Showing 165001 words to 168000 words out of 479911 words
da wayar Al'amin, aikuwa ya ɗaga.
Wata muguwar ashar ya narka wa P.A sannan ya ce "Saboda kai ɗan haramun ne, nake kiran wayarka tun jiya, ka ƙi ɗagawa. Saboda baku da mutunci daga kai har ubangidan naka, saboda kare ƙuri'arku, da ƙoƙarin hana ƙona sakateriya, yara sun fi sha biyar suka rufar masa da sara, ban da Mu ma akwai yaranmu a wurin da sai sun kashe shi, ka san ba maganin tauri yake sha ba, bakomai ba. Ka tsaya ka saurareni ma jiyan ka ƙi, da ƙyar aka samo kuɗin yi masa aiki, to wallahi ku saurari abun da zamu yi mu ma, wallahi hukumar zaɓen zamu cinnawa wuta, uban kowa ma ya rasa. Zaka gane ba ka da wayo daga kai har shi"
"Ka ga tsaya, duk na san a cikin yaransa ne, ku yi haƙuri kun san yanayin halin da muke ciki ba a nutse muke....
"Halin da ku ke ciki ya fi rayuwarsa kenan? Ku sauraremu nan da wani lokaci" ya kashe wayar.
Ya koma ɗakin da Al'amin yake, ya tarar da ya farfaɗo, har an ɗaga shi zaune ma, jauhar ta haɗa tea tana bashi, sai dai idanunta sun gaza daina zubar da hawaye.
Al'amin ya zuba mata ido ya ce "Abbu ya zo nan?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.
"Dan ke ya zo ko bani ba? Ke ki ka yi masa magiyar ya zo?"
"A'a"
Walid ya ce "Liti mu ba su wuri, abun na baru ne"
"Master"
Ya kalleta, idanunsa sun yi ja, alamar yana jin jiki.
"Ba na ce ka daina yi wa kanka illa ba, ko dan saboda ni? Sai zuciyata ta fashe hankalinka zai kwanta ko? In sha Allah kujerar nan ko ya sameta sai ta zame masa masifa. Ban taɓa yi wa wani muguwar addu'a ba amma na yi masa. Nayi nayi ka rabu da mutumin nan, ba mutumin arziki bane ba, amma ka ƙi aishikenan gashi nan yanzu ka janyo mana wahala".
Ya lumshe idanunsa, dan ba ya son ya ga tana zubar da hawaye.
Jauhar ba irin addu'a da ba ta ja wa indabo ba, dan shi ne kanwa uwar gamin ƙara ta'azzara rashin jin Al'amin.
A washegari hukumar zaɓe, ta sanar da soke zaɓen ƙaramar hukuma uku, ciki har da ta su Al'amin wadda kuma take ta indabo, sakamakon tashe-tashen hankali da aka samu, da kuma ƙona wasu daga takardun da aka kaɗa ƙuri'a.
Tuni P.A ya sanar da Indabo saƙon su Walid, kuma kansile ƙanan hukumomin, babbar barazana ce ga nasarar indabon.
Babu shiri, washegari da daddare suka shirya suka tafi wurin malamin su, da shi da P.A, malamin ya tabbatar musu da cewa, an samu tangarɗa a aikin da aka yi ne, yarinyar da yayi amfani da ita, ta haura shekarun da ake buƙatar, kuma a yanzu ba abun da zai iya yi musu, sai dai a bi wasu sabbin dabarun, a samu a haye.
Suna tafe a hanya P.A ya ce "Honorable, wallahi yakamata ka duba mai zamani, da ƙyar idan ba yaransa ne, suka tayar da tarzoma ba, ka san dole zamu sake buƙatar su, mussaman yanzu da zaɓen ya zama inconclusive".
Indabo ya ce "Matsalar yaron nan na ta ƙarewa wallahi"
"To ya zamu yi, haƙuri zamu yi tun da muna amfanarsa". Indabo ya amince da hakan, P.A ya kira liti ya tambaye shi in da suke kwance
Al'amin so yake Jauhar ta zauna a kusa da shi, ya ji ɗuminta su yi hira, amma alamu suka tabattar masa da fushi take yi, dan da tayi masa abun da za ta yi masa sai ta koma gefe, ta ɗauki wayarta tana karanta Alqur'ani.
Ga kawo-kawo ɗin da ake yi, kuɗin hannunta duk sun ƙare, dan ma su liti suna tsaye suna tallafawa, kuma idan Abbu ya zo ya kan ba ta kuɗi, duk da zuwan nasa biyu ne kawai.
Wajen ƙarfe ɗaya na dare ne, Ranar Walid da liti duk suna nan, duk da da facemask, a fuskar Indabo sai da suka gane shi, suka tashi suka ni bayansu.
Jauhar ta ɗaga kai ta kallesu, Al'amin ya buɗe idonsa da yake a rufe a da.
Jami'an tsaron suka bashi kujera ya zauna, yana kallon Al'amin da satar kallon jauhar.
Ta tashi ta ce "Lafiya?"
P.A ya ce "Baki gane ni bane, wanda ku ka zo wurina lokacin yana prison, honorable ne wannan, ya zo da kansa ba saƙo duba shi" ta haɗe rai sosai, kamar ya make shi ta huta haka take ji.
Ya sauke facemask ya ce "Sannu kin ji, ya mai jikin?"
Shiru tayi tana cigaba da haɗe rai.
Ya kalli Al'amin ya ce "Wannan ce 'yar madarar kenan?" Al'amin ya ƙura masa ido, bai yi magana ba.
Ya kalli Walid ya ce "Ba ya iya magana ne?"
"Yana yi"
"Dama cewa na yi bari na zo na ga yanayin jikin naka, Allah ya ƙara sauƙi. Ban sani ba ko ka samu labarin an soke mana wasu ƙuri'un abun bai yi daɗi ba, muna nan dai muna ta addu'a "
Ya karkace ya ciro kuɗi kaya guda, ya miƙawa jauhar ya ce "Ga wannan a sai magani"
Ta girgiza kai cikin takaici ta ce "Ba ma so, ka riƙe kuɗinka ni babban burina da fatana, ka fita daga rayuwar mijina, nima ina burin na ga ya shiryu ya zama mutumin kirki, kai ne ka ke saka shi aikata duk wani abu na rashin kyautawa. Idan ya shiga matsala kuma ka zame ka bar shi. Yanzu an riga an cuce ni, an tsugunar da shi. 'ya'yanka su suka fi cancanta su yi maka irin aikin da yake yi maka, tun da sun fi morarka, idan abun na Allah ne ka karɓi takardunsa ka sama masa abun yi mana, amma babban burnku yaran wasu su sha su bugu su sayar da rayuwarsu a banza gare ku".
Ɗaya daga cikin jami'an tsaron ya daka mata tsawa, ta ce "Wallahi ko zaku kashe ni sai na faɗi gaskiya, nima 'ya ce, kuma na cancanci zama da nagartaccen miji, na san akwai iyaye da yawa da suke da burin ganin yaransu a hanya madaidaiciya amma duk hana hakan, ni dai dan Allah ka rabu da mijina, ka ƙyalemu"
Maimakon ya ji haushi, sai yayi murmushin ya ce "P.A wato duk isa da kwarjinin namiji ya je gaban mace, sai abun da Allah ya yi, kalli Mai zamani a gaban matarsa. Aishikenan yarinya haryanzu baki san rayuwa ba, wannan yanayin mafita kawai ake nema, ki daina yi wa manya rashin kunya. Kuma mijinki zaki gaya wa ya daina abun da yake yi ba ni ba. Tun da a haka na ganshi, ki karɓi kuɗin nan".
"Ba ma so, ba zamu karɓa ba" tayi maganar tana kuka.
Ya miƙawa P.A kuɗin, ya karɓa ya miƙawa Viper, shi kuma ya karɓa.
Indabo yayi murmushi ya fice da tawagarsa.
"Master ni ka dizga ka kunyata a gaban mutane, gara ka cigaba da karɓar kuɗinsu kana shaye-shaye ana yi maka lahani, ni ko? Kai am tired na gaji, ba zan iya ba na sare. Na ɗauka abun mai sauƙi ne, amma ya wuce yadda nake tunani, you are not willing to change. Kana samun sauƙi gida zan koma, na gaji da auren"
Liti ya ce "Subhanallah, dan Allah kar ki yi mana haka anty ƴar madara, muna murna Allah ya saya mana shi, kuma ki tafi ki barmu, ba fa shikaɗai ba har mu zamanki tare da shi muna amfana"
"Eh, kuma har da ku ai, kullum ku kuke ƙara haɗuwa da shi, ku ke ƙara abun da bai kamata ba, Allah ya sa na mutu na huta".
Duk wannan abun, yayi burus yaƙi magana.
"In sha Allah, ba zaki mutu ba, ana mugun tare ai"
"Ba wani tare, ku daina shaye-shaye mana, kuma kullum a kansa tsautsayi yake faɗawa, ni na gaji, yana warkewa tafiya zan yi na haƙura da zaman da shi" tayi maganar tana kuka, har ta fara tari mai haɗe da haki.
"Mai laya"
"Allah ya ƙara maka lafiya"
"Ayi walƙiya, sai da safe"
Walid ya ce "Iya wuya, yadda ka ke so haka za ayi" suka tashi suka fice, ya juya ya saukko daga kan gadon.
Kamar ba ciwo ne a cikin sa ba, ya tunkaro in da take ya zauna, ya ƙura mata ido tayi shiru ta sunkuyar da kai, tana haki sama-sama.
"Ki ka ce tafiya zaki yi?"
"Eh" ta bashi amsa kai tsaye.
"Yaushe?"
"Kana warkewa gida zan koma, tun da ba ka so na, kullum cikin sakani ka ke a tashin hankali, na ce maka ba na son ka din ga zuwa in da za a ji maka ciwo, amma ka ƙi, ka dizgani a gaban wannan mutumin. Wallahi ba zan taɓa yafe masa ba, duk shi yake ƙara ɓata ka".
"Yanzu abun da ki ka yi dai-dai ne? Ubangidana ne fa, ki ka tsaya kina yi masa rashin kunya".
A ƙule ta ce "Shi dai-dai ɗin yayi mini, ba dan Allah ya yi da sauran kwananka a gaba ba, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, ni na rasa in da zan saka raina, abun da nake ta tunanin zan iya ashe ya fi ƙarfina, shikenan".
Gyara zamansa yayi, ya janyota jikinsa, yana kissing ɗin ta a hankali.
She's not in mood, ta so ta ƙwace, sai dai kuma raunin jikinsa ya hanata yin hakan, kar ta fama masa.
A hankali ya cire bakinsa daga nata yana kallon ta, amma ta haɗe rai tayi kicin-kicin.
"Ki gaya wa likitocin nan su sallameni gobe, ko kuma na yi tafiyata"
Da sauri ta kalleshi ta ce "A hakan ba ka warke ba?"
"Eh na gaji da yadda ake zuwa ana magana da ke, haushi nake ji, shi kansa indabo shirun da nayi masa, shi ne mafi alkhairi da mummunan naushi zan yi masa"
"Dan Allah ni ka daina taɓa ni, asibiti ne fa, idan wani ya shigo fa?"
"To je ki rufe ƙofa ki dawo, zafi nake ji, ina buƙatar fankata, lamba uku kawai, ba sai an ƙure mata gudu ba"
"Ko mafici ba zaka samu ba, ni rabu da ni" tayi maganar tana sake ture shi.
Ya ƙi tashi ya din ga takura mata, duk dan ta sake ta ɗan samu nutsuwa daga fushin da take yi.
"P.A wane mahaukaciya ne ya aura wa yarinyar nan mai zamani?"
"Allah masani honorable"
"Ikon Allah, kalarta kalar muryarta, ai rannan na kira ta ɗaga, kai ka ga yarinya zuƙeƙiya kamar ita tayi kanta. Amma kamar ta dace da aikin da malamin nan fa ya bayar, ya aka yi ba ka yi mini zancenta ba, gashi wannan an samu matsala"
P.A ya ce "Honorable, kai ka san ba kowane kaya ne yake taɓuwa ba, idan aka taɓa wannan za a iya samun matsala, kuma na manta da ita ne gaba ɗaya wallahi"
Indabo ya ce "Wace irin matsala? Ai tsaf za ta taɓu, ba tare da ya sani ba, idan ma ya sani na san yadda zan yi da shi. Lallai 'yar madara tayi kalar madarar sosai. Wannan yarinyar ita ce rauninsa kenan?"
"Sosai kam, dan alamu sun nuna yana mugun sonta"
Indabo yayi wani irin murmushi yana shafa tumbinsa.
Maƙwabtan su Jauhar sun yi mata kara, na zuwa duba Al'amin, suka kakkai mata abinci, daga gidan su Baba ya je Saifu sai mama, sun je sun duba shi, duk da maman ta gaggaya mata baƙar magana a kansa.
Satinsa ɗaya da ƙyar, ya uzzura akan lallai, sai an sallame shi, haka aka sallame su suka koma gida.
Cikin ikon Allah, Indabo yayi nasara, bayan faɗi tashi, da shige-shige yayi nasarar samun kujerar ɗan majalisa.
Har gida Abbu ya sake zuwa duba Al'amin, sai dai kamar wurin jauhar ya zo, da ita suka ɗan yi hira, ya tashi ya tafi.
Hafsa kuwa abun duniya ya hanata sukuni, da ƙyar ta samu Alhaji mu'azzam ya fara saurararta, sai dai yadda yake bin matarsa sau da ƙafa, yake ƙona mata rai, sai abun da ta tsara yake yi a gidan, idan ba ta ga dama ba, sai ya shafe kwana goma bai taka wurin Hafsa ba, amma kuɗi akwai su, komai take buƙata akwai shi, sai dai fa tsakaninta da miji sai an ga dama a bata aro, wataran yana wurin nata ma, za ta kira shi, kuma haka zai tsallaketa ya tafi wurin matarsa, ga yaransa marasa kirki, sun rainata rashin kunya kala-kala.
Da ta matsa ma da ƙorafi, ya ce idan ta gaji ta tafi, shi fa duk lokacin da ya zo wurinta, baya gane komai, haƙuri kawai yake yi shi ma, ta ƙyale shi.
Ta gaji tayi yaji, Anty ta din ga yi mata masifa, a kan dan me zata dawo gida, sai asirinsu ya tonu, dole ta cigaba da zama har zuwa lokacin da za a samu mafita.
Al'amin ya warke sarai, ya cigbaa da harkokin sa, sai dai jauhar kusan kullum tana gargaɗinsa a kan indabo.
Gashi ta riƙe masa wuta a kan yin salla a kan lokaci, da yin azkar, har zama tayi ta ciro masa addu'oi na musamman ta rubuta masa su.
Ita kanta ta san ikon Allah ne, da ƙarfin addu'a da take yi, da kuma yadda take bin sa da kyautatawa da biyayya, ya sanya take iya sarrfaa Al'amin, har yake jin nauyin aikata wasu abubuwan saboda ita.
Da asuba idan ya je salla ya dawo, da kanta take ajiye masa sigari, kara biyu ko uku, ta ce masa ya sha banda shan ƙwaya kuma.
Ta jira ya gama sha, yana ƙaurin yana komai, ta naniƙe masa a jikinsa, dan mantar da shi damuwa, kewar kayan shaye-shayen sa.
Da daddare suna kwance, ta ce "Master, ka san abun da matar nan tela tayi mini?"
Ya ce "A'a"
"Wai na cewa matar nan dan Allah, ta koya mini ɗinki, idan ta yarda zan tambaye ka, na din ga zuwa, ta ce mini za ta yi shawara, wai daga baya ta ce mini mijinta ya ce a'a bai yadda na din ga zuwar masa gida ba, ko kara ba ta yi mini ba, duk wahalar da nake yi mata, wani abun ta biyani wani sai dai na yafe kuɗin, na ji haushi dama kuma ba ta zo tayi mini jajen abun da ya same ka ba"
"Saboda ni me mijin ya ce bai yadda ki je gidansa ba?"
"Wallahi ban sani ba, na dai ji babu daɗi gaskiya, amma ban san dalilinta ba"
Al'amin ya ce "Manta da ita, Allah ya baki wani abun da ya fishi, uwar son kuɗi"
"To wa ya ƙi kuɗi master" yayi murmushi yana shafa bayanta.
Da asuba, mutane sun fito daga masallaci, faruku tela ya ga Al'amin a ƙofar gidan sa.
Gabansa ya faɗi ya ce "Lafiya kuwa?"
Al'amin ya ce "Saƙonka na ji, 'yar madara ta ce a koya mata ɗinki ka ce a'a, fine idan na kuma ganin 'ya'yanka sun tako mini gida, sai na daddatsa su, na zuba a leda na kawo maka.
Na kuma yi suspending ɗin shagonka, na wata guda, wallahi ka buɗe sai an sassara mini kai" yayi tafiyar sa ya bar faruku a wurin, cikin tashin hankali.
Ƙarshe sai da aka haɗa da zuwa har gida, magidanta suka zo ban haƙuri, jauhar tayi mamakin abun da yayi, ita kawai hira tayi masa abun miji da mata, amma ya je yana yi wa mutumin barazana. Ta ce zata yi masa magana ba wani abu, malam faruku ya cigaba da buɗe shagonsa.
Ya dawo da daddare, ta sha kwalliya, kamar yadda ta kan caccanza tare da ƙirƙiro da sabbin abubuwa, domin sabunta abubuwa da yawa a rayuwar auren na su, saboda rage barazanar gundurar juna.
Ya nemi wuri ya zauna a falo, yana ta sauke numfashi, ta fito ta na murmushi ta haye kan cinyarsa, ta zuba masa ido ya lumshe idonsa yana ta huci kamar kumurci.
"Nawan" tayi maganar tana shafa sajensa.
"Yau kuma me aka sha haka? aka ƙi kulani" yayi shiru bai ce mata komai ba.
"Master"
"Mmm"
"Me ka sha yau?"
"Wiwi"
Jauhar ta ce "Da me?"
Ya girgiza mata kai alamar babu.
"Ba ka saba ƙarya ba" ta saka yatsanta a bakinsa, ta ciro guntuwar ƙwayar da take ƙasan harshensa, laɓɓansa sun yi fari.
"Ƙwaya ko? Meyasa. Na ce fa idan an ɓata maka rai ne, ko kana cikin damuwa ka yi ta ambaton Allah, kana azkar, meyasa za aje a sha ƙwaya, ka ɓata mini shirina na yau gaba ɗaya"
Babu tsammani, ya miƙe da ita a jikinsa, ya tafi da ita ɗakinsa, rabi a buge yake, rabi a cikin hayyacinsa, yayi ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta ce "Ba zaka sumbace ni, da sauran ƙwaya a bakinka ba master, me aka yi maka?"
"Mhmmm bakomai, i need you"
Ta ce "A hakan, a buge fa ka ke"
"Ina hayyacina, kin yi mini kyau ne sosai" kasa hana shi tayi, ya gama ya cigaba da yi mata surutai.
Ta rungume kansa a ƙirjinta tana shafawa ta ce "Na san wataran zaka daina master, Allah ya shirya mini kai mijina"
"Madarata"
Ta ce "Idonka biyu"
"Mmm"
"Me zaka gaya mini?"
"In sha Allah zan daina, ki cigaba da yi mini addu'a" yayi maganar cikin muryar maye sama-sama.
"Addu'a kullum ina yi maka master, Allah ya nuna mini ka daina"
"Madarata"
"Master na"
Ya ja jikinsa, ya kai bakinsa saitin kunnenta, ta yi shiru, tana jiran ya yi mata magana.
Kawai ya fara murmushi, yana yi mata numfashi a kunne.
"Zaki koma makaranta"
"Allah ya ja zamaninka, godiya nake"
Cikin mayen ya sake cewa "Ki daina yawan kuka ba na so"
"To ka daina sakani"
"Allah ya bani kuɗi na kai ki makka"
"Amin Mijina, da alama ƙwayar nan nishaɗi take sawa"
"Ke ce nishaɗin nawa" yayi maganar yana dariya.
Ita ma murmushin ta yi masa, ya kwanta a gefenta, bacci ya ɗauke shi.
Da Asuba ya rigata tashi, ya tasheta shi kuma yayi wanka yayi alwala ya fita.
Da wani irin tashin zuciya ta tashi, kamar za ta yi amai, ta danganta hakan da awarar da ta yi wa cin ƙoshi jiya da daddare ulcer ta tayar mata.
A ɗakinsa ta yi sallar ta idar, idonta ya sauka a kan robar cocala da ke gefen katifarsa.
A take ta ji idan ba ta sha coke ɗin nan ba, akwai matsala.
Ta ɗaukko, ta buɗe ta kafa kai ta fara sha, sai da ta shanye tas, sannan ta ajiye jarkar, still ta din ga jin kamar za ta yi amai. Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki, ta yanke jiki ta faɗi, jini ya fara gangarowa daga hancinta.
Ayshercool
08081012143
41
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Al'amin a masallaci, magidanta suka tare shi suna ƙara bashi haƙuri, a kan abun da ya ce wa faruku tela.
Ya koma gida ya shiga ɗakinsa, yanayin kwanciyar da ya ga jauhar ne ya sanya ya tsaya yana kallonta.
"Wace irin kwanciya