Showing 177001 words to 180000 words out of 479911 words
a wannan maganar"
Baba ya ce "Al'amin kama hannun matarka ku tafi, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba"
Jauhar kuwa kuka ta din ga yi wiwi, har da roƙon Al'amin ya bari ta zauna, amma ya ƙi ya ce sai dai su tafi gida.
Saifu kuwa ya ce "ba dai kuna murna kun cuci marainiya kun aura mata ɗan wiwi ba, kun aurawa taku mai kuɗi, ai ga reshe nan ya juye da mujiya".
Jauhar har sai da ta ji haushin Al'amin, na hanata zama a wurin 'yar uwatta.
Aka rasa ainihin abun da yake damun hafsa, shaye-shaye ne? Sihirin ne ko aljanu aka kasa gane kanta, wasu lokutan babu magana abinci ma taƙi ci sai kuka, da daddare ta kasa bacci tayi ta koke-koke tana ihu kamar mahaukaciya.
Iyaka Alhaji mu'azzam ya zo dubata, ya zube musu uban kuɗi ya tafi.
Jauhar ta samu admission a legal, ta fara karanta shari'a law, indabo ne ya bata scholarship, sauran hidimar makaranta kuwa shi yake yi mata.
Har keken ɗinki, ya samo mata a irin wanda Indabo yake cewa zai rabawa mata goma, amma ace an bawa mata ɗari, ya ce ba zai bashi ba, sai idan ya yadda za a ɗauki hoton jauhar da keken a saka a social media.
Ya ce babu wanda ya isa ya ɗauki hoton matar sa, ya saka a social media, a kan wani keken ɗinki kuma sai an bata.
Indabo ya ce wa Al'amin, ya saka yaron da ya ce a samowa aiki a abuja, an samu gurbin direba a wata babbar ma'aikata top 10 na Nigeria, tare da albashi mai tsoka ya ce ya kai takardunsa na sakandare da aka ce yayi.
Guduma bakinsa ya ƙi rufuwa, saboda tsantsar farinciki da murna ta gaske, jin zai tafi Abuja aiki, alhalin idan da wanda ya kamata ya tafi, shi oga kwata-kwatan ne.
Mahaifiyar Nura, sai da ta zo tun daga garin da take aure, ta zo ta yi wa Al'amin godiya, tare da jauhar, dan Nura duk ya bata labarin irin zaman da suke yi da su.
Jauhar ta mayar da hankali a kan karatu sosai, duk da a gefe guda tana yi wa Al'amin magiyar shi ma ya koma makaranta. A kaso ɗari yanzu babu kaso arba'in na shaye-shaye da neman rigima da Al'amin yake yi.
Ya shiga ya fita, aka bawa unguwar su sabuwar transformer daga wurin indabo, lokacin da ta su ta lalace, a cewarsa 'yar madara ba ta son zafi.
Har burji aka yi wa unguwar aka gyara musu kwatocin layukansu, aka zuba musu burji a manyan hanyoyin su.
Abu kamar wasa, sai 'yan unguwar suka fara girmama Al'amin, ganin cigaban da suke samu a dalilin sa, duk da wani abun Indabo ba a son ransa yake yi wa Al'amin ba, dan dai kawai ba shi da yadda zai yi da shi ne.
Aka bashi kuɗin sa na garin tofa, na gonakin mahaifiyar sa, kuɗi ne masu yawa, ya yi wa jauhar gyaran gida sosai da sosai, ya canza mata wasu abubuwan, ya saka mata talabijin, dan ma tana hana shi yi mata wasu abubuwan, saboda kar kuɗin su ƙare a banza.
Ya buɗe wurin sayar da shayi, a can unguwar su, liti zai din ga kula da wurin, ko Abbu bai san ya buɗe wurin ba. Ta saka shi sun yi addu'a sosai a kan buɗe wurin.
Al'amin ya cewa jauhar tafiyar ggagawa ta kama shi zuwa Lagos, juyin duniya ya gaya mata me zai je yi, ya ce mata bakomai, zai je ya duba ne, idan da wani abun da zai iya sayowa ya zo ya sayar a kano.
Kafin ya tafi, wasu irin mahaukatan karnuka ya ajiye a layin, su uku masu faɗan tsiya, malam lawan ya tambayi dalilin ajiye wannan karnuka da suke barazana ga rayuwar su.
"Tafiya zan yi, gadin mata ta za su yi mini"
"Amma banda abun ka, ai Allah ne zai kareta ba karnuka ba"
"Meyasa ka gina gida ka saka matrka a ciki, duk da ka san cewa Allah ne zai kare maka ita, ba ka bar ta a titi ba?" Yayi shiru.
"Kar ka sake shiga harkat da abun da nake yi na gaya maka"
Ita kanta jauhar da fari ba ta ma san saboda ita aka ajiye su ba, ita kanta tsoronsu take ji, gashi sun san lokacin da take dawowa daga makaranta, a bakin titi take tarar da su, da sun ganta, sai biyu su shige gaba, ɗaya kuma yana bin ta a baya.
Sai da yayi kwanaki takwas a lagos, sai dai kullum su yi waya amma still bai gaya mata me ya je yi ba.
Wurin shayin su liti kuwa, jauhar ita ce yin meatpie, cin-cin, dafaffen ƙwai ne, duk abun da ya samu yi take yi, a lokacin ana processing tafiyar Nura guduma bai tafi ba tukuna, shi yake zuwa ya ɗauka ya kai.
Ko ta tsiri yin awara bayan magariba ko wainar fulawa, ya ɗauka ya kai can wurin shayin, kasancewar matasa na taruwa a wurin, sai dai ya kawo mata kuɗinta an saye.
Ta ce "Nura ina yi maka murnar tafiyar nan, amma ta wani fannin ni aka yi wa"
Ya ce "Wallahi ni kaina na fara kewar ku, na san a can babu abinci mai daɗin naki"
Tayi dariya ta ce "Halinka ɗaya da yayan naka ai".
Ranar da Al'amin ya dawo kuwa, ta sha tsaraba, har maƙwabta sai da suka samu.
Ga kyakykyawar tarba da ya samu daga wurin Uwargida sarautar mata.
Hafsa kuwa haka nan aka sasanta, bayan ta ɗan samu sauƙi aka mayar da ita gidan Alhaji mu'azzam, sai dai ba a wani samu sauyi ba, a kan abubuwan da suke faruwa, a baya damuwa da take yi mata yawa ya sanya take shiga tashin hankali, amma tun da ta samu maganin damuwarta ta hanyar shan magunguna masu sanya bacci, sai ta yi overdose yadda za ta bugu sosai ta manta duk wani abu da yake damunta.
Dawowar Al'amin ya zo da kuɗaɗe, kuma ya ƙi gaya mata yadda aka yi ya same su. Ba ta zargin sa, dan ta san ba ya taɓa kayan wani, duk abun da zai kai shi ga taɓa abun da ba nasa ba, ba ya ci.
Cikin ikon Allah, tun zuwan da suka yi tofa, hajiya take zuwa kawo musu ziyara, da wasu daga dangin mahaifiyar Al'amin.
Ana ta shirin tafiyar guduma babban birnin tarayya, ya ce ya fasa ba zai je ba, mahaifiyar sa ta zo har gida ta gaya wa Al'amin, dan bai gaya wa Al'amin cewar ya fasa zuwan ba, mamansa ya je ya gaya wa.
Mai unguwa yana ta barbaɗa an yi wa nura hanya zai tafi Abuja aiki.
Al'amin ya sa aka nemo masa Nura guduma, ya tambaye shi, menene dalilin sa na fasa tafiya.
Ya girgiza kai ya ce "Bakomai"
"Ban gane babu komai ba, idan ka zauna a nan ɗin uwar me zaka ci ko ka yi, iyayenka na murna ka samu wurin da zaka rufawa kanka asiri ka ce ba zaka je ba, saboda me?"
"Babu komai".
A fusace Al'amin"Zan fasa maka kai, ka buɗe baki ka yi mini bayani, meye dalilin da ya sanya lokaci ɗaya ka ce ka fasa tafiya? Duk yaran da suke ƙarƙashina babu wanda na ɗauka na zaɓa sai Kai ka watsa mini ƙasa a ido?"
Yayi shiru.
"Ba magana nake yi maka ba"
"Yaya bakomai"
Jauhar ta ce "Master, ka kira shi indabon a waya, ko cire sunansa suka yi? Ko wani abun ne ya faru, tun da ai da murna yake yi zai tafi".
Yana huci ya kira wayar indabo, yana ɗagawa ya ce "Yaya aka yi Nura ya ce ya fasa tafiyar nan, ko akwai matsala ne?"
Indabo ya ce "Shi zaka tambaya, su kusan bakwai ne, ranar juma'a za su tafi, a kai su wuraren da za su yi aiki, ni ban ma san ya fasa ɗin ba, P.A ne yake kula da shirin tafiyar su".
Al'amin ya kashe wayarsa, ya ce "Ba ka da wani dalili ko hujja, dan haka tafiya ranar juma'a " Nura yayi shiru.
"Ba magana nake yi maka ba?"
Ya ce "To in sha Allah "
Bayan tafiyar sa, Jauhar ta ce "Master da ka ƙara matsawa ka bincika, babu yadda za ayi ace da farko yana ɗokin tafiyar nan, lokaci ɗaya kuma ya ce ya fasa, anya babu lauje cikin naɗi?"
Ya girgiza kai ya ce "Iskanci ne kawai, maybe abokai suke ziga shi, idan ya tafi can zai zama busy sosai, ba zai samu isasshen lokacin yin rashin ji ba".
Ta ce "Eh to, zai iya yiwuwa Allah Ubangiji ya tsare shi, ya sa sanadin shiriyar kenan. To kai ma master a samo maka mana"
Ya kalleta ya ce "Wa?"
"Kai mana"
"Kema kin san ba zan yi ba"
Ta ce "Amma ai na ga ba ka raina sana'a komai ƙanƙantarta"
"Ba sana'ar na raina ba, ba zan ɗauki duk wani nau'i na rashin mutunci bane, kema kin sani"
"Haka ne kam, shiyasa nake mamakin yadda ka ke yi wa indabon nan, yake ƙyaleka, yadda suke wulaƙanta mutane wasu lokutan"
Yayi murmushi ya ce "Ni da shi wannan kar ta san kar ne ai"
"To ayi amfani da takardunka mana, a samo maka aikin"
Ya ce "Ni fa aikin ne ba na so, da zan yi da tun kan maigida dodo ya ware, da na yi, kuma uwa uba yanzu na ajiyeki, yaushe zan iya nesa da ke?"
Ta kwantar da murya ta ce "Master nema babu in da ba ya kai mutum, ka taimaka mana"
"Ba in da zani, ina maƙale da ke, ga wurin shayi Allah ya dafa mana, wurin bulo ma zamu buɗe, indabo nake jira, shi zai sai injin bugawar"
"Ubangiji Allah ya taimaka ya dafa, idan Nura ya tafi, kai zaka din ga kai mini kayan sayarwa ta wurin shayin"
Yayi dariya ya ce "Ai idan ma cewa ki ka yi na sayar miki zan sayar madarata, balle kuma kaiwa kawai.
"Sannu mijin ta ce"
"Bakomai, normal ne" suka cigaba da hira cikin nishaɗi.
Al'amin ya tattara Nura sai da ya tafi, Jauhar kuma haki ya addaba mata, wasu lokutan tana makaranta, za a kira Al'amin ace masa an kai ta Asibiti babu lafiya.
Sati ba ya zuwa ya shafe, asma ba ta tayar mata ba, kusan kullum suna hanyar asibiti, har ta fara tsoron kar ya fara gajiya. Sai dai sam ba ta ganin alamar gajiyawa, ko ƙosawa a tattare da shi.
Ga jiri ga haki, abinci ma gagararta ci yake yi, ga ciwon mara da ya sakata a gaba, period ɗin ya ƙi zuwa sai kaɗan ta gani a phant.
S uka sake komawa Asibiti, aka tabattar da ƙarancin jini a tare da ita.
Likitan ya ce "Zahra, kina cin abinci ki ƙoshi kuwa?"
Ta ce "Sosai ma, master yana ƙoƙari a wannan ɓangaren"
Ya ce "To ai ba kowane irin abinci ne ya dace da ke ba, kin manta rashin lafiyar da ki ka yi, da irin abincin da muka ce ki din ga ci".
Juahar ta ce "Wallahi Alhamdilillah, dai-dai gwargwado yana bani, duk abun da nake so, ko ba na so ma yana sayo mini"
Al'amin ya ce "Ka ga likita, da dai idan na sayo tana ci, amma yan, kwanakin nan, zaɓe-zaɓen abinci take yi, ba komai take ci ba".
Likita ya ce "Ayi gwajin ciki gaskiya"
Jauhar ta ce "Ai ka ce ayi mini allurar tsarin iyali, an yi mini kuma "
Ya ce "Guda nawa?"
"Ɗaya aka yi mini, an ce in dawo ta biyun, amma na ji an ce idan baka period ba ta sake ka ba, to period ɗin ma so yake ya zo, amma yaƙi zuwa sai wahalar da ni yake"
Ya ce "A nan asibitin aka gaya miki?"
Ta ce "A'a"
Yayi rubutu ya ce su je ayi scanning.
Suka je suka yi, suka dawo, ya karɓa ya duba, ya ce "Ikon Allah, to akwai ciki, kuma jinin da yake zuba alamu ne na akwai tangarɗa da yiwuwar ya zube idan ba a ɗauki mataki ba"
Al'amin ya rasa me zai yi, murna ko kuwa.
"To amma likita kana ganin babu matsala, tun da kun ce kar ta ɗauki ciki, a nan kusa bai fi watanni biyar ba yanzu"
"Eh, zamu bar ta a ƙarƙashin kulawar mu, in Allah ya yarda babu matsala, yanzu haka ya fara alamun zai fita, tun da ta fara zubar da jini, dan haka muna buƙatar ta samu bedrest, na sati guda daga ci sai bacci, ban da aikin wahala".
Cikin damuwa ta ce "Ko a hankali ba zan yi ba"
"A'a ba zaki yi ba"
"Amma master ka san ba wanda zai zo ya zauna da ni yayi mini fa"
Al'amin ya ce "Ni zaman me nake yi?"
Doctor Khalid ya ce "Allah dai ya bar wannan ƙauna, sannan kai master kana ji na"
"A'a fa, wannan sunan ba kowa yake faɗa ba, kira ni da Al'amin ɗina"
Yayi murmushi ya ce "Bedrest ɗin da muka ba ta har da kai a ciki"
Ya ce "Kamar yaya kenan?".
Doctor ya ce "Ba zuwa turaka"
"Meye turaka?"
Cikin jin kunya jauhar ta ce "Idan mun je gida zan gaya maka"
"A'a ai ba sai kun je gida ba, bayani zan yi masa yana sane ai, babu kai ba ita zuwa mu ga abun da Allah zai yi, ba cikakken hutu ake so ta samu"
Al'amin yayi shiru yana kaɗa ƙafa.
"Ina magana ka yi banza, idan ka na son babyn ya rayu lafiya kenan, ba tare da an samu matsala ba, idan kuma ka ƙi ba ruwana"
"Ai ni sai abun da Allah ya yi ne ban gane ba, nan da yaushe ka ke nufi ne?"
"Zuwa cikin yayi ƙwari mana"
"To" ya amsa a taƙaice.
Doctor ya ce "Ba ka yadda ba kenan?"
"Na yadda mana, sallame mu na mayar da ita gida, rana tana yi"
Doctor Khalid yayi counseling ɗin su sosai, sannan suka tafi gida, Allah ya taimaketa a cikin hutu suke a makaranta.
Sai dai ba a rufa sati da zuwan su Asibiti ba, laulayi ya saka jauhar a gaba, komai ta ci sai ta yi amansa, duk ta rame, har abun ya fara damun Al'amin, yake ganin kamar ɗaukar cikin da tayi da wuri ne, ya sanya take shan wahala har haka.
Babu tsammani Abbu ya zo gidansu da daddare, sun yi mamaki sosai da sosai.
Bayan sun karɓe shi ya ce "Al'amin ina can ina jiranka, ka kai mini business plan, in ga abun da yakamata na taimaka maka, ashe ka zagaye ka je wurin kakarka ka karɓi kuɗi har ka buɗe wurin sayar da shayi".
"Eh, na san ko na rubuta, matarka ba zata bari ka bani ba"
Jauhar ta ce "Abbu dan Allah ka yi haƙuri, bai kamata a ƙi gaya maka ba, dan Allah ka yi haƙuri mun yi kuskure"
Al'amin ya ce "A'a ni ne ban gaya maka ba, ta ce a gaya maka na ce a'a, saboda ba na son matar nan ta din ga saka mini baki, a abun da ya shafe ni"
Abbu ya girgiza kai ya ce "Jauhar ba ki yi laifin komai ba, ni yabo da godiya na zo takanas na yi miki, rayuwar Al'amin ta canza sosai da sosai, fiye da yadda nake tsammani, da na san aure zai katange shi daga wasu laifuffukan da tuni na yi masa an wuce wurin. Allah ya saka miki da alkhairi. Duk da daga baya na samu labarin yadda aka yi, aka zo ga gaɓar aurenki da shi, amma ki ka yi haƙuri ki ka zauna da shi a yadda yake, ki ka din ga gwagwarmaya, a gaskiya ina ƙara yaba miki, Allah ya yi miki albarka ya sa ki gama da duniya lafiya"
Jauhar ta ce "Babu komai Abbu, da na yi watsi da shi nima, kamar yadda sauran al'umma suka yi, da ba a samu Wannan nasarar ba"
"Haka ne, kai kuma" yayi maganar yana kallon Al'amin.
"Ka ji tsoron Allah, a zaman da ka ke yi da yarinyar nan, kana ganin duk wata masifa da kake ɗaukkowa babu mai tsayuwa a kanka, sai ita sai abokan shashancin ka, kai kanka ka san yanzu rayuwarka ta canza ba kamar da ba. Duk rintsi duk wuya, ka rayu da yarinyar nan da mutuntawa da girmamawa, idan ka sake ka cutar da ita, ko wani abu mara daɗi ya faru da ita a dalilinka, to ni da kai sai dai kowa ya kama gabansa".
"A'a Abbu ba za ayi haka ba, yana iya ƙoƙarin sa, babu wani abu da yake yi mini ma na rashin kyautawa, ni yanzu roƙo ɗaya nake da shi Abbu, dan Allah ka janye maganar a dalilinsa a ka kashe ɗan uwansa, kuma ka saka baki a kan yayi haƙuri da batun ɗaukar fansar da zai yi a kan madakin nan, tun da ya fita sabgarsa ya zauna lafiya kwana biyu, hankalinmu a kwance"
Aikuwa Al'amin ya haɗe rai, Abbu ya ce "Ka ji abun da matarka ta ce, ka yi mata wannan alfarmar da ta nema, kuma nima na nema"
"Tom" kawai ya faɗa a taƙaice.
Abbu ya din ga saka musu albarka ya tashi ya fita.
"Ban yi miki alƙawarin kawo ƙarshen gaba ta da madaki ba, har sai ranar da na tabattar na daina jin ɗanɗanon baƙin cikin, abun da ya yi mini"
Cikin kwantar da murya ta ce "To ka bi ta hanyar da ta dace ta shari'a, ba ta makami da illata junanku ba dan Allah"
"Ta in da aka hau, ta nan ake sauka" ya bata amsa.
Ta fuskanci muddin tana son ganin ɓacin ransa, to tayi masa maganar madaki.
Washegari hafsa ta kirta a waya, ta ce "Kwana biyu bana ganinki a online, ko ba data ne matar master?"
Jauhar ta yi dariya ta ce "Wallahi akwai data, kawai bana jin daɗi ne, wayar ma ba iya taɓa ta nake yi ba, ya jikinki kuwa?"
Ta ce 'Hmmm jiki gani nan dai, ko dai ciki ne kin ce ba kya jin daɗi?"
Tayi murmushi ta ce "Ba wani ciki, jikin ne dai kawai".
"Bari zan wuce ta unguwar taku, sai na tsaya mu gaisa, me zan taho miki da shi?"
"Babu komai, ke dai Allah ya kawo ki lafiya".
Bai fi awa biyu ba, sai ga hafsa, sai dai yanayin da jauhar ta ganta bai yi mata daɗi ba.
"Yaya, wannan shigar fa kamar ba matar aure ba?
Hafsa ta ce "Taɓ, matar aure ai na ajiye aure a gefe, mafita nake nemawa kaina"
"Ban gane ba"
"Wanda yakamata na yi wa ya gani, bai damu da ni ba, ya haɗa kan matarsa da yaransa sun tafi dubai, sun bar ni ga kuɗi ga gida, nayi-nayi anty ta fahimce ni a raba auren nan, taƙi har tana nema tayi mini baki, zan cigaba da ba ta kuɗi, nima kuma