Showing 135001 words to 138000 words out of 479911 words
watan azumi ya kama ranar da za su bi Indabo campaign, tun dare ya haɗa yaransa da wurin da za su haɗu su tafi.
Da sassafe bayan Jauhar ta tashe shi yayi sahur, ta idar da sallar asuba ta kwanta bacci, ya silale ya fice.
Wunin ranar ba ta ganshi ba, ba ta damu ba sai da ta ga an kusa shan ruwa, ta din ga kiran wayarsa, amma ba ta shiga, sai hankalinta ya fara tashi, dan ta san duk in da ya je da an kusa shan ruwa yake tahowa gida.
Al'amin kuwa bayan sun dawo daga campaign, an yi sare-sare sun yi shaye-shaye, an yi wa indabo aikinsa yadda yakamata, Al'amin ya sallammi yaransa, shi kuma Indabo ya ce ya bishi gida, da shi da wasu 'yan jami'iyya su sha ruwa a gidansa, ya sanya an shirya abun shan ruwa.
Al'amin ya ce sai dai su tafi tare da walid.
Ƙaton falo ne na musamman, mai ɗauke da haɗaɗɗem dining, kayan abinci aka kawo, na ƙasaita aka din ga jerewa a kan dining ɗin nan, cikin fulasai na alfarma.
Walid ya ce "Mu na cin albarkacinka mai zamani, wannan sabga haka?"
Al'amin ya bari, aka gama jere abinci, ana ta rawar jiki a fara ci ayi buɗe baki, ya tashi, ya bubbuɗe fulasan.
Wani irin farfesu aka yi na kajin gidan gona, ƙosassu, ga flask ɗin dankali dana ƙwai abincin ma har da na almubazzaranci.
Al'amin ya ja flask ɗin kaji, ya janyo na dankali, ya haɗe kan kayan shayi madarar gwangwani da milo, ya kalli Walid ya ce "Dafe mini wannan mu ɓace".
Indabo ya ce "Ina zaka tafi kuma, za a ci abinci?"
"Gida" ya bashi amsa.
"To kuma na ga kana harhaɗe kan kwanukan abincin, ya zaka yi da su ga mutane za su ci?"
Kai tsaye ya ce " 'yar madara zan kaiwa"
"A'a ya mage zata yi da wannan uban abinci haka?"
Walid ya ce "Ba mage ba ce, madam za a kaiwa"
Indabo ya ce "Haba mai zamani, sai ka ce a ɗibar mata, amma yaya za ayi mutane na zaune abincin mutum sha biyu duk ka kwashe rabi?".
"Ba zai yiwu da ni da na saka rayuwata a hatsari, da wanda ku ka tsaya a cikin rumfa hankali kwance, ka yi mana sallama iri ɗaya ba, ai kana da kuɗi a dafa musu wani. Ka san son zuciya ba halina bane, a baya ban yi ba ba zan fara yanzu ba. Ba zan ci wannan abincin ita ba ta ci ba, kuma ai ga wasu nau'in abincin nan ku ci. Walid ɗaukko kwandon kayan marmarin nan ma"
Indabo ya ce "To fulasan fa? Ka tsaya sai a juye maka a leda, na madam ne wannan"
"Madam ba ta fi madam ba, sadaki bai fi sadaki ba. Ina fatan ka fahimci lissafin? kuma kuna da kuɗin sayen wasu, ko ba yanzu ba idan kun ci zaɓe zaku samu, dan haka har fulasan mun cinye" Indabo yana ji yana gani, Al'amin ya yarfa shi a gaban jama'a, suka kwashe abinci suka tafi.
Jauhar ban da ruwa babu abun da ta sha, har bayan sallar isha'i sai yawo take yi a cikin unguwar tana nemansa, hankalinta a tashe. Ta gaji ta dawo gida da nufin ta kira Walid.
Kawai ta dawo ta tarar da shi.
"Master ina ka tafi, hankalina ya tashi tun safe rabonka da gida, ba ka gaya mini ina zaka je ba, gaba ɗaya tun da aka sha ruwa na kasa cin komai, ban san ina ka ke ba".
"To kukan zaki yi?"
"Baka gaya mini ina zaka je ba, hankalina gaba ɗaya ya ƙi kwanciya haba master dan Allah"
"Ohh murya kamar tsuntsuwa, yenyenyen, ki din ga buɗe baki ki yi magana sosai" kawai tayi shiru cike da takaici, idonta kawai ya kalla, ya san hankalinta a tashe yake.
Ƙeyata ya tura, zuwa ɗakinsa kawai ta tarar da jeren kwanuka, haɗaɗɗun fulasai, da uban kayan marmari.
Tayi saroro tana kallon kayan.
"Zo ki zuba mana mu ci, ba kayan wani bane, mun je campaign ne muka dawo aka shirya shan ruwa, na ce a gida zan ci na taho da shi".
A ɗan tsorace ta ce "Master duk wannan kuma?"
"Eh kwaso kwanuka"
Iya kajin sai da suka tsorata ta, dan sun kusa goma, fulasai ne na alfarmar gaske.
Ta ce "Ai ba zamu iya cinyewa ba".
"Gasu nan dai, ki yi abun da ya dace".
Duk son Jauhar da nama, sai da ya isheta, ta bawa maƙwabta, ta zuba wani ya kira guduma a waya, ya ce masa ya zo ya karɓa.
Hatta magenta, sai da ya ƙoshi da ciye-ciye.
Haka kurum ya din ga jin annashuwa a ransa, ganin ta ci ta ƙoshi, har abun ya gundureta.
Bayan jera masa godiya da ta gama yi, kamar yadda ta saba, tare da addu'oi, ta ce "Master Alfarma zan nema a wurinka dan Allah"
"Ina jinki"
Ta saka hannu ta karɓi wayarsa ta ce "Dan Allah kar ka ce mini a'a, ko ba zaka yi ba".
"To kar ki tambayi abun da ba zan iya ba".
"Zaka iya mai babban suna, kaga naman nan yayi mana yawa, duk da an babbayar dan Allah sonake na ƙara gyara shi, ayi miya gobe in Allah ya kaimu, mu je yi wa su baba sannu da shan ruwa"
A take ya tsuke fuska, ya ƙi magana.
"Dan Allah Master, na neman albarka mu je mu gaishe su"
"Wai ke wace iri ce ne? Tun da muka yi aure, bayan su hajiya, kin ga wani ya zo gidan nan daga ɓangarena? Ko Abbun kin ga ya zo? Dama maraba suke nema da ni, har gara mahaifinki ma ya zo"
Jauhar ta ce "Kar ka ce haka, dama ba su yakamata su zo ba, mu yakamata mu je, ai su iyaye ba a fushi da su, kai fa ka yi wa wani faɗa a kan haka, bai kamata kai ace ka aikata haka ba, dan Allah ka yarda mu je" An kai ruwa rana sosai tsakaninta da shi, kafin ya amince.
Washegari suka shirya, bayan azahar suka fara zuwa gidan su Al'amin.
Suka fara zuwa gidan su Al'amin, suka yi sa'a Abbu yana nan, sai dai rahila tayi mamakin ganin Al'amin, yayi wani shar da shi, sai ƙamshin turare yake yi kayansa sun sha guga.
Ashe Abbu zuwansa gidan su biyu, ba ya samun kowa, a gidan, gashi Al'amin ya wanke ƙafarsa ya daina zuwa gidan.
Abbu baki ya kasa rufuwa, mamaki yake ganin Al'amin, a nutse da shi ya sako 'yar matarsa a gaba gwanin sha'awa, sai dai sai cika yake yi yana batsewa yana wani basarwa.
Dan tun da suka gaisa da Abbu, bai sake cewa komai ba, jauhar ce take bashi amsa idan yayi magana.
Rahila ma sai zuba take ta ce "Ikon Allah, anya ba a canzo wani Aminun ba, kun yi kyau abunku kun ƙara ƙiba, an ce kin yi rashin lafiya kwanaki, To na san dai ba zai wuce laulayi ba, Allah ya raba lafiya"
Al'amin ya ce "Amin, tashi mu tafi rana tana yi" kawai ta girgiza kai jin Al'amin ya amsa, idan ma haka ne ai kamata yayi, yayi shiru kawai.
Rahila ta sake cewa "To sai ayi ta kula da ita, ka san masu ciki sai ana lallaɓa su, ban da hantara da abun da zai ɓata mata rai, kuma ba zama zaka yi ba, ciki tun yana ƙarami ake fara sayayyar kayan jariri".
Jauhar ta ajiye food flask, da leda ta ce "Mama ga wannan, kwa yi buɗa baki, a saka mu a addu'a"
Abbu ya ce "Masha Allah, addu'a kullum cikin yin ta ake, Allah ya yi albarka"
Rahila ta ce "Iyee har da su suga da kayan marmari?" Ta buɗe fulas ta ce "Abbu kaza ce fa a ciki, ikon Allah sana'a ka samu ne haka? Ko kuma haryanzu miyagun ƙwayoyi ka ke sayarwa, gara mutum ya san halaccin abun da zai ci".
Al'amin ya kalli jauhar, irin kallon kin ga abun da nake gudu ko?.
Ya ce "Ubana na zo gani, kuma banda 'yar madara ta matsa, da sai dai na je ƙofar masallaci, idan ya fito na ganshi kamar yadda na saba, dan haka ba sai kin san sahihanci da halaccin cin sa ba, tun da bani da alaƙa da ke" ya tashi ya danƙi hannun jauhar a gaban su.
Abbu ya ce "Aminullahi tsaya mana"ya tsaya cak yana huci, jauhar sai ƙoƙarin zame hannunta take yi daga nasa, saboda kunya.
Abbu ya ce "Allah ya saka da alkhairi, ya yi albarka. 'ya ta Allah ya saka miki da alkhairi, yayi muku albarka gaba ɗaya"
Ta ce "Amin Abbu, a sha ruwa lafiya "
A zatonta, zai ta yi mata masifa, sai dai ta ji bai ce mata komai ba, ya wuce da ita unguwar su, ya kaita har ƙofar gida.
"Ki yi sauri ki fito mu tafi, mu koma gida"
Ta ce "To*
Ta sauka daga babur ɗin ta shiga gidan, suka gaggaisa, sai dai baba baya nan, ta ce "Dama ɗan abun sannu da shan ruwa na kawo masa, sauri nake yi na bar shi a waje, kar ya gaji da jirana"
Anty Zakiyya ta ce "Lallai jauhar, shi mijin naki ya fi ƙarfin ya shigo ya gaida mu kenan?"
"A'a ba haka bane Anty, kin san ba ya jituwa da 'yan unguwar nan, bana son wani abu ya faru ne"
Mama ta ce "Haryanzu bai shiryun ba kenan? Sai labari muka ji wai ya fito ai, Jauhar wannan naman kajin, shi ya saya ko ke?"
Ta ce "Shi ne"
Suryaya ta ce "To a dai yi a hankali, Allah ya sa ba na sata bane ba".
Jauhar ta ce "Allah ya tsare shi, Al'amin ba ya sata".
Anty Zakiyya ta ce "Wato Jauhar ba zaki yi mana Allah ya sanya alkhairi ba ko, ko kishi ki ke yi?"
Cikin rashin fahimta jauhar ta ce "Anty na me?"
"Alhaji mu'azzam ya dawo, tun da kin yi aure yanzu hafsa zai aura, ya bayar da miliyan biyu tayi lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin aure!"
Ayshercool
08081012143.
34
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA
Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??
Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??
Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??
Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.
Muna da kaya available masu kyau da rahusa💃🏾💃🏾
Ko kimin mgn ta👇🏽👇🏽
08093932955
Abunka da zuciya, dumm haka ƙirjin Jauhar ya buga, da ƙarfin gaske, take wani abu da ba ta san menene ba ya taso mata.
A ranta ta ce "Saboda haka dama ku ka aura mini Al'amin, dan rusa aurena da Alhaji mu'zzam?"
'kul jauhar, Al'amin zaɓin Allah ne a gare ki, babu wanda yake da ikon canzawa wani ƙaddararsa, dama haka Allah ya tsara miki'
Cikin sauri ta ce "Ahh haba, amma ba a gaya mini ba, ga shi muna waya, ina yi muku magana ta what's app, Anty ke ma ina da lambarki, amma ba a gaya mini, ko dan kar in haɗa lefen na zo na ɗauki kayan kwalliya ne ya sa ba a gaya mini ba?"
Anty Zakiyya ta ce "A'a kar a gaya miki ki ji wani abu a ranki ne, dama Allah bai ƙaddara mijinki bane"
Jauhar ta ce "Haka ne, mijin wata baya auren matar wani, idan an gama haɗawa ni dai zan zo a bani kayan kwalliya".
Surayya ta ce "Au, ashe fa ba ayi miki lefe ba ke ko?"
Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a kin manta an yi mini sayayyar kaya?"
"Duk da haka wannan ai ba lefe bane ba"
Wayar jauhar ta fara ringing, ta cirota daga jakarta ta ce "Master"
"Fito mu tafi"
"To gani nan"
"Bari na tashi yana jirana, idan an saka lokaci sai a gaya mini"
Hafsa ta ce "An saka bayan salla da sati uku ne"
"To Allah ya sa zamu gani, a gaishe mini da baba, sai kuma Allah ya kaimu salla, Anty walida ku kuma na gaji da roƙonku ku zo gidana, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa yi mini kara ya zo".
Hafsa ta ce "Ke fa babu wanda zaki gani a gidanki, muna yayyenki zamu din ga zuwa gidanki, ko so ki ke mu zo mijinki yayi mana illa?"
"Haba dai, ba fa mahaukaci ba ne, da zai yi muku illa, da ban kawo yanzu tare da shi ba, sai anjimanku"
Zuba mata ido yayi, har ta ƙaraso, sai dai ya lura da jikinta a sanyaye yake, bai ce mata uffan ba, ya kunna babur ɗin, ya karkata mata ta riƙe shi ta hau suka tafi.
Sai yanzu ta ƙara gane dalilin yin amfani da yi mata sharri, wurin aura mata Al'amin, ba wai tana baƙin ciki da auren hafsa bane ba, ta san haka Allah ya ƙaddara kawai mamakin tsananin ƙin da suke yi mata take yi, ta san ko da kuɗi ba za su yadda su aurawa 'ya'yan su mutum irin Al'amin ba, saboda kar ta huta shiyasa suka yi mata wannan muguntar.
Kallon bayan Al'amin take yi, a ranta ta ce "Kai Allah ya zaɓa mini, kuma in sha Allah sai na yi kyakywar rayuwar aure da kai master'.
Da haka suka ƙaraso gida, sai dai yana ankare da yadda walwalarta ta gushe, take komai jiki a sanyaye babu kuzari.
Ɗan muzurunta na ta kewayata, yana yi mata ɗan kuka, amma ta kasa kula shi, wanda da tana cikin walwala da tuni ta ɗauke shi tana yi masa rawa, da ma shi ba shiri yake yi da muzurun ba, dan dana sanin kawo mata shi ma yake yi, saboda yadda take tsananin ba wa muzurun kulawa, kamar ya jefar da shi haka yake ji wasu lokutan.
Ya zuba mata ido, tana ta yi wa wani mayafi ado da beads, na kayan sallar mutane da take ta yi, sai dai a saɓule take aikin.
Muzurun ma ya gaji, ya koma gefe ya kwanta, saboda ta kasa kula shi.
Har aka sha ruwa, ko surutun yau ba ta iya yi, abincin ma cakalarsa kawai take yi, ta kasa ci ta ajiye ta tashi tayar da sallar taraweeh.
Ta cigaba da aikin beads.
"Ssss, Ji mana" ta ɗaga kai ta kalleshi.
"Zo mana"ta ce "To" ta yinƙura ta tashi, ta ƙaraso gaban sa, tana ƙoƙarin zama a ƙasa, ya nuna mata kusa da shi, ta zauna tare da sunkuyar da kanta.
"Kin ga muna zamanzamanmu, ki ka kwashe mu, muka je wurin mutanen nan, gashi kin je an yi miki wani abun kin kasa sukuni, shiyasa tun farko na ce kar mu je, ki ka dage, kin dawo kin kasa nutsuwa, me aka yi miki?"
Ta girgiza masa kai ta ce "Bakomai"
Ya ce "Bana tambaya sau biyu"
"Ka yi haƙuri dan Allah, babu komai, zuwa da safe zan wartsake in sha Allah".
"Ba ki da juriya, kin fiye rauni, da wuri ake ganin gazawar ki, ki ƙara ƙoƙarin zama jaruma, ko dai ayi miki ki shanye ko shirya ramuwar gayya sama da abun da aka yi miki. Ki ajiye wannan abun da ki ke yi, ki tafi ki je ki kwanta"
Ta jinjina masa kai ta ce "To master, na gode sosai" ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ta kwanta.
Sai dai bacci ya gagari idonta, ta din ga tunanin, meke damunta kishi ne ko hassada. Sai dai ta tabattar wa da kanta ba kishi bane ba, saboda ta riga ta zama matar wani, ko ba komai a yadda yake ɗin nan, ta fara appreciating yanayin zaman na su yanz saɓanin da, dan haka tana matar wani ba zata yi kishi a kan wani ba.
Hakazalika ba hassada ba ce ba, ba ta ji ta damu dan hafsa zata shiga cikin daular da, da ita ce zata shiga, ta san wannan nufin Allah ne, kawai tana jinjina yadda suka shiga suka fita, suka aura mata Al'amin dan kawai kar ta auri Alhaji mu'azzam.
Wannan gillin ɗabi'a ce ga zuciya, da duk yadda ɗan adam ya kai ga dannewa sai yayi tasiri, ta din ga istigfari da roƙon Allah ya sanyaya mata ranta, ta manta ta fuskanci Rayuwarta.
Yanayin yadda Al'amin ya fara nuna damuwarsa a kanta, ya ke sanya wa ta ji tabbaci da ƙwarin gwiwar cewa wataran za ta ji daɗinsa, tun da dai babu duka ko zagi a tsakanin su, shaye-shayen sa da nema rigimarsa ne babbar matsalarta, gashi yanzu cefane ma yana yi ko ba kullum ba.
A cikin kwanakin da ta dage da addu'a, sai ta fara jin sassauci ta fara mantawa, ta cigaba da mayar da hankali a kan sana'arta, da yi musu Addu'a babu dare babu rana.
Al'amin ya fara rage yin shaye-shaye a gabanta, sai ta yi bacci, sai ya fita tsakar gida, ko ƙofar gida yayi, duk da wasu lokutan idan ta shiga ta tarar da shi yana yi, mazewa yake yi ya haɗe rai ya cigaba da shan abun sa, amma sosai yake rage abun da zai yi, wanda zai sanya ta shiga damuwa.
Ya mayar da ita asibiti, likita ya tabattar da jininta ya sauka, kuma ya dakatar da ita daga shan magani, na wani ɗan lokaci.
Saura sati guda salla, gidan jauhar mutane ne kawai ke shiga suna fita, masu mayafai, masu ɗinkuna da zata yi wa stone work, masu kitso da lalle, a haka kuma tana kasa kayanta, na shirin dutse, sarƙa abun hannu, jigida, ga kayan lemo, masu zuwa kitso suna yi mata ciniki. Ta zama very busy, idan yamma ta gabato, ga aikin abinci, sai dai garin Allah yana wayewa, ya fice ya bar gidan, saboda mutane.
Sai dai ana shan ruwa take sallamar kowa, ta ce sai gobe, za ta kula da mijinta.
Yana falo a zaune, ya gama shan ruwa ya kasa tashi, wata mata tayi sallama, tayi ta yi wa jauhar magiya, wai tana son ta turo yaran, ta wanke musu kai, tayi musu kitso, kowace yarinya ɗari da hamsin, su huɗu.
Jauhar ta ce "Haba Maman Nana, ki bani ɗari bibbiyu mana, ga wanke musu kai, ga kitso?"
"Taimakawa zaki yi jauhar, idan ki na son gobe mu kawo miki coustomers, kin san yadda garin yake, ubansu bai bani ko sisi ba, ni nake wahalata dan yaran su fito fes, ko hankici bai yi mana ba"
Jauhar ta ce "To shikenan, bari na sallami master, gobe in Allah ya kaimu akwai mutane sosai, turo su yanzu a wanke musu kan, in dafa ruwa a heater tun da da wuta, gobe in Allah ya kaimu da sassafe sai ayi kitson"
"Ke, na hana kitson, kwashi yaranki ki tafi wani wurin ayi miki" ta ji muryarsa a ƙofar falo.
Jauhar ta ce "Master