Showing 171001 words to 174000 words out of 479911 words
su Baba suka zo, suka tarar da Al'amin yana ba ta abinci an zaunar da ita.
Gab ɗaya zamansu a wurin, bai hana shi tattalin matarsa ba, dan gani yake yafi kowa sa'a farfaɗowar da ta yi.
Babban abun da ya yi wa jauhar daɗi, bai wuce ganin 'yan gidan su, sun zo dubata ba, ko ba komai sun nuna damuwar su da ita.
Duk saifu na ta zuga Baba ya bi diddigin yadda aka yi tayi ɓarin, ko dukanta Al'amin yake yi, amma yanayin yadda suke mu'amala ita da Al'amin ya sanya kowa yin wani tunanin daban, dan saɓanin abun da ake tunani ake gani.
Har Abbu sai da ya zo duba jauhar, su shahida ma duk sun zo, Baba sai da ya yi ta yi wa wasila godiya da Addu'a, tana ta ƙoƙari da jauhar, maƙwabtan su ma na ta zuwa dubata.
A kwana na uku, da daddare take tambayar Al'amin "Master wai dan Allah meya same ni ne? Na san kawai na ga lemo a ɗakinka na sha, daga nan ban san meyafaru ba, kuma na ji ana cewa nayi ɓari, ya aka yi na yi ɓari ai bani da ciki, ko kuma ina da shi ban sani bane? To yaya aka yi ya zube?"
"Ki yi haƙuri, likita zai yi miki bayani in sha Allah"
"To kai ka yi mini mana, wai shikenan babyn yanzu babu a cikina" tayi maganar tana shafa cikin ɗauke da damuwa.
"Ni likita ne?"
"A'a amma ka gaya mini, haryanzu ina da cikin?"
Al'amin ya ce "Wai abun da baki san da shi ba ma, zaki bi ki damu, ki yi haƙuri za su yi miki bayani"
Ta ce "To shikenan, yi mini addu'a na yi baccin".
Ya ce "To"
Gari ya waye, su surayya ma suka zo dubata, saifu ya kawo su, take tambayar ina yaya hafsa, aka ce mata ta tafi umara.
Jauhar ta ce "Dan Allah ku ce ta yi mini addu'a sosai da ni da master"
Suryaya ta ce "Wai ke kowa na gaya wa miji sunan 'yan gayu ke kina master"
Tayi murmushi ta ce "Baki ga mastern ne ba? Kuma ai mu ba 'yan gayu bane"
Kasancewar Al'amin ba ya ɗakin ya sanya saifu cewa "Ke, ki faɗa mini gaskiya, wani abun yayi miki ko?"
Ta ce "A'a me ka gani?"
"Wallahi ki ka rufa masa asiri sai kin daku, har likita na saka baba ya tambaya, ko dukanki yayi ya ce babu alamar duka a jikinki da aka kawo ki"
Jauhar ta ce "Master ba ya duka, bai taɓa dukana ba".
"Na san halinki da shegiyar gwaninta ne, da kare mai laifi ki gaya mini gaskiya"
"Wallahi babu abun da ya yi mini"
Dawowar Al'amin ya sanya su yin shiru, ya ƙarasa gaban gadonta ya ce "Me zaki ci?"
"Bakomai, kawai a sallame ni"
Ya zauna a gefen gadon ya ce "Ba na son rigima, wace irin sallama kuma?"
"Kai ka koya mini ai, kai fa har guduwa ka ke daga asibiti"
Yayi murmushi ya ce "Zaki gudun kenan?"
Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kashe kuɗin yayi yawa, ina iya tashi ai"
Rarrashin ta ya din ga yi, dan shi kansa ya san zaman asibiti da gundura.
Sai da ta kwana shida, an saka mata jini ya kai leda biyar, sannn aka fara zancen sallamar ta ranar.
Daga likitan sai ita da Al'amin a ɗakin, yayi mata bayanin abun da ya faru, tare da gaya mata akwai buƙatar ta huta kan ta sake ɗaukar ciki.
Ya yi wa Al'amin faɗa a kan ya kiyaye sosai da sosai, wannan karon sun rufa masa asiri idan ya ƙara faruwa.
Jauhar ta sunkuyar da kai, sai kuka.
Likitan ya ce "Menene? Meyafaru? Kuma?"
Al'amin ya ce "Bakomai, zamu yi magana da ita"
Likitan ya rubuta musu sallama ya fita.
Yana fita ya ce " 'yar madara menene kuma?" Shiru ta yi masa ta cigaba da kuka.
Duk yadda ya rarrasheta, tayi haƙuri ta ƙi yin magana.
Baba ya zo da mota, ya ɗauke su ya kai su gida, ya yi ta yi wa Al'amin godiyar ɗawainiyar da ya yi ta yi da jauhar a asibiti, yayi musu sallama ya tafi.
Al'amin ya zauna kusa da jauhar ya ce "Dan Allah ki gaya mini menene?"
"Komai ma, kawai ka janyo na rasa babyna, kuma wai ba zan haihu yanzu ba, wataƙila ma ba zan sake haihuwa ba".
"Subhanallah kar ki yi mana wannan fatan, zaki kuma haihuwa cewa suka yi kawai ki bayar da tazara saboda yanayin jikinki".
Cikin kuka ta ce "Ai da ka daina shan Wannan abubuwan, duk da ba haka ba. Kawai ka ja na yi asara ga jinina ya ƙare, kuma wai ba zan haihu yanzu ba"
Cikin tsananin nadama yake rarrashinta, sallamar mutane ya sanya ya tashi, 'yan dubiya suka din ga zuwa duba jauhar.
Al'amin na ta hidima da ita, da sassafe yake tashi ya yi aikace-aikace, girki ne kawai sai maƙwabta sun shigo suke yi mata.
Shahida ma ta yi ƙoƙari sosai, dan tana zuwa ta taya jauhar aiki, a haka suka saba.
Guduma ya sake zuwa har gida ya duba jauhar, tare da gaya mata abun da ya faru.
Jauhar tayi masa nasiha sosai a kan shaye-shaye.
Al'amin ya fara bata tausayi, har rama yayi sosai, mussaman daina kula shi da tayi, sai yayi ta kame-kame.
Yau da ya dawo, normal ta karɓi abun ta.
Har ya tafi ya kwanta, ta bishi ɗakinsa.
Ta hau gadon ta kwanta ta ce "Master"
"Mmm"
"Ka yi haƙuri dan Allah, komai ya wuce na ji babu daɗi ne kawai shiyasa kawai"
Ya ce "To"
"Kayi magana mana, ba to ba"
"Ina jin babu daɗi, missing babynki da ki ka yi, ki yi haƙuri laifina ne"
"Ba fushi na yi dan cikina ya zube ba, fushi na yi saboda bani ba har kai kana yi mini ganganci da rayuwarka, ka daina dan Allah for our own good and safety"
Ya ce "To in sha Allah"
"Yaya za a sha fankar ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Likita ya ce ki huta tukuna kar ki sake ɗaukar ciki".
"Sun yi mini allura ai, ko haryanzu ba ka jin komai"
Ya ce "Da ɗin ma ina ji, mazewa nake yi, a madadin hakan sai in sha in bugu in manta da ke"
"Master nawa nikaɗai, daga ni ba ƙari"
"A'a saura uku"
Ta ce "To ga fili ga mai doki nan ai"
Ya ce "Filin da dokin naki ne ai, ki yi yadda ki ke so madarata"
***
Jauhar ba ta samu damar yin jamb ba, saboda rashin lafiya, dan haka Al'amin ya samu indabo ya ce A alƙawarurrukan da ya yi masa, yana son ya samawa jauhar admission, tare da samawa Nura guduma aiki ko na direba ne, a manyan ma'aikatu.
Al'amin ya daina shigo da duk wani abu na shaye-shaye gidan, ko zai yi a iya waje yake tsayawa yayi abun sa.
Jarin su duk ya ƙare a asibiti, dan haka ya yanke wata shawara a ransa.
Ayshercool
08081012143
42
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Jauhar ya fara samu da maganar, da daddare suna tare ya ce "Na ce ba"
"Ka ce me ranka ya daɗe?"
"Wani abu na yanke ne, ina son na samu Abbu, ya bani gadona na wurin ummi, in sayar da abun da zan sayar na karɓi kuɗi a wurin indabo na haɗa na fara wata sana'ar ina son barin sayar da wiwi gaba ɗaya".
Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah, tunani mai kyau, amma ba a yadda ka gaya mini haka zaka je ka gaya wa Abbun ba ko?"
"A yaya zan gaya masa?"
"Cikin kwantar da murya, zaka yi masa bayani, ka san iyaye sai ana lallaɓa su, ka sani ma ko ya kai ka kasuwa?"
Ya ce "Ko ya kai ni ba na so, ya je ya cigaba da riƙe 'ya'yan matar can. Dama alhkina ne ya sa yanzu ba shi da kuɗi kamar da"
Jauhar ta ce "Haba master, Abbun ka ke gaya wa haka, kai zaka ji daɗi ka haifi ɗa yayi maka haka?".
Cikin ko in kula Al'amin ya ce "Duk tsanani, ba zan yi wa ɗa na abun da yayi mini ba"
"Master ka san shiga tsakaninka aka yi da Abbu, dan Allah ka daina irin wannan maganar".
Yayi mata shiru, ta sake cewa "Master yaushe zaka kai ni mu gaida su Hajiya?"
"Ba rana? Tun bayan kawo ki sun kuma zuwa?"
"Hmm master, Allah ya baka damarmaki, duk da ka rasa ummi da yaya sadik, da kuma uban gidanka. Ko yaya dole nan gaba yaranka su so ganin 'yan uwanka, dan da dangin uba ake ado. Ni fa duk wannan abun da ake yi, bani da wayo sanin mahaifiyata ta rasu, ba 'yar gari bace, yar jalingo ce, ba a taɓa kai ni garinsu ba, ba a taɓa nuna mini ko mutum ɗaya a danginta ba, kuma ban taɓa ganin kowa ya zo daga garinsu ba. Da na fuskanci babu uwata a gidan, na nemi ba'asin in da take, baka ga dukan da mama tayi mini ba, ban haƙura ba na tambayi baba, amma ya ce idan na kuma yi masa zancen dangin mamana, sai ya zane ni. Yadda yake nunawa da yadda su mama ke faɗa yana son mamana, amma nayi mamakin yadda yaƙi yadda a kai ni garin su na ga ko 'yan uwanta, da naga ba ya so kawai na daina maganar. Kai kuwa da ka rasa uwa akwai makwafinta, yakamata mu je mu ga hajiya mu gaisheta, ni ba wanda zan kalla na ce daga wurin dangin mahaifiyata yake".
Yayi ajiyar zuciya ya ce "Kuma ba ki san a ina take a jalingon ba?"
Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, kawai iya abun da na sani kenan"
"Shikenan, zamu je mu gaida hajiya, amma sai na tambayi Abbu in da take a tofan ba zan iya tunawa ba"
"Yauwwa maigidan Allah dai ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora "
Ya shafa fuskarta ya ce "Amin madarata"
"Yauwwa milona"
Ya ce "Ga madara ga milo, sai Shan shayi" suka yi dariya tare.
Washegari da safe bayan sun karya, ya bata magunguna ta sha, tana ta lallaɓa jikinta, za ta yi aikace-aikacenta, ya hanata ya fito ya yi mata share-share, har tsakar gida ya wanke mata.
Kayan da ta cire yake wankewa, aka buga ƙofa, ya je ya buɗe hafsa ya gani a tsaye, hannunta riƙe da leda.
Ya bata hanya ta shigo, a tsorace ta kalli Al'amin fuskarsa a haɗe ta ce "Ina kwana"
"Lafiya ƙalau".
"Dan Allah wurin jauhar na zo" da hannu ya nuna mata falo.
Daga falon ta ce "Muryar wa nake ji kamar Yaya hafsa"
Ta ce "Nice"
Ta tashi ta taro hafsa ta ce "Sannu da zuwa".
Hafsa ta ce "Yauwwa sannu ya jiki?"
"Jiki Alhamdilillah, ya aka yi ki ka gane gidan?"
"Yaya saifu ne ya gaya mini hanya, kuma direbana da yayi tambaya aka nuna masa gidan ba wuyar ganewa".
Ta ce "Allah sarki yaya hafsa tun ina Asibiti nake tambayar kina ina, aka ce mini kina umara, na ce baki gaya mini ba muna chat, ai da na jero addu'a ayi mana ni da mai gida"
Tayi murmushi ta ce "yanzun ma an yi miki, wai jauhar ɓarin da wahala ne, na ga kin rame haka kin yi fari?"
"Kai da wahala mana, jini na zubar sosai shiyasa na yi haka, amma kwanaki ai ƙiba na yi sosai, ashe ciki ne ban sani ba"
"Allah sarki, Allah ya kawo mai amfani, sannu"
"Yauwwa ai na warware "
Al'amin ya shigo falon, jauhar ta ce "Master ba ka ganeta ba ne? Yayata ce da muka je gidanta fa, ba ka ga muna kama ba?"
Kai tsaye ya ce "Na gani, kin fita kyau"
Jauhar ta ce "Kai fa ka fiye son kai ta ina?"
"Ta ko ina" yayi maganar yana shigewa ɗakinsa.
Hafsa tayi murmushi ta ce "Aikam kin fi mu kyau ai duk gidan nan"
Jauhar ta ce "Rabu da shi, shi ma faɗa kawai yayi" suka cigaba da hira, ya sake fitowa ya shirya tsaf zai fita.
"To yau me ki ke so? Kayan cikin ko ganyen wanne ki ke so?"
Ta shagwaɓe fuska ta ce "Kai"
"Ni ki ke so?" Ta ɗaga masa gira tana murmushi.
"Aikuwa zaki kwana da yunwa, me ki ke so?"
"Komai ka samu na gode"
Ya ce "Abun da zai ƙara miki jini aka ce ai"
"Jininka zan sha" ta yi maganar tana dariya.
Yayi murmushi ya ce "You are not serious, ki yi addu'a Allah ya sa na samu kuɗi, na sayo miki kaza".
Hafsa ta ce "Ai ga miya ma na yi miki, da kazar a ciki"
Jauhar ta ce "Ashe zaku yi faɗa da master, tun da ki ka riga shi kawo mini kaza"
Murmushi ya sake yi, wanda ya bawa hafsa mamaki, take bin su da kallo, gwanin burgewa.
Har zai fita ta ce "Master"
Ba tare da ya juyo ba ya ce "Kar na yi shaye-shaye da yawa, kar na yi faɗa da kowa, banda rigima da mutane" ta kwashe da dariya ta ce "Au ka haddace ma kenan, addu'a zan yi maka ai, Allah ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora ya wadatamu da halal ya nesanta mu da haram"
Ya waiwayo ya ce "Amin ya haiyyu ya ƙaiyyum, 'yar aljannata" ya juya ya tafi.
Yana fita Hafsa ta ce "Innalillahi, jauhar dan Allah ya aka yi ki ka canza mutumin nan, dariya fa yake yi miki, kalli yadda yake yi miki, dan Allah jauhara ya ki ka yi ki taimake ni" tayi maganar cikin tsananin damuwa.
Jauhar ta ce "Ban fahimci in taimake ki ba yaya hafsa, meyafaru? Wannan ai normal ne tsakanin ma'aurata, kodayeke shi ya koya mini rashin kunya, da ko kallonsa bana iya yi a gaban mutane"
Idon hafsa ya cika da hawaye ta ce "Jauhar, wallahi tun da na auri Alhaji mu'azzam hankalina bai kwanta ba, bai taɓa bani awa biyar cikakkiya ba. Sai abun da matarsa take so yake yi, bai tare a ɗakina ba sai da matarsa ta amince. Ga kuɗin yana da su, yana kashe mini ya sakar mini amm ba su nake so ba, kulawarsa nake so da lokacin sa".
Juahar ta ce "Yaya hafsa ba fa abun da ki ke kalla a film ne soyyaya ba a ƙasar hausa da wurin mijin bahaushiya, dole ki fara kallon wane irin mutum ne shi, kin ga mijinki mutum ne mai hidindimu da yawa, ba zai yiwu ace kullum yana da lokacinki ba yakamata ki din ga yi masa uzuri"
"Uzuri jauhar, yana da lokacin matarsa da yaransa, gaba ɗaya auren ya fita daga kaina, na je na gaya wa anty, wai wallahi na ɗaga maganar nan, sai ta yi mini Allah ya isa, wai zan saka ayi mata dariya, na zama kamar hoto a wurinsa, ko ɗan abun ɗokin nan na amarci, duk fa ban san su ba. Ke da ki ka auri wanda ake yi wa kallon sai a hankali, babu imani da tausyai a zuciyarsa kalli abun da yake yi miki fa. Ni dai dan Allah idna wani malamin ne da ke, ki haɗa ni da shi"
Cikin damuwa jauhar ta ce "Yaya hafsa ni wallahi ban san in da ake ganinsu ba ma, canza mutum daga wani abu da baka so zuwa wani, ba abu ne mai sauƙi ba. Kin san ni irin wahala da gwagwarmayar da na sha kafin mu zo wannan matakin kuwa?
Da fari nima damun kaina na din ga yi, daga baya na kama addu'a babu dare babu rana, na haɗa da biyyaya da kuma haƙuri.
Master mutum ne, kallon da mutane suke yi masa daban, wanda nake yi masa daban, biyayya da addu'a ne suka canza mini shi. Alkhairin da yake yi mini nake kalla kullum, nake yi wa laifukansa uzuri, har gara ke kina da uwa a raye, ni daga ni sai Allah, da na san bani da wata mafita, na bi abun da ƙaddara ta zaɓa mini, na rungumi abuna hannu bibbiyu. Kuma Allah ya shiga lamarina Alhamdilillah, mijina talaka ne, amma ba kowace mace take da ikon da nake da shi a gidan aurena ba. A zahiri shi nake bawa girman, shi ne jagoran amma a baɗini ni ce sitiyarin rayuwarsa, ina fatan kasancewa da shi har aljanna. Ke ma ki nutsu ki gano menene kurakuranki, sai ki gyara".
"Ba wani kuskure, ina kyautata zaton asri aka yi mini wallahi "
"A'a yaya hafsa, ki daina faɗar haka, ki miƙa wa Allah lamuranki, wallahi zaki ga canji "
Duk yadda jauhar ta so nusar da Hafsa muhimmancin haƙuri da juriya, da dagewa a kan addu'a amma taƙi ganewa kuma taƙi yadda.
Zuwa azahar ta tafi, ta yi wa jauhar uban farfesun kaji, da abinci, ta kuma ajiye mata kuɗi ta tafi.
Har a lokacin ba ta yadda har da hakkin jauhar a abun da yake faruwa da ita ba.
Al'amin ne zaune a gaban Abbu, tun da ya gaishe shi, yayi shiru.
Abbu ya ce "Ya jikin 'ya ta?"
"Da sauƙi"
Abbu ya ce "To Alhamdilillah yarinyar kirki, 'yar aljanna Allah ya ƙara mata lafiya, matso ka haɗa shayi ga kayan breakfast nan"
Sai da Al'amin ya kalli Abbu, ya girgiza kai ya ce "Na ƙoshi"
"Too, yau kai ne ka ƙoshi da abinci kuma?"
Ya bashi amsa da "Eh na ci a gida"
Abbu ya yi murmushi ya ce "Na manta ne, ashe fa magidanci ne, ya aka yi?".
"Sonake a sayar da gadona, zan ja jari, sana'oin da nake yi, ba sa iya riƙe mu sosai, gashi ina so ta koma makaranta, babu isasshen kuɗi a hannuna.
Sai kuma ina son ka bani full adress ɗin hajiya, zan kaita ta gaisheta ta matsa a kan haka"
Abbu yayi shiru yana ƙarewa Al'amin kallo, duk ya ɗan yi sanyi daga wani rashin mutuncin, babu uwar sumar da yake tarawa da faratan da yake bari zaƙo-zaƙo, gashi yadi ne a jikin sa saɓanin da, da idan bai ga dama ba da 3quater yake yawo da shirt damatsansa a waje, ya wani nutsu sosai.
Abunka da uba da ɗa, wani irin shauƙi ya ji yana kama shi, a yadda ya ga tarin sauye-sauye a tattare da Al'amin.
"Kai amma 'yar nan tawa ta kyauta, amma wace sana'ar zaka yi?"
Al'amin ya ce "Da wurin buga bulo nake so, ko wurin yin buredi, amma ban gaya mata ba tukuna, ban sani ba ko tana da wata shawarar"
Abbu ya numfasa ya ce "Kana ji na Al'amin, tsawon shekarun nan, filayenka sun yi daraja sosai da sosai, idan ka bari suka ƙara kwana biyu sai sun fi haka sosai. Ka je ka rubuto business plan ɗin ka kawo mini, tare da list ɗin abun da za ayi mata na makarantar, sai na baka kuɗin, idan Allah ya dafa maka, aka samu cigaba, sai a sayar da ko