Showing 381001 words to 384000 words out of 479911 words
shi wannan asibitin jinya, kamar ma ba wanda ake tsare da shi ba.
Nabila na ɗaga kai ta hango babar Abdul na tahowa, tare da security ɗin ta, hannunsu da fulasai.
Abdul kuwa bayan ta gama ba shi abinci, sai ya marairaice wai dan Allah ta yi masa wanka, wai da kansa yake yi, baya bari kowa yayi masa, kuma idan yayi baya fita.
Ya lallaɓata da daɗin baki, ta saɓa hijjabinta, su ka tafi toilet.
Maman Abdul na zuwa Nabila ta tashi, ta ce "Sannu da zuwa, bari ayi musu knocking tukuna, ya na da baƙuwa ne" kallon banza ta yi wa Nabila, kawai ta buɗe ƙofar ɗakin.
Abdul ya na kwance ruf da ciki, ta yi masa wanka, ta na shafa masa man zafi a bayansa.
Tashi ta yi cikin tashin hankali, ramma ta ja da baya, ta na zazzaro ido, tare da ƙoƙarin sanya hijjabinta.
"Me zan gani haka, wannan matsiyaciyar yarinyar har asibiti me ki ke yi a nan, ke wace irin 'yar isaka ce ne?"
Abdul ya ce "Mummy ba 'yar iska ba ce, mata ta ce fa"
"Rufe mini baki ko na ɗauke ka da mari"
Nabila ta ce "Hajiya, ba ramma ce ta kawo kanta ba, shi ya nemi ya ganta ta hanyar lauyansa, su ka roƙi alfarma na kawota, amma ba 'yar iska ba ce"
"Rufe mini baki, banda munafunci, kun haɗa baki a kan lallai sun kun kassara mini iyali, kun dage sai kun kulle mini ɗa, kuma saboda iskanci kin kawota ta na yi masa karuwanci, ƴar ƙanƙanuwa da ke kin iya bariki"
"Mummy dan Allah ki daina aibata mini mata, wane irin karuwanci fisabilillahi. Ni fa ina buƙatar matata a kusa da ni"
Ta ƙarewa ramma kallo, ciki ne a jikinta ya fara tasawa.
"Me nake gani a jikinta kamar ciki ma? Amma dai ba na ka bane ko?"
Abdul cikin damuwa ya ce "Dan Allah Mummy ki daina aibata mini mata, ba dan ni ba, ina son matata, idan laifi ne na yi musu laifi, dan Allah ki daina aibata mini ita, ina jin zafi sosai" galala ta buɗe baki ta na kallon Abdul.
Nabila ta ƙarasa ta danƙo hannun Rahama, ta ce "Zo mu tafi"
Riƙeta Abdul ya yi, ya na yi mata magana ƙasa-ƙasa.
"Na gode sosai da sosai your excellency tun da aka kama ni, ina cikin baƙin ciki da damuwa, amma na yi farinciki sosai da sosai, na gode rahama. Allah ya saka da mafificin alkhairi, ki cigaba da yi mana addu'a"
Jan shi mahaifiyarsa take yi, amma ya yi ƙam da rahama, ya na yi mata magana a kunne.
Jinjina masa kai kawai take yi, idanunta na cika da hawaye.
Hankaɗe ramma ta yi ta na ce mata munafuka, Nabila ta riƙe ta, ta kalli maman Abdul ta ce "Ki bi a hankali, wannan zafafa ƙiyayyar ba naki ba ne ba, rayuwar ɗanki na hannun Allah ta na da alaƙa kuma da Rahama, duk wannan fusatat da ki ke yi akwai rabo a tsakanin su, gara ki kwantar da murya ki lallaɓata da iyayenta, dan wannan abun da yake yi a kanta, ba soyayya ce kawai ba jarrabawa ce".
"Wallahi ƙarya na bi matsiyata yan ƙauye ina roƙonsu, shi ma asiri su ka yi masa"
Nabila ta ce "Idan ke ba ki bi su ba, shi gashi ya lalace ai a kan yar ƙauyen"
"Ke ki iya bakinki ko na kifa miki mari, na saka ayi dukan tsiya"
"Barrister ce ni, tsaf hakan zai saka ke ma a yanka miki tikitin tafiya in da mijinki da ɗanki ke shirin tafiya".
Ramma kuka kawai take yi, Abdul kuwa ya kasa magana, sam bai ji haushin abin da aka yi wa mummyn ba, shi matarsa ce kawai damuwarsa.
Nabila su na tafe a hanya, ta ce "Rahama za ki iya yafe wa Abdul yasar?" Ramma ta kalli Nabila amma ta yi shiru.
"Ki na son mijinki ko?" Still shirun ta yi ta na wasa da yatsunta.
"Ki gaya mini masalaha nake son a nemo"
"Ba na son shi, kawai tausayi yake bani"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Rahama kenan, menene son menene tausayin, ki na tsoron abin da zai biyo bayan amsar da zaki bani ne kawai. Abin da ki ke so dole shi za ayi, idan ki na son mijinki, ki gaya mini a nema masa sassauci ko ma ki yafe masa, ku yi rayuwar aurenku, na san yadda zan ji da Mama da Vi"
Ramma dai ta yi shiru, ba ta iya cewa uffan ba.
Tunani ta tsunduma, yadda suka kasance tare yau tare da Abdul, "Dan Allah rahama kar ki bawa kowa zuciyarki har na fito, zuciyarki tawa ce nikaɗai"
"Ba zaka yi shiru ba, sai na saka maka sabulun nan a baki, da kyar ka ke magana sai haki ka ke yi"
Ya marairaice ya ce "Dan Allah ki bar mini zuciyarki"
"Nawa zaka saya?"
Yayi murmushi ya ce "Ai darajar zuciya, ba a iya musayarta da komai, sai zuciya 'yar uwatta"
"Ji yadda ka ke magana, kamar a film juya ko na zuba maka dundu ni"
Ya lumshe ido ya ce "Dundun ƙauna ne" murmushi ne ya suɓucewa ramma, ba tare da ta shirya ba, Nabila kawai ta kalle ta, ta girgiza kanta.
A falo su ka tarar da Viper, fuskarsa babu rahama babu annuri, tuni Ramma ta tsure, Nabila kuwa ta sha jinin jikinta.
Cikin dakewa ta ce "Vi sannu da zuwa, dama zaka biyo nan ne? Na zata tafiya kawai ka yi"
Miƙewa ya yi tsaye ya ce "Daga ina ku ke?"
"Amm...mm" ganin ta na neman ƙaryar da za ta yi masa ta kare kanta, ya sanya shi ɗago mata wayarsa.
"Duk in da ki ka je ina gani, kuma na jira Emanuel, ya gaya mini in da ya kai ku, Me ki ke shirin yi ne, me ki ke shirin aikatawa? Are you human being, kamar ba mace ba? Idan ita ba ta da hankali ke fa? Dan me za ki ɗauke ta ki kaita wurin wannan ɗan iskan yaron? Me ki ke shirin aikatawa ne? Yadda da na yi da ke ya sanya nake jin za ki iya ragamar komai yadda ya dace, amma na rasa in da ki ka dosa. Ko ke ma kin sauya layi daga in da na sanki, ta kanki su ka biyo kenan saboda case ɗin ya sha ruwa? Rahama ba za ta taɓa zama da wannan yaron ba, kuma dole a hukunta shi"
Maman rahama ta ce "A'a Aminu, a bi komai a hankali, ta na ƙoƙari ai"
Nabila ta kalli ramma ta ce "Jeki abinki rahama, Allah ya huta gajiya"
Ta kalli Viper ta ce "I so much respect humanity, yardar da ka bani, yanzu babu ita ka na doubting a kaina, saboda kawai na kai rahama wurin mijinta. Idonka ya rufe fansa ka ke so ko ta halin ƙaƙa shiyasa ka ke son sai an hukunta Abdul da laifin da ya yi da wanda ba na sa ba.
Hukuntaka da aka yi da laifin da ba naka ba ya sanya na tsaya kai da fata, tun ban san ina da alaƙa da kai ba, a kan ƙwato maka hakkinka. Ko hukunci za ayi, iya laifin da Abdul ya yi kawai za a hukunta shi da shi.
Ina rashin karɓarka da al'umma su ka ƙi yi a lokacin da ka ke buƙatar su, shi ne musababbin sake shigarka mawuyacin hali? Da na ƙyamace ka, ko na gujeka da a wani stage ka ke yanzu? Kar ka manta har yinƙurin kashe ni ka yi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, an nemi rayuwata wuri daban daban saboda kai, amma hakan bai sanya na haƙura na ƙyaleka ba.
Kar ka manta a yadda ka ke, aka ɗauki auren 'ya aka baka, shikenan mutum ba zai yi kuskure ya tuba a karɓe shi ba, sai a ɗauki laifin nasa kawai a saka a gaba.
Zunzurutun kuɗi miliyan nawa ya kashe a garinku, kuɗin da a sanadinsu, ubansa ya na can ya na fuskantar tuhuma, ya biya kuɗin makarantar ramma har jami'a, kuɗin rainon cikinta da abin da za ta haifa, hatta kuɗin kula da al'amuransu na yau da kullum ya bayar, duk dan ya wanke laifin sa,ni da ku mun san banda ƙaddara rahama ba ta isa zuwa in da Abdul yake ba, son da yake yi mata jarrabwa ce kawai. Ban da an tsaya mana mu ma, Abdul ya na da gatan da za a iya sakinsa, kawai dan mun samu manya sun shiga abin ne, amma ya zaɓi a hukunta shi, muddin rahama za ta yafe masa.
Mama ke ma fa uwa ce, kuma Allah ya taɓa Jarabtar ɗanki da kauce hanya, ke ki ka zaɓa masa zama hakan? Duk da yanayin abin da ya faru, da Abdul sakaci da tarbiyyarsa ne, amma za a iya kamanta rahama da jauhar, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce ka yi sanadin shiriyar mutum ɗaya, ya fi a baka jajayen raƙuma guda ɗari. Ba mu san me Allah ya ɓoye a lamarin nan ba, ga juna biyu a tare da ita, ku na nan ta yi masa alƙawarin ya je ya gama prison ya dawo ta na jiransa. Duk wannan abun fa zai iya yiwuwa wata jarrabawar ce daga Allah muma yake yi mana, Abdul fa bawansa ne shi ma, kuma ya na kishin abin sa, ci gaba da jansa dan Allah ya ara mana dama ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Amma ina mai neman afuwar ku, ba ina nufin shari'ar Abdul ta sha ruwa ba ne, sam sonake ayi tunanin mafita.
Yallaɓai Al'amin, Allah ya baka haƙuri ni babu wanda ya bani wani cin hanci, ba kuma ƙoƙarin cin amanarka nake yi ba. Zan yi iya yi na Abdul zai je prison in sha Allah, muddin hakan zai samar muku da nutsuwa" ta ƙarasa maganar a nutse, ta ja da baya ta fice.
Ramma ta na tsaye ta na ji, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta fashe da kuka, ganin yadda ta ja aka ɓatawa Nabila rai.
Sojan da yake ba wa Nabila kariya, ya bi ta ya na yi mata magana, amma ta share shi, a ranta ta ce "Tsohon munafiki kawai"
Napep ta tara, ta nufi gidan Abba.
Maman ramma na shirin yin magana, Viper ya rigata, ya ce bari ya tafi.
A ɗaki ta iske ramma, ta yi mata ta tas, ta ce "Ramma ba kya tausayina, ɗa na ya rasa ransa a banza, a gabanki yaron nan saboda rashin tarbiyya, ni kaina so yayi da ya haike mini, amma yanzu kin fifita shi a kaina, na gode rahama"
Tabbas da zuciya za ta yi mata adalci, to da ba ta fara ƙaunar Abdul ba, amma ita haryanzu ta fi yarda tausayin sa take ji, ya ake so ta yi da rayuwarta ne.
Viper na fita, sojan ya fara gaya masa tafiya ta yi, ya ce ya rabu da ita, su tafi kawai.
Da daddare Viper ya din ga kiran wayar Nabila, amma ta ƙi ɗagawa, hakan ya tabattar masa da ta yi fushi ne.
Gidan major babu wanda ya kulata, babu wanda ta kula sai baba uwani, ta shirya ta tafi gidansu sumayya, sun daɗe su na tattaunawa, ta na yi mata nasiha da ba ta ƙwarin gwiwa.
****
Monday morning 9:30a.m
Tsaye take a gefen wani gini, tana ƙarewa harabar kotun kallo. Yadda aka cika harabar da manya da ƙananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari'oi za a gudanar a yau.
Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate ɗin shigowa harabar kotun.
Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ɗin ta, sai dai tsayuwar motar babu daɗewa wata danƙareriyar motar, ta shigo harabar kotun.
A ƙalla an kai mintuna goma da parking ɗin motar, sannan aka buɗe bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat.
Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka karɓi jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa.
"Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko ina, amma kai ne abun dogarona, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari'ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ƙarya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake buƙata" ta jima a tsaye tana karanto addu'a, tare da yi wa Allah kirari.
A hankali ta furta "What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini" cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ƙasaita, shigarta ta lawyoyi tayi matuƙar yi mata kyau, tana tunkarar ƙofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta.
Ayshercool
08081012143
91
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Sannu a hankali ta ke ƙoƙarin shiga cikin kotun, "Nabila" ta jiyo muryar sumayya a bayanta.
Ta waiwaya, sumayya ta ƙaraso ta ce "Ya aka yi ki ka riga ni zuwa?"
"Oho miki dai"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Best of luck my dear, Allah ya ba da sa'a"
Nabila ta ce "Amin sumayya, amma a tsorace nake, wannan shi ne trial mafi haɗari da nake tunanin zan fuskanta a rayuwata"
Sumayya ta ce "Haba mutuniyar, tsoro ba naki ba ne ba, ke jaruma ce i trust you dear, mu je kawai"
Su ka ƙarasa su ka shiga cikin kotun.
Su na nan zaune, Alhaji mu'azzam ya shigo, barrister Habib ma ya ƙaraso, sai ga murtala, su liti da Walid, cikin mamaki sai ga Nasir ma duk a cikin kotun daga baya sai ga mai gayya mai aikin shi ma ya iso kotun.
Ƙirjin Nabila na ta bugawa, amma ta tsananta maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, la haula wala ƙuwwata illa billah"
Ana ta gabatar da shari'oi, aka kira ƙarar su Nabila.
Tashi ta yi cikin nutsuwa, ta fita gaban shari'a.
Ta tsaya ta gabatar da kanta a da cikakken sunanta, da kuma wanda take karewa.
Lauyan da yake kare lakwari, ya fito ya gabatar da kansa, da wanda yake karewa.
Nabila ta nemi a karantowa masu laifi, laifin da ake tuhumar su da shi, a nan ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ya karantowa lakwari laifin da ake tuhumar sa da shi, da Madaki, duk da madaki ya na gadon asibiti ya na jinya.
Aka karanto tuhumar da turanci, cewar ana zarginsu da shiga cikin gidan Aminu Viper, su ka kashe mata da ɗan da kuma ɗan yake cikinta.
Kotu ta waiwayi lakwari domin jin ta bakinsa, bayan an fassara masa ƙusnhin tuhumar da ake yi masa, cikin harshen hausa.
A nan take lakwari ya musanta zargin, kamar yadda ya musanta a wurin 'yan sanda, da kuma yadda lauyansa ya jaddada masa kafin zuwan su kotu, domin kuwa ba ƙaramin kuɗi aka ba wa lauyoyi ba, a kan su yi duk mai yiwuwa ayi ta jan Shari'ar har ta lalace.
Daga haka kotu ta ɗaga cigaba da shari'ar, zuwa sati biyu domin bayyanar shaidun kowanne bangare.
Viper daga in da yake zaune, lakwari kawai yake kallo, ko ƙiftawa ba ya yi, zuciyarsa na raya masa kawai ya kashe shi ya huta, yanzu da haka za ayi ta jan ƙafa a shari'ar nan a ɗauki dogon lokaci ba a kammalata ba? Zuciyar sa azalzalarsa kawai take yi, ya na jin tamkar ba zai iya jira ba.
Ya na kallon lakwari, taswirar abin da ya faru a daren da jauhar ta mutu, na ƙara dawo masa a cikin ƙwaƙwalwarsa, yadda ya kasa kataɓus, ya na ji ya na kallonta ta na miƙo masa hannu.
Knasa ne ya yi wata irin sarawa, ya tashi cikin hanzari ya fita daga cikin kotun, gaba ɗaya fuskarsa ta sauya, tsantsar baƙin ciki da ɓacin rai, haɗi da tashin hankali ya mamaye ilahirin fuskarsa, tuni idanunsa su ka kaɗa su ka yi jawurrr.
Nabila ta na daga in da take ta bishi da kallo, ta san a rina, wani irin tausayin sa ya kamata, kamar ta tashi ta bishi, sai kuma ta tuna fushi take yi da shi, dan haka kawai ta basar.
Walid ne ya tashi ya rufa masa baya, liti ma biyo su yayi.
Walid ya cimma sa cikin hanzari, ya na kiran sunansa.
Bai tsaya ba, Walid ya riƙe rigarsa ta baya, ya juyo ya ture shi, amma ya sake riƙe shi.
"Mai laya" ya furta muryarsa na rawa.
Walid ya ce "Mai zamani"
"Idan zuwana wurin Shari'ar nan zai din ga fama mini gyambon da yake cin zuciyata ina ga zan haƙura kawai"
Walid ya ce "Ba zamu haƙura ba, bakin rai bakin fama, sai in da ƙarfinmu ya ƙare da yardar Allah"
Wata baranda Viper ya samu, ya zauna, ya miƙe ƙafafuwan sa, ya na jin yadda kansa yake ci ga ba da sarawa bugun zuciyar sa na ƙaruwa.
Liti ya zauna a kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa ya ce "Haba maza, zuwa yanzu yakamata ace fa ka saba da jurewa, ka yi haƙuri"
Viper ya kalli liti ya ce "A ganinka ragwancina ya yi yawa ko? Ba ka san me nake ji ba, yau da jauhar mutuwa kawai tayi Allah ya karɓi rayuwarta, zan yi mata addu'a na haƙura na dangana, sai dai zan rayu da begenta a raina. Abdullahi a kan idona fa aka kasheta, ban iya aikata komai ba, a kan cikinta na watanni tara ta faɗi, ta na kiran sunana, ba ta ji ba ba ta gani ba fa" Viper ya yi maganar cikin ƙunar rai, ya na sauke numfashi.
"Mun sani mai zamani, amma ka ƙarfafi gwkwarka, ko ita ma ta samu ta yi abin da ya dace".
Ya sauke numfashi ya ce "Wannan karon, muddin aka kuma yi mini abin da aka yi mini a baya, zan ɗauki matakin da nake ganin ya dace"
Nabila su ka fito tare da Sumayya, Sumayya cikin damuwa ta ce "To a haka za ayi shari'ar, yau ai ba a yi komai ba"
"Ba a yi wa shari'a gaggawa, mace ce mai ciki ba a san me za ta haifa ba, a sannu a ke bi, ba aikin jarida ba ne ba, jakadun yaɗa gulama kwando kwando"
Duka wasa sumayya ta kai mata, a lokacin da barrister Habib ya fito, tare da Alhaji mu'zzam su na magana.
Viper ya na cikin mota, ya na jiran Nabila su tafi, kawai ta shiga motar barrister Habib, tare da Sumayya.
Bai ce uffan ba, ya yi umarnin a ja motar su tafi.
Gidan da su ramma su