Showing 366001 words to 369000 words out of 479911 words
ai yana kallon hotonta wasu lokutan, wai dan Allah maman saifu, wurin wani malamin ki ka kai Bashir, da aikin nan ya ci shi, ya manta da chubaɗo gaba ɗaya daga rayuwarsa, ashe a tagayyare haka ta haife su?"
A ƙule ta ce "Ban gane wurin wani malami na kai shi ba, muka kai shi dai, ke da yarinyar nan ta rayu a gidan nan, ai da wallahi kashinmu ya bushe, yadda ya din ga rawar kan nan, ya nemi ya mayar da mu borori a kan bafulatanar daji, kawai a daina wani tone-tone"
Zakiyya ta ce "Uhumm ai shikenan, zan ga yadda dramar nan za ta ƙare, shi ya ɗauki zafi shi ma wan uwarta ya ɗauka, amma abin da ya bani mamaki na kasa ganewa shi ne, yaya aka yi mijin jauhar ya samo ta, a ina ya ganota ya kawota nan ɗin?"
"Oho sanin gaibu sai Allah"
Su ka ci gaba da hira, su na mamakin yadda al'amuran suke cike da sarƙaƙiya da ban mamaki.
***
Nabila kamar tana tura magani, haka take shan youghurt ɗin gabanta, ta na yamutsa fuska, fuskar tayi jawur, Viper ya zuba mata idanunsa ko ƙiftawa ba ya yi.
"Kin ce ke youghurt, ku ma kin ƙi sha"
Hawaye ya gangaro kan fuskarta ta ce "Ka takura mini ne, babu yadda zan yi, dan Allah ka nuna mini hoton 'yar uwata na sake ganinta, idan an tuna ba zan taɓa ganinta ba, wallahi sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi ban santa ba, amma wallahi ina son ta, meyasa tuntuni ban sanka ba ka haɗani da ita ba?"
Ya shafi fuskarsa cikin dakiya ya ce "Allah ne bai ƙaddara ba"
"Kenan kai nake mafarkin tana nuna mini a cikin sarƙa?
Yayi ƙuri da ido yana kallon ta.
"Wallahi Vi da gaske nake son ta, ashe haka ka ji, kai da ka santa ya ka ji da ka rasata, gara ma kai ni fa ban santa ba ma, tsakani da Allah iyayen nan nawa sun kyauta mini?" Tayi maganar tana rushe masa da matsanancin kuka.
Allurar gefen gadonta, ya ɗauka ya buɗe ya zuƙe ta, ya ce "Kwanta ki bani hannunki na yi miki, sun shigo za su yi miki ki na salla" ta kalleshi tana sheshsheƙar kuka.
"Kar ki damu, ɗan ƙwaya ne ni, kuma ɗan daba na saba riƙe sirinji da allura.
Ya buɗe cannulan ya fara yi mata allurar, a hankali jikinta ya fara sanyi, ya kwantar da ita.
"Tun daga lokacin da na fuskanci bijirewa ƙaddara na nufin halaka ta dindin ko samar da damejin da ba shi da hanyar gyaruwa, ya sanya na yi saranda, na bawa ƙaddarar damar ci gaba da jujjuya akalar rayuwarmu, domin na fuskanci ƙaddarorinmu na da alaƙa da juna. Tamkar na kashe kaina, haka na ji bayan rasa matata, ni har hauka na yi ai, na kuma yi ƙoƙarin sake sabauta rayuwata. Kar ki tafka irin kuskuren da na yi, nake ta fama da dana sanin da ba shi da wani amfani a gare ni, ina guje miki aikata haka. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara, ki karɓi mahaifinki kuma ki karɓi mariƙinki, ki sasanta tsakaninsu" cikin muryar jin bacci ta ce "Maza wasu ba su yi ba, Allah sarki babarmu 'yar fulanin riga, abin tausayi"
"Idan kuma abin da ya same ta ya na da alaƙa da jinsinta fa, su suka aikata komai, mu daina zargin jinsinmu da cutar da ɗaya, kawai mu mu zama adalai a kowane lokaci, da mahaifinki da major duk ba na yarwa. Zan iya rantse miki ban san mahaifinku da wani mugun hali ba, mutumin kirki ne, duk da ba ni hali na kirki, amma auren 'yar sa da na yi, ɗa ya ɗauke ni ba siriki ba"
Ta buɗe idanunta da kyar, cikin raɗa ta ce "Spy, wai nasiha ka ke yi mini? To ka fara yi wa kanka, zan iya rantse maka, Abbu mutumin kirki ne, bamu haɗu a zahiri ba, a waya muka yi magana amma dattijon arziki ne" ta yi maganar daidai lokacin da bacci yayi awon gaba da ita.
Dare ya fara yi, Viper ya fito daga sashin in da ɗakin Nabila yake, daga major har Baba duk suna nanz har a lokacin ba su tafi ba.
Viper ya ce "Ina ganin zaku iya tafiya gida, zuwa in Allah ya kaimu da safe, tun da an ce ƙwaƙwalwarta na buƙatar hutu, kar ta rikice gaba ɗaya. Amma dai yakamata ku sasanta kanku kafin Allah ya sanya ta sake farfaɗowa".
Major ya kalli Viper rai a ɓace ya ce "Ai kai ne kanwa uwar gamin komai, dan me zaka ɗauke ta, ka kai ta wurin wannan mutumin mara tsoron Allah, ita ma ya bari rayuwarta ta wulaƙanta kamar yadda ya wulakanta ta uwatta, kuma saboda rashin tsoron Allah ya aura maka yarinyar da ba ta ji ba, ba ta gani ba ka kasheta, kuma saboda zalunci ka dawo ka sanya ta tssya maka, take baka kariya, alhalin ka kashe yar uwatta, wane irin abu ne wannan?. Duk a dalilinka zumuncin da yake tsakanin yaran nan, ka watsa shi, ba ta jin maganar kowa sai ta ka, idan abin gaskiya ne, meyasa ni ba ka je ka same ni a gida, ka yi mini bayani ba kawai ka ɗauke ta ka kai wa wannan mutumin"
Maganganun Major sun yi wa Viper zafi sosai, yayi ƙuri da ido yana kallon major, amma bai yi magana ba.
Baba cikin mamaki ya kalli major ya ce "Ka ga wani iko na Ubangiji da yadda yake jujjuya al'amura yadda ya so, duk guje-gujen naka, da Allah ya ƙaddara, Nabila ce za ta tsaya wa mijin 'yar uwatta, ka yi ƙoƙarin tsayawa a kan iliminta da tarbiyyarta, amma Al'amin ba mutumin banza ba ne ba, haryanzu ban yadda zai iya kashe mini 'ya ba, kar ka ƙara danganta shi da kisan kan jauhar"
Saifu ya ce "Baba ka daina wannan maganar fa, ba ka da tabbas ya aikata ko be aikata ba"
Liti ya ce "Ji wani ɗan wahala kuma, to ai sai ka jira kotu ta tabattar da shi ya aikata, tun da shari'a za a fara kwanan nan. Mu mu ka yi rayuwa a gidan Viper a tsakanin sa da Jauhar. Mun san yanayin zamantakewar su, tsabar ƙauna ko sunanta ba ya iya faɗa sai 'yar madara, sai ka jira kotu tukuna, kafin ka yi wannan maganar"
Shiru saifu yayi, dan ya san halin liti farin sani, 'yan a mutun mai zamani ne.
Da kyar da siɗin goshi, aka samu suka tafi gida, shi ma sai da su ka tabbatar da Nabila tana cikin tsaron da babu wanda zai gudu da ita, dan kowa zargin kowa yake yi.
Viper a makwancinsa, yana ta jujjuya al'amarin ya san akwai sauran ƙura a gaba, major ya ɗauki zafi sosai da sosai, kuma haɗin kansu ne zai ba wa Nabila nutsuwar ci gaba da gudanar da shari'ar da take yi a cikin nutsuwa.
***
Sumayya duk wani abu da ya shafi Indabo, haka take yaɗa shi a kafafen watsa labarai ba tare da tsoro ko fargaba ba, ba shi kaɗai ba, mussaman Alhaji mu'azzam yake sanyawa ake nemo mata manyan rahotanni na bankaɗa tare da cikakkiyar hujja a kan miyagun harƙallolin da ake yi a ƙasar nan. Sai dai kash, ko an bankaɗo babu wani abu da talaka zai iya yi a kai face Allah ya isa. Dan ƴan siyasar sun din ga ƙoƙarin kare kansu kenan, lokutan zaɓe su sake lallaɓowa tare da fara ayyukan babu gaira babu dalili, da raba tallafin abin da bai kai kaso goma a cikin abin da suke wawaso na al'aumma ba. Sai dai a wannan karon al'ummar sun yi rawar gani wurin yin abin da ya dace, karo na farko a Nigeria da ake ƙoƙarin yi wa sanata kiranye. Duk da irin barazana da matasan da suke jagorantar abin suke yi, amma suka dage babu gudu babu ja da baya, dan tuni sun miƙa wasiƙa ga hukumar zaɓe ta ƙasa a kan son yi wa Indabo kiranye. Hakan ya ba wa wasu matasan daga sassa daban-daban na ƙasar nan ƙwarin gwiwa da ganin cewa ashe za su iya kawo canji ga waɗanda suke wakiltar su su ma.
Alhaji mu'azzam mutum ne na mutane, dan haka mutanensa su ka din ga kiransa a kan ya fito takara.
Dama harin kujerar inda
Bayan kammala program ɗin ta, ta ga kiran waya.
Lambar Nabila ta gani, ta ɗaga ta ce "Ke ya ne, program na kammala ko numfashi ban shaƙa ba, kin doko mini kira"
"Ta na asibitin barrack, ta na buƙatar ganinki da gaggawa" ƙuuu cikin sumayya ya yi ƙara, muryar Viper ce, a duniya Allah ya yi masa kwarjini, muryarsa da ta ji kawai gabanta ya faɗi. Kashe wayar ya yi, bayan kammala gaya mata saƙon.
A gurguje Sumayya take ƙoƙarin kammala ayyukanta, dan ya je ya ji me ya sami Nabila.
A jiya da major ya koma gida, kasa gane kansa matansa suka yi, dan babu wadda ya kula, kuma ya ce baya buƙatar kowa ta zo masa turaka.
Sai Nasir suka tutsiye, su na tambayar sa, ina su ka je jiya wuni guda ba sa nan.
Nasir ya labarta musu komai, gaba ɗaya suka yi shock. Anty ta ce "Dama mahaifin Nabila yana raye?"
"Eh, mun ganshi jiya ma, ɗan daban nan Viper da ake nema, 'yar biyun Nabila ya aura ya kashe, kuma saboda shirme take kare shi, shi ya ɗauke ta ya kaita wurin mahaifinta" al'amarin yana buƙatar nutsuwa kan a warware shi, dan ba kowa ne zai iya fahimtar bayanin ba sama-sama.
Ko da sumayya ta je, ba wanda ya hanata shiga, da ta tambayi in da Nabila take, Nabila na ganinta ta miƙe tsaye, fuskarta ta kumbura suntum saboda kuka.
Ta rungume sumayya ta ci gaba da kuka, Sumayya ta ce "Subhanallah, Nabila waye ya mutu? Kin ga yadda ki ka rame fuskarki ta kumbura kuwa?"
Cikin kuka ta ce "Sumayya na ga babana jiya" waro ido sumayyan tayi ta ce "A ina?"
"Viper ne ya kai ni, Sumayya ashe yar biyuna ya aura aka kashe, duk wannan haƙilon da nake yi, 'yar uwata aka kashe"
Sumayya ta ƙurawa Nabila ido, ta ce "Anya kanki ɗaya?"
"Kai na ɗaya Sumayya, amma ai kin san lokacin da nake ce miki ina mafarki da mai kama da ni, ki ke yi mini dariya, wallahi sumayya ina da 'yar uwa da ban taɓa ganinta ba, a kanta nake shari'ar Viper"
"Nabila, gaba ɗaya kin rikita ni, ban gane in da ki ka dosa ba wallahi, gaba ɗaya na rikice" Viper ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo.
Jiki na rawa sumayya ta gaishe shi ya amsa, ta kalli Viper ta ce "Vi ka yi wa sumayya bayani, ta ƙi yadda ta kuma kasa gane bayanin da na yi mata"
"Wa zai fuskanci wannan bayanin naki at once dama, ki ƙwarara jikinki, ki yi haƙuri ki daina wannan kukan, yana daga dalilin da ya sanya tun farko ban gaya miki ba"
Sumayya za ta yi magana, Abba ya turo ƙofa ya shigo da sallama, suka amsa masa. Sumayya ta gaida Abba ya amsa mata, suka gaisa da Nasir ma.
Viper ya yi masa barka da zuwa, amma ya yi masa shiru.
"Arfa, kin ji sauƙi ina son a sallame ki, mu koma gida ne" kawar da kanta gefe ta yi, ba ta kalle shi ba.
Sumayya ta ce "Nabila Abba ne fa"
Ta ɗaga kai ta kalli Sumayya ta ce "Abba disappointed me, meyasa ya ɓoye mini ina da 'yar uwa, gashi ta mutu ban taɓa ganinta ba...
"Wai mahaifiyarki ma ba rasuwa ta yi baki taɓa ganinta ba?" Viper ya yi maganar a kausashe.
"Amma jauhar ta yi tsawon rai ai, meyasa aka hukunta mu da laifin babanmu"
Nasir ya ce "Nabila Abban ki ke gaya wa haka?"
Major ya yi shiru, kawai ya tashi ya fita.
Sumayya ta ce "Nabila meyasa ki ka yi haka? Baki kyauta ba, duk ɗawainiyar da ya yi da mu, hakan da ki ka yi ba dai-dai ba ne ba. Idan aka sallame ki, dole mu je ki ba shi haƙuri.
Kiran gaggawa aka yi wa sumayya, ta tashi ta tafi, cike da mamaki da tunani daban-daban a cikin zuciyarta.
Bayan tafiyar major, sai ga Bashir, har da kayan abinci niƙi-niƙi sun zo duba Nabila.
Tana zaune, a kan gado, Viper yana gefe yana waya, yana ganinsu ya kashe wayar, ya risuna suka gaisa da Baba.
Ƙarasawa yayi gaban gadon Nabila ya zauna ya ce "Sannu ya jikin naki?"
Ƙura masa ido ta yi, amma ta kasa masa uffan.
Ya zauna ya dafa hannunta, amma ta janye ta sunkuyar da kai.
Bashir jiki a sanyaye ya tsaya yana ci gaba da kallon Nabila.
Viper ya ce "Ina ga ko zaka ɗan bata lokaci, kafin Nabila ta ganka, tana ɗokin da muradin ganinka, abin da ta ji ne dole za ta ji wani iri, amma in sha Allah za ta maye maka gurbin jauhar.
"Na san ni mai laifi ne, amma ƙaddara ta riga fata, wallahi tamkar an shafe ni tunanina a cikin kaina, haka na manta da mairamu. Yaya za ayi ace ka auri mace ka manta da ita, ban san meyafaru ba a lokacin. Kuma ni maitama bai gaya mini ku biyu ba ne, amma ki yi haƙuri ki yafe mini dan Allah" ya kalli Viper ya ce "Bari na je, hafsa ma za su zo dubata yanzun nan in sha Allah" Viper ya tashi ya raka shi har harabar Asibitin.
Nabila ta jingina da jikin bango ta lumshe idanunta, hawaye na bin gefen idonta, Viper ya dawo ya tarar da ita.
"Ba ki kyauta ba abin da ki ka yi? Duk ɗokin ganin mahaifin naki, abin da ki ka yi kin kyauta kenan?"
"Ba ka san me nake ji ba ne?"
"Ko ma me ki ke ji ba ki kai ni ba, abin da ki ke yi ba ki kyauta ba, ke zaki jajirce ki daidaita wannan rashin jituwar da yake tsakaninsu, ki rungumi mahaifinki"
Ta zuba masa ido hawaye na bin idonta.
"Menene kuma? Kukan be isa ba haka?"
"Vi" tayi maganar muryarta na rawa.
"Abla"
"Ka ga abin ƙaddara ko? Ƙaddara ce ta sanya na din ga bibiyarka"
Ya ce "Haka ne"
"Kwatsam na fara sonka daga wasa, na yarda da maganarka, ba zan taɓa jauhar ba, kuma idan na ci gaba da sonka ban yi zumunci ba na ci amanar 'yar uwata. Zan fara jin kunyrka a matsayin ka na mijin yayata, ba soyayya tsakanin mu yanzu, zan yi iya ƙoƙarina na ga an ƙwatarwa 'yar uwata hakkinta, kuma na ga an wanke ka daga zargin da ake yi maka. Na gode sosai da sosai da ƙoƙarin da ka yi mini".
Ayshercool
08081012143
88
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*
Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_GYARA SHINE MACE_*
*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_*
🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾
*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327
*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,
Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍
Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍
Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃
Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai ,
Mmn Yusuf likitar Mata💃😍
Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃
Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃
Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima
KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻
Kalolin gumba
Kalolin matsi
Kalolin gari
Kalolin tsumi
Zumar dabino
Zuma Mai rubutu
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Dahuwar kaza
Dahuwar zabo
Dahuwar zuciya
Dahuwar ciccibi
Dahuwar tsoka Tara
Dahuwar Yan shila
Dahuwar kwai Mai rubutu
Turaren mallaka
Turaren Mara
Turaren tsugunno
Turaren k'irji
Shuumar humra
HATSABIBI turare
Hatsabibiyar humra
Matan gaske
Maltinat Mata
Shayin Mata
Tsumin kankana
Sirrin tafin k'afa
Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini
Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a
Akwai hadin farinjini na matar aure
Akwai kwallin mallaka
Zoben mallaka
Set na Jigidar mallaka
*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai