Showing 408001 words to 411000 words out of 479911 words

Chapter 137 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6187

fito yaya za ku yi da su ne, dan ko da me ku ke yawo ba zai saki rahama ba, ban taɓa tunanin ana irin wannan son a gaske ba gaskiya"

Ya ce "Abin da mahaifiyarta ta yanke kawai, ni dama babban fatana a hukunta shi, maganar aurensu ni bani da abin cewa"

Nabila ta ce "Vi dan Allah ku yi haƙuri, ku yafe wa gayen nan, yayi nadama kuma wallahi suna son junansu da rahama, ku bar masa kayyasa, tasa ce"

"Ba za a bashin ba, bashi da nasaba mai kyau"

"Vi sai ya ci albarkacin ku, nasabar tasa ta gyaru, wallahi ni gaba ɗaya karya mini zuciya ya yi, dan Allah a bar masa ita, yana sonta sosai"

"Anƙi"

"Vi baka san menene so ba, ba ka san zafinsa da wahalarsa ba"

Ya ce "Eh ban sani ba, kuma bana fatan na sani. Ke da liti ban san wanda ya fi wani raina ni ba, shi ya ce ba zan sake yin aure ba, na shiga ittikafi, ke kin ce ban san so ba, ina ga ni duniyata daban, ba a jinsin mutane nake ba"

Sosai Nabila take dariya ta ce "To mutum ne kamar boss, kullum rai a haɗe kullum cikin tsare gida, dole a yi tunanin baka jin komai, da ya shafi soyayya"

Tunawa yayi da Jauhar ta taɓa gaya masa magana makamanciyar wannan.

"Ba na tunanin akwai wanda so ya azabtar kamar ni, a lokacin ban san menene shi ba.
Ranar da na fara ganin jauhar, ta ganni rungume da liti cikin jini, ta ƙwala ihu ta suma.
Haka kurum gabana yayi mummunar faɗuwa, na je na ɗagata na ga ta suma, tun daga ranar nake yawan mafarkinta, da na tuna a yanayin da ta ganni, za ta yi zaton kisan kai nayi, sai na ji babu daɗi na damu, har zuwa lokacin da Allah ya haɗamu a inuwa ɗaya, tsarki ya tabatta ga Ubangiji mai jujjuya al'amura yadda ya so, a lokacin da ɗan Adam bai taɓa tsammanin faruwar abin ba. Allah ya jiƙan Zahra"

Jiki a sanyaye Nabila ta amsa da Amin, tare da jin begen ina ma ko sau ɗaya ta ga jauhar a rayuwarta, tana matuƙar jin daɗin yadda ake faɗar kyawawan halayenta.

Viper ya ga likita kamar wancan lokacin, ya bashi shawarwari, sai dai a tattauanawar da suke yi ne, likita zai gano bakin zaren, sai dai fafur Viper ba ya son magana, sai dai Nabila ta yi ta ɓaɓatun itakaɗai.

Bayan sun fito sai da suka je gidan su Ramma, suka gaisa, Viper da maman suka din ga hira, Nabila kuma suka shiga ɗaki da ramma.
Sai azahar suka bar gidan su ramma, Nabila ta yi ta rarrashin ramma, ta kwantar mata da hankali.

Bayan sun fito wani store ya kai Nabila, ya ce ta ɗauki duk abin da take so.

Ta kalleshi ta ce "Meyasa ka kawo ni nan, ina fatan ba biyana kuɗin aikin da na yi zaka yi ba, ka riga ka biyani, haɗa ni da mahaifina bana buƙatar komai daga gareka, komai na yi maka kaina na yi wa"

"Ai bani da abin biyanki, dake da iyayenki, bani da abin biyanku, wani ihsani ne kawai, wani abu da na daɗe ina burin in ga ina yi wa jauhar, a lokacin ba ni da halin hakan, amma tun da gaki sai na yi miki a madadinta"

Tayi murmushi ta ce "Na gode sosai da sosai Vi, amma idan ka yi mini haka, zan ga kamar ka biyani ne abin da na yi maka, maganar gaskiya ba zan iya yadda ka yi mini sayayya ba, domin hakan tamkar cin amanar jauhar ne, kuma kaga Jauhar daban ni Nabila ma daban".

Ayshercool
08081012143

97
Shiru yayi yana dubanta, domin ya tabattar idan da gaske take, sai dai yanayin fuskarta ya tabattar masa da gaske take yi ba wasa ba.

Basarwa yayi ya ce Shikenan su tafi, amma deep down ya ji zafin abin da ta yi masa nesa ba kusa ba, he wish 'yar madararsa tana raye, da ya san ita ba zata watsa masa ƙasa a ido ba, kamar yadda Nabila ta yi yanzu ba.

Dan rashin kunya, su na tafiya a hanya kuma, ta na yi masa hira da surutu, ganin ya yi mata banza, ya sanya ta ja bakinta ta tsuke, kuma ta tabattar fushi ya yi.

A hanya ya sauka, ya bar ta da Joseph, ya mayar da ita gida, shi kuma yayi nasa wuri.

****

Washegari da yamma, Abba yana gidan gonarsa, yana office ɗin sa, ana ta fitar da ƙwai na kaji, da na sauran tsuntsaye ƙaton gidan gona ne sosai da sosai, gidan gonarsa na cikin manyan gidajen gona da yake fitar da ƙwai, har maƙwabtan garuruwa. Da su kansu kajin da kifaye, ban da sauran dabbobi.

Masinja ya sanar da shi ya yi baƙo, Abba ya ce a shigo da shi.

Mintuna kaɗan aka buɗe ƙofar Office ɗin aka shigo, ajiye biron hannunsa ya yi yana kallon Viper.

Viper ya yi sallama, Abba ya amsa a hankali yana ci gaba da kallonsa.

Ya ƙaraso ya tsaya, ya gaida major cikin girmamawa kamar yadda suke yi a tsakaninsu masu ɗamara, hakan ya tabattar wa Major akwai wani abu tattare da baƙon nasa. Ya bashi dama ya zauna.

Viper ya ce "Duk mun taɓa haɗuwa ba na da tabbacin ko ka gane ni, amma bari na sake gabatar maka da kaina, sunana Al'amin Ibrahim, wanda 'yar ka Nabila ta tsayawa a kotu, kuma mijin 'yar uwar Nabila da Allah ya yi wa rasuwa"

"Mijin wadda ka kashe dai, da babanta bai san ciwonta ba ya ɗauketa ya aura maka. Ta yaya zan kasa ganeka, da ka ɓata mini shirina na shekara da shekaru ka ɗauki Nabila ka haɗata da babanta, mutumin da bai martaba rayuwar uwarta da ta 'yar uwatta ba har ya iya aura maka ita ka kasheta".

"Ba ni na kasheta ba, kamar yadda kotu ta tabattar kuma ta wanke ni, ina roƙonka saboda Allah, kar laifin da ba namu ba ya shafe ni da ni Nabila, mussman ma ita.
Makamancin abin da ya faru da Jauhar, irinsa ne a rayuwata, da ya jefa ni cikin ƙaddara. Duk wannan mummunar rayuwa da nayi, ta samo asali ne daga rashin samun ingantaccen bangon da zan jingina rayuwaya da shi, sai da ƙaddara ta saka aurena da Jauhar, ba zan taɓa mantawa da ita ba har duniya ta naɗe, kuma ban kashe jauhar ba.
Kamar yadda kotu ta tabattar, duk da na fuskanci mutum ne kai irina, muna amfani da ƙwaƙwƙwarar shaida da muka gani a zahiri ne, ba dan haka ba, ba zan so na baka wata gamshashshiyar hujja da shaida da zata tabattar maka da Nabila a kan dai-dai take, kamun da aka saka ɗanka yayi mini ba bisa ƙa'ida bane ba.
Da fari hukumar'yan sanda ce ta bashi umarnin, daga baya kuma an bashi maƙudan kuɗi dan ya kama ni, hakan ya sanya ya din ga ɓata Nabila a idonka. Duk ban gaya maka wannan abun da raba maka kan iyalinka ba, roƙonka kawai nake yi, ka daina fushi da Nabila, duk da ganin mahaifinta da ta yi, a duniya ba ta da wani wanda ta shaƙu da shi take ƙauna sama da kai. A madadinta ina mai ƙara baka haƙuri, domin kuwa na san duk ni ne silar komai, amma dan Allah na roƙe ka, ka yi haƙuri ka yafe wa Nabila da mahaifinta, ci gaba da fushi da ita, zai kua jefa rayuwarta a cikin damuwa"

"Ka gama?" Major ya yi maganar yana kallon Viper.

Viper ya yi shiru bai ce komai ba.

"Na ji na kuma gode, amma ka tashi ka tafi, ka ɓata ruwa ba domin ka sha ba, ka ɓata mini haɗin kan iyali"

"Abba ban ɓata maka kan iyali ba, son abin duniya ne ya rinjayi Nasir, ya ƙara ta'azarra al'amarin, ina sake baka haƙuri, saboda Nabila kar azo ta shiga wani halin" ya na gama maganar ya tashi tsaye ya fice daga ofishin.

Bayan fitarsa Major ya yi shiru yana kallon ƙofar da ya fita, da nazartar maganganun da ya yi.

Gaba ɗaya Viper ya daina kiran Nabila a waya, ita ma kuma ba ta neme shi ba, hakan ya ƙara tunzura shi, ganin yadda ta watsar da shi gaba ɗaya.

Major ya so ya yi wa Nabila maganar zuwan Viper in da yake, amma yayi mata shiru ya rabu da ita.

*****

Satin awon Ramma ya zagayo, Nabila ta je ta ɗauki ramma, suka je asibiti. Aka yi mata awo aka duddubata, komai nata lafiya ƙalau.
Su ka tsaya suka yi sayayya, suka tafi prison. Ramma sai murna take yi tana jin daɗi za ta ga Abdul.

Saboda yadda Nabila ta zama popular yanzu, duk in da ta shiga an santa, tana samun alfarma, yau ma har ciki aka shiga da su.

Aka je aka fito musu da Abdul, yana ganin ramma ya saki murmushi, ita ma murmushin ta sakar masa, ta miƙe tsaye ba tare da ta san ta miƙe ba.
Nabila ta ce "Bari na baku wuri, idan kun gama ma gaisa" ta fita waje, bai damu da gandiroban da yake wurin ba, ya rungume abar sa.

Ta ce "Doctor ya jikin ka warware?"

"Inyee an daina gantsara mini sunana,  Abdul yasar"

Ta saki murmushi ta ce "Ko dan saboda wannan ai yakamata na fara saye sunan" tayi maganar tana nuna masa cikinta, da ya kai watanni shida ya fito sosai.

Murmushi yayi ya zira hannunsa cikin hijjabinta, ya shafa cikin nata.

"Ina fatan dai wurin awon babu wata matsala da babyn namu?"

Ta ce "Anty Nabila tana kula da ni sosai, tana kai ni awo"

"To ki na cin abincin da shan maganin dai ko?"

Ta jinjina kai ta ce "Eh, kawai dai ina son na ga ka fito ne, ina cikin damuwa tsareka a wurin nan"

Ya kalli wurin ya ce "Kar ki damu, ai na riga ma saba kuma ba wata wahala nake sha ba your excellency, kewarki nake tayi ne dai kawai, amma yaya zasu bar mu mu cigaba da zaman aurenmu?"

Ta rausayar da kai, ta ce "To gashi nan dai, ban san ya ake ciki ba, basu sake cewa komai ba. Ina son in roƙi Anty Nabila, ta ɗan ƙara lallaɓa mini su, amma nauyinta nake ji".

Ya ja hannunta suka zauna, ya ce "Ni zan roƙeta, ko sake durƙusawa zan yi a gabansu na basu haƙuri, ni dai su bar mini ke babyna, da ke jaririnmu mu rayu tare ko Rahamana?"

Ta jinjina masa kai, ta numfasa ta ce "To yaya yanayin abincin kana samu ka ci kuwa?"

"Eh mana, komai nawa normal kawai dai ina tsare ne, ki kwantar da hankalinki, ki rainar mana babynmu, ina fatan lokacin da zan fito yayi dai-dai da lokacin da zaki haihu, a karɓi haihuwar nan da ni. Na so ni zan kula da ke ayi rainon cikin nan da ni"

"To yaya zamu yi, kana naka Allah ya sa shi ne dai-dai, Allah ya fito mini da kai lafiya"

Abdul ya dafa kafaɗarta ya ce "Naki ne ni?" Ta jinjina masa kai cikin jin kunya tana murmushi.

"Naki ne ni rahama, ƙaddararmu ce ta zo mana a hagunce, amma mun gode masa Allah ya sassauta mana, ya sanya su barmu mu yi rayuwarmu ta aure"

Ta ce "Amin, bari ta zo ku gaisa, mu tafi, na san yanzu za su ce mu tafi"

Ya marairaice ya ce "Haba dai, kwata-kwata yaushe ku ka zo, ban gaji da ganinki ba, yayi maganar yana sumbatar goshinta.

Gandiroba ya ce "To sharokhan baban soyayya, lokaci yayi"

Abdul ya yi murmushi ya ce "Ai shi sharokhan na shi film ne, ni kuwa soyayya ce ta zahiri, dan haka ni na fi shi ma" yayi maganar yana dariya.

Nabila ce ta dawo, suka gaisa da Abdul, sai dai da ta ga farinciki a fuskokinsu, sai ta ji daɗi.

"Ina godiya sosai da sosai, rahama ta gaya mini yadda ki ke kula mini da ita da babyna, Allah ya saka miki da alkhairi"

Nabila ta ce "Amin, ai yi wa kai ne, rahama ƙanwata ce, ina jin daɗin ganinta cikin farinciki. Nayi mamakin yadda aka yi ka yi mata laifi kamar wannan kuma ka iya dasa soyayyarka a cikin zuciyarta. Meye sirrin ne?"

Yayi murmushi ya ce "Ita zaki tambaya ai"

Ramma ta harare shi ta ce "Ba wani sirri, ban da faɗa me ka iya?"

"Soyayya" ya bayar da amasa kai tsaye, da sai da ramma ta ji kamar ta nutse.

Suka yi dariya, ya sake cewa Nabila "Dan Allah na ga kamar ke kina tausaya mana, dan Allah ki rarrashi mama, ki ba ta haƙuri su bar mana aurenmu dan Allah"

Nabila ta sauke numfashi ta ce "To bani da ta cewa ne, idan na matsa yayanta hayayyaƙo mini zai yi, amma zan lallaɓa ta ɓangaren mama na cigaba da shawo kanta, in sha Allah komai zai wuce"

Ya ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi. Idan da wani abu ko kuɗi sun yi kaɗan, ayi mini magana"

Nabila ta ce "Kai wane irin kuɗi sun ƙare, wannan maƙudan kuɗi har haka, akwai kuɗi sosai in sha Allah ba wani abu"

Ya ce "To shikenan, muna godiya sosai barrister, babyna sai yaushe kuma?" Ramma ta galla masa harara, amma bai fasa ba, ya riƙe hijjabinta, ta waiwayo ta fizge ta na murguɗa masa baki.

Shafar sumar kansa ya yi, yana dariya, suka fice ita da Nabila.

Suna tafe a hanya, Nabila ta ce "Ramma har mamaki ku ke bani da ke da Abdul, dan Allah me Abdul ya yi miki, har ki ka fara sonsa, duk da girman laifin da ya aikata miki?"

Ramma ta jinjina kai ta ce "Na san da yawa ba za su fahimce ni ba, za a zata ko kwaɗayin wani abu ne na hannunsa, ko kuma wani abu nake yi wa, wanda ni har muka rabu ban san menene auren ba, kawai dai ina jin daɗin shiryuwar sa a dalilina. Kuma yana da wasu nagarta, wanda shi kansa bai san yana da ita ba. Da ya samu isashshiyar tarbiyya, ba zai yi wasu abubuwan ba.
Ya nuna tsantsar nadamarsa, gani nake idan na rabu da shi, zai iya koma wa ruwa, duk da da gaske, yake tuba a kan abubuwan da yake aikatawa. A matsayin ya aureni, ya tabattar mini da ya aure ni, babu irin zagi da rashin mutuncin da ban yi masa ba, amma ko a jikinsa, bai taɓa damunsa ba, kawai zai yi abin da ya ga dace yayi domin ya kyautata mini, ko na yaba ko na kushe bai dame shi ba.
Sannan daga halayensa masu kyau, yana da tausayi da taimako, mutum ne mai kyauta ta ban mamaki, kuma ya san aikinsa sosai da sosai, ina duba wannan abubuwan ne, amma ni kaina na san ta wani ɓangare kamar ban kyauta wa kaina da mama ba"

Nabila ta ce "Kar ki ce haka, wannan shi muke kira da jarrabawa, Allah ya jarabce ka ya ga yaya zaka yi? Bar ganin Abdul ba ya ji, wallahi sai ki ga saboda yawan kyautarsa da taimakonsa, ya sanya Allah ya din ga ji da shi, maybe shiyasa ya sanya tsautsayin nan a tsakaninku, domin ya rabauta ya tuba, yadda ya daina zina within shot period of time da ku ka zauna, ya cancanci a yaba masa daga ke har shi, ina fatan Allah ya tabattar da alkhairi a zamanku, ya sanya sanadin shiriyar sa kenan, idan Allah ya tabattar da zamanku, ki yi ƙoƙari ki rufa masa asiri, ki zauna da shi da zuciya ɗaya, ki yafe masa".

Ramma ta ce "In sha Allah Anty, na gode sosai da sosai, Allah ya nuna mana aurenku ke ma, da Yaya Al'amin"

Nabila ta kalleta ta ce "Da wa? Wannan yayan naki ai sai Jauhar ɗin, Allah ya bashi mace ta gari dai ba Nabila ba" Cikin mamaki Ramma ta ce "Amma Anty Nabila saboda me? Wallahi yana da kirki, yana da faɗa ne dai kawai"

"Wasu dalilai rahama, ki manta kawai, ba soyayya muke yi ba dama, kawai dai nima yayananne"

Jiki a sanyaye ta ce "A'a shi sonki yake yi"

"Yaya aka yi ki ka sani, shi ya gaya miki?"

"Ni a wa zai gaya mini, bai gaya mini ba, amma wasu lokutan irin kallon da Abdul yake yi mini, yake yi miki. Idan mutane sun kai goma a wuri, duk wanda zai yi magana ba zai damu ba, amma da kin fara magana, zai tattara nutsuwar sa da hankalinsa a kanki. Ko wani abin ki ke yi daban, yana kallonki ta ƙasan idonsa"

Kwashewa da dariya Nabila ta yi, ta ce "Kai rahama, haka ki ke saka masa ido kina kallonsa, ke duk a ina ki ka san hakan shi ne so?"

"Wurin doctor, amma Wallahi yana sonki"

"Daina rantsewa rahama, Viper mace ɗaya tak yake so a duniya, kuma yanzu ba ta raye, babu kuma macen da za ta iya maye gurbinta, dan haka ki manta kawai"

Rahama ta ce "Shikenan, tun da kin ce haka, amma ai kamarku ɗaya ita, kema yana sonki, ina ga dai ke ca ba kya sonsa kawai" Rahama tayi maganar cikin sanyin jiki sosai, dan tana son ta ga sun yi aure, dan sun dace sosai.

****

Abubuwa suka din ga damun Major, game da maganganun da Viper ya gaya masa, sai ya kasa haƙuri, ya kira Nasir ɗakinsa.

Ya dube shi sosai sannan ya ce "Nasir tambayarka zan yi, kuma ina so ka ji tsoron Allah, ka gaya mini gaskiya"

Ya ce "To Abba in sha Allah"

"Waye ya saka neman yaron nan da Nabila ta kare?"

Ya numfasa ya ce "Abba maitaimakin CP ne"

Abba ya ce "Da kuma wa?"

"Shikaɗai ne Abba"

"Gaskiya na ce ka gaya mini, waye ya baka kuɗi a matsayin cin hanci, ya ce lallai ka nemo shi? Kar ka yi mini ƙarya, ka san nima tsohon ma'aikaci ne"

"Ba kuɗi aka bani ba, senator ma'aruf Indabo ne"

"A kan me zai saka ka nemo masa wani ɗan daba, menene alaƙarsa da ɗan daba yana sanata?"

Nasir ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba Abba"

"Baka sani ba, kawai ka karɓa ka fara yi, Nasir idan baka ji tsoron Allah a kan aikinka ba, a tsiyace zaka shekara talatin kana wahala, ka gama aiki ka zama abin tausayi.
Na fara yadda wasu abubuwan kai ka ta'azzara su, kamar Nabila ta fika gaskiya".

"Abba mutumin fa ɗan daba ne, da yake zubar da jini, da aikata miyagun laifuka"

Major ya ce "To meyasa ba ku nemi kama shi a kan laifin da yake aikatawa ba, wani zai ja ka gefe ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login