Showing 423001 words to 426000 words out of 479911 words

Chapter 142 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6073

ake tunanin samun Walid, an duba ba a same shi ba, Liti har wata irin rama yayi.
Duk ƙaunar Viper da Abinci, baya gabansa, ba ya iya ci, saboda damuwa da tashin hankali.
Gashi yana ta gargaɗin Nabila a kan yawo anyhow, dan ya san tun da aka farmaki Walid, a kowane lokaci za a iya sake kai ma wani na kusa da shi hari.

Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, yana zaune ya kasa bacci, yana ta tasbihi, yana fatan Allah ya kuɓutar masa da Walid, wayarsa ta fara ringing.

Cikin azama ya ɗaga, ya saka a kunnensa ya yi shiru.

"Ban yi mamakin jin idonka biyu ba, saboda sai da na duba, na duba na tabattar da wanda na kama, shi ne na kusa da zuciyarka, da taɓa shi zai tabattar maka da ina sane da kai, ban manta da kai ba".

"Ina ka kai Walid, kar ka bari sabgar nan ta juye zuwa wani abu daban, ka fito da shi, duk in da ka kai shi"

"Ta daɗe ba ta juye ba, ka manta tare ku ka din ga yi mini aiki a baya, ai ina ganin kamar shi haryanzu ba shi da wani muhimmin tabo, da bangar siyasa tayi masa kamar kai.
Ai talaka ba shi da wani amfani, ban da ku yi mana hidima, amma kun dage zaku kai ni ƙasa, zan saki Walid ne, a lokacin da wa'adin zaman Abdul yasar ya ƙare a gidan yari. Sannan zan sake duba abu mai muhimmanci a gareka, na yi masa ɗaurin talala, yana raye amma kamar matacce, kamar yadda ka saka aka ɗaure mini ɗa a ƙasashen waje. Na samu labarin kana aiki a kaina, sai ka ga bayana, gani gaka, ɗan halak ka fasa".

Viper ya ce "Wannan shi ne kuskure na biyu mafi muni da ka aikata Indabo. Ni da kai muke harƙalar nan, kuma batun ɗanka, hukunci aka yi masa dai-dai da abin da yayi. Ina mai gargaɗinka da kakkausar murya ka saki Walid, idan ba haka ba zan razana duniyarka da abin da baka taɓa zata ba, awanni arba'in da takwas kawai ka ke da su, kuma ka fara ƙirgawa daga yanzu" yana gama maganar ya kashe wayar, ya dafe kansa, cike da wata irin nadama da danasanin biye wa Indabo ya din ga aikata ɓarna.

Wato a duniya idan amfaninka ya ƙare kai ba a bakin komai ka ke ba, meyasa zai ɗauki Walid maimakon ya ɗauke shi, tun da da shi yake yi, ba Walid ba.

Da sassafe Viper ya tafi barrack, saboda Nabila, yana tsoron ita ce next target na indabo, tun da tare suke yin komai da ita, sai dai tayi noticing rama da kuma damuwa a tattare da shi.

Tana ta shiri, yana falon madam yana jiranta, gani yane da ya kawar da kai, komai na iya samunta.

"Vi" ya ji ta kira sunansa.

"Ka karya sai mu fita" ya girgiza mata kai bai ce komai ba.

Ta fuskanci damuwa na ƙara saka shi miskilanci da rashin magana.

Nabila ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah ka ci ko kaɗan ne, duk ka yi wani iri"

"In ci Abinci ban san halin da ɗan uwana yake ciki ba? Shi ya ci? Duk a dalilina, shikenan duk wanda ya raɓe ni a haka rayuwarsa za ta ƙare a wahala da tashin hankali, menene laifin Walid ne?"

Cikin rauni ta ce "Na sani, na kuma fahimce ka, amma hakan babu abin da zai canza. Addu'a da ci gaba da jajircewa ce kawai za ta kawo mafita, ka yi haƙuri dan Allah Vi ka saka wani abu a cikinka" ya ƙura mata ido na wani ɗan lokaci, kawai ya tashi tsaye ya ce "Idan kin gama ki same ni a mota" sosai tausayin sa ya mamaye mata zuciya.

Jiki a sanyaye ba tare da ta samu ta yi breakfast ɗin ba, ta bi bayansa.

Da suka kai ta wurin aikin ma, har ta shiga ta ji kamar ana bin ta, ta waiwaya ta ga shi ne ya biyota. Ba ta ce masa komai ba, ta shiga office ɗin ta ya bi bayanta.

Kujerar cikin office ɗin ya samu ya zauna, bai kulata ba, ita ma ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da aikinta, gani yake yi yana kawar da kai, wani abun zai sameta ita ma.

Har ta gama aikinta na ranar yana zaune, sannan Liti ma ya saka an mayar da shi cikin barrack.

Duk yadda ya bi wayar Indabo abu ya gagara, sai taƙi shiga, gashi gani yake yi kamar babu wani ƙoƙari da ake yi a kan neman Walid ɗin.

Kwatsam Nabila na shirye-shiryen tafiya, ya sake jarraba wayar Indabo, cikin sa'a ta shiga kuma ya ɗaga, Viper ya miƙe cikin zafin rai ya ce "A karo na ƙarshe, ina Walid yake?"

"Babu wata barazana da zaka yi mini Viper, sharuɗɗa zan saka maka, wanda dole sai ka bi su. Na farko ka saka wannan yarinyar ta janye ƙorafin da ta shigar a kan Bunkure a ma'aikatar Shari'a, sannan ka tattaro duk wani bincike da ka yi a kaina, na yinƙurin tona mini asiri, da wannan wayar da ka ke amfani da ita ka bani, sai a saki Walid, idan ba haka ba wannan banzar yarinyar ita ce next target ɗina a kanka, sai na saka an wulaƙanta ta, wulaƙanci mafi muni na tagayyara rayuwarta, fiye da yadda ka ke tunani" Viper ya ɗaga kai ya kalli Nabila da take kallonsa, amma ba ta san me ake cewa ba.

Viper ya ce "Saboda abin da nake shiryawa a kanka ne ya sanya ka kashe P.A?"

Indabo ya ce "Eh, ban damu da a in da ka samu labarin hakan ba, iyaka na san ba ka da wata cikakkiyar shaida a kan ni ne kashe shi, duk wanda ya ci amanata, sai na kawar da shi. P.A ya ci amanata ya haɗa kai da kai, domin yana ganin ya zame ya bar ni shi ne zai sanya ka ƙyale shi".

Viper ya sauke numfashi mai zafi, cike da dana sanin, sanin Indabo a rayuwarsa ya ce "Idan kuma ina da shaidar kisan kan da ka yi wa P.A da hannunka fa?"

"Gwargwadon yadda ka ci gaba da zurafafawa, gwargwadon yadda zan ci gaba da hura wutar da ka ke ciki, ba dai kana yi wa kanka iƙirarin ƙarfen cikin wuta ba, idan ba zaka ɗakku da hannu ba, zan ci gaba da iza wutar da ka ke ciki, sai ta kai matakin da zata narka ka"

Viper ya datse laɓɓansa na ƙasa, ya fesar da wani zazzafan numfashi, ya ce "A ina zan kawo maka abin da ka buƙata?"

"Zan turo maka adireshin wurin, kuma ba kana bayarwa za a sake shi ba, sai na ba wa ƙwararru sun tabattar da ingancin abin da ka bayar, kuma a yau ba gobe ba, yarinyar nan ta janye maganar Bunkure"

"Na ji, zan yi abin da ka ce, amma yarjejeniya ɗaya idan ka saɓa, wutar da kake ƙoƙarin narkani da ita, kai zata ƙona" Indabo ya katse kiran.

Viper ya kalli Nabila, ta ce "Vi wai lafiya?"

"Zamu je ma'aikatar shari'a, ki janye ƙorafin da ki ka shigar a kan Naja'atu Bunkure"

A razane Nabila ta ce "Saboda me?"

"Saboda haka na ce" yayi maganar a fusace.

Nabila ta ce "Akwai dalili dole, ka gaya mini, idan ba haka ba zan iya janyewa ba gaskiya, gaba ɗaya wahalata a kan lamarin matar nan na ɓata lokacina, kawai kuma sai na janye?"

"Sai kin janyeta, babu wani bayani da zan yi miki, dolenki ki janye" yayi maganar yana kallon Nabila, yana hasko cikin bala'i da tashin hankalin da zai shiga, idan aka taɓa ta.

****

Goye yake da Jaka a bayansa, a dajin Allah shikaɗai, sai waige-waige yake yi.
A kan babura da manyan bindigu, wasu mutane suka ɓullo, suka zagaye shi.
"Ka ajiye jakar, ka ɗaga hannayenka sama" wani yayi masa umarni.

Ya ajiye jakar, ya ɗaga hannayensa, ɗaya ya karɓi jakar, ya zazzage, ya dudduba ya ce "Kayan ne"

Wani daga cikinsu ya ce "Za a aika shi ne?"

"A'a kai ba a ce ba, jami'i ne, asirinmu zai iya tonuwa, mu ware kawai".

Suka ja baburansu, suka yi gaba, suna tafiya aka turo masa saƙo.

"Ke je dutsen da yake in da kuke, ka ɗauki gawarsa" kamar mahaukaci, haka Viper ya sake gigicewa, daga in da aka saka shi kai kayan, bai isa in da Walid yake ba, sai bayan awanni uku.

Yana zuwa ya lura da ba a lokacin aka yar da shi a wurin ba, kamar ya kwana a wurin, an ɗaure masa hannu da ƙafafuwa, an tura masa tsumma a baki, an ɗaure wuyansa da wayar cable, ga jikinsa ko ina a farfashe saboda duka.
Fuskarsa ta kumbura suntum, duk jini, ƙanan ƙwari sai bin sa suke yi.

Kamar yaro ƙarami, Viper ya fashe da kuka yana kwance Walid, ya kwance wayar da take wuyansa, ya ɗaga shi yana kuka, yana kiran sunansa.

Ya ƙanƙame shi a jikinsa, kawai ya ji zuciyarsa na bugawa, a hankali.

Zumbur ya miƙe, yana ambaton Allah, ya goya shi a bayansa, gani yayi idan ya tsaya buge-bugen waya, zuciyarsa zata daina bugawa, haka ya kwashi tafiya, har rukunin kamfanunnukan nan, ya ce su taimaka masa su kai Walid Asibiti.

Kai tsaye barrack ya tafi da shi, ya kai shi asibitin cikin bariki, babu wani jinkiri aka rufu a kansa, yana da rai bai mutu ba, sai dai babu tabbacin ya tashi.

Duk da Nabila tana cike da ɓacin rai da damuwar sakata janye ƙorafi da yayi, ba tare da ya yi mata bayanin komai ba, amma tana ganin saƙonsa na yana Asibitin cikin barrack tare da Walid, ta tashi tana tsuma, ta saka hijjabi ta fita.

Yanayin da ta ganshi ne ya karya mata gwiwa. Ta ce "Vi ya ake ciki?"

"Yana ciki sai dai babu ya rayu" yayi maganar yana zubar da hawaye.

"Kayi haƙuri vi, ka kwantar da hankalinka, in sha Allah Walid zai tashi da ikon Allah"

Sai ita ta kira su Alhaji mu'azzam, da Liti ta sanar musu an ga Walid.

Babu jimawa wurin ya ɗinke da jama'a.

Hatta Abbu yana wurin, Shahida ma kasa zama tayi, sai da ta biyo Abbun.

Abbu sai shi ya kama hannun liti, yana ta rarrashin sa, gaba ɗaya ya firgice, an tuɓe Walid daga shi sai gajeren wando, duk jikinsa shaidar duka, aka yi dressing ɗin raunukan jikinsa, aka ɗebi jininsa ana ta gwaje-gwaje.
Duk wani abu da za a buƙata wurin bincike, sai da suka ɗauka, kafin a taɓa shi.

Ɗaya daga cikin likitocin ya fito, ya ce "Ku kwantar da hankulanku, Alhamdilillah. He's responding to treatment. Vitals ɗin sun dawo normal, in sha Allah muna saka ran ya farka a kowane lokaci. Idan ya farka zamu tura shi sauran gwaje-gwaje.

Sai a lokacin suka ɗan samu nutsuwa.

Cikin dare aka kira Viper wurin ogansa, Ya sha faɗa a kan abin da ya yi ba tare da ya sanar musu ba. Shi dai yayi shiru, dan a halin da yake ciki, babu umarnin wanda zai iya tsayawa saurara, ya sha faɗa duk da yayi bayanin abin da ya faru a yanzu.

Ya numfasa ya ce "Jami'anmu sun tafi, za su dawo da wayar, duk wanda aka kama da wayar ɓatar da shi zamu yi, cin amanar ƙasa da ƙoƙarin tonon asiri ne, duk wanda aka kama da wayar ba jami'inmu ba" Viper dai yayi shiru, domin an ce ya saurari punishment ɗin da za ayi masa.

****

Sai da Walid ya kwana a Asibiti, ya wayi gari, sannan ya motsa ya farka.

Liti ne ya ga ya motsa hannunsa, ya tashi da sauri, ya nufe shi yana zazzare ido yana kiran sunansa.

Walid ya buɗe ido ya kalli Liti, ya yinƙura zai tashi Liti ya ce "Kai kar ka tashi, a asibiti kake"

Ya ɗaga kai yana kallon ɗakin, Viper ya ƙaraso, yana cewa "Mai laya, kalleni ka gane ni?"

Murmushi ya yi ya ce "Na kiyayi mai zamani"

Viper ya rasa me ma zai yi dan farinciki, ya zuba masa ido, yana haɗiye ƙwalla.

"Na kasa tashi ku ɗaga ni"

Viper ya sako hannu ya ɗago Walid, sai da ya yi ƙara saboda ji yayi kamar su na kakkarya shi.

Liti ya ce "Wai dan Allah meyafaru, suwaye suka ɗauke ka?"

"Jama'ar Indabo ne, wai sai na gaya musu abin da Viper yake shiryawa a kansa. Na ce ban sani ba, na daku tun da suka ɗauke ni, a ɗaure nake, sai ranar da suka shaƙe mini wuya da cable na zata mutuwa ma nayi wallahi"

Viper ya ce "Muhsin, ka yi haƙuri, duk ni ne sila ka yafe mini dan Allah"

Walid ya ce "A'a rashin jinmu ne dai sila"

Likitoci sun yi mamakin ganin Walid a zaune yana ta magana.

Sai dai aka yi masa wanka, aka saka masa kaya, ya ci abinci, aka je aka yi masa hoto, aka tarar da karaya a hannunsa na dama.

Da yamma Viper yaje har gida, yake gaya wa Abbu yanayin jikin Walid, suka yi ta murna, Shahida tana son ta ce masa tana son sake zuwa duba Walid, amma ta kasa.
Babban abin da ya tsaye mata, bai wuce jin yadda yake bawa Abbu labari cewa Walid ba shi da uwa ba shi da uba, ba wa ba ƙani, shikaɗai yake gararambarsa, dangin iyayensa ba masu zuciya bane ba, duk ba su da ƙarfi, amma babu wanda ya damu da shi a cikin su.

Lokacin da Viper ya yi wa Shahida tayin auren Walid, ita dai ba ta ji tana son shi ko akasin haka ba, amma abin da Viper yake gaya wa Abbu, na cewar maraya ne gaba da baya, sai ta ji wani irin matsanancin tausayinsa, ya cika mata zuciya. Ta ji zata iya kowace irin sadaukarwa, domin rayuwa da shi.
Sai dai ta sha mamaki jin cewa wai har ya farfaɗo ya tashi yayi magana, dan lokacin da ta je, baya cikin hayyacinsa.

A cikin daren ranar, aka yi wa Walid ɗori a hannu, wajen ƙarfe biyu aka fito da shi, liti ya ce Walid sai ya matsa masa saman gadonsa sun yi squating, tun da shi ne zai kwana da shi, kar yaje yana bacci a zo a sake sace shi bai sani ba.
Abin ka da an kwana biyu babu bacci, yana hawa gadon, sai bacci, Walid kuwa zugi ya hana shi bacci, tun bayan da alluran da aka yi masa suka sake shi.

Da Viper ya zo ya tarar da su, fizgo liti ya so yi daga kan gadon, amma Walid ya hana shi.

Duk wata sangarta da rashin mutunci, idan suna tare liti ya iya ta, amma idan aka fita fagen rashin mutunci na 'yan daba, babu wasa.

Viper ya ce "Shahida na gaisheka, ta ce ayi maka sannu"

Kawai yayi murmushi yana kawar da kansa gefe.

"Au ba zaka ce kana amsawa ba? Aishikenan. Ni dai ina ta sake yi wa Allah godiya, da Allah sa ka farfaɗo, da ka mutu ba zan yafe wa kaina ba, kuma da tarayyar mu, ba ta da wani amfani, Allah ya ƙara tsare mini ku, ya baka lafiya".

Walid ya ce "Tarayyar mu tayi mini rana ni, Viper nifa abin da ka yi mini, ban ga wani abu da zai sameka na ja da baya na barka, babu shi. Ka yi mini da aljihunka da jikinka, da lafiyarka babu wanda baka wahalata mini....

"Ka daina wannan maganganun, bau ne past ya riga ya wuce, kuma ni mahaifiyarka tawa ce, a haka na ɗauki abin"

Yayi murmushi ya ce "Mai zamani, wanda zai tsaya maka, a lokacin da baka da komai, ka ke neman taimako, ba tare da tsangwama ko tunanin samun wani abu daga gareka ba, baka da babban masoyin da ya wuce shi, shiyasa da kai da mai gida dodo, ba zan gushe ba ina yi muku fatan alkhairi, da roƙa mana gafarar Allah"

Viper ya ce "Nima hakan take ai, a duniya yanzu bani da tamkarku, da kai da wannan garujen" yayi maganar yana nuna liti.

Walid ya kalli liti yana dariya.

"Ya fi ni shiga tashin hankalin rashin ganinka, baya bacci, baya iya cin abinci wai ina zai saka kansa, babu kai ɗan mama" dariya suka yi tare, liti kuwa bai san suna yi ba.

****
Ƙaton ɗaki ne babba sosai, ɗauke da computers, da wasu na'urori, Viper yana zaune a kan computer da shi da wasu a cikin wurin.

Wani video ya kunna, aka saita a jikin majigi, Videon babu murya, amma Imdabo ne a ciki, yayi wasu maganganu, P.A yana ja da baya, kawak ya harbe shi sau uku da bindiga.

Viper, mutumin nan yaƙarsa sai da techniques, ba za su taɓa bari a hukunta shi a cikin ƙasar nan ba, ya aka yi ka samu Videon?.

"Eh kamar yadda na gaya maka da farko ne, P.A ɗin sa ne ya samo mini wasu informations ɗin a kansa, saboda a zaman kotu ya ɗauka za a ambaci sunansa, yayi hakan da a wanke shi.
Lokacin da Indabo ya buƙaci ganinsa, na bashi cameran, na ce ya saka a gaban rigarsa, zan din ga ganin komai, ni kaina ban yi zaton zai kashe shi ba".

Mutumin ya dafa kafaɗar Viper ya ce "Ka kwantar da hankalinka, na san yadda ka ke ji a zuciyarka a kan mutumin nan, kuma na san legally ba zasu hukunta shi ba, tun da yanzu ayi shiru da maganar tuhumar da ake yi masa. But you have my support hundred person, either legally or illegally sai mun ɗauki mataki a kansa. Saboda ba shi da amfani a cikin al'umma ko kaɗan, da kunya ace irin wannan ne suke mulkar al'umma, amma ba wani abu in sha Allah"

Cikin damuwa Viper ya ce "Sir na baku recording na wayar da muka yi da shi, yarinyar da zan aura, tana cikin hatsari sosai da sosai, ban san me zai iya yi mata ba, ba zan iya jurewa ba idan ya taɓa ta, ga aikinta da ta sha wahala a kai ya salwanta"

"Bai salwanta ba Viper, kuma ina baka tabbacin babu abin da zai sameta, babu kuma abin da zai samu wani naka, kar ka damu" Viper ya jinjina kai yana jin ƙwarin gwiwa.

Asibiti ya koma wurin Walid, ya tarar da Shahida, ta yayyanka masa ayaba a kan plate, ta ajiye masa yana ɗauka da hannun hagu yana ci, yana ganin Viper ya zabura, kamar wanda yake aikata rashin gaskiya, sai da Viper ya so yayi dariya, amma ya maze.

A haka Nabila ta zo ta tarar da su, tayi masa sannu, Walid yayi ta yi mata godiyar suna ɗawainiya da shi.

Nabila ta ce "Vi ai su suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login