Showing 228001 words to 231000 words out of 479911 words

Chapter 77 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6054

tayi, tare da girgiza kai.

Ya ce "Ke, kwanan nan fa nayi mata ta biyu, da na sani ma da ke nayi ta biyun nan, wannan shagwaɓar taki ai sai ki hanani karyawa"

"Taɓ matarka ta daka ni kenan, ni dai ka zauna Please muyi magana"

Ya zauna ya ce "Na zauna Nabila menene?"

Wayarta ta ciro ta kunna masa voice message ɗin nan, cikin mamaki ya kalleta ya ce "Waye ya turo miki?"

Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, shiyasa na zo na nuna maka"

"To ai tun jiya naso na kira ki, na je garinsu yarinyar da kaina, har gidan su na je, amma ban tarar da kowa ba, maƙwabta sun tabattar mini da ta shafe kwanaki ba su san in da take ba, kuma ba ta yi wa kowa sallama ba" Nabila tayi turus ta ce "Ban gane ba, uwar ta ɓata kenan? Ko kuma guduwa tayi saboda gudun abun kunya?"

"Shi ne dai ban sani ba"

Nabila ta ce "Na kasa gane kan lamarin nan, to waye ya turo mini voice ɗin nan, an ce shi wanda yayi mata fyaɗen, ya zo ya ɗauke ta, to ya aka yi da uwar, waye ya naɗi wannan recording ɗin?".

Barrister Habib ya ce "Gaskiya dai abun tunani ne, lamarin akwai ɗaure kai, amma kar ki damu, koma waye sauƙaƙa miki aiki yayi"

"Amma abun da mamaki fa, kuma wanda yayi hakan ba shi da wata manufa ta yin hakan, ya bayyana kansa mana idan yana da gaskiya koma waye"

Barrister Habib ya jinjina kai ya ce "Yauwwa, ya ku ka yi da Alhaji wada M karofi?"

Ta yamutsa baki ta ce "Soyaya muke yi "

"Soyayya kuma? Cewa yayi yana son ki shiga cikin lawyoyinsa, masu kula da dukiyarsa fa"

Ta ce "A'a gaskiya, ce masa nayi a'a, sai ya ce to shi na din ga kula da shi, shikenan"

Habib ya ce "Innalillahi, wallahi baki da lissafi Nabila, kin san waye mutumin nan kuwa? Kin san kuɗin da muke samu a wurinsa kuwa? Babban mutum ne fa a ƙasar nan"

Ta tashi ta ce "Oho, a hakan ma ai yana bani kuɗi, bana son dai ya zo gidanmu, naga he's very serious, kar ya zo suyi magana da Abba ace sai na aure shi, dan yasin bana son tsoho".

Ya girgiza kai ya ce "Ƙuruci dangin hauka, Allah ya shiryeki"

"Amin, ayi aiki lafiya" ta fice daga office ɗin.

***
Ramma na zaune tana ta gyangyaɗi, ta ji ana murɗa ƙofar falon, Abdul ya shigo da akwatinsa.

Suna haɗa ido ya sakar mata murmushi ya ce "I am back" murmushin ita ma tayi masa.

Ya ƙarasa ya zauna tare da rungumeta, yayi kissing ɗin goshinta ya ce "Kina zaune baki yi bacci ba kina jirana?"

"Ƙarfe tara fa ka ce, amma sai sha biyu, Club ka je ko?"

"Wallahi ban je club ba, abubuwan da na tarar da yawa a can, Shiyasa na kuma samu matsala ne da flight ɗin shiyasa, gudowa fa nayi saboda ke"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "To sannu"

"Yauwwa sweetheart "

Ta ce "Taɓ babu daɗin ji"

Ya ce "Wallahi da daɗi, rantse baki ji daɗi ba da na ce sweetheart"

"Wallahi ban ji ba"

Abdul ya ce "Ƙarya ki ke yi, santaleln mutum kamar ni, na kira ki da sweetheart, ki ce ba ki ji komai ba"

"To waye kai ɗin? Sai ka ce wani mutum na musamman"

Ya kaɗa ƙafa ya ce "Ke kin san matan da suke crushing ɗina kuwa?"

"To ina ruwana?"
"Kina da ruwa mana, na gaji fa sosai Saboda na san maybe kina nan kina jirana, ko abinci ban tsaya na saya ba, yanzu zan yi wanka, sai ki rakani mu duba in da suke 24hrs, mu ci abinci"

Ramma ta ce "A'a, na yi girki ai tun magariba ma na gama, tun da nan gidan ba mak aiki, kayi wankan ka ci"

Ya ce "Iyee zan ci jagwalgwalo yau, bari nayi wankan" ya ja akwatinsa, ya shiga bedroom ɗin da take.

A falo ya tarar ta ajiye fulasai.

"Rahama kayan miyan cikin fridge ɗin ba su lalace ba kenan?"

Ta ce "Eh, har fruit ɗin, na iya reserving ɗin su ai"

Yana cin abincin yana murmushi, ya ce "Yanzu har sakwara ki ka yi, gaskiya kina ji da ni, ga shayin ma yayi daɗi sosai"

"Ba wani ji da kai da nake yi, tunani nake ina ma da guba a ciki, ka ci ka mutu"

Yayi dariya ya ce "Koma dai menene, idan ma da gubar na ci, ba mutuwa zan yanzu ba, sai kin haifa mana babies, kuma fa zama zaki yi kiyi kuka idan na mutu. Anyway abinci yayi daɗi sosai, yaya aka yi ki ka iya girki haka?"

Ramma ta ce "Aikina kenan a gidan Anty maijidda, ta ce ba ta taɓa yar aiki kamata ba, sai gashi iftila'i ya faru da ni a gidanta, amma ta kware mini baya, saboda kai ɗan ɗan uwnta ne, ni kuma bata da alaƙa da ni, ko ganin idonta ban yi ba, wai sai ma umarnin idan mun zo kar a bari mu shiga da ta bayar, aka canza masu gadi.shikenan bakomai, shi talaka ai Allah yana son abun sa" tayi maganar tana share hawayenta.

Sai jikin Abdul yayi sanyi, ya ce "Rahama duk laifina ne, nayi kuskure, kuma duk sharrin giya ne da ruɗin shaiɗan, amma na rage shan giya ma, kuma wallahi rahama na daina bin mata, da ɗin ma sharrin giya ne da kuma abokai" tashi ta yi ta bar masa wurin, saboda tuno hanyar da ya bi ya ci mata zarafi da yayi.

Shi ma gaba ɗaya sai jikinsa yayi sanyi, duk da irin zaluncin da yayi mata, tana da matuƙar tausayi da imani, duk da yana shan zagi da tsinuwa, amma wasu lokutan sauƙin hali ne da ita.

A zaune ya tarar da ita a kan gado, tana ta uban kuka, bai ce mata uffan ba, ya rungumeta yana shafa bayanta, a hankali yake furta "Am very sorry for what i did, ki yi haƙuri" ya din ga rarrashinta, har suka kwanta, yana ta magana, amma tunani ne daban-daban a cikin kanta, babu tsammani ya ji ta ce "Abdul yasar"

"Your excellency"

"Wai dan Allah da gaske ana yi wa maza fyaɗe?"

Ya ce "A'uzibillah, wannan wace irin magana ce?"

"Shekarun baya, kan yayanmu ya mutu, kamar haka na so naji an ce, wani ne ya ce zai samo masa aiki a Abuja, shi ne yayi masa fyaɗe yayi rashin lafiya ya mutu, kullum mama ta tuno da shi, sai ta kusa kwana tana kuka, sai ta daina cin abinci, kusan shekara shida fa, amma ta kasa mantawa. Kuma dama ba a hannunta yake ba, shi yana wurin babansa a birni. To ni haryanzu ban taɓa jin an ce an yi wa namiji fyaɗe ba sai mace, shi ne nake tunanin, ko wani abun suke nufi daban ban gane ba".

Dummm haka Abdul ya ji kansa yayi, ita kanta kalmar ga mace ma babu daɗin ji, balle ga namiji, sai yanzu ya ƙara tabattar da in dai zancen ramma gaskiya ne, ya zalunce su. Hakan ya saka ya ji dolensa ya ƙara ƙaimi, ya nemo mahaifiyarta, ya nemi afuwarta, amma bai ji a ransa zai iya mayar mata da ramma ba.

"Abdul ka yi shiru, ka gaya mini mana"

"Ke kin ga alamar in da za a yi wa namiji fyaɗe ne? To ban sani ba ko ana yi, tun da nima yaro ne haryanzu, ban sani ba ko ana yi"

"Waye yaron?"

"Ni mana"

"Ka fiye abun haushi, da takaici, a'a mahaifa ne kai" murmushi ya yi yana sumbatar ta.

***
"Mai zamani" Walid ya kira sunan Viper.

Ya ɗaga ido yana kallon Walid.

"Da gaske ka haɗu da madaki? Ko kuma yaransa ne suka yi maka wannan raunin na damtsenka? Na ji an ce an neme shi an rasa, kuma ban ji labarin yan sanda sun kama shi ba. Abun duk ya ɗaure mini kai, daga majiyarmu ta dabarsa, hatta su yaransa ba su san a inda yake ba. Kuma na san abu ne mawuyaci ku haɗu ace iya illar da yayi maka kenan, bai kashe ka ba, tun da ya san nemansa ka ke yi, kuma kai ma da ka kashe shi da an ji labari, kuma bana tunanin zaka iya kashe shi a yanzu".

Viper ya gyaɗa kai, ya ɗaga russia da take hannunsa yake ta goge ta, yana shafa mata mai.

Ya miƙawa Walid ita, ya karɓa. Ya ce "Meyafaru?"

Al'amin ya ce "Duba da me aka ƙerata?"

Mamaki ne ya kama Walid, tun da suke bai taɓa yi masa wannan tambayar ba, ya karɓa ya dudduba ta, ya ce "Ƙarfe ne"

Viper ya ce "Duba dai"

Ya sake dubawa ya ce "Ƙarfe ce Viper"

Viper ya haɗa tafukan hannayensa biyu ya ɗaga ya ce "Allah ya jiƙan maza"

Walid ma ya haɗa ya ɗaga ya ce "Amin, dodo babban sarki"

Viper ya ce "Shi ya saka aka ƙera mini russia. An yi amfani da ƙashin ƙwaurin zaki ne, a samanta, ƙasanta kuma azurfa ce haɗe da ƙarfe, sai kuma aka yi amfani da magunguna wurin ƙarasa haɗa aikinta. Shiyasa ba ko yaushe nake amfani da ita ba. Ya saka an ƙera mini ita, ita ce makarin taurin da madaki yake amfani da shi.

Sai dai a lokacin ban ji cewar ya dace na kawar da madaki farat ɗaya, na kashe shi ba, na cigaba da ajiyeta.

A wannan karon naga yakamata na nu na wa madaki, talala kawai nayi masa. Saboda shi aka ƙera russia, na gwada aikinta ne a kansa, kuma tayi tasiri, dan kuwa ta huda shi, ya kuma zubar da jini.
Ƙafar da na soka masa, ta tashi daga aiki har abada, ba zan kashe shi farat ɗaya ba, sai na gama sabauta rayuwarsa, Indabo ya watsar da shi a dalilin Rashin amfanin da ba zai yi masa ba. A lokacin da sauran waɗanda yake cuta, za su farga asirinsa ha karye ya daina tasiri, su ma su fara far masa da kai masa hari. A haka zan cigaba da yi wa gaɓoɓinsa yankan ƙauna, har sai na fara jin sanyi a zuciyata".

Walid ya ce "Kan uba, yanzu duk tsawon lokacin nan, kana da makarin tsafin madaki, ka zauna muke bulayi? Har yayi maka illa ta biyu?"

Ya sunkuyar da kai sannan ya ɗago ya ce "Tun a baya, nayi niyyar ɗaukar fansa, amma daga cikin alfarmar da matata ta nema a wurina, ya haɗa da na bar madaki da Allah, kar na kashe shi, ba ta son nayi kisan kai, sunana ya ƙara ɓaci, hatta gabarmu sai da ta roƙi na kawo ƙarshenta, idan ban manta ba, har Abbu ta sako a al'amrin.
Kukanta ne ya tsaye mini a rai, tare da magiyarta, har na ji a raina na yadda, na haƙura zan kawo ƙarshen gabata da shi, domin in faranta mata amma.... Sai kuma yayi shiru, ya fara huci, jijiyoyin sa suka fara kumbura, gumi yana tsatstsafo masa a goshinsa.

Walid cikin damuwa, ya daddaki kafaɗar Viper ya ce "Am sorry mai zamani, ka yi haƙuri, kayi haƙuri"

***
Nabila na ta rubuce-rubuce a cikin system, ta jiyo muryar Abba yana "Ina Arfan Abban ne, ko ba ta dawo ba ne?"

Daga ɗakin ta amsa ta ce "Ina nan Abba, gani nan" ta fito tana murmushi.

Ya ɗago mata key, ya ce "To, ga 206 ɗin ki can an kawo, duk da na san ba kya son kalar motar"

Wani irin tsalle tayi, ta rungume Abba, ta na "Subhanallah, wayyo daɗi ina zan saka kaina, Abba dama zaka sai mini motar? Na zata da wasa fa ka ke yi mini" murmushi ya yi, ya kama hannun ta, suka fita harabar gidan, wanda suka kawo motar ma ba su tafi ba, Vibe ce blue black sai sheƙi take yi.

Kawai ta fashe da kuka, Abba ya ce "Ya kuka kuma?"

"Abba na gode, na ma rasa me zan ce ne" 'yan gidan duk suka fito suna kallon motar, masu tayata murna nayi, masu tsaki suna yi.

Ana haka Nasir ya shigo, ta nufe shi da sauri, tana nuna masa key ɗin motarta.

"Congratulations, amma tawa zaki ɗauka ni bani sabuwar"

Tayi dariya ta ce "Ai ba aro ba ɗani, balle kyauta" dama a karambani, Nabila ta iya mota, a kan ta Nasir, ya karɓi mukullin, walida ta ce bari ta zo a ɗana su, amma Nasir ya ce mata a'a, su biyu kawai za su fita.

Suna tafe yana driving, bakinta yaƙi rufuwa.

"Wow na zama big girl, idan zan je trial, sai dai a ganni a motata, a din ga cewa hajiya, shikenan na huta da hawa ɗan sahu, da masu warin hammata da zarnin fitsari" ya ƙare mata kallo, sai nishaɗi take yi tana murmushi.

"Arfa"

"Yes sir"

"Ina son mu yi magana ne"

Ta kalleshi ta ce "To yaya"

"Shari'ar da ki ke yi, da kuma adawa da Naja'atu Bunkure"

"Ok ina jinka"

"You have to withdraw the trial"

"What?"

Nasir ya ce "For your own good and safety, mace ce mai hatsarin gaske, kar wani abu ya same ki, Abba ba zai iya jurewa ba, nima kuma haka ki rabu da matar nan"

Nabila ta ce "Yaya, ni fa dama masu ƙaunata ba su da yawa a duniya, dan haka ka ƙyaleni, why would that innocent old man suffer just to cover someone's evil did, ita kuma ta din ga zaluntar mutane, kuma ayi mata shiri, i can't nima Allah ya tsaya mini".

"Shut up, ina magana kina mayar mini, babu wanda ya shiga cikin maganar sai ke, tun da ki ga kowa baya tsoma baki a lamarinta, dan me ke zaki yi? Ki janye shri'ar nan tun ban saɓa miki ba, tun da baki san ciwon kanki ba. Ya zama dole ki janye, idan ba ƙafar wando ɗaya ki ke so mu saka da ke ba" ya haƙiƙance yana yi mata masifa. Tayi masa shiru, gaba ɗaya ta nemi farincikin da take ciki ta rasa, saboda maganar da Nasir yayi, ya gama zagayawa suka koma gida.

Matan Abba kuwa mussaman mama, ta din ga mita a kan saya wa Nabila mota, itakaɗai a gidan, amma ya ce gidansa ne, abun da ya tsara shi za ayi, ba wanda aka tsara masa ba. Lokaci ne yayi da zasu girbi abun da suka shuka masa a kanta.

Gaba ɗaya sai ta rasa karsashi, ta na ta zumuɗin kiran sumayya, amma yanzu ta kasa, saboda haushi da mamakin abun da Nasir yayi mata yanzu.

Kawai sai ta kira Viper, ya ɗaga ya saka a kunnensa.

"Ina wuni, ya jikinka kuwa?"

"Alhamdilillah" sai da ta tashi tsaye jin ya amsa ta ce "Kai, yau ka amsa mini, masha Allah, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, ya kare mana kai. Dama na kira ne in ji ya jikinka, kuma" sai tayi shiru, shima shirun yayi bai yi magana ba.

"To ka tambayeni menene mana? Shikenan ma na san ba kulani zaka yi ba, sai anjima" ta kashe wayar ta ajiye, ta kwanta tayi shiru, zuciyarta a cunkushe babu daɗi, ga abun farinciki, amma Nasir ya ɓata mata. Kawai ta fashe da kuka, ta yi ta gama, ta kwanta ta hau bacci.

***
Yau a kotu, hujjojin da Nabila ta bayar masu kyau ne sosai da sosai, sai dai lauyan gwamantin da yake kare ɓangaren ramma, sun fita gogewa suka din ga dankwafar da ita, kuma alƙalin ya din ga ɗaukar side, tare da soke wasu daga cikin hujjojin Nabila. Ya sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda. Ta kalli dattijon, gaba ɗaya sai ta ji ta fara karaya.

Jiki a sanyaye ta fito, tana fitowa murtala yana tsaye a harabar kotun yana jiranta.

Kamar ta fashe da kuka ta ce "Yaya murtala kaga yadda shari'ar nan ke tafiya ko?"

Murtala ya ce "Kar ki damu, ai idan sun san wata, ba su san wata ba, kamar yadda muka tsara zan tattauna da ke a kan shari'ar yanzu, ki faɗi hints mai muhimmanci, zamu saka a live program yau da ni da Sumayya, sai dai duk mai faruwa ta faru.

Cikin damuwa ta ce "Kar fa ku samu matsala a wurin aiki"

"Manta da su, duk da su ake haɗa baki ai, dattijon ne ma abun tausayi"

Nabila ta ce "Wallahi ko kallonsa nayi, sai tausayinsa ya kama ni, bana son na kasa sakawa a wanke shi"

Murtala ya ciro recorder ɗin sa, ya tattauna da Nabila, na mintuna biyar, a kan shari'ar sannan ya tafi.

***
Indabo tamkar zai kwaɗawa Abdul mari, saboda takaici "Abdul wai me kake nufi da ni ne? Sai ka yi mini asarar wahalata, uwar me ka dawo kanon ka yi? Uban wa ka ajiye da ka taho, mutane sun zauna suna jiranka, kawai a nemeka a rasa, wane irin rashin mutunci ne, da iskanci har haka? Wato tona mini asiri zaka yi, ka nuna wa duniya ban isa da kai ba ko?"

"Daddy, uzurin gaggawa ne ya taso mini, wata tiyat.....

"Ubanka da kai da tiyatar, ko tunanin ɗan uwanka da yake mexixo a tsare baka yi, dole sai ka nuna mini ban isa da kai ba, ka cigaba kar ka fasa ka kuma kyauta"

Wayar Abdul ta fara ringing, ya cirota ya ga lambar ramma, ya ɗaga a saka a kunnensa, yayi ƙasa da murya ya ce "Beb"

"Abdul kana ina?"

"Ina gida meyafaru?"

"Tun jiya fa zazzaɓi nake yi, cikina sai ciwo yake ina amai"

A rikice ya ce "Subhanallah, kina ji na, ki duba side bed drower, akwai pcm, ki ɗauka ki sha, daga shi kar ki sha komai, gani nan zuwa kin ji, ki samu ki kwanta" sai da ya kashe wayar, ya tashi tsaye, ya ankare da katoɓarar da yayi, gaba ɗaya ya manta a gaban wa yake.

"Abdul karuwa ka ajiye gidanka, har take rashin lafiya, saboda iskanci a gabana kuma kake waya da ita?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ba karuwa ba ce Daddy..ammm....

"Abdul, yanzu ba zaka daina sakarcin nan ba, sai abokan adawa sun farga, sun fitowa da duniya waye kai? Uban wa zai yadda ya zaɓeka, idan mutane suka san you are womanizer? Kuma har ka ajiye mace a gida, bama ka yi shahshashancin ta tafi ba. Na haramta maka kwana a waje, duk in da kake ka dawo gida ka kwana, kuma a cikin watan nan za ayi bikinka, ko ka yarda ko baka yadda ba".

Abdul ya kalli Indabo ya ce "Dan Allah Daddy ka bari na kawo wadda nake so na aura, ni wallahi bana son waccan yarinyar, ni ka bari zan yi maka bayani"

"Babu wani bayani da zan saurara daga gareka, dan nawa bayanin ne gaba da naka, kuma kaje ko sallami koma wace karuwar ce daga gidanka, tun kan na biyoka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login