Showing 411001 words to 414000 words out of 479911 words

Chapter 138 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6090

kuma tunzuraka, ba tare da ka san abin da ya haɗa su ba, Nasir ka san aikinka kuwa? Kaga tashi ka je kawai jeka"

Ya buɗe baki zai yi magana major ya ce "Jeka ba zan sake magana da kai a yanzu ba, ina dai tunatar da kai muddin ka gauraya halal ɗinka da haram, babu in da zaka je wallahi. Kuma ka ji tsoron Allah, kar masu ƙarfi su din ga amfani da kai, a kan marasa ƙarfi, saboda kana saka wannan kakin lokaci ne" Sosai kunya ta kama Nasir, saboda yadda asirinsa yake nema ya tonu, na ya karɓi cin hanci, ya din ga matsawa Nabila da ƙoƙarin daƙileta a kan nata aikin.

***
Cikin dare hasken farin wata ya gauraye ko ina, Viper na tsaye a bakin window, yana shan sigari, hannunsa ɗaya yana kallon wayarsa, kwanaki shida kenan rabon da su yi waya ko ya sanyata a idonsa, babban mamakin da ta bashi, yadda ƙiri-ƙiri ya nuna mata yayi fushi, amma ko ta sake neman sa. Haka kurum ya ji ya ƙara fusata.
Ya harɗe ƙafarsa, yana ci gaba da shan sigarin, kawai sai watarana ta faɗo masa, Jauhar ta tsare shi a gida, ta hana shi fita ko ina, kuma ta bashi kara uku na sigari kawai.
Cikin dare ta yi bacci, ya tashi ya fita tsakar gida, ya shiga banɗakin tsakar gida, ya sha son ransa, ya daɗe hayaƙin ya ragu, sannan ya koma ɗakin ya kwanta.
Ashe tun da ya tashi ya fita, tana kallonsa, yana kwanciya ta tashi ta matso kusa da shi, ta saka hannu ta matsa bakinsa, ta sinsuna, dan ta tabbatar masa ta san me yayi, ba ta ce masa komai ba, ta juya ta kwanta.
Kamar wanda ta kama yana alfasha, yayi tsuru-tsuru, ya rasa me ma zai ce mata, kawai ya basar. Aka jima yana ƙoƙarin ya rungumeta, dan ya mantar da laifin da yayi, ta tashi ta bar masa gadon, ta yi alwala ta tayar da salla.
Asubar fari ba ta tashe shi ba, yaje masallaci ya dawo, a gida yayi azkar, ya din ga 'yan kame-kame, amma taƙi kula shi, har gari ya waye, sai da ya gaji ya ce "Ni fa guda uku na sha kawai ba da yawa ba"

Ta kalleshi ta ce "Me fa?"

"Sigarin" ta ɓata fuska ta ce "Hakan ya tabattar mini da zaka iya cin amanata wataran, ka yi abu ban sani ba"

Ya girgiza kai ya ce "Ai uku ce kawai ba wata mai yawa ba, ki ke wani haɗe rai "

"To Allah ya baka haƙuri, na ga kamar na matsa maka" daga haka ta ci gaba da sabgarta.

Ranar ba ta hana shi fita ba, ya zauna bai fita ba, ko zata huce, har da yi mata aikin gida, amma ya kasa cewa ta yi haƙuri, ta tabbatar da ya sha jinin jikinsa, duk ya damu, amma ya kasa ba ta haƙuri. Duk sallolin ranar a jam'i ya yi su.
Kafin ya dawo daga sallar isha'i, ta sha kwalliya, yana dawowa ta rungunmi abin ta, kamar ba fushi tayi da shi ba, iya punishment ɗin nan da tayi masa, sai da ya ji kamar ya shekara a prison. Jauhar akwai iya dealing ta cikin ruwan sanyi, a lokacin babu wani abin da yake shakka irin yi mata laifi, saboda ta riga ta sanshi, ciki da bai ta san hanyoyin hukunta shi. Sakin guntuwar sigarin yayi, ya koma ɗaki ya kwanta ya cigaba da tunaninta.

Da haka wani nannauyan bacci ya ɗauke shi, sai dai kasancewar da ita ya kwanta a ransa, sai ya din ga mafarki da ita, mafarki mai cike da shauƙi da nishaɗi irin na ma'aurata.

"Master salla fa, zaka rasa sallar asuba." tayi maganar tana shafa sumar kansa.

Ƙanƙameta ya ƙara yi, yana tura kansa cikin wuyanta, da yake fitar da daddaɗan ƙamshin turaren da yake matuƙar son jin tashinsa daga jikinta.

"Viper wai ina zaka shiga a cikin pillown nan ne? Wai ko dai ka sha wani abu bamu lura ba, tun ɗazu fa muke tashinka, ka tashi mu yi salla dan Allah"
A hankali ya motsa, ya buɗe idonsa ya ga hasken fitilar solar, ya haske ɗakin, sai a lokacin ya lura da ya ƙanƙame pillow.
Yayi miƙa tare da yin salati, ya kalli liti da yake tsaye a kan sa ya ce "Akwai gas ne?"

"A'a ɗan kaɗan ne sosai, sai an yi refiiling ma zamu iya dafa karin kumallo".

"Ɗora mini ruwa, ku yi sallarku zan yi wanka"

"Wai Viper meyake faruwa ne kwana biyun nan, ko ka fara dawowa bil adama ne? Ni ina cewa ka yi wa addini hidima meyake faruwa"

Ashar Viper ya yi masa, ba shiri liti ya ce "Allah ya baka haƙuri, ya ƙara lafiya"

Walid kuwa dariya yayi, ya ce "Allah ya ƙara, uban son jin ƙwaƙwaf".

Bayan sun karya Baba ya kira Viper a waya, ya ɗaga suka gaisa, ya ce "Aminullahi, dan Allah idan baka komai zuwa azahar ina son ganinka"

"To Baba in sha Allah zan zo, nan gidan zan zo na same ka?"

"Eh dan Allah"

"Zan zo in sha Allah"

"Yauwwa Allah ya yi maka albarka"

Viper ya amsa da Amin.

Ɓangaren Nabila ita ma kwanaki bakwan nan da suka yi, ba sa magana da Viper, abin ya dameta, ƙishirwar son ganinsa ta addabeta, ga ayyuka sun fara yi mata yawa, 'yat shaharar da tayi ta kwanan nan, ya sanya take ta samun cases ko ta ina.
Ban da masu nuna suna sonta, manyan mutane da suke sonta da aure.
Yau da mafarkin da tayi ta tashi a zuciyarta, mafarki tayi da mai kama da ita, wadda take da tabbacin jauhar ce.
Tana nuna mata inuwar mutumin da yake ɗaure cikin sarƙa a baya, yanzu babu sarƙar, sai dai daga yanayin inuwar tasa, kamar a galabaice yake, duk da babu sarƙar sai tangaɗi yake yi.
Tana murmushi ta cigaba da nuna mata shi, ta nufi in da take nuna mata, sai dai da ta waiwaya ba ta ganta ba, tana ƙoƙarin ƙarasawa in da mutumin yake, kawai ta farka daga baccin.
A hankali ta furta Viper, a gurguje ta shirya, tayi ta trying lambarsa, amma yaƙi ɗagawa, ta din ga jin ko me zai yi mata, yakamata ta kira shi, ta ji ya yake.

****
Ko da Viper ya je gidan su Jauhar, ya tarar da motoci a ƙofar gidan, bai damu da ko me ake yi ba, ya kira Baba ya ce masa gashi nan yana ƙofar gida.

Baba ya ce ya shiga kawai, ya ƙarasa ya shiga, babu wanda ya kula a mutanen gidan, sai hafsa da suka gaisa ya shiga ɗakin Baba.

Alhaji mu'azzam ya tarar, da Abbu, da kuma shi kansa Baban.

Gefe ya samu ya zauna a ƙasa ya gaishe su, sai dai da ya zo kan Abbu kamar an yi masa dole, haka ya gaishe shi.

"Ya gida ya ƙoƙarin Kuma?" Baba ya tambayi Viper.

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah"

"Ina yan uwan naka?"

Viper ya ce "Su na gida, nikaɗai na zo".

Baba ya ce "babu laifi, Al'amin"

"Na'am Baba"

"Na san zaka yi mamakin kiranka da muka yi, babu tsammani da wuri haka.
To bakomai bane ya janyo, Nabila ta same ni, tayi mini wata magana ne, kuma nima naga hakan yakamata, duba da yadda abubuwa suka wakana.
Al'amin su iyaye, ba a fushi da su, kuma duk lalacewarsu iyaye ne, balle babu lalacewa a cikin iyaye, yakamata ka sasanta da mahaifinka, yanzu ina jauhar, ina mahaifiyarka, ina ɗan uwanka, ko da kuɗi ba zaka sake ganinsu a gidan duniya ba. Dan haka ka yi haƙuri, mun san mu masu laifi ne a wurinku, amma ku yi haƙuri a yafe ya wuce dan Allah ba dan halinmu ba".

Viper ya yi shiru, kamar mai nazari amma bai ce komai ba.

Abbu ya ce "Al'amin, nauyinka da nake ji, ya sanya na kasa nemanka gaba da gaba na nemi afuwarka, na san in dai dan halina ne, da abin da na aikata maka, ba zaka sake kallona a matsayin mahaifi ba, amma ba dan halina ba domin Allah.
A ƙaddarar rayuwarmu, na ɗauki darasi da dama, daga illar da mutum zai yi wa rayuwarsa, shi ne auren mace domin buƙatarsa kawai, ba tare da tunanin abin da gobe ka iya haifarwa ba.
Duk da ni a zatona dan gobenku na auri Rahila, amma ta ci amanata, kuma nima na san da laifina na rashin bibiya da tantance abin da take ɗora ni a kai, amma dan Allah ka yi haƙuri Al'amin, ka yafe mini ka dawo gida mu yi rayuwa a ɗan abin da yayi mini saura na rayuwata"

Alhaji mu'azzam ya ce "Viper, ka yi haƙuri dan Allah, duk wani abu da ya faru, ya wuce tun da bawan Allah nan shi yayi silar zuwanka duniya, kuma wani abin idan bai yi maka ba, wani yayi maka, yana cikin tashin hankali da damuwa sosai"

Viper ya numfasa ya ce "Ko a baya ni ban ƙi Abbu ba, ina matuƙar ƙawazucinsa da son kasancewa tare da shi, Abbu shi ne ya ƙi ni ya kore ni, amma tun da yanzu ya nemi na dawo shikenan, ya riga ya wuce. Amma ni a yanzu na girmi zaman gida, ba zan iya rabuwa da su Walid ba, sai na tabattar da rayuwarsu ta inganta suma, kamar yadda suka rayu da ni lokacin da kowa yake mini kallon mara amfani.
Kuma idan na koma gidan nan, zai iya cigaba da haddasa husuma, wanda ni kuma bana fatan hakan".

Abbu ya ce "Hakan ma na gode Al'amin, Allah ya ƙara shirya mini kai, dan Allah idan ka samu dama, ko zuwa gobe in Allah ya kaimu ka zo gida, ina son mu yi wata muhimmiyar magana da kai"

Viper ya jinjina kai, Baba ya ce "Bari a kawo abinci mu ci baki ɗaya"

Al'amin ya ce "Baba ayi mini uzuri dan Allah, ana jirana ne, ayi mini afuwa" ya fita ya sanya takalmansa ya tafi.

Rarrashin Abbu suka din ga yi, saboda yadda jikinsa yayi sanyi, dan gani yake yi, kamar da wani abun a ran Al'amin haryanzu, duk da ya san halinsa farin sani, ba kowane lokaci ake iya gane yanayin sa ba.

***
Washegari Nabila ta kira Abbu a waya, domin ta ji ya ake ciki, ko Al'amin ɗin ya saukko?.

Abbu ya ce "Kin san ɗan nawa hukuma ne sai da rarrashi, ya ce dai ya wuce, amma bai tsaya mun ci abinci tare ba, yau dai ina jiransa, ina son ya zo zamu yi magana da shi, idan ya zo kin ga sai na ɗan ƙara saka ran ya saukko ko?"

Sai ya ba wa Nabila tausayi, ta ce "Abbu ka kwantar da hankalinka, Viper yana sonka haryanzu, shi ba abubuwan da ka yi masa ne suka dame shi ba, korar da ka yi masa ce kawai ta tsaya masa, amma tun da ya ce maka ya yafe, ya yafe ɗin ne, dan Allah ka kwantar da hankalinka Abbu, idan ma bai zo ba na yi maka alƙawarin kawo maka shi har gida in sha Allah"

Abbu ya ce "To shikenan, na kwantar da hankalina, Allah ya saka miki da alkhairi"

"Amin bakomai Abbu, sai anjima"

Shahida ita tayi girke-girken zuwan Al'amin, Rahila na gefe tana kallonsu, sai yan surutai take da ƙanan maganganu saboda ƙwaƙwalwarta ta riga ta taɓu, amma har aka yi sallar magariba Viper bai zo ba.
Hakan ya ƙara sanya Abbu karaya nesa ba kusa ba, domin kuwa yana da muhimmiyar magana da yake so su yi.
Shahida tayi ta ci gaba da bashi haƙuri, amma a washegari ma still babu Viper, babu dalilinsa, tun Abbu yana sanya ran ganinsa har ya sare.

****
Viper yana ganin kiran Nabila, amma ya shareta.
Message ta turo masa "Ka ɗaga wayata, is an emergency"

Sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga yana hura hanci.

"Vi wai dan Allah meyake damunka ne, kai mutum nawa ka yi wa laifi kai ko neman yafiyar ma baka yi, kai shikenan komai naka babu sauƙi, Abbu ya nemi afuwarka, amma ka yi burus, ya ka ke so yayi ne?.
Idan shi ma ya mutu sai ka huta, ni dai nayi iya yi na, sauran na bar wa Allah, ban san ya zan yi maka ba kuma, Abbu yana Asibiti ya yanke jiki ya faɗi, ana addu'a Allah ya sa ba ɓarin jikinsa ne ya taɓu ba, yana ta kirana a waya, yana gaya mini kamar baka yafe masa ba, ya nemi ka je ka ƙi zuwa, to yanzun ma Viper idan ka yi ra'ayi ka je, idan ba ka yi ra'ayi ba shikenan, ni fara gajiya da halinka"

Ba tare da ta kashe wayar ba, ya ajiye wayar, yana duba agogon hannunsa, sauran awa ɗaya ya shigo garin Kano, ranar da ya baro wurinsu, aka tura shi Jos, kuma yana sane da kiran da Abbun yayi masa, dajin da yaje ko network babu.
Sai dai ƙirjinsa ya din ga bugawa, hankalinsa yayi mummunan tashi, ya shiga fargaba da zullumin rasa abu mai muhimmanci a rayuwarsa karo na babu adadi.

Ayshercool
08081012143
98
Shiru yayi yana dubanta, domin ya tabattar idan da gaske take, sai dai yanayin fuskarta ya tabattar masa da gaske take yi ba wasa ba.

Basarwa yayi ya ce Shikenan su tafi, amma deep down ya ji zafin abin da ta yi masa nesa ba kusa ba, he wish 'yar madararsa tana raye, da ya san ita ba zata watsa masa ƙasa a ido ba, kamar yadda Nabila ta yi yanzu ba.

Dan rashin kunya, su na tafiya a hanya kuma, ta na yi masa hira da surutu, ganin ya yi mata banza, ya sanya ta ja bakinta ta tsuke, kuma ta tabattar fushi ya yi.

A hanya ya sauka, ya bar ta da Joseph, ya mayar da ita gida, shi kuma yayi nasa wuri.

****

Washegari da yamma, Abba yana gidan gonarsa, yana office ɗin sa, ana ta fitar da ƙwai na kaji, da na sauran tsuntsaye ƙaton gidan gona ne sosai da sosai, gidan gonarsa na cikin manyan gidajen gona da yake fitar da ƙwai, har maƙwabtan garuruwa. Da su kansu kajin da kifaye, ban da sauran dabbobi.

Masinja ya sanar da shi ya yi baƙo, Abba ya ce a shigo da shi.

Mintuna kaɗan aka buɗe ƙofar Office ɗin aka shigo, ajiye biron hannunsa ya yi yana kallon Viper.

Viper ya yi sallama, Abba ya amsa a hankali yana ci gaba da kallonsa.

Ya ƙaraso ya tsaya, ya gaida major cikin girmamawa kamar yadda suke yi a tsakaninsu masu ɗamara, hakan ya tabattar wa Major akwai wani abu tattare da baƙon nasa. Ya bashi dama ya zauna.

Viper ya ce "Duk mun taɓa haɗuwa ba na da tabbacin ko ka gane ni, amma bari na sake gabatar maka da kaina, sunana Al'amin Ibrahim, wanda 'yar ka Nabila ta tsayawa a kotu, kuma mijin 'yar uwar Nabila da Allah ya yi wa rasuwa"

"Mijin wadda ka kashe dai, da babanta bai san ciwonta ba ya ɗauketa ya aura maka. Ta yaya zan kasa ganeka, da ka ɓata mini shirina na shekara da shekaru ka ɗauki Nabila ka haɗata da babanta, mutumin da bai martaba rayuwar uwarta da ta 'yar uwatta ba har ya iya aura maka ita ka kasheta".

"Ba ni na kasheta ba, kamar yadda kotu ta tabattar kuma ta wanke ni, ina roƙonka saboda Allah, kar laifin da ba namu ba ya shafe ni da ni Nabila, mussman ma ita.
Makamancin abin da ya faru da Jauhar, irinsa ne a rayuwata, da ya jefa ni cikin ƙaddara. Duk wannan mummunar rayuwa da nayi, ta samo asali ne daga rashin samun ingantaccen bangon da zan jingina rayuwaya da shi, sai da ƙaddara ta saka aurena da Jauhar, ba zan taɓa mantawa da ita ba har duniya ta naɗe, kuma ban kashe jauhar ba.
Kamar yadda kotu ta tabattar, duk da na fuskanci mutum ne kai irina, muna amfani da ƙwaƙwƙwarar shaida da muka gani a zahiri ne, ba dan haka ba, ba zan so na baka wata gamshashshiyar hujja da shaida da zata tabattar maka da Nabila a kan dai-dai take, kamun da aka saka ɗanka yayi mini ba bisa ƙa'ida bane ba.
Da fari hukumar'yan sanda ce ta bashi umarnin, daga baya kuma an bashi maƙudan kuɗi dan ya kama ni, hakan ya sanya ya din ga ɓata Nabila a idonka. Duk ban gaya maka wannan abun da raba maka kan iyalinka ba, roƙonka kawai nake yi, ka daina fushi da Nabila, duk da ganin mahaifinta da ta yi, a duniya ba ta da wani wanda ta shaƙu da shi take ƙauna sama da kai. A madadinta ina mai ƙara baka haƙuri, domin kuwa na san duk ni ne silar komai, amma dan Allah na roƙe ka, ka yi haƙuri ka yafe wa Nabila da mahaifinta, ci gaba da fushi da ita, zai kua jefa rayuwarta a cikin damuwa"

"Ka gama?" Major ya yi maganar yana kallon Viper.

Viper ya yi shiru bai ce komai ba.

"Na ji na kuma gode, amma ka tashi ka tafi, ka ɓata ruwa ba domin ka sha ba, ka ɓata mini haɗin kan iyali"

"Abba ban ɓata maka kan iyali ba, son abin duniya ne ya rinjayi Nasir, ya ƙara ta'azarra al'amarin, ina sake baka haƙuri, saboda Nabila kar azo ta shiga wani halin" ya na gama maganar ya tashi tsaye ya fice daga ofishin.

Bayan fitarsa Major ya yi shiru yana kallon ƙofar da ya fita, da nazartar maganganun da ya yi.

Gaba ɗaya Viper ya daina kiran Nabila a waya, ita ma kuma ba ta neme shi ba, hakan ya ƙara tunzura shi, ganin yadda ta watsar da shi gaba ɗaya.

Major ya so ya yi wa Nabila maganar zuwan Viper in da yake, amma yayi mata shiru ya rabu da ita.

*****

Satin awon Ramma ya zagayo, Nabila ta je ta ɗauki ramma, suka je asibiti. Aka yi mata awo aka duddubata, komai nata lafiya ƙalau.
Su ka tsaya suka yi sayayya, suka tafi prison. Ramma sai murna take yi tana jin daɗi za ta ga Abdul.

Saboda yadda Nabila ta zama popular yanzu, duk in da ta shiga an santa, tana samun alfarma, yau ma har ciki aka shiga da su.

Aka je aka fito musu da Abdul, yana ganin ramma ya saki murmushi, ita ma murmushin ta sakar masa, ta miƙe tsaye ba tare da ta san ta miƙe ba.
Nabila ta ce "Bari na baku wuri, idan kun gama ma gaisa" ta fita waje, bai damu da gandiroban da yake wurin ba, ya rungume abar sa.

Ta ce "Doctor ya jikin ka warware?"

"Inyee an daina gantsara mini sunana,  Abdul yasar"

Ta saki murmushi ta ce

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login