannan matsalar"
"Ai bama sai kin faɗa ba, shi ne ba wani abun ba"
"Dan Allah oga walid ku daina wannan rayuwar, idan ba haka ba da ƙuruciyarku haka zaku rasa lafiyarku ku mutu, dan Allah" yayi murmushi ya ce"Karki damu, za a daina in sha Allah"
"Allah ya sa, ayi masa sannu dan Allah"
Ya ce "Zai ji in sha Allah" bayan ya kashe wayar, ya fita yana mitar ina ɗan mama ya tafi har wannan lokacin bai dawo ba.
A harabar Asibitin ya haɗu da ɗan mama, kamar ya kwaɗe shi, dan haushin abun da yayi, shi kuma bai gaya masa ainihin abun da ya faru ba, ya ce masa wani wuri yaje.
"Ka wuce ka je ka zauna da shi, liti ya je nemo wani magani, ni kuma zan je gida".
"Kar ka je gidan nan oga Walid, hanya babu kyau, cinnakun nan sun ɗana mana, akwai wani abu a ƙasa ka ɓad da sahu, ka lafe a wani wurin, akwaisu sosai a hanyar gidan nan"
Walid ya ce "Na fahimta, muddin kaga wani abu da baka yarda da shi ba, ka kira sanar mini" ya jinjina masa kai.
Nasir yana zaune ya gama cin abincin dare, aka kira shi a waya.
Ya ɗaga a take, ganin daga office ɗin su ne.
"Yallaɓai yaron nan fa, wasu sun zo sun yi belinsa"
"Wane yaron?"
"Wanda muka kama, kuma sun ɗauki motar ma"
Tashi tsaye yayi ya ce "What? Meyasa ku ka bari suka ɗauka? Waye ma ya ce a sake shi?"
"Manyanmu ne yallaɓai" mukullin motarsa ya ɗaukko ya fito da sauri, kawai ya tarar da motar arfa a gareji.
Bin motar ya din ga yi da kallo, dan ya tabattar ita ce, ko ba ita ce ba. Bai haƙura ba sai da ya dangana da zuwa ya dudduba ya tabattar dai ita ɗin ce.
Bai tsaya ba, ya shiga cikin gidan, ya tarar da ita a falo, suna kallo a falon ita da mutanen gidan.
"Arfa waye ya kawo miki motarki?"
"Ina ga bakanike ne, yaro ne ya kawo mini key ya ce an kawo motar" tayi maganar cikin ko in kula.
Ganin da mutane a wurin, ya sanya bai ja maganar ta yi tsawo ba, ya bar falon.
***
Liti yana zaune yana game a wayarsa, likita ya shigo, ya kalli likitan, likitan ya ce "Sannu ko, ya mai jikin?"
"Da sauƙi"
"Masha Allah, naga ya samu bacci ma, shi ne mai hepatitis ko? Yayi maganar yana duba file ɗin Al'amin. Kodayeke ma bacci yake yi, bari ba sai an tashe shi ba, idan aka yi x-ray ɗin na duba shi, idan ya farka gaba ɗaya" yayi maganar yana taɓa cikin Al'amin. Sai dai yayi shiru yana kallon Viper, yana ƙoƙarin ganin fuskarsa sosai, dan kamar ya san shi, sai dai yanayin kwanciyar da ya yi, bai bashi damar yin hakan ba.
Ya kalli file ɗin Al'amin, an rubuta Muhammad Ibrahim. Ya juya zai fita, ya tsaya ya sake waiwayowa ya kalli Al'amin ya ɗan yi shiru sannan ya fita.
Yayi iya ƙoƙarin sa wurin tuna a ina ya san shi, amma ya kasa dan haka dolensa ya haƙura.
***
"Rahama"
"Na'am"
"Zan fita da ke, zamu je asibiti, wallahi idan ki ka yi misbehaving, ke da ganin mahaifiyarki har abada"
"Idan da zan yi misbehaving, da tuntuni da kake fita da ni da nayi, amma na fara gajiya da ƙaryar da kake yi mini, na cewa gwargwadon bin umarninka da nake yi, shi zai sanya ka sada ni da mahaifiyata. Ina tsoron tonuwar asirina na wulaƙanta a idon duniya, shiyasa bana yi maka ihu, da neman agaji, sonake ka mayar da ni cikin sirri da rufin asiri, yadda ba zan tozarta da yawa ba, amma haryanzu na kasa gane in da ka dosa"
Ya ce "Zaki fahimta ne, muddin ki ka yi yekuwa, to ke zaki kunyata fiye da ni, kuma ni zan iya wanke kaina, ke kuwa zaki tozarta, dan sai kin samu masu ɗoraki a social media kowa ya ganki, kin san duk abun da namiji yayi ado ne"
Ta girgiza kai ta ce "Wannan wani banzan tunani ne, na waɗanda ba su san girman Allah ba, babu al'ada a batun saɓon Allah. Allah bai ware wutar mace ba, kuma bai ware ta namiji ba, bai ce zai sassautawa wani ba dan yana wani jinsi idan ya saɓa masa ba, dan haka babu ado da zunubi, idan al'ada ta nuna maka duk abun da ka yi ado ne, addini kuma ya koyar da kai tsoron Allah da tsoron azabarsa"
Wato ramma akwai baki, wasu lokutan duk abun da yake ji da shi, sai ta ƙure shi ta hanyar kafa mishi, hujjoji da addini, dan haka ya ja bakinsa yayi shiru, suka cigaba da shiri.
Tana sanye da niƙab, a kan dogon hijjabinta, yake nuna mata wurare a cikin asibitin, wai nan ma branch ne na Asibitin, ba shi ne main branch ɗin ba, sai dai yayi kyau ya tsaru sosai da sosai.
Washegari da safe Nabila ta je court ɗin da take da trial, tayi ta kammala, ta samu wurin parking, ta bayar da ajiyar motar, ta hau napep ta fita asibiti.
"Ki zauna a nan, zan je na fara zagaywa na duba marasa lafiya na,