Showing 261001 words to 264000 words out of 479911 words

Chapter 88 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6132

ma ta ɗauke, tana mita "Wallahi Allah ya hore maka taurin kai, wannan shaye-shayen ne ba zaka daina ba ko?" Ya ƙura mata ido, saboda jin tana ƙamshin turaren florie irin na 'yar madara.

"Ina magana kana kallona, baka tausayin lafiyarka, yanzu duk ƙoƙarin jauhar a kanka ya tashi a banza, yawaita yi mata addu'a, istigfari da mayar da hankali a kan addu'a, shi zai rage maka damuwa, amma baka ji, kullum cikin hayaƙi, da shan miyagun ƙwayoyi"

"Faɗa fa ki ke yi mini"

"Au kar na yi maka? Ka daina mana da na yi maka mana, wannan abubuwan da kake yi ba shi yake nuna halaccinka a gareta ba, ka daina abun da ka ke yi, ka zama mutumin kirki, shi ne cikar halaccinka a gareta"

Kawar da kansa gefe yayi a hankali ya ce "Angry bird"

"Ni ce bird ɗin? Wallahi ni ba tsuntsuwa ba ce ba, da ba ka neme ni ba, ni gani ai na zo, ba a kama ni ba fa"

"Dama na san ba za a kama kin ba ai"

"Haba ya aka yi ka sani?"

"Bani wayarki" ta ciro wayarta ta miƙa masa.

Ya ciro tasa ya danna, sannan ya saka a kunnensa.

Muryar P.A ta fito rangaɗau a waya ya ce "Hello"

Viper ya yi shiru, bai ce komai ba.

Ya sake cewa "Hello", still bai yi magana ba.

"Waye ne ya ɓoye lamba yake kirana, idan ba za ayi magana ba, zan kashe, waye?"

"Mai zamani ne" waro ido P.A yayi ya ce "Wane mai zamanin?"

"Zuwa yanzu, na san saƙona ya iske shi, ya shirya, zan bayyana a lokacin da bai yi tsammanina ba, kuma ya daina wahalar da kansa a kan lallai sai an kamani, ko da an kama ni, nafi ƙarfinsa, ya kuma jirani aikena na biyu" ya katse wayar yana ajiyar zuciya.

"Kai, Oga kana burgeni, ka din ga acting kamar a film ɗin indiya hausa, wai dan Allah, a ina ka ko yi wannan halin naka?"

Ya jefa mata wayarta jikinta.

"Amma wait, wai ne ka ke yi a wayata ne baka gaya mini?"

"Yaushe zaki fara shari'ata?"

Nabila ta ce "Shari'arka akwai sarƙaƙiya boss, sonake na gama da ta ramma gobe in Allah ya kaimu zamu koma kotu." Ya jinjina mata kai.

"To zaka fara bani kuɗin aiki ai, ka ɗan ragen wani abu, na din ga zuba mai, tun da na je fa aka nuna mini file ɗin ka, nake ta up and down, ina tattara abun da zan tattara. In sha Allah zan zama sanadin daina zubar hawayenka"

"Dama kuka nake?"

"A'a murna ka ke yi"

Ya girgiza kai ya ce "Ko matata da muna tare, ta daɗe kafin ta iya kallona ta yi mini magana, balle ta yi mini baƙar magana, amma ke kin mayar da ni kamar wani sa'anki, har hantarata ki ke yi"

"Ni ɗin ce na rainaka? Ni na isa wacece ni? Amma dan Allah sweetheart meyasa ka kusa kashe ni ranar farko da na zo wurinka?"

Ya ɗago ya kalleta ya yi shiru.

"Ka amsa mini dan Allah"

"A lokacin ai kamar mahaukaci nake shiyasa"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, wani abu na din ga gani a idonka, da na rasa menene? Dan Allah meyasa?"

"Ke ban sani ba, tashi ki bar wurin nan"

Ta noƙe masa kafaɗa tana kallon idonsa, abun da ya tsana. Yayi tsaki ya kawar da kansa gefe.

Turare ta ɗaukko a jakarta, ta toshe hancinta, ta fesa a wurin. Ba shiri ya waiwayo yana kallon hannunta.

"Gashi yanzu na saka ka waiwayo ai, gashi saya maka na yi" ya karɓi turaren, ya din ga juya shi a hannunsa yana kallo.

Ta na ƙoƙarin ɗaga wayar da ake yi mata, ta ga hawaye na ɗiga a hannunsa.

Sai jikinta yayi sanyi gaba ɗaya. "Haba mai babban suna, a yanzu fa kuka ba naka bane ba, wanda ka yi ya isa, mu cigaba da addu'a da ƙoƙarin tattara shaidun da zamu shiga kotu da su, dan Allah ka daina bana jin daɗi.

"Da jauhar na raye, da yanzu na san ta kammala law school, maybe ta haifi yaronmu na biyu ko uku, ina da tarin burika a kanta, na kyautata rayuwar ta, ta ji daɗi ta huta, saboda wahalar da ta sha a rayuwarta, amma wauta ta da rashin hankali, ya sanya ta mutu ta bar ni a duniyar. Lokacin da duniya ta yi watsi da ni, ake yi mini kallon mara amfani, ta rungume ni, ta karɓi ƙaddararta, ta kula da ni, a lokacin da nake ƙoƙarin kyatata ratuwarta na fara bata kulawa, lokacin da na fara gano haske yana tunkaro rayuwarmu, ashe yayi daidai da lokacin da zan yi girbin ya mummunar hanyar da na zaɓawa rayuwata, na rasata" yayi maganar yana ƙoƙarin mayar da hawayen sa, amma suka cigaba da zuba, kamar an kunna famfo.

"Viper, ka yi haƙuri, Allah ya ambaci masu haƙuri a wurare daban-daban a alƙur'ani, tare da yi musu bushara. Viper Allah ya fi kowa so da kishin bawansa, wataƙila mutuwar jauhar a wannan lokacin shi ne mafi alkhairin ta, a duk buɗe ido muka yi muka ganmu a duniya, dan haka ba zamu tsarawa Allah yadda muke son kasancewa ba a duniya.
Ba kowa Allah ya tsarawa jin daɗi a duniyar nan ba, ai dama ita duniyar kurkukun mumini ce, aljannar kafiri. Wani ga jin daɗin yana cikinsa a zahiri, amma a baɗini rayuwar kawai suke yi mara ma'ana.
Yanzu tsohon ubangidanka ga duniyar ya samu, yana jin daɗin amma nauyin zunubin da yake aikatawa ba zai taɓa barinsa ya rayu cikin kwanciyar hankali ba. Ba sai mutum ya samu wadata dan ya sha wuyar rayuwa, shi ne tabbacin Allah yana son sa ba, duk tsananin rayuwa da ka ke ciki, idan har ya barka da imaninka, kuma ka yi kyakywan ƙarshe, wallahi ya fiye wa ɗan Adam duk wani abun more rayuwa.
In dai ana samun aljanna a biyayyar iyaye, da biyayyar aure in sha Allah Jauhar ta samu" ya jinjina kai yana cigaba da zubar da hawaye.

Ta bashi handkerchief ɗin ta, ta ce "Share hawayen haka, kaga ni ma ka saka ni kuka, bana iya jure in ga mutum a cikin damuwa ko yana kuka, alhalin ba zan iya yaye masa damuwar sa ba.
Yanzu ni kaina, duk abubuwan da nan da nake yi, ƙarfin hali nake yi, zuciyata akwai wani ciwo da yake addabata, ina kuka iya yi na wasu lokutan, sai dai babu yadda na iya, da abun da ƙaddara ta zana mini" tayi maganar ita ma tana kuka.

Ya ɗago ya kalleta, ya motsa baki, yana son ya faɗi wani abu.

Ayshercool
08081012143

63
Ta share hawayenta, ta ɗaga kanta ta ga ita yake kallo ta ce "Ka ce mini ka yi wa Indabo aike, me ka aika masa?"

"Hotona ne"

"Hotonka kuma?"

"Eh, hotona ne da ni da wani yaronsa da yake zaton ya saka an kashe masa shi"

Ta zaro ido ta ce "Wai shi mutane nawa ya kashe kenan a rayuwarsa?"

Ya rausayar da kai ya ce "Mutane sun ɗauki duniya fiye da yadda ki ke tunani. A baya bayan matsalar da nake fuskanta a gidanmu, fatan da nake yi kullum, Allah ya bani abun yi, ko iya abinci in din ga samu ina ci, sai da na haɗu da uban gidana dodo, ya haska mini duniya da in da mutane suka saka gaba. Da na so na yi kuɗi da yanzu ni hamshaƙin attajiri ne.
A lokacin da jauhar take ciyar da ni, da fari babu abun da yayi mini zafi, gani nake kawai auren dole aka yi mini, sam ba ta gabana, sai dai abun mamakina da ita, duk abun da zan yi mata bata jin haushi, naga yadda take sana'a tuƙuru iya yin ta, dan kar mu zauna da yunwa, daga baya nayi noticing idan abinci ba zai isa ba, sai ta bani ita tayi kame-kame ba ta ci ba, a lokacin ba wai dan tana so na bane take yi mini haka, ta rungumi ƙaddara ne, kuma tana tausayina.
Daga baya sai na fara jin kunyarta, lokacin da ta roƙi na sayo mata omo, naga responsibility ɗina, amma na zuba mata ido take yi, kuma bata taɓa nuna mini ta gaji ba. Sai dai a lokacin ba ni da wata sana'a sai sayar da wiwi da ƙwayoyi, yadda take yi mini addu'a Allah ya wadata ni da halal, ya nesanta ni da haram, ya sanya na ji ba zan iya ciyar da ita da kuɗin wiwi ba.
Sai a lokacin naga ashe, bayan mutuwar Sadik kukan daɗi nayi, da na ce na rasa sana'a, dan a lokacin na din ga faɗi tashi, saboda kar na ciyar da ita da kuɗin ƙwaya.
Da in ciyar da ita da wannan kuɗin, gara na dawo na maze na ce bani da kuɗi, na san ba ɗaga mini hankali za ta yi ba.
Gashi lokacin tana ta ƙoƙarin rabani da hulɗa da Indabo, wataran idan na ga wahalar tayi mata yawa, haka nan nake zuwa na tsitsiye Indabo ya bani kuɗi.
Zuciyata ta sha raya mini, na faɗa mummunar hanya, na samu kuɗi saboda jauhar ta huta, bana nuna mata hakan a zahiri, amma zuciyata kullum a takure babu daɗi. Duk da tsamin alaƙar da ke tsakanina da mahaifina, sai da na din ga jin tamkar na je na ce ya bani aron kuɗi nayi jari, amma na kasa, mussman tuna halin matarsa.
A lokacin da tausayinta ya fara zama tsananin so a cikin raina, da tana uzzura mini ko yi mini tashin hankali, da babu abun da zai hanani kauce hanya, dan yahoo zan fara, kuma kuɗi zan samu sosai da sosai, haka nan na san in da zan yi dillancin miyagun ƙwayoyi a tsakanin manyan mutane, har da ƙasashen ƙetare na samu kuɗi, amma ban taɓa burin tara kuɗi da mummunar hanya ba.
Ina ga lokacin da tayi ɓari ne, bani da wasu kuɗi sai na wiwi, shi ne aka yi mata magani da su, amma banda haka, ban taɓa ciyar da ita da kuɗin ƙwaya ba".

"Viper, labarinku abun tausayi, kuma gwanin daɗi, Allah ya bani ikon zama kamar jauhar, ina sonta sosai"

"Sai dai ki kamanta, ba zaki iya ba, ke mafaɗaciya ce, matata kuwa kan tayi faɗa sau ɗaya ana daɗewa, shiyasa nake kiyaye abun da zai ɓata mata rai ya sa tayi fushi, har ta yi faɗa. Na gode sosai da saka ni kuka da ki ka yi"

"Saka ka kuka kuma?"

"Eh, tun da na rasa jauhar, ban zubar da hawaye ba"

"Ai kai jarumi ne, bari na tashi na tafi gida, ka yi mini addu'a, gobe in Allah ya kaimu zamu zauna a kotu"

Ya jinjina kai ya ce "Allah ya bada sa'a, bani maganina"

"Dan Allah ka daina shan magungunan nan, lafiyarka fa"

Ya ce "Duba na na menene?"

Ta ciro maganin ta duba, cikin magungunan sa ne na Asibiti, ta ajiye masa ta ce "Allah ya baka lafiya mai amfani, ya bamu nasara a kotu, in sha Allah case ɗin ka ne next, ka yi mana addu'a" ya jinjina mata kai.

Ta tashi ta ɗauki jakarta tana ɗaga masa hannu.

***
Daren yau Nabila tayi ta addu'a, suka yi waya da Barrister Habib, ya ce su haɗu a kotu.
Ya ƙara mata ƙarfin gwiwa, kafin shiga shari'a, suna tsaye a harabar kotu, tana dudduba abun da zata tsaya a gaban shari'a da shi.

Nabila ta tsaya a gaban kotu, ta ce my lord, kamar yadda na gabatar da hujjojina a wancan zaman da aka yi, akwai voice na  muryar mahaifiyar ramma tana kokawa akan a nema mata hakkin 'yar ta.
Haryanzu ina da ja, a kan zargin da ake yi wa wanda nake karewa, a hirar da aka yi da mahaifiyar ramma, a gidan rediyo, wanda suka yi iƙirarin ya yi wa ramma fyaɗe, ya sha banban da wanda aka gabatarwa kotu.
Haka zalika, voice message ɗin da yake yawo, na mahaifiyar ramma, ta koka a kan wanda ya yi wa ƴar ta fyaɗe, ya dawo ya ɗauketa ta ƙarfin tsiya daga gabanta.

Lauyan gwamanti yayi suka, ya nemi da a gabatar da mahaifiyar ramma, ba wai kame-kame da abun da babu wanda ya san tushen sa ba.

Nabila nan take ita ma ta buƙaci, a gabatar da ramma, tayi mata tambayoyi.

Lawyan gwamnati ya ce Ramma na ƙarƙashin kulawar, likitoci haryanzu, dan haka ba za a gabatar da ita a gaban kotu ba.

Nabila ta sake cewa Wane irin illa aka yi mata, da har zuwa wannan lokacin za ace ba ta warke ba, a shekarun baya shekara sha uku sha huɗu ake yi wa mata aure, ba a samun matsala, suna zaune lafiya, a report ɗin da aka bayar na case ɗin ramma, abun bai zama complicated da za ace tsawon wannan lokaci tana Asibiti ba.

Lauyan gwamanti ya soki maganar Nabila, tare da neman a bashi dama ya gabatar da shaidunsa na gaba.

Wata mata ce ta fito, aka tambayi baba mai gadi, ko ya santa? Ya ce Eh, ita ma mai aiki ce a gidan.

Aka tambayi me ta sani, a game da abun da ake tuhumar mai gadi da shi, babu kunya babu tsoron Allah, ta bayar da shaidar zir, tare da tabattar da mai gadi ne yayi laifin, sai bayan da yayi aika-aikar, ta dawo daga sayen kayan miya, ta tarar da ramma, kuma daga shi sai ramma ta bari a gidan.

Baba mai gadi ya sunkuyar da kai cikin matsanancin ɓacin rai da mamaki.

Nabila ta ce ya za ayi ace gida kamar wannan babu cctv camera, akwai buƙatar idan da cctv camera a duba abun da ya faru.
Daga nan Nabila ta nemi a bata damar ta gabatar da nata shaidar ma, aka bata dama, ta buƙaci wata mata ta fito.

Nabila ta buƙaci matar ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a matsayin maƙwabciyar su ramma a can garinsu.

"Me ki ka sani game da abun da ya faru da ramma?"

"Eh to, bayan an dawo da ramma gida, ta cigaba da jinya, dan sallamo su aka yi daga Asibitin birni, saboda rashin isashshen kuɗi. Babar ramma ta gaya mini wata mata ta zo ta ce zata taimaka musu, amma sai sun yarda sun janye shari'ar.
Da suka ƙi, ta ce zasu gani, bayan wasu 'yan kwanaki, wani mutum ya zo da shi da wasu, ya gaya mata shi ne ya yi wa ramma fyaɗe, kuma ta ƙarfin tsiya, ya kama hannunta ya tafi da ita"

Nabila ta ce "Ko ta gaya miki sunan wanda ya keta wa yar ta haddi?"

"A'a, ba su san sunansa ba, ramma ba ta daɗe da fara aiki a gidan ba, amma ta tabbatar da ƙanin matar gidan ne. Bayan ya sace mata 'ya, ta je birni gidajen radiyo ba a saurareta ba, haka zalika wurin jami'an tsaro, kawai lokaci ɗaya muka nemeta muka rasa".

"My lord, shaida ta tabbatar da cewa wanda ya yi wa ramma fyaɗe, ya dawo ya saceta, wanda nake karewa da ake zargi yake tsare, tayaya zai je ya sace yarinyar. Kuma har zuwa wannan lokacin, ba mu ga ramma a zaman kotu ba, shin ina ramma take?"

Lauyan gwamanti ya ce bai kamata a karɓi shaidar maƙwabciyar su ramma ba, tun da ba a kanta abun ya faru ba, dan haka ayi fatali da shaidarta.

Duk yadda Nabila ta so bayyanar da nagartar hujjojinta, amma kotu ta din ga soke su.

Nabila tana ji tana gani, aka yankewa dattijon shekara goma sha huɗu a gidan yari, wata irin bahaguwar shari'a, mara fasali balle ɗigon adalci, yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da kammala tabattar da ingancin shaidun kowane ɓangare ba, sai dai an basu damar ɗaukaka ƙara.

Yanayin yadda ta fito a gigice kawai zai tabattar wa da mutum ba a hayyacinta take ba, sumayya da suka zo ɗaukan report ce ta nufeta da sauri, watsi ta yi da file ɗin hannunta, ta faɗa jikin sumayya tana kuka.

Barrister Habib ya ƙaraso, ya ce "Haba Nabila, wannan ai sai ki saka ayi mana dariya, akwai appeal a gaba, dan Allah ki nutsu.

Cikin kuka ta ce "Sumayya mu tafi gida, ba zan iya sake haɗa ido da mutumin nan ba, i try my best, ai kun ga yanayin shari'ar da aka yi, dama haka aka koyar da mu, an bi Principles na law a wannan shari'ar?"

Sumayya ta din ga rarrashinta, suka sakata a mota, barrister Habib ya ce "Bari mu kaita gida, Bashir kai ka tafi da motata"

Suna tafe a mota tana cigaba da kuka, Barrister Kabir ya kira Habib, ya ce "Ya ake ciki ne?"

"Gamu zamu tafi, ba ta yi wining ba, sai kuka take yi"

Kabir ya ce "Ai dama na gaya mata, waye ya gaya mata jayayya da mutanen nan abu ne mai sauƙi?"

"Dan Allah kar ka saka ta sare gaba ɗaya, za mu yi appeal, kuma saboda ita nima zan yi abun nan kyauta fisabilillahi i really appreciate what she did" ya ajiye wayar yana cigaba da yi wa Nabila nasiha.

Bunkure ta ƙyaƙyace bayan kammala wayar da ta yi, ta kalli badi'a.

Badi'a ta ce "An kammala komai kenan?"

"Eh, an ƙarƙare shari'ar a yau, uba ya yi abun da ya dace, wallahi da bai yi wani yinƙuri ba, sakar musu zan yi su ƙarata daga shi har ɗan nasa, su ta shafa, amma a wannan karon dole na ɗauki mataki a kan yarinyar nan, da gaske so take yi sai ta tona mini asiri, dole zan tattauna da indabo, ya ɗauki mataki a kan ta"

"Amma kina ganin hakan zai yiwu, tun da abu ya shiga social media, kuma ta fara samun masu mara mata baya?"

"Iyayen gidanta ma, ba su kai ko ina ba, amma an ce mini an hangeta da barrister Habib, kuma ina kyautata zaton da saka hannunsa a wani abun da take yi, amma duk na san matakin da zan ɗauka akan dukkansu" ta ƙarasa maganar tana haɗiye ƙwayoyin da suke hannun ta, ta bi su da ruwa.

Nabila bayan sun kaita gida kuwa, ba ƙaramin kuka tayi ba, gaba ɗaya sai ta ji ta karaya, komai ya fita daga kanta.

A ɗakin Nasir, ya sameta bayan ya dawo daga aiki, ko da ya tarar da Nabila ta sha uban kuka, tuntsirwa yayi da dariya, ya ce "Haba barrister, ina ƙwarin gwiwar ta ki? Har kin karaya haka?. Abun da na yi ta nuna miki kenan, nake gargaɗinki a kan ki fita daga sabgar nan, ba ke kaɗaice mai gaskiya a ƙasar nan ba, amma tun da ki ka ga kowa ya ja baki yayi shiru, to abun ya gagari kundila, amma ki ka ƙi ganewa ki ka cigaba da dagewa,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login