Showing 390001 words to 393000 words out of 479911 words
yafe masa kamar yadda ya nema, yayi nadama na je na ganshi ai, saboda na taimaka muku, matata ƙanwar ubansa yanzu ta bar mini gida, wai na tozarta ɗan uwanta, kuma rahama mai aikinta ce, ba irin bautar da ba ta yi mata ba, kuma ban tsaya muku dan ina son ɗaukar fansa a kan ubansa ba, na tsaya muku ne a matsayina na uba, wanda na haifa nima, ba zan so ayi mini haka ba, amma ki yi haƙuri, ba kuma dole zan yi miki ba ba a yafiya dole, amma ba ki san me Allah zai yi miki ba albarkacin yafiyar ba. Abin alfahari ne a sanadin rahama Allah ya shiryi Abdul" ya daɗe ya na yi mata nasiha mai ratsa zuciya.
Ta amince da a kai ƙarar shari'a Court, dan Abdul ya samu sassauci.
Amma hakan bai yi wa babar Abdul daɗi ba, a gaban Alƙali aka karantawa Abdul laifinsa, a chamber alƙali a ka yi shari'ar, domin privacy ɗin rahama da identity ɗin shi kansa Abdul ɗin.
Ana karanta masa laifin, Abdul ya amsa, Alƙali ya ce a kai masa shi prison, bayan sati uku a dawo ya ci gaba da saurarar ƙarar.
Waro ido Rahama ta yi, ta san Abdul ba zai iya zaman prison ba, babu yadda lauyoyin Abdul ba su yi ba, a kan a bayar da belin Abdul, amma Alƙalin nan ya murtuke ya ce babu wannan.
Babarsa ta ce "Shi ya janyo wa kansa, dama haɗa baki aka yi, aka zo shari'a court, dan a kulle shi a tozarta shi"
Aka taso ƙeyar Abdul, Rahma ta kasa damuwarta da ruɗewa, ya kalli maman ramma ya risunar da kansa.
Ta bakin lauyoyin sa, suka yi wa su Viper godiya, bisa alfarmar da aka yi musu, aka gabatar da shari'ar kotun addinin Muslunci.
***
Nabila na office ɗin ta a zaune, Sumayya ta turo ƙofar ta ce "Suprise"
Nabila ta ce "Ko ma ki yi mini sallama malama"
Sumayya ta ce "Ba zan yi ba"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ki ci kanki"
Sumayya ta ce "Nabila ana ƙoƙarin hana gudanar da recall election, an kuma sake ɗagawa ba ki ji raina ba"
Nabila ta kwaɓe baki ta ce "Mhmm, ai na san a rina, sai dai idan ba a ƙasar nan muke ba, na ji ana maganar EFCC za su sake shi, amma haryanzu babu wani tartibin bayani a kan laifukan da ake tuhumarsa da shi"
Sumayya ta ce "Za kuwa mu yi raising alarm a social media, lallai ayi mana bayanin meyake gudana ina kuɗin al'umma suke?"
Nabila ta kwashe da dariya ta ce "Ɗansa ya wawushe fiye da rabi, ya yi wa matarsa hidima, Ai Allah ba azzalumin sarki bane, kuma wani ikon Allah yaƙi faɗar ɗansa ne ya wawushi kuɗin"
"Ya za ayi ya faɗa, dama fa ware su aka yi dan yayi campaign, shi kuwa yayi campaign a in da ya dace. Wai ina mutuniyar ki Naja'atu Bunkure ne?"
"Oho mata na daina jin ɗuriyarta, ina nan ina tattara ƙorafe-ƙorafe a kanta, zan kai ma'aikatar Shari'a, she's not suppose to practice law at all, her licensed must be seazed in sha Allah"
Sumayya ta duba wayarta ta ce "Ke ni fa tare nake da baƙo, bari na yi masa magana ya shigo".
Babu tsammani Sumayya ta shigo tare da wani mutum, da ko ba a gaya wa Nabila ba, kamaninsa ya bayyanar mata da waye.
Babu in da Viper ya bar kamanin mahaifinsa, shi ma haka yake dogo mai jiki, akwai alamar hutu a tare da shi, daga yanayin suturar jikinsa.
Babu shiri Nabila ta miƙe, ta ce "Abbu sannu da zuwa, Sumayya ai da ni ki ka yi wa magana sai mu je mu same shi.
Ta gyara masa kujera, ta ce "Bisimillah" sai dai ya daskare a wuri guda ya na kallon Nabila.
"Jauhar ya na ganki a nan kuma?"
Sumayya ta ce "Ba jauhar ba ce ai, wannan Nabila ce"
"Ya za ki ce mini ba jauhar ba ce ba?"
Nabila ta ɗan yi murmushi, ta ce "Abbu ni sunana Barrister Nabila Yusuf maitama, ita kuma sunanta Fatima Bashir Azare. Ka zauna dan Allah" ya zauna a hankali ya na bin Nabila da kallo.
Ta kawo masa ruwa, ta nemi wuri ta zauna ta ce "Abbu ya gida ya iyali?"
"Alhamdilillah, amma idan ba jauhar ba ce ba, ya aka yi ki ke kirana da sunan da iyalina suke kirana da shi?"
"Saboda na san tarihin rayuwar Viper, an sanar da ni komai"
Ya jinjina kai ya ce "Kin yi abin da ya tabattar mini da be ke ce Jauhar ba"
Nabila ta ce "Me na yi?"
Ya ce "Jauhar ba za ta taɓa kiransa da sunan da ki ka kira shi ba na Viper"
Nabila ta ce "Afuwan Allah ya sa ba laifi na yi ba?"
Abbu ya ce "Ko kaɗan, ba ki yi laifi ba, amma ina cike da mamakin yadda ya zamana ba ke ce jauhar ba, duk da a zahiri ban ga bambancin naku ba"
Nan Nabila ta labarta masa kaɗan daga abin da yakamata ya sani, game da alaƙarta da jauhar. Ta numfasa ta ce "Abbu, duk da mu yaranku ne, kun fi mu tunani da hangen nesa, amma iyayenmu maza kuna tafka kuskure.
Da mahaifiyar Viper ta na raye, ko a gabanta ya kashe jauhar, da ya dawo ba za ta kore shi ba.
Har mahaifin jauhar ya ce bai yarda zai kashe masa 'ya ba, amma Abbu kai ka kasa karɓar Viper. A lokacin da ƙaddara ta kai ni cikin rayuwar Viper, ya fid da ran samun sassauci a rayuwa. Ga ƙwaƙwalwars ta taɓu ga shaye-shaye fiye da da da ya din ga yi.
Allah ne kawai ya bani sa'a a kansa, daga shi sai abokansa da su ka riƙe shi, su ka karɓe shi su ka sadaukar da ta su rayuwar, saboda su rayu da shi.
Na yi iya ƙoƙarina a kansa ya dawo in da kake, amma yaƙi sosai yake fushi a kan abubuwan da su ka faru"
Abbu ya yi shiru, cike da jimami da kaico a kan wasu abubuwa da ya aikatawa rayuwar ɗan sa.
Ya numfasa ya ce "Haka ne, haƙiƙa ni mai laifi ne a rayuwar Al'amin, duk da ni na haife shi, na cancanci na nemi gafararsa, dan sai daga bayan nan na fuskanci a lokacin da ya lalace, watsi da na yi da shi, ba shi ne masalaha ba.
Amma dan Allah babu yadda za ayi ku taimaka ku haɗa ni da shi. Zan yi duk mai yiwuwa na ga na gyara kuskuren da na aikata a baya. Sannan duk wani support da ake buƙata in sha Allah zan bayar".
Nabila ta numfasa ta ce "Ina haɗaku zai sauke mini kwandon masifa, duk wani ƙoƙari da nake yi a kan shari'ar ku, zai iya mayar mana da hannun agogo baya. Ranar da na haɗaku a waya ma, sai da muka yi faɗa da shi sosai.
Sannan duk da ka na mahaifinsa, idan na haɗaku na saɓa yarjejeniyar privacy ɗin sa, da aka ja mini kunne a kai. Abu ɗaya zan iya ce maka, shi ne ka din ga halartar kotu wurin gudanar da shari'ar sa, kuma a sakamu a addu'a, sannan in sha Allah zan cigaba da ƙoƙarin shawo maka kansa"
Abbu ya yi shiru sannan ya ce "Na yi kuskuren biye wa zigar mace, da hawa dokin zuciya na wofantar da ɗa na, na riƙe na wani, ƙarshe na zama mara kima a idanunsu. Ki ba wa Al'amin haƙuri, ki gaya masa abbu ya na kewarsa".
"In sha Allah zan sanar masa, kuma komai zai dai-dai ta, na yi maka alƙawarin bibiyarsa da ci gaba da tausar sa, kamar yadda ya jagoranci haɗa ni da mahaifina"
Ya jinjina kai ya ce "Na gode muku sosai da sosai, Ubangiji Allah ya biya ku da gidan aljanna, 'yar jarida ke ma na gode sosai"
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na gode sosai Abbu"
Nabila ta tashi ta ce "Abbu ba ka sha ruwan ba, na saka order ma a kawo maka abinci"
Yayi murmushi ya ce "A'a Alhamdilillah, bari na sha ruwan dai, kasuwa zan tafi"
Nabila ta ce "Allah ya tsare hanya, in sha Allah za mu zo har gida mu gaishe ka"
Ya ce "Da kuwa na yi farinciki da haka. Ai daga ke har Sumayyan, na zata zan ga manya, na ganku duk 'yan yara matasa, Ubangiji Allah ya dafa muku yayi muku jagora baki ɗaya, Allah ya raya mana ku, ya tsare ku daga Sharrin mai sharri"
Su ka raka shi har gaban motarsa, sai sanya musu albarka yake yi, ya buɗe motar, ya ɗaukko kuɗi ya ce "Ga wannan kwa sha ruwa, na gode sosai"
Nabila ta ce "Haba Abbu, ai Addu'ar da ka yi mana ma ta isa, mun gode sosai da mu da Viper a cigaba da sanya mu a addu'a"
"Addu'a kullum cikin yin ta ake yi, amma sai kun karɓa, sai dai idan kyautar Abbun ce ba kwa so" da kyar su ka karɓa, ya yi ta yi musu godiya ya tafi.
Bayan sun koma ofishin Nabila, Sumayya ta ce "Ohh su Abla sai ɓare-ɓare ake yi, an ga siriki"
Nabila kawai ta girgiza kai, ta din ga jinjina maƙudan kuɗin da ya basu kyauta, mutumin da zai iya bayar da wannan kyautar kuɗin, lallai mutum ne mai rufin asiri.
***
Laraba ta bawa ranar samu in ji hausawa, ta kasance ranar da za a ci gaba da sauraren shari'ar Viper.
Kotu ta cika iya cika, da masu ƙara waɗanda ake ƙara, lauyoyi 'yan jaridu ƙungiyoyi kotun cike fal.
Bayan an kira ƙarar su Nabila, aka fito da lakwari da aka aike da shi magarƙama a wancan zaman da kotu ta yi.
Babban abin da ya bawa Nabila mamaki, bai wuce ganin barrister Naja'atu Bunkure a cikin kotun ba, duk da ta ji gabanta ya faɗi, amma ta dake ta adana mamakinta a zuciyarta.
Ta fito ta gabatar da kanta, aka fito da lakwari, Nabila ta nemi Walid ya fito.
Walid ya fito ya tsaya, ta dubi Walid ta ce "Ko zaka iya bayyana wa kotu sunanka?"
"Sunana Muhsin Hassan, wanda ake kira da Walid".
Ta nuna masa lakwari, ta ce "Ka san wannan?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh na san shi"
"Ka san laifin da ake tuhumarsa da shi?"
"Eh na sani, laifin ki san kai ne na matar Al'amin da ɗan cikinta"
"Ka tabattar?"
"Eh na tabattar"
"Za ka iya shaidawa kotu abin da ya faru?"
Walid ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ranar da za a kasheta, ni na aro babur ɗin adaidaita sahu, kamar yadda Al'amin ya buƙata, da ni da shi da abokinmu liti, mu ka je asibiti. Likita ya dubata ya ce ta wuce lokacin haihuwar ta, dan haka za ayi inducing ɗin ta, amma idan bai yi ba tiyata za ayi mata.
Ta ce tana son cin ƙosai, muka yi ta yawo bamu samu ba, na yi alƙawarin zan nemo ƙosai da sassafe na kai mata, daga nan mu ka ajiye su a gida, mu kuma muka wuce.
Da sassafen da na je, na tarar da layin a cike da jami'an tsaro, wai an yi kisan kai"
"Ka ga gawar jauhar da ciki?"
"Eh, a kan idonmu aka fito da ita an rufeta a cikin ledar gawa, ta na zubar da jini".
"Waye ya kira jami'an tsaro ya sanar da su abin da ya faru?"
Walid ya ce "Ban sani ba gaskiya"
Nabila ta yi godiya, Bunkure ta taso ta gabatar da kanta a matsayin lauyar lakwari, sannan ta yi suka ga shaidar Walid, cewa shaida ce mai rauni, tun da bai tabattar da ganin lokacin da lakwari ya kashe jauhar ba.
"Ya mai girma mai shari'a, ina son kotu ta bani dama, zan yi wa Al'amin wasu tambayoyi"
Viper ya fito ya tsaya, ya na tuna abin da ta yi masa a wancan lokacin.
"Malam Al'amin, a haka ba ka yi kama da malamai ba, balle ace wa'azi ka yi wa su lakwari ba su ka ji haushi, suka kashe maka mata ba.
Me zai haɗa mutum kamar ka da mutane irin su lakwari har su shiga gidanka, su kashe maka mata? Ko ka na ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ne kai ma?" Tayi maganar tana tsare shi da idanunta.
Ayshercool
08081012143
93
Har Nabila ta zaburo za ta yi magana, Baba ya ce "Amma kamar ƙoƙarin tabattar da mutuwar jauhar ake yi, wannan tambayar abin da ya shafe mu ne personal issue ne"
Nabila ta yi carf ta cafe, da sukar abin da Bunkure ta aikata.
Da haka dai aka saurari wasu daga cikin shaidun na ranar, aka sake ɗaga shari'ar.
Viper ya din ga jin jikinsa wani iri, sai da ya fito ya tsaya su na gaisawa da Baban su jauhar.
Bayan Nabila ta fito daga cikin kotun, ta samu wuri tana amsa waya, babu tsammanni Nabila ta ji an janyota baya, an riƙe damtsenta.
Ta waiwaya ta ga Naja'atu Bunkure, ta yi wa Nabila wani munafukin murmushi ta ce "Sannu da ƙoƙari barrister Nabila, lallai na yadda da kirarin da ƙawarki take yi miki, na a lady of her words, the voice of voiceless. Kin yi alwashin kai ni ƙasa, ki na ta faɗi tashin ganin kin ga bayana. To kafin ki ga nawa bayan ni zan ga naki, sai na tabattar miki da wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi.
Zan kunna miki wutar da sai ta ƙonaki har lahira, abu mai daɗi da ya sauƙaƙa mini komai shi ne, samun labarin ke yar uwar matar Viper ce, ki na kare mijin yar uwakki, da kuma neman hakkin jininta da ya riga ya tafi a banza a wofi, zan illataki da wutar zahiri da ta baɗini ta zuci, sai na tona asirin miyagun ayyukan Viper sun koma kansa, na kassara Rayuwarki yadda zai zame muku baƙin ciki goma da ashirin, kamar yadda ku ka tarwatsa nutsuwarmu da ni da uban gidana Indabo"
Nabila ta saka hannu, ta buge hannun Bunkure daga damtsenta, sannan ta hankaɗata iya ƙarfinta ta nunata da yatsanta ta ce "Jinin 'yar uwata ya fi ƙarfin ya tafi a banza, ƙarya ki ke yi, kuma wutar da ki ke shirin kunnawa, reshe ne zai juye da mujiya, dan kuwa ke zai koma ya ƙona, daga ni har Al'amin ƙarafa ne a cikin wuta da babu abin da wutar da ki ka kunna ta isa ta yi mana. Jinin yar uwata bai tafi a banza ba, duk wanda ya saka hannu wurin zubar da jininta, sai jinin jauhar ya zame masa mummunar gubar da sai ta kai shi lahira".
Nabila ta daki ƙirjinta ta ce "Gani gaki Naja, ki tsammaci abin da zatonki da hangenki bai taɓa tsammani ba" tayi maganar ta na nuna Naja'atu.
Sumayya ce ta hango abin da yake faruwa, Viper ya na can ya na magana da Baba cikin girmamawa, ya na tsugunne Baba ya riƙe hannunsa, ya na ta yi masa nasiha da bashi ƙwarin gwiwa, Alhaji mu'azzam har mamaki abin ya bashi, dama haka Viper ya iya ladabi.
Karaf idanun Viper su ka sauka a kan na Abbu, da bai san ma Abbun ya zo kotun ba, gabansa ya yi mummunar faɗuwa, Baba ne ya kalli in da Viper yake kallo, shi kansa bai lura da mahaifin Vipern ba sai yanzu.
Cikin hanzari ya nufe shi, shi ma ya nufo shi cikin sauri, Viper kuwa kawar da kansa ya yi daga kallon Abbu, zuciyarsa na ci gaba da harbawa da sauri.
Suka gaisa Abbu ya ce "Malam Bashir kwana da yawa, kawai sai samun labari mu ka yi kun tashi, babu ko sallama"
Baba ya ce "Wallahi kuwa, ai na yi laifi ayi mini afuwa, ashe ka zo zaman shari'ar Al'amin, kuma kawai sai ka ga Nabila ita ce lauyarsa"
Abbu ya ce "Abin ya bani mamaki sosai ya ɗaure mini kai, duk wannan abun ashe Jauhar ta na da 'yar uwa, ban taɓa sani ba, ta hanyar yar jaridar nan ƙawarta sumayya muke magana, ta kaini wurinta, wallahi na razana sosai, Allah na zata marigayiyya ce"
Baba yayi murmushi ya ce "Allah kenan, mai jujjuya lamarinsa yadda ya so"
Viper ya bar wurin da zai ci gaba da ganin Abbu, saboda yadda zuciyarsa ke neman tsinkewa, sai azalzalarsa zuciyarsa take yi ya ƙarasa wurin da Abbu yake.
Can ya hango Sumayya ta danƙo hannun Nabila, sai surutai take yi, fuskarta ta koma ja, da alama ranta ne ya ɓaci.
Nufar su yayi da sauri, ya na tambayar su ko lafiya.
Sumayya ta ce "Faɗa su ka yi da Naja'atu Bunkure"
Cikin mamaki ya ce "Faɗa kuma?"
"Eh"
Ya ce "Meya haɗa su?"
"Wallahi ban sani ba, ƙarar da aka yi bayan taku na tsaya saurara, na yi picking wani abu a cikin rahotannin da zan yi yau, kawai da na fito na gansu su na cacar baki"
A nutse ya kalli Nabila da take ta huci ya ce "Meya haɗa ki da ita?" Shiru Nabila ta yi ta kasa magana.
"Ina tambayar ki menene?" Still ta kuma yin shiru, sai sauke ajiyar zuciya take yi.
Ya ce "To wuce mu tafi"
Ya sakota a gaba su ka fito harabar kotun, a wannan karon har da Alhaji mu'zzam kankarofi suke tare da su Abba, Abban ya gabatar wa da Alhaji mu'zzam Abbu mahaifin Viper.
Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kan su Viper, da su ka taho fuskar Nabila sam babu annuri.
Rige-rigen tambaya su ka fara yi, ko lafiya Nabila take cika ta na batsewa.
"Ya aka yi ne, meyafaru?" Baba ya tambayeta cikin kulawa.
Kawai ta durƙusa ta fashe da kuka.
Viper ya ce "Wai ke wace irin yarinya ce, wannan ai halin yarinta ne, barrister ce fa ke, a harabar kotu ki zauna ki na kuka saboda wauta da abin kunya?"
Alhaji mu'azzam ma ya ce "Nabila menene, kar ki ɗaga mana hankali mana"
Abbu ma cewa ya yi "Idan yanayin yadda shari'ar ya gudana ne bai yi miki ba, ki yi haƙuri mu je a ci gaba da addu'a da neman ɗaukin Ubangiji"
Abbu na fara magana, Viper ya yi ɗif, ya juya ya bar wurin.
Abin da Viper ya yi ya ƙara wa Nabila takaici, cikin mamaki Baba ya ce "Ya haka kuma?"
Abbu ya girgiza kai ya ce "Rabu da shi kawai, komai yayi mini na cancanci hakan"
Still wani mamakin ya sake cika Alhaji mu'azzam, ya na mamakin wane irin mutum ne Viper haka, baban na sa ma.
A dai-dai lokacin liti da Walid su ka ƙara so gaban Abbu, su na zuwa suma durƙusawa su yi a gaban Abbun, cikin matuƙar girmamawa su na gaishe shi tare da Baba.
Abbu ya dafa kafaɗunsu ya na amsawa.
"Ya ƙoƙari ya fama da Al'amin"
Walid ya yi murmushi ya ce "Babu fama Abbu"
"Ina ta godiya Ubangiji