Showing 432001 words to 435000 words out of 479911 words
shirya mini shi, Allah ka yaye masa wannan shaye-shayen, Allah kar saka ya dawo gareka yana aikata ɓarna, Allah ka bashi halal, ka bashi juriya da jarrabawar rayuwa. Allah ina son mijina a haka, Allah ka sanya yana da rabon shiriya" a cikin bacci take ganin kamar tayi salla, take ta jerin wannan addu'oin a fili.
A hankali ya dawo daga tunanin da yake yi, ya kalli hoton ya ce "Wannan ce juriyar da ki ke roƙa mini, juriyar rashin ki 'yar madara" ya ajjye hoton ya canza kwanciyarsa, yana jin yadda zuciyarsa take yi masa zafi.
Bacci ne ya kwashe shi, sai dai yau a maimakon Jauhar, da Nabila yayi mafarki, cikin yanayi na ma'aurata, ko da ya farka ya makara sallar asuba, tsaki ya yi ya tashi, tare da furta jarababbiya, ko meya kawo ta baccina"
Ta ƙarfin tsiya yake son sanya wa kansa jin haushin Nabila, amma abu ya gagara, wata irin kewarta ce ma take damunsa, gaba ɗaya tunanin mafarkin da yayi, yaƙi barin kansa.
Wato nutsuwa da kwanciyar hankali ba abin da ba ya sanyawa, a lokacin da yake cikin ha'ulai'in tashin hankali, ko kusa baya wani tunani, balle ya kwanta ya yi wani mafarki, ba ma haka ba, baccin ma ba iya yin sa yake yi ba, balle yayi wani mafarki.
Yanzu kuwa hankalinsa a kwance yake a cikin nutsuwa, ya shirya ya auri Nabila da zarar komai ya daidaita, saboda ya san yana buƙatar hakan, amma lokaci ɗaya ta hau dokin naƙi, wai ba ta son sa.
Ɓangaren Nabila ma, yanzu zaman gidan major bai fiye yi mata daɗi ba, duk sun ƙara tsangwamar ta, yanzu ta fi zama a barrack, ta fi jin daɗin zaman wurin madam, sai dai kuma da an kwana biyu sai ta ji gida take son komawa.
Tana zaune ta idar da sallar asuba, ta yi azkar, ta kifa kanta tana ƙarasa azkar ɗin, bacci ya kwasheta, dan kuwa yanzu bacci rabi da rabi take yin sa, saboda tunanin halin da Viper yake ciki, tana ta addu'a da fatan Allah ya sa kar ya koma halinsa na da.
Kawai tayi mafarkin farkon haɗuwarsu da Viper, a lokacin da yake Vipern sa, tamkar mahaukaci, ya soka mata wuƙa a ciki. Ihu ta kurma ta tashi tsaye tana dafe cikinta.
Baba magajiya ce ta shigo ɗakin a razane, Abba yana daga saman benensa ya jiyo ihunta, sun saba da irin wannan ihun na Nabila wasu lokutan, amma kwana biyu tayi lafiya.
A sukwane ya saukko shi ma, ya shiga ɗakin nata, ya tarar baba magajiya ta riƙeta, sai kuka take tana riƙe cikinta, tana dubawa ko zata ga jini.
"Menene kuma?"
"Viper ne ya caka mini wuƙa, a kai ni Asibiti"
"Wane Viper kuma, kalli dai a ina ki ke?" A hankali take ƙarewa ɗakin kallo, ta kalli jikinta ta ga lafiya ƙalau.
"A garin shegen kwashe-kwashen ki, kin kwaso abin da zai hanaki bacci, bayan kwaso masu farautar rayuwarki, kin yi azkar ma kuwa?" Ta jinjina masa kai, ta nuna masa wayarta da sautin karatun Alqur'ani yake tashi ƙasa-ƙasa.
"Nemi wuri ki kwanta ki huta" ta ƙarasa kan gadon, tana ajiyar zuciya.
A ranta ta ce "Vi fushi ka ke da ni har haka?" ta lumshe idanunta, ƙirjinta na ci gaba da bugawa cike da matsanancin tsoro.
Wajen ƙarfe sha ɗaya na rana ta gama shirinta, ta fice zuwa wurin aiki.
Tana zuwa ta tarar da Walid tare da Liti suna jiranta.
Cikin mamaki ko gaisawa ba su yi ba, ta ce "Allah ya sa lafiya na ganku, ba wani abin ne ya same shi ba ko?"
Walid ya ce "Kwantar da hankalinki, babu abin da ya same shi, yana nan ƙalau"
Ta ce "To Alhamdilillah" ta jagorance su zuwa cikin ofishinta, bayan sun gaisa Walid ya ce "Na san zaki yi mamakin zuwanmu, duk da ba abin mamaki bane ba, amma dole ki ganmu.
Nabila dan Allah me Viper yayi haka ki ke wahalar mana da ɗan uwa, kin san komai zai iya faruwa ƙin auren nan nasa da ki ka yi, idan ba ke ɗin ba wacece zai je ya aura su zauna lafiya?"
"Ni ɗin ma babu lallai mu zauna lafiya" ta bashi amsa.
"Amma meyasa ki ka ce haka?"
Nabila ta ce "Halin Viper ai sai dai Jauhar ɗin, kuma ma duk ba wannan ba, gani nake cik amana ne kamar ban kyauta ba, ace na auri mijin Jauhar, dan Allah ku yi haƙuri, ku bashi haƙuri, na san a fusace yake da ni, tun da nayi mafarkinsa yana caka mini wuƙa"
Walid ya ce "A'uzibillah lallai kam ya tabatta Mai zamani yana fushi da ke, amma dan Allah ki yi tunani, ki taimaki rayuwar ɗan uwanmu"
"Oga Walid ina jin kunyarka, dan Allah mu bar wannan maganar"
Walid ya ce "To shikenan, amma dai dan Allah ki yi tunani a kai"
Nabila ta yi murmushi ta ce "To Oga walid in sha Allah za ayi"
Ɓangaren Viper kuwa, abu kamar wasa, ya damu da rashin Nabila sosai da sosai, wasu lokutan sai ya shiga what's app ɗin sa, yana sauraren Voice message ɗin ta. Gashi ba yau ba gobe cikin mafarkinta yake, abin har ya fara bashi tsoro, domin kuwa abin ya fara yawa.
Tabbas yana buƙatar sake yin wani auren, dama Nabilan ce ya saka rai, kuma gashi ta ce ita ba zata aure shi ba.
****
Kwanci tashi asarar mai rai, Abdul ya cika wa'adin da aka ɗebar masa, na zaman gidan yari, tun safe mahaifiyarsa ta haɗa motoci ta tafi ɗaukar sa.
Ɓangaren ramma ma ji take yi kamar salla, saboda a lissafinta yau ne fitowar Abdul, sai dai Nabila ba ta ce masa komai ba. A ɓangaren sa ma Abdul ɗin, murna yake yi na fitowarsa, ko ba komai ya fuskanci ƙalubale na gaba, na samun damar ci gaba da rayuwa da matarsa, kuma gashi ya fito dag da lokacin cikar EDD ɗin ta.
Ramma ta kasa zaune ta kasa tsaye, mama ta fara bacci, ta ɗauki wayarta, ta tafi ɗakinta ta rufe ƙofa, ta kira lambar Abdul. Cikin sa'a kawai ta ji muryarsa.
"Doctor"
"Babyna da wayar wa ki ka kirani?"
"Shi ne ka fito ko ka neme ni, ina ta zullumi da lissafin yaushe zaka dawo?"
"To ta ina zan neme ki, ba waya a hannunki yanzu, ni kuma tun da na dawo Mummy ta kafa ta tsare, ba zata bari na fita ba, amma kina raina wallahi, EDD ɗinmu ya kusa cika ko?"
Ta ce "Eh, duk na gaji wallahi, cikin yayi mini nauyi, na ƙagu na haihu na huta"
"Dan Allah kar ki saka damuwar sai kin haihu abin ya dame ki kin ji sweetheart?"
"To doctor, ka huta lafiya"
"Ina batun hutu, na so da na dawo a gidana zan zauna, in ci abincin da ki ka dafa, mu kasance tare cike da so da ƙaunar juna, na yi missing ɗinki da yawa fa, yanzu dai ga abinci ga komai, amma duk ba wannan nake buƙata ba, ke nake buƙata a kusa da ni"
"Kaga sai anjima, ba zaka yi wannan zancen da ni ba"
"Au haka ma zaki ce, shikenan anyway in sha Allah a satin nan duk yadda ake ciki, zan zo na ganki"
Suka yi sallama cike da kewar juna.
Abdul ya saka ranar da zai zo ganin rahama, sai dai ta rasa yadda za ta sanar wa mama, gani take kamar ba zata yadda ba.
Dan haka ta kira Nabila ta gaya mata, Abdul yana so ya zo ya ganta, ko zata gaya wa mama, ita tana jin tsoron ta gaya mata, Nabila ta ce ba damuwa.
Ta kira mama a waya, suka gaisa Nabila ta ce "Mama, mijin rahama zai zo ya ganta, zai ga kayan sayayyar da na yi mata, da kuma yanayin jikinta, ina fatan ban yi laifi ba, na bashi adress na ce ya zo nan gida"
Mama ta ce "Mhmm ba ki yi laifi ba, ba wani abu"
"Yauwwa mama na gode sosai, a ci gaba da haƙuri dai dan Allah"
Ta ce "Ba komai"
Ramma da ciki ya sanya, wataran idan tayi wanka, ko mai ba ta shafawa, amma mama na kallonta, har da su fesa turare, da saka kwalli da shafa man leɓe mai kala, ita dai ba ta tanka mata ba ta rabu da ita.
Yaro ne ya shigo, ya ce "Wai Abdul ya zo yana waje"
Ramma ta ce masa "To ana zuwa" ta saci kallon mama, taga tayi banza da ita, ƙarshe ma ta tashi ta bar falon.
Hakan ya bata damar tashi tana jan ƙafa da kyar, ta fita harabar gidan.
Yana tsaye cikin yadi ash, kansa babu hula, ya goya hannunsa a bayansa yana kallon gidan, yana jinjina wa Alhaji mu'azzam, ya taimaki su ramma, mussaman da ya tuna gidansu na ƙauye da ko ƙofa babu.
"Me ka ke kallo ne?" Ya juyo ya kalleta.
Duk ta kumbura ta cika, ga uban ciki tana ja da kyar, hangowa yayi kamata yayi ace tana makaranta, ko idan cikin ne, ace a gidanta na aure take, gaba ɗaya sai jikinsa yayi sanyi.
Ya kalleta ya ce "Sannu uwar biyu"
Ta harare shi ta ce "Wane irin biyu kuma? Ɗayan ma ya aka ƙare, sannu da zuwa. Lallai prison ta karɓe ka, ka ƙara haske sosai ka yi kyau"
"Hmm ina daɗi a prsion, ke dai ayi sha'ani kawai"
Ramma ta yi masa jagora, suka ƙarasa cikin sitting room ɗin da yake harabar gidan.
Ta shiga cikin gida, ta ɗaukko masa abincinta, da ruwa da lemo ta kawo masa ta ajiye.
Tana ta ƙoƙarin yadda za ta juya ta zauna, kawai ya zaunar da ita a cinyarsa.
Riƙe cikinta tayi ta ce "Wayyo Allana, kai ba ka ga halin da nake ciki ba, da na bige ciki fa?"
"Haba dai, na san abin da nake yi ai, na fiki son cikin nan fa" ya ɗaga rigar jikinta, cikin nan yayi girma sosai da sosai.
Cikin matsanancin shauƙi da ɗokin son ganin abin da zata haifa, ya ce "Sannu your excellency, Allah ya raba ki da cikin nan lafiya, na gode Allah da na fito kafin haihuwar ki, ni zan karɓi haihuwar nan, na rigaki ganin babyn"
"Taɓ, a'a gaskiya, ba zaka karɓa ba, ni wallahi tsoro ma nake ji"
Abdul ya ce "Ba wani tsoro, ki kwantar da hankalinki, ai na san ke mai yawan ibada ce, mu yi ta addu'a Allah ya sauƙaƙa miki. Yaushe zamu je sayayyar kayan baby ne?"
"Ka manta mun sayo ni da Anty Nabila, Alhaji mu'azzam ma ya sayo wasu ya kawo"
Abdul ya ce "To Allah ya saka da alkhairi, Anty Jidda sun haɗa kai da Mummy, suna ta yi mini faɗa, saboda ke wai ba ni da zuciya, ni kuwa in dai a kanki ne, ba zan yi zuciya ba duk tsanani, ni dai a bar mini ke, mu yi rayuwar aurenmu cikin kwanciyar hankali".
Ramma ta yi shiru ba ta ce komai ba, ya numfasa ya ce "Zuba mana abincin mu ci tare, ina fatan dai ke ki ka dafa?"
Ta jinjina masa kai, tare suka ci abincin, sai dai sai da ya so ya wuce gona da iri, ramma ta ankarar da shi a in da yake.
Ya ce "Rakani mu je na gaida mama"
Sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta shiga gaba ya biyota a baya, aka yi sa'a maman tana falo a zaune.
Abdul ya shiga da sallama, ya durƙusa har ƙasa yana gaisheta, ta kawar da kanta gefe sannan ta amsa masa.
Daga haka ya miƙe ya ce "Na tafi to, sai anjima"
Mama ta ce "To ka gaida gida"
Da suka fito Ramma tayi zaton zai nuna ya ji babu daɗi, yadda ta amsa masa, amma bai nuna mata ba, sayayyar da ya yi mata ya bata, yayi mata sallama ya tafi.
Ramma ta kasa gane kan mama, haushinta take ji ko kuma yaya, gaba ɗaya ta ɗauke mata. Abdul yana son kiran waya yayi magana da ramma, amma ta ce kar ya kira wayar mama ce, shi kansa shakkar ramman yake ji.
Kotu ta bayar da umarnin a kamo Naja'atu Bunkure, tun da taƙi gurfana ta kare kanta bisa ga tuhume-tuhumen da ake yi mata.
Viper ya dira a garin Kano, da misalin ƙarfe huɗu na yamma, a can gidansu da suke zaune yaje ya sauka, ya tarar daga Walid har liti duk ba sa nan, yayi wanka ya huta, sannan ya shirya ya tafi cikin gari.
Ya tarar Abbu baya nan, kawai Rahila ta fito ta ce "Sannu munafi mara mutunci" ya tsaya yana kallonta.
"Eh, na ce sannu munafuki, saboda algungumi ne kai, baka tsoron Allah, shi ne ka haɗa kai da babanka, zaka aura wa Shahida ɗan iska kamar ka, to baka isa ba, Shahida gidan tsohon mijinta zata koma"
Viper kamar ya tanka mata, amma sai ya rabu da ita ya fita.
Yana nan a ƙofar gidan daf da magariba, sai ga Abbu ya dawo, tare da Walid, Walid ne yake jan motar, Abbu yana gaba suna hira.
Walid ya din ga yi wa Viper horn,ya taso ya nufo su, Abbu ya ce "Ya aka yi ka dawo kuma? Ni na yi ɗa dama baka dawo yanzu ba"
Viper ya yi murmushi ya ce "Ai ba daɗewa zan yi ba, yanzu ma idan aka ce na koma tsaf zan tafi"
Abbu suka fito daga motar, Walid ya ba wa Abbu mukullin ya ce "To Abbu sai Allah ya kaimu gobe"
Abbu ya ce "A'a, kira wo mini Abdallah a waya, ya ƙaraso shi ma ku ci abinci tukuna"
Suka yi alwala, suka je suka yi sallar magariba suka dawo, suka yi shimfiɗa a ƙofar gida suka zauna, har ƙarfe tara na dare suna tare, wajen tara da rabi, Viper ya ce su tafi zai taho.
Abbu ya din ga bawa labari jin daɗin zamansa da Walid, saboda biyayyarsa da riƙon amana, kuma ya ga sun fuskanci juna da shi da Shahida, dan haka baya son a wani ɓata lokaci, saboda Rahila na ƙoƙarin ɓata lamarin.
Haka suka cigaba da tattauanawa, a kan yadda shirin bikin zai tafi.
Liti kuwa Alhaji ya ce sai ya koma makaranta ko per time ne, sannan kuma zai kai shi kasuwa.
Liti ya ce "Amma dai da daddare idan na dawo, an je rumfar shayi"
"Wai rumfar shayin nan, ba cewa aka yi kayan shaye-shaye kuke sayarwa a ciki ba?"
"Wallahi mun daina sayarwa, harkar shayi da indomie da sauransu ake yi a wurin, kuma wannan rumfa tana da tarihi domin tunawa da marigayiyya Jauhar matar Viper, ba zan bari rumfar nan ta mutu ba. Kuma a yanzu haka wallahi yaranmu sun kai biyar da suke cin abinci a wurin, ni kula nake yi da ita, akwai amana ai, duk in da na je da daddare sai na je rumfar nan"
Alhaji ya ce "To, Allah ya tallafa"
Ya amsa da Amin.
***
Kwana na biyu kenan ramma ramam tana ta zubar da ruwa, ta rasa yadda za ta yi, gashi mama yanzu ba wani sakar mata fuska take yi ba, dan haka ba ta gaya mata ba, ba ta zata hakan wata matsala ba ce, dan haka ta ja bakinta tayi shiru.
Sai da Nabila ta bushi iska, ta je gidan, take gaya mata, Ba ƙaramin ƙuluwa Nabila tayi da abin da mama take yi ba, ta karɓi lambar Abdul, ba tare da ta saurari mama ba, ta kira shi ta sanar masa, a sukwane ya ce gashi nan.
"Ina zaka je kana zauna kana cin abinci kuma?"
"Mummy asibitina zani, aikin gaggawa ne ya taso"
"Yaushe ka dawo har ka koma aikin da zaka ce mini wani aikin gaggawa? Da da kake tsare waye yake aikin?"
"Ki yi haƙuri na je na ji menene" ya ajiye cokalin ya yi gaba. Ya kira lambar Nabila ya ce ta ɗaukko ramma su haɗu a asibitinsa kawai.
Nabila ta fito falo ta ce "Mama zan tafi da ramma asibitin royal, can asibitin mijinta, ba ta da lafiya ya ce lallai a kaita shi ma ya tafi, kwana biyu tana zubar da ruwa"
Sai kuma ta tashi a kiɗime, ta ce "Ramma naƙuda ki ka fara baki gaya mini ba?"
Ramma tayi shiru, ta ce "Ai akwai tofinta, da kayan haihuwa da na haɗa, ko da su za a tafi, ko haihuwar ce?"
Nabila ta ce "A'a bari muje kawai, tun da ba ciwo take ji ba, idan haihuwar ce sai muyi waya ki taho"
"A'a ba haka za ayi ba, mu tafi kawai bari na ɗaukko mayafina" tana shiga ɗaki, sai ma ta rasa wa zata kira, kawai ta kira Viper tana gaya masa.
Ya ce "Ai yau da daddare nake son zuwa da ni da Abbu ku gaisa, amma gani nan zan biyoku asibitin"
Ko da suka je asibitin, a harabar wurin suka tarar da Abdul, yana ta kaiwa da komowa, suna isowa, ya nufe su, Nabila ta kamo hannun ramma, ta fito daga cikin motar, tana takawa da kyar, duk da ta saka pad, amma ruwan da take zubarwa duk ya ɓata mata jiki.
Wheel chair ya ɗaukko da gudu, ya ajiye suka ɗora ramma a kai, ya tura ta cikin asibitin.
Tuni ya kira doctor Muktar, wanda abokinsa ne, kuma shi ya yi wa ramma awo.
Bayan fitar Abdul, doctor Muktar ya yi wa ramma scanic, ya kalleta ya ce "Yaushe rabon da cikin yayi motsi?"
Ta ɗan shiru ta ce "Tun jiya da safe"
Abdul ya dawo ya ce "Muktar, yaya ake ciki ne?"
Ya gyaɗa kai ya ce "Low amniotic fluid, a shirya OR kawai, ayi mata EMCS"
Ya ce "Ya subhanallah, amma ya babyn" ya faɗa a rikice.
Muktar ya ce "Meye haka? Wato saboda wannan taka ce shi ne zaka wani ruɗe? Dan Allah ka nutsu mana, normal in sha Allah, ka shirya ka yi assiting ɗina, sai a ciro babyn, ka kira anesthetic ɗin"
"Abdul meya same ni?" Tayi maganar kamar zata yi kuka.
Ya ƙarasa ya riƙe hannunta, ya ce "Ki kwantar da hankalinki, tun yaushe ki ke zubar da ruwan nan?"
"Ni na manta, ka gaya mini Meya same ni?"
"Ruwan da babynmu yake ciki ne yayi masa kaɗan, saboda rashin sanarwa da wuri da ba ki yi ba, duk ruwan ya zube, yanzu tiyata zamu yi miki a ciro shi"
Ramma ta fashe da kuka ta ce "Yanka ni za ayi kenan, wayyo Allah tsoro nake ji"
Ya ce "Ki yi haƙuri, babu wani abu in sha Allah"
Ya kalli muktar ya ce "Doctor Muktar, ko zaka yi wa mamanta bayani, suna falon office ɗina" ya jinjina kai ya fita.
Doctor Muktar yana zuwa, ya tarar da Nabila da mama, ya ce "Matar master, sannu fa"
"Matar master ai ta rasu"
Ya ce "Ai ni duk abu daga nake gani, amma ya aka yi ta gama awo